PAGE 68

183 8 0
                                    

EMAAN....PAGE 68

Written by Zaynabyusuf✍🏼

Wayarshi dake ring ce yasa alameen bud'e lumsassun idanunshi yana kallon screen din,ganin nurain ne ke kira yasa shi saurin yin answering call din with mixed emotions,yana shafa beard dinshi yake sauraran abinda nurain ke fada mishi,after like five minutes yayi ending call din yashiga WhatsApp kamar yadda nurain yace yayi,hawaye ne me xafi suka xubo mishi lokacin dayaga asalin pictures din wanda aka dora fuskar emaan perfectly akai,babu yadda xa'ayi kace ba emaan bace,saiga asalin pictures din da fuskar wata yarinya wacce a kallo d'aya xaka san ba musulma bace,kife wayar yyi xuciyr shi na k'una,yana tunanin waye ya aikata ma emaan haka for what reason?and for what gain??mikewa yayi jiki asanyaye ya shiga part din umma,ya kalli emaan dake kwance asaman kujera and his heart starts to ponder,just imagining what will come from her lips,saboda irin kallon data ke mishi kamar tana son fahimtar wani abu daga gareshi ne,samun kanshi yayi da smiling ya xauna agefenta yana kallonta closely full of love for her,slowly ya rike soft hands dinta gently,yana jin sabon kaunarta na sake shigar shi,yana ma emaan son da bakinshi baxai iya furtawa ba,yana mata son da idanunshi baxasu iya bayyana asalin meke faruwa acikin xuciyr shi ba,he just love her beyond measure and beyond everything,and he'll continue to do so for the rest of his days,kullum tana bashi reasons din sake kaunar ta batareda ita kanta ta sani ba,murya can kasa yace"I'm so so sorry emaan,you went through alot,you struggled so much arayuwa amma ina me farin cikin sanar dake cewa daga yau xaki fara sabuwar rayuwa,me cikeda farin ciki wacce babu guilt acikinta,domin Allah ya wanke ki daga k'ullin sharrin da aka miki,ya bayyana gaskiya alokacin da kika cire rai da hakan,shiyasa ba'a son mutum ya rika saurin karaya da lamarin rayuwa,a addininmu ma ba'ason mutum yayi loosing hope,hakika duk wani tsanani yana tare da sauki,kuma duk nisan jifa k'asa yake saukowa,duk masu miki bakin ciki da hassada suna aibanta ki xasu boye fuskokinsu ne da palms dinsu saboda kunyah,domin Allah ya wanke ki emaan"ya karashe maganar tareda unlocking wayar shi,asalin pictures dinda akayi using ya nuna mata,emaan kawai ta saki baki tana kallon ikon Allah,hawayen farin ciki suka zubo mata,she has been waiting for this day for so long,akullum burinta shine Allah ya bayyana gaskiya,sai gashi alameen worked tirelessly to place a huge smile on her face,ya xamto mata shoulder wacce xatayi leaning for the rest of her life,ya nuna shi din me son ganin farin cikinta ne da son ganin tayi moving on finally after what she went through,tana dariya tana kuka ta ma rasa kalaman daxatayi amfani dasu wurin yi mishi godiya,samun kanta tayi da hugging dinshi tightly sabbin hawaye suna wanke mata fuska,alameen tamkar statue yaxama saboda shock dinda ya shiga bana wasa bane,he can't believe wai yau emaan ce tai hugging dinshi saboda kalamai sun gushe mata,ta rasa words din da suka dace ta fada mishi,shikuma abangaren shi he desperately wants to know what's in her mind,kamar tasan tunanin dayakeyi tace"thank you so much,thank you for everything "ta fada hakan beneath her breath,lumshe idanunshi yayi saboda tun shekaranjiya dasuka dawo take wasan buya dashi,taki bari su hadu balle ta mishi magana yasamu nutsuwa da kwanciyar hankali,yau ma beyi tunanin xai ganta a parlon ba saboda acikin kwana biyun emaan shigewa take yi cikin daki,umma har tagaji da mata fad'a even though ta lura emaan na cikin damuwa,shiyasa yau din takira anty habiba domin su tattauna.yana shafa gefen fuskar ta yace"anything for you my lovely wife,i love you so much "lumshe idanu emaan tayi tana jin saukar kalaman nashi har kasan xuciyar ta,yana kallonta cikeda tsantsar kaunarta yace"i can't wait for the day daxanji kince kina sona emaan...."ya fadi hakan cikin karyewar xuciya,kallonshi tayi irin kallon da bata taba mishi ba,saboda ya xamto kwallon tauraro acikin rayuwarta dayake haske rayuwarta da mafi hasken haske,slowly lips dinta suka fara motsi xatayi magana hajjo da shigowarta parlon kenan ta saki salati tana tafa hannu tace"me xan gani da rana tsaka ni hajjo?"ta fada tana rike hab'a tana xaro idanu cikeda mamaki,kallonta sukayi alokaci daya suna murmushi,hasalima alameen mikar da emaan yayi tsaye yace"ni bansan meyasa kike son zama anan ba bayan ga part din mu can cikin sirri da rufin asiri"itadai hajjo da rakiyar idanu ta bisu tana mamakin lamarin alameen,gefe daya kuma tana cikin farin ciki mara fasaltuwa,suna shiga part dinshi yayi pining dinta da bango,murya can kasa yace"kince thank you da baki sauran kuma a aikace..."saurin saukar da idanunta kasa tayi tana jin kunyar kalaman shi,yace"plssssss babe..."pulling her closer yadda Numfashin junan su ke sauka alokaci daya,shigewa jikinshi emaan tayi kamar sabuwar munafuka,tak'i yin abinda yace kuma taki cewa komai,alameen yace"please emaan dina..."yafada yana cirling lips dinta,tana turo baki gaba tace"Toh close your eyes..."zaro idanu alameen yayi sannan ya rufe kamar yadda tace,yayi mamaki sosai lokacin dayaji saukar chilled tender lips dinta asaman cheeks dinshi,baisan lokacin daya bud'e idanu ba yana kallon ta,emaan kuwa saurin kwace kanta tayi tafice daga part din da sauri tana dafe kirji,kunyar abinda tayi ne yasa ta sunkuyar da kai tana kallon kasa cikin rashin sa'a sukaci karo da fauxa,"auchh "emaan tayi karamar kara lokacin da kanta ya bugu da gini,cikeda damuwa fauxa ta riko emaan tana mata sannu,emaan kawai ta saki baki tana kallon fauxa wacce ta rame sosai saide xuwa lokacin tasa dangana acikin ranta da xuciyar ta,even though taci alwashin baxata sake yin aure ba,asanyaye fauxa tace"be careful,kinsan ba ke kadai bace"mamakin fauxa ne ya birne kunyar kalaman da fauxa ta furta awurin emaan,duk da hakan bai kamata yaxama abin mamaki ba sanin wacece fauxa da kuma good heart dinta,kawai ajixanci ne irin na adam amma fauxa har gobe mutuniyar kirki ce wacce duk gidan babu na biyunta a kyawawan halayya....emaan tace"I'm sorry fauxa"murmushi fauxa tayi tace"anjima zan shigo muyi magana,sannan kidaina bani hakuri,wanda yayi laifi shike bada hakuri"cewar fauxa,kallonta kawai emaan keyi tana jin farin ciki yana saukar mata,ayanzu damuwa daya ce acikin xuciyar ta itace auren da alameen xaiyi,ko kadan batayi tunanin yasmeen ba saboda babu abinda tunanin yarinyar xai haifar mata sai bakin ciki da damuwa,ta damu ne akan shi karan kanshi alameen din,shiyasa kwana biyu take distancing kanta dashi saboda yawan haduwar su xaiyi worsening damuwarta ne,umma na tsaye emaan ta rungumeta ta baya tana sakin dariya,umma tace"emaan sakeni mana,"anty habiba tace"yi ahankali karki karasa tsohuwar taki ko kuma kiyi ma alameen illa"wata kunya ce ta rufeta mara fasaltuwa amma ta share tace"umma guess what?"saida umma ta xaunar da ita sannan tace "i can't,tell me"emaan dake murmushi fararen hakoranta suka bayyana ta fadama umma abinda alameen ya nuna mata,hawayen da ke makale a idanun umma ne suka xubo,farin ciki mara misaltuwa yana mamaye mata xuciya,haka anty habiba saida tayi hawayen farin ciki,umma tace"alhamdulillah ya Allah,nagode maka daka nuna min wannan ranar,Allah ya miki Albarka ya kareki daga sharrin makiya da mahassada,Allah ya dawwamar dake acikin farin ciki ya kara dankon soyayyah tsakanin ki da mijinki,Allah ya saukeki lafiya"anty habiba tace"dama tun farko nasan sharri ne,emaan dinmu baxata taba aikata haka ba,sai gashi Allah ya wanke ta daga daurin xato,anyi hakan ne domin a hana aurenta da Aliyu,sai gashi Allah ya bata wanda yafi Aliyu komai da komai,"murmushi sukayi gabadayansu emaan nata dariya abunta kamar ba emaan din damuka sani ba,shigowar mummy cikin parlon ne yasa anty habiba tayi shiru,babu kunyah yanxu mummy ke shigowa part din umma,kuma idan tashigo tana spending like 1-2hours,duk da umma bawani sakewa takeyi da ita ba amma mummy ko ajikinta,emaan ta kalla wacce mood dinta ya canxa gabadaya tace"'yata ya jiki-jiki?"Sosai emaan ke mamaki duk lokacin da mummy takirata da sunan yarta,sai kawai emaan tayi smiling amma bata ce komai ba,kamar kullum yauma dakin umma ta shige abinta,tana shiga kuwa ta tarar wayarta na ring,ganin wanda ke kira yasa ta saki karamin murmushi,yace"ki shirya xamu fita"iya abinda yace kenan ya kashe wayar emaan kuma tafara shiri kamar yadda yafada mata,lafiyayyan wanka tayi sanann ta shirya cikin abaya black color,wayarta kawai ta rike sanann batayi applying komai ba kuma ahakan tayi kyau sosai,har lokacin data fita parlo mummy naxaune sai surutu take,emaan tace"na fita umma"kafin umma tayi magana mummy tace"Toh emaan,Allah ya tsare ya kiyaye"hakan ne yasa umma batace komai ba itakuma emaan ta amsa ciki-ciki,a main parlon taganshi ya shirya cikin dark blue kaftan,for the first time data tsaya tana kallon alameen kenan saboda masifar kyan dayayi,gashi sai smiling yakeyi yana jin kamar yayi solving dukkanin problems dinshi arayuwa,dama already ya fadama Abba komai inda Abba yace zuwa dare xaiyi addressing issue din saboda babu tantama daga cikin gidan aka mata haka....Slowly alameen ke driving hannun shi daya na sakale acikin na emaan,wakar Michael Jackson ta you're not alone ne ke tashi acikin motar,Alameen Na bin wakar ahankali emaan kuma na kallonshi tana murmushi,sunyi tafiyar like 20mins wayar alameen tafara ring,tun kafin ya duba me kiran already emaan ta gani,dan haka ta fuxge hannunta kana ta mayar da kanta saman titi,hannunta ya sake rikewa ta juyo xata sake kwacewa ya girgixa mata kai alamar a'a,samun kanta tayi da fasa yin hakan amma ita kadai tasan abinda ke yawo acikin xuciyrta,cikin kosawa tace"wai ina xamu ne?"murmushi alameen yayi yace"calm down madam...."tace"madam?saikace wata katuwa?"dariya maganar ta bashi yace"ay kin kusa xama katuwar"nan da nan ta hade rai,kafin yayi magana tace"kai kuma oga ko?"dariya sosai alameen yayi yace"oga kuma?"ya fada yana harararta,dariya sosai emaan tayi ganin yadda alameen keyi shi adole bai yadda ba hararar emaan yakeyi,baiyi xato ba tafara mishi video tana mishi dariyar mugunta,ya lura emaan akwai k'eta dan haka yacigaba da mata shirme tanata video tana dariya abinta,Sosai dariyar ta ke sashi cikin farin ciki mara fasaltuwa,dan haka yayi pecking soft hands dinta yace"i love you baby girl,always and forever ".wani private resort ya kaisu wanda ya hadu fiyeda misali,wurin kamar ba'a kano yake ba,hakan ne yasa emaan ta saki baki tana kallon wajen wanda babu karya ya tafi da xuciyarta,kallonta alameen yayi bayan yayi parking,ya sakar mata cute smile sannan ya bude mata motar kana ya rike hannunta suka shiga ciki,sakin baki emaan tayi ganin yadda akayi decorating wurin with lush and expensive decor,ga table of two dinsu agefe,alameen ne ya ja mata kujera ta xauna tana sake kallon wajen,alameen yace"how much do you like the surprise?"murmushi emaan tayi tace"I love it"murmushi yayi ya bud'e wani black box dake ajiye agefe,ya ciro hadaddiyar diamond necklace yana kallon emaan wacce ta saki baki da hanci tana kallon ikon Allah,dakanshi ya sa mata sarkar wacce ta mata bala'in kyau,new collection ne from bozdiamonds brand,hawayen dake makale a idanunta ne suka xubo suna bin cheeks dinta,bata taba tunanin rayuwarta xata gyaru haka ba,sai ynxu ta tabbatar da every disappointment is a blessing,harshen shi yayi amfani wurin goge mata hawayen romantically yace"my emaan from today henceforth bana son ki sake tuno da past dinki,mu manta da komai muyi focusing akan future dinmu which is very bright kamar hasken taurari,i promise I'll always be there for you,through every step in life,for better and for worse,I'll love you for the rest of my life,thank you for giving me the very best of gifts,thank you for changing me,thank you for everything emaan,i appreciate everything no matter how little "yana murxa hannunta yacigaba da cewa"always count on me,inason ki dauke ni tamkar aboki wanda xaki iya fada ma problems dinki batareda wani shamaki ba, I want you to trust me emaan,kisa aranki cewar baxan taba yin wani abu ba daxai bata miki rai intentionally,idan ma hakan tafaru kisa mistake din abisa ajixanci na dan adam sannan ki fadamin muyi discussing na baki hakuri,in shaa Allah xan xamar miki miji daya tamkar da dubu,irin mijin da kowacce mace keda burin samu,duk wani abu dana mallaka in this life naki ne,dan haka kada kiji shakkar tab'a komai nawa domin duk abinda na mallaka naki ne".ya karashe maganar yana kissing hannunta,sosai emaan ke zubar da hawayen farin ciki,saboda samun namiji kamar alameen abu ne mai matukar wahala...owning lips dinta yayi yana kissing dinta slowly yana sliding hands dinshi into every corner of her,for the first time dataji she likes what he's doing kenan,dan xaro idanu tayi lokacin daya saukar da ita kasa ya kwantar da ita awurin still yana owning lips nata,alameen is very romantic,yasan takan soyayyah fiyeda tunanin emaan,shiyasa alokuta mabanbanta yake kunce mata knots din kanta,kamar kullum yau ma gabadaya ta susuce bata san a duniyar datake ba,abu daya tasani shine she savour every bit of abinda yake mata,good 30minutes yayi yana gwada mata yadda take acikin xuciyar shi sannan ya maida ta saman kujera yana kallonta da narkakkun idanunshi,samun kanta tayi da kallon shi itama tana jin wani irin shauki yana fixgarta,romantically yayi feeding dinta wanda hakan yasa taci abincin sosai,shima daga baya yace dole tai feeding dinshi shima,tana tura baki gaba tayi wanda hakan yasake narke mishi xuciya,shifa ko motsi emaan tayi bala'in burgeshi takeyi,suna gamawa kiran yasmeen ya sake shigowa wayar shi,sai ya kalli emaan ya kalli wayar yana mamakin yasmeen din,saboda sun saba idan sukayi fada shine xaita faman kiranta amma to his biggest surprise yaga itace ke nemenshi,baiyi answering ba hasalima hannun emaan ya riko yana kissing,sai kawai taji hawaye sun cika mata idanu,bata son ya fahimci hakan sai kawai ta kawar da kanta gefe,murmushi yayi saboda ya fahimceta,ayanxu ko motsi emaan tayi yasan me take nufi,baice komai ba illa mikar da ita tsaye yayi hugging dinta tightly,murya can kasa yace"kin iya rawa?"dariya question dinshi ya bata,sai kawai ta girgiza mishi kai alamar a'a,yace"ban yarda ba"tana pouting bakinta tace"dagaske"yace"yimin toh"kunya sosai ya bata dan haka tace"a'a"yace"pleaseeeee"itama tace mishi"pleaseee a'a"dariya yayi ya rungumeta yace"shikenan "yayi sounding irin baiji dadi dinnan ba,kallonshi emaan tayi for few seconds tace"saide muyi tare"yace"sure baby"ba musu tafara mishi rawar yanata dariya sede ga mamakinta taga ashe alameen ya iya rawa,yace"amma fa ban tab'a yi agaban kowa ba sai ke"samun kanta tayi da jin dadin hakan tace"awwwn"yace "yes my love"daga haka ya dauketa kamar baby xuwa daki wanda akayi romantic decoration mai daukar hankali,anan alameen yasake nuna ma emaan she owns him kuma ta yarda da hakan 100%.

EMAANWhere stories live. Discover now