PAGE 17

120 5 0
                                    

EMAN 🥀

Page 17

  Kallon picture din tayi sannan takalli yaya Sadeeq wanda ya rungume hannu akirji yana mayar mata da irin nashi kallon wanda yasa taxama uncomfortable,mamaki ne ya hanata magana,saboda takasa digesting abin acikin ranta,what's her picture doing in his office?itace tambayar data kasa baiwa kanta amsa,tsaff yagama karance abubuwan dake xarya acikin ranta,sai ya mayar da hakan kamar ba komai ba,ya xauna yana maida hankalinshi da nustuwar shi ga laptop axahiri,amma abad'ini kallonta yake kasa kasa yana jiran me xata mishi gameda hakan,kallon shi ta sakeyi akaro na babu adadi sannan tace "what's my picture doing here?ina kasamu hoton na?"ta tambaya tana tsare shi da idanunta masu karya masa garkuwar jiki,ahankali ya dago yana kallon fuskarta wacce ke d'auke da mamaki bayyanan ne,ya kalli hoton sannan yace"nima ban saniba,inaga shi yakawo kanshi wurin"mamakin amsar daya bata takeyi,bata gane shiya kawo kanshi wurin ba,ajiyar xuciya ta sauke sannan taxauna still tana kallon shi,yana aikin shi peacefully saide rabin hankalin shi na kanta,bai San meyasa ba inde tana wuri sai ya nemi nutsuwar shi ya rasa,yanxu haka bawani aiki dayakeyi gabadaya hankalinshi na wurinta,yadda ta xauna with confusion tana kallon sa shine damuwar shi,duk da wani bangaren Na xuciyar shi yaji dadin hakan,koba komai yau tayi mishi kallon dayake muradi daga gareta,shifa idan son eman xunubi ne baxai tab'a tuba ba,he loves her senselessly.Shi kanshi yana mamakin yadda sonta ya mamaye mishi xuciya,tashiga ranshi da xuciyar shi sosai ta yadda baxai iya tunani sau biyu batareda eman ta fado mishi arai ba,abaya yayi tunanin fauxa captured his heart da baxai iya son wata ba bayan ita,sai ayanxu ya tabbatar akwai sauran gurbin da bata karasa cikawa ba acikin xuciyar shi,gurbin da eman ta shiga ta kanainaye,shi kadai yasan me yakeji akan yarinyar,asanyaye eman tace"pls tell me,a ina kasamu picture dinnan?"ta tambaya innocently kuma ahankali,intonation din maganar ya daki xuciyar shi, batasan yadda voice dinta ke rikita shi ba,sai ya lumshe idanu yana breathing in and out ahankali tareda placing huge smile on his face,ita dai kallonshi take cikeda mamaki,yace" dana fada miki you're very important arayuwar mu kinyi tunanin karya ne?"ya tambaya yana tsareta da idanunshi wanda suka danyi ja masu dauketa da matsananciyar kaunarta,tace"No I never doubt your words,kawai mamaki nakeyi".saida ya furxar da warm iska daga bakinshi sannan ya bud'e ido yana sauke ganinsa akan medium size lips dinta masu tafiya da hankalinsa harma da nustuwar shi,magana da eman Na sashi cikin nishadi mara fasaltuwa,gabadaya ya nemi damuwar shi ya rasa,bai k'i su dawwama ahaka ba su biyu abinsu,yace"kinada muhimmanci Sosai eman,wanda baki baxai iya furtawa ba,wanda xuciya baxata bayyanawa ba sannan idaniya baxasu iya nunawa ba,you've become part of us,you're now my responsibility,kinsan bana wasa da sauke nauyin daya rataya awuyana "yacigaba"ganin picture dinki anan shouldn't surprise you,saboda nayi tunanin xuwa yanxu kin fahimci babban matsayin dakikai awurin mu,ko sai na fada miki Hakan da kaina?".far far tayi da xara-xaran eyelashes dinta,wanda hakan ya sa yaya Sadeeq runtse idanun da bai shirya ba,ita mamakin yadda suka damu da ita takeyi,musamman yaya Sadeeq wanda yanxu yake nuna damuwar shi Sosai da Sosai akanta,they're so sweet,fatan ta shine Allah ya dawwamar da xaman lafiya a tarayyar su.cikeda gamsuwa da maganar shi tace"thank you Yaya Sadeeq,Allah ya barku tare da ya fauxa ku rayu ku biyu abinku"dan xaro ido yayi yace"kina taya yayarki kishi ko?"sai tayi murmushi tace "ehh mana,we're team no kishiya".yace "you must be kidding me,idan fa yanxu me mata da yara uku ko Hudu yace yana sonki kuma aurenki xaiyi xaki yarda?"without twice thought tace"a'a"da mamaki yace"koda ace yana masifar sonki sannan mutumin kirki ne,a husband material 1000 yards"tace"ehh"bud'e baki yayi yana kallonta batareda yace komai ba saboda ta rufe mishi bakin magana,sai ta cigaba da kalle kalle acikin office din idanunta ya sauka akan wani diary black color,tasa hannu xata dauka yaya Sadeeq yayi saurin dora hannun shi akai,da mamaki ta juya tana kallon shi,sai ya yi murmushi yace "ai da cewa kikai na miko miki"kallon shi kawai tayi batace komai ba yabata diary din xuciyar shi na dukan goma goma,saboda babu komai acikin littafin sai xancen eman da yadda yake bala'in sonta.nutsuwarta ta mayar tana karanta first page of the diary,wanda yafara rubutu kamar a story book,"she looks at me and my heart starts to ponder just imagining what will come from her sexy lips,her eyes is like the moon,so white like succulent in the winter,no words can describe her stylish beauty..."tsayawa tayi cak ta kalli fuskarshi wacce ita yake kallo,haka yaya Sadeeq ke son fauxa Ashe?,har xama yake yana rubuta abubuwa akanta masu dadin karantawa?sai taji she missed those days da Aliyunta xai tsaya har past 1am yana fada mata kalamai masu sanya xuciyarta cikin shauki da farin ciki,sai tacigaba da karantawa "she came into my life like a ray of sunshine that lightens my world with the best of all lights,I love her beyond imagination,beyond every written words,even in paradise I'll love to love her".da saurin ta ajiye diary din saboda yana tuna mata da soyayyar datayi a baya.tace"ya fauxa is so lucky "a yau yaya Sadeeq ya sake burgeta kwarai dagaske,da ace haka maxa ke kaunar matansu da an rage matsaloli masu yawa arayuwar aure.
"A'uxubillahi minasshaidanir rajim "ya fauxa ta furta sanda gabanta ya fadi akaro na uku,tun daxu take jin wani abu na xarya acikin xuciyarta gameda yaya Sadeeq,wayarta ta dauka jiki asanyaye tayi dialling numbar shi,suna shirin fita daga office wayar shi tafara ring,ya duba yaga fauxa ke kira,saurin dagawa yayi yace "yes sweetheart,how are you doing?"ajiyar xuciya ta sauke sannan tace "kana ina?dawa kake tare nasan sai yanxu xaka tafi dauko eman,tun daxu I'm feeling restless,inajin kamar kana tare da wata"mamakin fauxa ne yasa gurmi suka karyo mishi duk da sanyin Ac,ya gyara tsayuwar shi yace"I'm sorry you feel that way,amma babu kowa yanxu xan bar office ma"dayake ta aminta dashi Sosai tace"I trust you yaya Sadeeq,nima yanxu xamu yi closing see you soon "yace "I love you baby"tace "love you too"sannan ya kashe wayar yana sauke ajiyar xuciya,eman na tsaye bakin kofa tana jiranshi,yana gama wayar suka shiga mota kowa da tunanin dake ranshi suka karasa gida,gaban yaya Sadeeq ne yafadi ganin motar Bilal,ya saki siririn tsaki yana had'a abubuwan daxai fada ma Bilal din Dan baxai xuba ido bilal ya wargaxa mishi plans ba.yana ganin shigowar motar yaya Sadeeq yafito daga cikin tashi motar ya tsaya yana kallon eman wacce kallo daya ta mishi ta watsar,bata San meyasa ba she doesn't rate him at all,ko tsayawa su gaisa bata yiba tayi shigewarta ciki wanda hakan yayi ma yaya Sadeeq dadi,shine yakarasa suka gaisa sannan suka shiga ciki,basu tarar da ita afalo ba dan already ta haura sama,tana shiga daki ta ajiye jakarta sannan ta cire kaya tafada wanka,agurguje tafito tasa homewears sannan ta sauko domin girka musu abinci,tana tafiya tace"Ina yini"ko saurarar amsar shi batayi ba ta shige kitchen abinta shikuma yabita da wani irin kallo,yaya Sadeeq yayi murmushin jin dadi.

Salima ce ke hada kaya cikin trolley hjy kwaise ta shigo dakin tana kallonta tace"yanxu gidan fauxa xaki tafi ki barni?bayan nan da kwana kadan xamu rabu?baxaki bari mu kara shakuwa ba acikin sauran kwanakin dasu ka rage mana"tayi maganar kamar xata fashe da kuka,aduniya yaranta are her weakness,tana masifar sonsu da kaunar su fiyeda tunanin mai tunanin,hawaye Salima ta goge sannan ta rungume hjy kwaise tace"ko kwana uku ne kibari naje nayi,nayi ma eman alkawari"da mamaki hjy kwaise tace"eman fa kikace?inde dan ta ita ce kiyi xamanki kawai na riqa kallon abata"murmushi Salima tayi tace"Toh two days pls"hjy kwaise mai son farin cikin yayanta ce,saita ce"idan haka xai saki farin ciki it's alright,kije kiyi two days din"Salima tace"thank you mami "inteesar ce ta shigo tana fadin"Mami xan bi yaya salima "hjy kwaise ta saki baki tace"Haba original auta kiyi xamanki mana kinga Fake auta na boarding sai satin biki xasu dawo,ni kadai xaku bari kenan?"murmushi inteesar tayi tace"wasa nake miki mami na"Ta hade su biyu ta rungume tana jin kaunar su na saukar mata,gefen xuciyarta na wurin fauxa,mariya ma na makale aranta wacce duk sanda sukai waya sai sun sha kuka,Nurain da Saleem kullum suna ranta,uwa uba Al'ameen na karkashin xuciyarta wanda take daurewa tana yin kara kasancewar shi d'anta nafari a maxa.tana son 'ya'yanta fiyeda tunanin me tunani and she wished for their happiness in every falling star.Abba dake tsaye abakin kofa ya saki karamin murmushin jin dadi,ina ma ace haka umma kema eman,ina ma ace umma irin hjy kwaise ce mai kaunar 'ya'yanta with passion,alokaci daya kuma ta hukunta su idan sunyi ba daidai ba,ina ma ace ana iya ciro halin mutum daya ciro wannan halin Na hjy kwaise ya baiwa umma,inteesar ce tace "laa abba sannu da xuwa"Salima da hjy kwaise suka juya cikeda murmushi suna kallonshi,duk da kasan xuciyar hjy kwaise na xafin yadda abban yayi mata akan umma da yarta,amma ko kadan bata nuna hakan akan fuskar taba,illa bud'e hannunshi dayayi Salima ta tafi da sauri ya rungume yarshi yana jin kewar ta tun yanxu,ya kalli hjy kwaise yana miko mata hannu suka rungume har da inteesar,shima ba baya ba wurin son 'ya'ya shiyasa yakejin xafin yadda umma ke banxatar da eman,mummy dake can tsaye tana kallonsu cikeda tsantsar takaici da bakin ciki,xuciyarta kamar xata buga saboda takaici,itafa ta lura abba yafison 'ya'yan hjy kwaise dana umma,nata ko oho baya mabi takansu,kamar ana cinna ma xuciyarta wuta haka takeji,tana jin tsanar hjy kwaise da umma wanda suka xame mata k'adangarun bakin tulu,musamman hjy kwaise wacce ta dade tana d'and'ana mata bakin ciki,gashi yanxu da girma yafara xuwar ma 'ya'yansu na hjy kwaise sunfi cigaba arayuwa,ta juya cikeda b'acin rai tana huci saboda yadda hjy kwaise tamata xarra ta kowani fanni,idan maganar kyau xaayi tafi mummy,haka soyayyar miji,balle axo kan kudi wanda tun kafin Al'ameen ya kud'ance tayi musu nisa balle yanxu da Al'ameen ya tara abin duniya,shegen yaron da bai san darajar su da mutuncin su ba,bedroom dinta ta shiga ta hada kai da gwiwa abin duniya sun taru sunyi mata yawa,mama wacce shigowarta falon kenan taga hjy kwaise da abba dasu Salima sunata hira gwanin ban sha'awa,taso xama amma ganin babu wanda yabi takanta acikin su yasa ta mike tashiga part din mummy cikeda bakin ciki.
Saida ta saki tsaki sunfi uku sannan tace "wace irin mayyar mata ce hjy kwaise?narasa gane dalilin da abba ya haukace akanta har yanxu take baxa mulkinta acikin gidan nan"mummy wacce kadan take jira tace"laifin mune damukayi sake har umma taxo abayan mu ta kafa babban gurbi axuciyar abba,saifa mun tashi tsaye munyi kamar munayi,idan ba haka ba yan kallo xamu xama agidan mijin mu,fatima da hjy kwaise su cigaba da baxa mulki son ransu "cewar mummy tana tsinewa mama acikin ranta,itama maman na tsinema mummy amma axahiri neman mafita sukeyi.
Cous cous eman ta dafa with vegetable chicken soup,kamshin abincin ya xagaye gidan kamar fauxa ce ke girkin,Bilal da yaya Sadeeq na falo fauxa tadawo,su Anum suka rungume Bilal cikeda farin ciki,chocolates yakawo musu masu yawa sunata murna suka nuna ma iyayen,fauxa tashiga kitchen tana kallon eman wacce ke dauraye abubuwan datayi using tace"ohh ni fauxa daga dawowa kika hau girki,karki damu idan kikai aure xakiyi for now ki bar mini abuna"dariya eman tayi tace"kai ya fauxa,kodai girkin nawa ba dadi ne".xaro ido ya fauxa tayi tace"ni na isa nace ba dadi?"adaidai nan yaya Sadeeq ya shigo kitchen din,ya fauxa tayi saurin cewa"kasan me eman tace?"eagerly yace"no tell me,I'm all ears"fauxa tace"she's asking wai ko abincinta ba dadi"dariya yayi mai tsaho wacce fauxa ta tsaya tana kallonshi da mamaki saboda lokacin daya sauka yana yinta,ganin yakusa sauka akan layi yayi saurin cewa"eman is so funny,akwai dadi mana"ita dai eman kallonsu kawai takeyi kamar yadda fauxa ke kallon yaya Sadeeq cikeda mamaki,what's so funny a wannan maganar da har xai dauki tsahon lokaci yana dariya cikeda nishadi????

Zaynab Yusuf ✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now