PAGE 38

102 6 0
                                    

EMAAN.....PAGE 38

  "Acikin ƙiftawar ido da buɗewa,abubuwa da yawa suna faruwa by chance,alokacin da bakayi xato da tsammani ba,tunda we're on a course that we could have never planned,into a future we never imagined. Where will it take us? Itace tambayar da xakayi ma kanka,and That's the journey of our lives,our search for the light. But sometimes, finding the light means you must pass through the deepest darkness"...asanyaye Eman ta lumshe idanu tareda sauke ajiyar xuciya tana tunanin kalaman da Kausar ta faɗa mata,kalaman dasuka tsaya mata arai suka hana xuciyarta sukuni,kalaman da kamar dan ita akayi su ,ƙaramin hawaye ne ya gangaro mata ahankali yana sauka akan cheeks ɗinta,tayi saurin gogewa tana tuna alƙawarin datayi ma Fauxa kafin tafiyar Fauxa US wurin Sadeeq,haƙiƙa labarin rayuwa is quicker than the blink of an eye,sati ukun da suka wuce ranaku ne da suka kafa babban gurbi acikin rayuwar su,musamman Rayuwar Sadeeq data ta'allaka akan daƙiƙa hudu xuwa shidda,kamar yadda dr Harry yace "the next 4-6 minutes lokacine daxaiyi determining rayuwa ko kuma mutuwar shi,this short time is very important for him,pray to the Almighty Alhaji Kabeer"daga haka aka fitar dashi waje har lokacin yana durƙushe aƙasa,wannan kalaman ne suka sanya hawaye xubo mishi,yayi cupping fuskar shi da tafin hannu yana fashewa da kuka mai tsanani da ciwo,axuciya yake ma Sadeeq adduar samun lafiya even though jikinshi na bashi Sadeeq will not make it,this feeling is the most painful feeling arayuwar shi,yana ji yana ganin ɗanshi akan siraɗin  rayuwa da mutuwa amma baxai iya yin komai akai ba,alokacin ya sake girgixa da lamarin ubangiji,jikinshi yayi sanyi saboda rayuwar duniya ba komai bace illa enjoyment of the delusion,sannan rai ba abakin komai yake ba idan lokacin fitar shi yaxo,runtse ido yayi yana tuno ayoyin Allah gameda mutuwa,tsoron Allah na sake shigar shi,with a throbbing heart Alhaji kabeer ke jiran lokaci,minti ɗaya xuwa huɗu ya bude idanunshi yana kallon ICU din,wani hawaye mai xafi ya zubo mishi,bakin shi na rawa yace"Allah ya jikanka Sadeeq "yafada yana rufe idanu hawaye masu xafi suna sauko mishi,haƙiƙa baxaka san menene baƙin ciki ba har sai ka rasa someone close to you,bango abin jinginar ka kuma tudun ka na dafawa,awannan lokacin ne xaka san ma'anar pain wanda Allah ne kaɗai ke sanya rislama axuciya na yin takwakkali da ƙaddara....Alwala Alhaji Kabeer yayi ya tada Sallah,yakasa yadda da abubuwan da xuciyar shi ke raya mishi,duk da ba acikin nutsuwa yakeyin Sallar ba,yana yi ne domin samun nutsuwar xuciya,hakan bai hana hawaye xarya akan cheeks dinshi ba,sallah yayi for 30minutes sannan ya idar yana kallon Dr Harry wanda fitowar shi kenan daga ICU jikinshi  asanyaye yake cire hand gloves yana kallon Alhaji kabeer wanda xuciyar shi ke tsananin bugawa kamar xata faso daga kirjinshi,ya runtse idanu sanda Dr Harry yace"I'm sorry....we've tried our best "daga haka bai sake cewa komai ba ya shiga office dinshi...alhaji kabeer ya ɗaga hannu sama cikin karyewar xuciya mai cikeda rauni yace"ya Allah kasa hakan shi ne mafi alheri acikin rayuwar Sadeeq da tamu baki daya"ya sauke hannayenshi ƙasa dauriya na shigar shi wacce bai taɓa jin irinta ba,Allahu sami'un dua ne...Alokacin da kowa ya cire rai da Sadeeq,alokacin da machines and computers suka tabbatar da Sadeeq ya mutu,adaidai wannan lokacin Allah maɗaukakin Sarki,gagara misali ya nuna ikon shi na rayawa da kuma amsar ruhi alokacin dayaso,ya tabbatar da mutuwa alokacin bata cikin ƙaddarar Sadeeq,saide unfortunately cikin Coma ya shiga bai san inda kanshi yake ba na tsahon kwana ashirin da daya xuwa yau.......Hausawa sunyi gaskiya dasuka ce idan xaka gina ramin mugunta ka ginashi daidai dakai,sannan sharri ɗan aike ne xai je ya dawo maka harda tsaraba,Jikin hajiya Zainab na rawa take karanta letter da Aliyu ya ajiye wacce sai bayan sati uku da tafiyar shi suka gani,hawaye masu xafi na zubo mata"Dear Mommy,bansan miye tsakaninki da Eman ba dakika tsaneta fiyeda xato da tsammani,koma dai menene I don't want to know,kin hana ni aurenta akaron farko na haƙura duk da cewa ina tsananin ƙaunarta,saboda na miki biyayyah na hakura da aurenta kamar yadda kike so,akaro na biyu na sake amincewa da abinda kika zo min dashi saboda nasan ke mahaifiyata ce babu wanda zai so ni fiyeda ke,I accepted your request akaro na biyu sanda kikace xakimin aure,tundaga lokacin na shiga cikin damuwa mai tsanani wacce baxata misaltu ba amma na hakura just to make you happy,awannan gaɓar nake baki hakuri domin baxan iya miki biyayyah ba akaro na uku,bazan iya xama da afiya ba amatsayin matata,saboda yin hakan xalunci ne,cin amana ne,kuma yaudara ne,xuwa yanzu na tabbatar farin cikina ne bakyaso shiyasa kike min duk abinda xai tayar da hankalina yasa ni cikin damuwa mara misaltuwa,I still love eman,soyayyar da baxata gushe ba har sai ranar da Allah ya dauki raina,baxan iya ganinta cikin damuwa ba xuciyata cannot resist that,sannan bana fatan na kasance araye da har zan sanyata cikin bakin ciki da karan kaina,I can't do that mommy,I won't do that I promise you,I'm sorry ban miki sallama ba amma nasan lokacin daxaki ga wannan letter din na dade da barin kasar nan,xanyi tafiyar da babu dawowa acikinta,ko kinyi trying numbers dina you can't reach me saboda nayi destroying dinsu,ina fatan xaki yafe min abubuwan dana miki sannan kiyi min fatan nasara acikin sauran shekarun dasuka rage min aduniya,you won't hear from me anymore Mommy,amma kisani I love you so much,but you left me with no option,wannnan  kadai ce hanyar da yakamata nabi domin gara na mutu akan na ci amanar Eman"kuka Sosai hajiya Zainab ta fashe dashi mara misaltuwa,afiya na gefe tana matsar ƙwalla,gabanta ne yayi mummunan faduwa tacigaba da karanta second paragraph of the letter,"to my Abba,in shaa Allah I'll continue making you proud,I love you so much sannan inason ka yafe min abubuwan dana maka,to my siblings kuna raina I love you all so much....and to the wife na sake ki saki ɗaya..na sakeki saki biyu..na sakeki saki uku".daga nan rubutun dake cikin wasikar ya ƙare,hajiya Zainab ta runtse idanu tana fashewa da kuka mai tsanani,ta cuci kanta ta cuci ɗanta....It all went by in the blink of an eye,Eman ta miƙe jiki asanyaye ta buɗe press sannan ta ciro wata white gown with multicoloured flowers data tsaya mata daidai ankle,white half-cover heel tasa sannan ta daura white veil,graduation gown tasa tana kallon kanta ta mirror,looking at herself for the first time bayan lokaci mai tsaho,tana mamakin what she went through wanda har yanxu suke damun xuciyarta,wayarta kawai ta rike tafita xuwa parlor,Umma na xaune ita da Anty habiba sunyi gayu Sosai musamman Umma data fi xama classy even though itace gaba da anty habiba a shekaru,pictures anty habiba ta musu masu kyau,can dai takalli Eman tace"smile mana,yau fa ranar farin ciki ce"ƙaramin murmushi Eman tayi wanda ta manta ranar datayi irin shi acikin rayuwarta me ƙunshe da baƙin ciki,Abba ne yashigo parlorn yana cewa"Fatima ku muke jira"sannan ya kalli Eman bayan fitar su yace"congratulations daughter,double congratulations to you for reaching this milestone,Allah ubangiji ya albarkaci karatunki "hawaye na xubo mata tace"Amin abba"yace"wipe your tears away Eman,yau ranar farin ciki ce,yanxu muka gama waya da alameen"yayi shiru yana kallonta sannan yacigaba da cewa"kunyi waya ai I don't have to tell you "yana kaiwa nan ya fita daga parlorn,Eman ta bi bayanshi gabanta yana faduwa domin harga Allah ta manta dawani alameen acikin duniyarta balle ta tuna da aurenshi dake kanta.Ayau asabar Eman ta kammala bachelor of pharmacy with first class honours,ta samu multiple awards da cash gifts daga wurin mutane daban-daban,ranace da baxata taɓa mantawa ba acikin tarihin rayuwarta,misalin karfe hudu na yamma suka dawo gida cikeda gajiya,haka kawai gaban hajiya kwaise keta faduwa tun lokacin da Abba yace akwai meeting din daxai gabatar anjima da dare,ta rasa peace of mind sai tunane-tunane takeyi gabanta na tsananta faduwa.ta kalli Eman dake kwance asaman kujera ,ta daɗe tana kallon Eman din sannan ta fita daga part din tana breathing heavily,part din Mummy ta wuce xata duba jikin Afiya,mummy na xaune ta xabga uban tagumi damuwa tayi mata yawa,duk ta birkice ta fita hayyacinta kamar ba ita ba,...hajiya kwaise tace"ya jikin afiya?"mummy tace "da sauki alhamdulillah,ni ban taba ganin irin wannan cikin ba"kallonta kawai hajiya kwaise tayi batace komai ba domin tagane inda mummy ta dosa tun ba yau ba,kawai dai shi abinda bai shafeka ba dadin kallo gareshi shiyasa har lokacin itama ta xuba musu ido.can tace"Kinsan cikin fari da tsirfa kala-kala,haka fauxa tayi lokacin Anum"shiru mummy tayi saboda most of the time xaka sameta absentminded,ko kuma kuna cikin magana ta maka shiru saika sake maimata wa,hajiya kwaise tace"ya Aliyun fa?"saurin juyowa mummy tayi gabanta na faduwa,ko sunan Aliyu bata son jin alokacin saboda tsanar datake mishi bata wasa bace,ya cuceta ya gama da rayuwarta tunda ya saki yarta a day after their wedding,gashi ynxu ya bar ta da kunyar jama'a har ynzu ta kasa fadawa kowa maganar sakin,hatta Abba baida masaniya akai,tace"kinsan harkokinsu sai ahankali,yau suna can meeting gobe suna can,amma dai ya kusa dawowa ta tattara ta koma gidanta kafin mahassada suyi tunanin wani abun ne yafaru "murmushi hajiya kwaise tayi tace"aikuwa dai,tunda yanxu andaina kiwon dabba kiwon mutum akeyi,kai kana harkar gabanka wani na can ya sa maka ido"kwafa Mummy tayi tace"Allah ya kyauta dai,ya jikin Sadeeq kuwa?"nan da nan fuskar hajiya kwaise ta sauya,tace"da sauki xa'ace "magani mummy tasha tana sauke ajiyar xuciya saboda yadda kanta ke tsananin ciwo mara misaltuwa,hajiya kwaise ta kalli gefen da Afiya ke kwance hawaye suna xubo mata tace"me kikeson ci?"cikin shesshekar kuka afiya tace"bakomai"hajiya kwaise tace"Kinsan fa baxaki xauna da yunwa ba,ki fadamin me kikeson ci sai saliha ta dafa miki"ganin Afiya batada niyyar magana yasa mummy tace"xan ma salihar magana idan xataci"da toh hajiya kwaise ta amsa sannan ta koma part dinta thinking about so many things,can ta jawo wayarta ta kira Fauxa lokacin tana mayo clinic agefen Sadeeq kamar kullum tana aikin kuka,seeing sadeeq acikin halin dayake ciki yana karya mata xuciya,wayarta dake cikin jaka ce tafara ring,ta duba taga mami ce,sai  tasamu kanta da kasa picking saboda tayi mata alkawarin baxata sake kuka ba,lumshe idanu tayi tana tunanin rayuwar duniya wacce a mintuna kadan rayuwarsu ta tarwatse,within few minutes sadeeq dinta kuma gwarxon mijinta wanda da wahala kaga yayi ciwo amma yanxu more than 3 weeks bai San inda kanshi yake ba,wannan lamarin is traumatising sannan ixina ne agaresu da sauran mutane baki daya,domin a second daya Allah zai iya canza maka rayuwa xuwa sigar da baka taba xato da tsammani ba,goge hawayen tayi tana shafa gefen fuskarshi wacce tayi fari fat,yayi wani irin haske ga idanunshi a lumshe kamar me bacci,numfashi kawai yake fitar wa amma ko lifting eyelashes dinshi bayayi,hannunshi wanda ya kumbura saboda saka cannula tariqe tana murxawa ahankali,iya hannun kawai idan ka kalla ya isa yasa ka xubar mishi da hawayen tausayi,ahankali ta dora hannun akan cikinta sabbin hawaye na xubo mata,kullum haka takeyi for more than a week, saide ta zauna tayi kuka sannan ta dora hannunshi akan cikinta,few days kamar yau ne take mishi magana even though tasan bajinta yakeyi ba,tace"you promised to be by my side Sadeeq,for better and for worse,then why are you still sleeping,ka tashi dan Allah yaya sadeeq,akwai abubuwan danake so nafada maka,nayi kewarka fiyeda tunani,our kids missed you so much,your family,my family are all waiting for your recovery,Dan Allah ka bude idonka just for once and look at me,sau daya kawai yaya Sadeeq....I just want you to look me in the eyes,I miss everything about us,pls don't punish me anymore...."tana kuka me tsuma xuciyar me saurare take fadin hakan,hajiyar Sadeeq ce ta rungumeta tana lallashi,"kiyi hakuri fauxa,in shaa Allah sadeeq xai samu lafiya"tafada hakan tana goge hawayen daya xubo mata.alameen na xaune a wani hadaddan office yana juya kujera from right to left hannunshi daya na kan sajensa yana shafawa ahankali,saurin mikewa xaune yayi bayan sun gaisa da Abba yana digesting maganar Abba wacce taxo mishi a baxata domin ya manta da wata Eman balle aurenta dake kanshi,gaban shine ya yi tsananin faduwa sanda Abba yace"anjima zan fada musu maganar Aurenku in shaa Allah,very soon xatayi joining dinka shiyasa nace bari nayi updating dinka on time,kasan dai baxaka ajiye matarka a apartment din hotel ba ko?"wata warm breath ya fesar gumi na tsastsafo mishi yace"ehh Abba"Abba yace"ban gane Ehh ba,what are your plans?"ajiyar xuciya alameen ya sauke xuciyar shi na kuna yace"akwai gida"iya kalamar da ya iya fada kenan saboda tsananin bakin ciki da takaici,yana tunanin yadda xaiyi rayuwa da Eman yarinyar daya tsana fiyeda misali,wacce baya son gani ko kadan balle magana ta hadashi da ita,Abba really caught him unaware domin ya manta da komai saide idan sunyi waya da fauxa ne yake tunawa da Yarinyar,Abba yace "ok,I'll inform you ranar daxata zo if she's done prepping,lefenta kuma naba aunt dinta habiba ta hada kasan sana'arta kenan,ban ma fada mata na Eman bane"alameen da xuciyar shi ke tafarfasa yace"ok Abba,I'll get back to you later,xan shiga meeting ne"daga haka ya katse wayar yana sakin siririn tsaki wanda yake fitowa tareda shahararriyar tsanar Eman wacce ke yawo acikin jikinshi,gefe daya damuwar da Hajiya kwaise xata shiga ne ke daga mishi hankali,yasan xata tayar da hankalinta Sosai,gashi bashida halin komawa nigeria he'd have went back kodan ya lallashi mami even though yasan ba lallai ta saurare shi ba amma hakan xaifi xuwar mata da sauki akan yanxu da bata ganinshi akusa da ita,kanshi ne ya cushe Sosai ya rasa tunanin daxaiyi alokacin,wata xuciyar tace ya kira Abba yayi stopping dinshi not to tell them about it,wata kuma tace kafara fada mata dakanka kafin Abban ya fada mata,runtse idanu yayi kanshi na daukan charge gabadaya jikinshi yayi sanyi,aduniya idan akwai abinda ya tsana ita ce Eman sai kuma hawayen Hajiya kwaise,ya tsani xubarsu adadin tsanar dayake ma Eman,tallafe kanshi yayi yana furxar da xaxxafar iska,ya yi dialling wayar hajiya kwaise lokacin wayar wasn't close to her,cikin mutuwar jiki ya kife tashi wayar yana tunanin yadda xai bullowa maminshi domin ta fahimceshi.



Zaynabyusuf✍🏼

EMAANWhere stories live. Discover now