PAGE 21

116 5 0
                                    

EMAN...PAGE 21

Tunda suka fara jin tafiyar mutum gaban eman ke tsananin faduwa,tayi hanxarin mikewa tsaye,cikin rashin kuxari ta dafa hannun kujera tana jin kafafuwanta baxasu iya cigaba da daukar ta ba,ido ta xaro gumi suna karyo mata jin ta kasa motsa kafarta,tayi hanxarin kallon Sadeeq wanda har lokacin yake kallon staircase,gabadaya ya maida hankalinshi da nutsuwar shi awurin,Can yayi jarumtar mikewa ya karasa gaban benen xuciyar shi is beating faster than normal,saboda ba haka ya tsara ba,baya son tun yanxu fauxa tasan halin da ake ciki,ajiyar xuciya ya sauke jin ankoma an rufe kofa,ya furxar da wata xaxxafar iska daga bakin shi sannan ya juya yana kallon eman wacce ke tsorace kamar xa'ace ke! Ta falla da gudu,jikinta sai rawa yakeyi hakan yasa xuciyar shi ta narke da tausayinta,she looks so afraid at the moment,asanyaye yayi closing gap din dake tsakanin su yace"sit"yana yi mata wani narkakkken kallo wanda yasanyata cikin naxari,xama tayi xuciyarta Na dukan tara-tara,idanunta masu maiko wanda suka cika da ruwan hawaye ta dago tana kallonshi sanda ya furta,"Ina jinki,wani sako xaki bayar abashi?ko kina ganin bai cancanci hakan ba?"lumshe idanu tayi for 3 seconds sannan ta bud'e tayi rolling dinsu alamar tunani,zuciyar Sadeeq ce tayi wani irin tsalle kamar xata faso daga kirjinsa saboda shaukin daya tsinci kanshi aciki,ahankali tace"meyasa baxamu bar maganar ba sai gobe ?ina ganin hakan xai fi kaga sai muji ta bakin ya fauxa ma"takarasa maganar tana kallon fuskarshi wacce ta canxa yanayi,murya a sark'e yace"yau yake son jin sakon naki"ahankali tace"kace mishi nagode,amma xuciyata ta dade da sanya mukulli ta rufe kofar shigar kowani mutum cikinta,xuciyar eman ta tafi hutun lokaci mai tsaho,idan da rabo kuma Allah ya qadarta sai kaga komai ya daidaita,amma ayanxu I'm still in my healing process ".ajiyar xuciya ya sauke sannan yace"nima na dade ina tunanin hakan,nayi tunani Sosai  kafin naxo miki da maganar shi,at this moment xuciyar shi is very weak,saboda kaunar ki yake bata wasa ba,kuma yayi kokarin baki lokaci amma hakurin shi ya kare,so yake ya san matsayin shi acikin xuciyar ki,idan kika amince tamkar kinyi mishi albishir ne da Sabuwar kuma ingantacciyar rayuwa,wacce xai shimfida tareda ke me cikeda eternal happiness and love,he'll be the happiest person ever saboda samunki agareshi babbar riba ce wacce he can trade his life domin ya sameki,kai tsaye nabashi dama domin he's worthy of your love eman,ya cancanci ki sonshi kuma ki kaunace regardless of who he is,yakamata ki tallafi rayuwar shi ki amshi tayin soyayyar shi,idan kuma rabon hakan be kasance ba sai kiyi mishi adduar dacewa alahira domin lokacin shi Na duniya ne yaxo karshe,rashin ki acikin rayuwar shi tamkar kisa ce batareda d'igon jini ba,saboda ke yake numfashi haka nan saboda rashin ki xai daina Numfashi!".
Mamaki ne yasa bakin ta yaki rufuwa,saboda abubuwan dayake fada sun wuce tunanin me Tunani,they're out of proportion,asanyaye tace"but I don't think this is love yaya Sadeeq, this is obsession which isn't healthy,he needs therapy,baka tunanin yana bukatar taimako?"smiling yayi yace"eman kenan,kinada abin dariya,koda yake ba laifin ki bane,har yanxu bakisan soyayyah ba amma ina me tabbatar miki idan kikayi accepting dinshi it'll be the best decision you'll ever make,saboda soyayyar shi xata bud'e miki idanu sannan ta xurfafa miki tunani,you just need to trust the process,I promise you won't regret having him as your own,your jannah idan Allah yaso".shiru tayi tacigaba da kallonshi tana naxarin wannan son dayake ambata,ita tsoro yake bata ma wanda batasan dalili ba,sai can tace"ok I'll think about it and let you know in due time ".tana gama fadin haka ta mike jiki asanyaye shikuma yabita da kallon kauna har ta kurema ganinshi,he's so in love with eman,wanda yake jin kullum karuwa yake acikin xuciyar shi.
Washegari eman bata koma bacci ba bayan ta idar da sallar asubah,tana xaune akan darduma ta dora kanta asaman gado tanata jujjuya maganganun da yaya Sadeeq yayi mata adaren jiya,ta dade Sosai xaune awurin sannan ta mike ta shiga wanka,cikin doguwar rigar atampa ta shirya sky blue color,tayi daurinta mai kyau sannan tasa earring,ko powder batayi applying ba ta yafa dark blue veil dinta ta riko school bag,tana fitowa shima yafito daga bedroom dinshi sanye da dark blue din yadi,wani masifar kyau tayi mishi kamar xai lashe ta haka ya zuba mata idanu yana kallo,kwana biyu irin kallon dayake mata suna sata acikin waswasi,can tayi karfin halin cewa"good morning "kamar jira yake yace"morning dear"sai yayi saurin sauka sanda yaji maganar fauxa,sai itama ta sauka sede afalo ta xauna tana karanta handout calmly,xuwan ya fauxa ne yasa eman ta dago kanta tareda placing smile asaman fuskarta tace"good morning ya fauxa"amsawa ya fauxa tayi tace"morning dear,test xakuyi?"gyada kai eman tayi tace"ehh wallahi gashi ban wani duba handout din dakyau ba"ya fauxa tace"ke ay basai kin duba ba,I know you and I trust your ability,na tabbatar marking scheme xaki basu"murmushi eman tayi tace "kai ya fauxa,you're exaggerating "tace "bawani,kede yanxu ki ajiye handout din kixo kiyi breakfast "eman tace"Ina axumi yau"ya fauxa tace "ok,ayi mana addua"tunda suka fara hira ya saki baki yana kallon lips din kowacce cikeda burgewa,Shide yana kaunar matan nan guda 2 arayuwa,so yake musu mara fasaltuwa,Anum ce tace"daddy what are you thinking about?"saurin d'auke idanunshi yayi ya dora akan fuskar yarinyar,fauxa ta tsura mishi ido tana naxari sannan tana jiran taji me xaice,shikam besan ma me xaice ma Yarinyar ba,sai kawai ya shafa kanta tareda mikewa yace"I've lots of work a office,eman muje,see you guys later,love ya"yana kammala fadin haka ya sa kai ya fice daga falon,eman ta mike asanyaye tana ma su Anum smiling masu cewa"bye aunt eman"fauxa dai Na xaune batace komai ba har eman din ta fita,driving yake calmly har suka hau babban titi,cikin rashin xato taji yace"you look cute,atampa Na miki kyau amma ke baki son sawa"dan xaro ido tayi tace"how did you know?"shi tambayar ta ma dariya tabashi,lallai har yanzu eman batasan matsayin data kai axuciyar shiba,shifa at this moment yasan alot of her favourites,yace"wear them more often "asanyaye tace"ni suna takura min ne,shiyasa nafison abaya"bai san sanda yace"abaya kuma na bayyana jiki Sosai "saurin d'auke kai tayi daga kallon shi,yacigaba"amma irin wannan kayan suna b'oye figure din mutum,kinga less attention kenan from strangers "itafa mamakin shi takeyi,yadda yake mata magana kai tsaye kwana biyu kamar ba yaya Sadeeq din data sani ba,tana cikin wannan tunanin taji yace"kin gama tunanin?"ta dan saci kallonshi sannan tace "a'a ban ma fara ba"yace"yakamata dai kifara,saboda kin saka xuciyar bawan Allah cikin Gararin rayuwa,jiya ma dakyar yayi bacci sai tunaninki yakeyi"handout dinta take kallo axahiri amma a bad'ini tunanin maganar yaya Sadeeq takeyi,yace" and good luck for your test",tace"thank you "shikuma yacigaba da kallonta freely,saboda yanzu ya daina mata kallon kasa kasa inde su biyu ne,dagewa yakeyi yana kallonta Sosai kuma bai damu ba ko xata fahimci wani abun,shifa yanxu babbar damuwar shi shine feedback dinta,baya tunanin komai inba hakan ba ayanxu.kamar ya fashe da kuka haka yaji sanda suka karasa school din,ya wani marairaice yace"banda magana da maxa "tadan xaro ido tace"dama can banayi "yace"good,take good care of yourself "tace"sure "xata fita yace"one more thing,ki kirani idan kin gama test din"tace"ok"yace"kada ki manta fa,I'll be waiting"Tace"in shaa Allah "tana kaiwa nan ta shige school shikuma ya lumshe idanu,yayi 5 minutes xaune acikin motar sannan ya samu courage din tafiya office,koda yaje office din yana aiki yana tunanin eman,yana hoping test din nata ya mata sauki sannan she's happy with the questions,hope she's lively,haka yariqa random thoughts akanta har wurin karfe daya Na rana,bayan ya idar da sallar axahar ya daga wayar shi yana kallo,sede har lokacin bega call dinta ba,sai ya mayar da wayar kan table sannan ya mike yakoma kan kujera,yana xama wayar tafara ring,wani irin sanyi yaji yana saukar mishi,ya yi saurin dagawa cikeda farin ciki yace"emaaan"yaja sunan wanda hakan yasa ta xama uncomfortable,tace"Naam"yace"kin cika alkawari even though tun daxu nake expecting call din"batace komai ba yacigaba da fadin"how's your test?nasan tayi dadi ko"tace"ehh alhamdulillah "yana shafa beard dinshi yace"kinci abinci?"saida takalli coconut rice din dake gabanta sannan tace"shi xanci sena tuna kace I should call you "yace"Allah sarki,I'm sorry about that,yanxu kici abincinki kinji,I'll call you later"Tana kokarin kashe wayar yace"wait! Ina axumin naki?ko dama can baki dauka ba?ko kuma karyewa ya yi?"ajiyar xuciya ta sauke sannan tace"ehh"tana kallon kausar wacce ta saki baki da hanci tana kallon eman fuskarta d'auke da mamakin abubuwan da yaya Sadeeq keyi akan eman wanda yau tayi alkawarin xata  ma eman magana saboda aganinta yakamata ace eman din ta fahimtci kaunarta dayakeyi kuma tayi acting accordingly yadda yakamata,murya can kasa yace"I get it,kici abincin we'll talk later "yana kaiwa nan takashe wayar tana sipping watermelon mojito,kausar tace"kar kice min baki fahimci wani abu ba gameda yaya Sadeeq dinku"eman tace"kamar me fa"sakin baki kausar tayi tace"but it's obvious mana,abun a bayyane yake,nifa tun ranar dayayi making scene harda marin khaleed nafara suspecting wani abu"kallonta eman tacigaba dayi batareda tace komai ba,kausar ce tacigaba da fadin"ko shi Khaleed yayi tunanin fa saurayin ki ne,dana fada mishi yayanki ne he was so surprised,sai dana fada mishi asalin relationship dinku yafara min rantsuwar cewar yaya Sadeeq is obsessed with you,kuma kema kin sani,sharewa kawai kikeyi duk da bansan dalilin ki ba"eman tayi saurin ajiye drink din daya kusa shak'e mata wuya,ta xaro idanu waje tana kallon kausar domin wannan tunanin be tab'a xuwa ranta ba,bata ce komai ba sai kallon kausar Data cigaba da yi tareda dora naxarinta akan mixanin hankali,ita fa ko xancen takasa nutsuwa tayi saboda girman maganar awurinta.

EMAANWhere stories live. Discover now