PAGE 32

114 5 0
                                    

EMAN......PAGE 32

  asanyaye Eman ta jinginar da kanta jikin window tana kallon moving vehicles da idanunta wanda suka cika da ruwan hawaye,abubuwan da suka faru da ita ne ke going through her restless mind,abubuwan da ko amafarki bata taɓa tunanin xasu faru da ita ba,she was lost in thoughts,lost in the world of her own bitter memories,tunanin rayuwarta takeyi trying really hard to bury her past without leaving a single trace,tana so ta manta da komai kamar hakan bai taɓa faruwa ba acikin rayuwarta ,tun daga lokacin data buɗe idanu agidan mahaifinta mai cikeda ƙunci da baƙin ciki tafara erasing hakan daga cikin ƙwaƙwalwarta,tana so ta manta da mutanen dasuka mayarda rayuwarta a living hell and any other thing daya faru in her past,tana son ta shimfiɗa sabuwar rayuwa that's full of joy saboda ta gaji da xubarda hawaye,ta gaji da shiga cikin damuwa da baƙin ciki,ta gaji da kukan da bashida ƙarshe,ta gaji da tafiya with a heavy heart and chest da babu komai acikinsu sai damuwa,she just want to be stress free,tana son gina sabuwar rayuwa mai cikeda farin ciki da kyakkyawar fahimta tsakaninta da Umma,she knows that wouldn't be possible har sai ta ajiye tunanin abubuwan da suka faru da ita agefe,wanda suke dragging ɗinta backward ayanxu dayakamata ace tafara gina sabuwar rayuwa akan turba mai kyau da kuma inganci,wayarta dake haske ta duba taga message din Sadeeq ne ya shigo,xaro ido tayi with a throbbing heart ta tsaya tana kallon message din na lokaci mai tsaho,remembering abubuwa masu yawa that are not worth remembering,lumshe idanu tayi feeling guilty akaro na ƙarshe na cikin tsohuwar rayuwarta kafin ta buɗe sabon shafi na rayuwa mai daɗi,ahankali ta danna ma numbar Sadeeq block after making her final decision,bayan tayi alƙawarin baxata taɓa amince mishi ba no matter what happens and what the consequences might be, abu ɗaya tasani yanxu shine she's done with this chapter of her life,baxata sake waiwayo wa baya ba,that she promised her self...tafiya ce da babu waiwaye acikinta,duk da haka saida tasamu kanta da kasa tsayar da hawayen da suke xubo mata,wanda suke fitowa tareda baƙin cikin data daɗe tana shaƙa aduniyarta mai cikeda ƙunci,ta runtse idanu ahankali hawayen na gangarowa tana tabbatar ma kanta wannan shine karo na ƙarshe da xata sake kuka akan past dinta,asanyaye ta goge hawayen lifting her head up high,assuring herself that's the end of that chapter in her life!!!!!!!!.misalin ƙarfe biyar ne na yammacin ranar juma'a,asanyaye ta shiga gidan wanda tun daga compound take jin hayaniyar jama'a,da ɗan mamaki tashiga tana kallon mutane kamar dai taro akeyi agidan nasu,if she could remember yau xa'a kawo lefen Afiya,sai alokacin ta tuna dalilin tara mutane da mummy tayi,karɓar lefe shine har dasu yin walima,batayi tunanin komai ba tashiga main parlor tana kallon yadda ƴan uwan mummy da ƙawayenta suka xagaye lefen wanda akallo ɗaya data mishi taga akwatuna guda goma sha biyar ne kuma kowanne cike yake da kaya designers masu kyau da tsada,bata bar xuciyrta ta raya mata wani abu ba tashiga part dinsu tana sauke ido akan alameen da Fauxa,sai kuma Hajiya kwaise da Umma,hajjo Na can gefe tareda musaddiq,gabanta ne ya fadi sanda ta sauke ƙwayar idanun ta akan fuskar alameen,wanda shigowarta yasa ya haɗe rai kamar me shirin kai duka,Eman ta tsaya mishi awuya saboda tayi mishi kutse acikin rayuwar shi fiyeda xato da tsammani,after trying to ruin fauxas life she has successfully ruined his life,amma he's not going down alone,wallahi she'll surely pay for that,looking at her sight na tayar mishi da hankali yana sashi cikin damuwa,hakan na saukar mishi da ciwon kai,kamar yadda ya tsani Sadeeq tsana mai tsanani,bai ɗago ido ba amma ya tabbatar she's starring at him,abinda daya ƙara baƙanta mishi rai kenan,yana tunanin ko uban me take kallo afuskar shi oho,sauke idanunta tayi xata xauna asaman carpet Fauxa ta jawo ta ta xauna in between ita da alameen,kamar wanda aka xabga ma mari yayi saurin miƙewa yana wurga ma Fauxa wani irin kallo,itama da mamaki take kallon reaction dinshi haka Umma da hajiya kwaise wacce taji kamar ta rufe fauxa da faɗa saboda abinda tayi yanxu,ganin irin kallon dayake wurga mata yasa ta cewa"sorry"ko bin takanta baiyi ba yayi tafiyar shi ranshi na ƙuna which is very obvious,Umma ta bishi da kallon mamaki har ya ƙurewa ganinta,tanata kallon  inda ya wuce for a very long time,wanda hakan ya ba hajiya kwaise mamaki,yaushe Fatima tafara damuwa da lamarin Eman?asanyaye Eman ta gaida hjy kwaise da Umma sannan ta mike fauxa ta bi bayanta suka shiga bedroom din eman,fauxa wacce idanunta suka cika da tausayin Eman tace"kinga lefen Afiya ko,kada kibari hakan ya dameki,dama sunyi ne saboda su tozarta ki,ke kuma ki maida komai ba komai bane,ki fita ayi harkar bikin dake ki mayar musu da aniyar su"murmushi Eman tayi wanda yasa Fauxa ta buɗe baki cikeda mamakin ganin Eman din very lively,Eman tace"ni yanxu abubuwan nan basa damuna Ya Fauxa,alokacin baya dai sun sani cikin damuwa amma banda yanxu,ayanxu I'm new Eman unavailed,wacce ta ɗauki matsalolin rayuwa ta ajiye agefe,with zero tension in mind,I don't care about them,idan ma sunyi ne dan su bani haushi toh sun makara,ire-iren abubuwan nan yanzu basa gabana,ba Aliyu ba idan ma babanshi xata aura is none of my problem ".Fauxa me saurin kuka saida hawaye suka xubo mata saboda farin cikin kalaman Eman,koba komai Eman has finally moved on with her life.Ta kalli Eman Sosai sannan tace "irin motivation din dana ke buƙata kenan ahalin danake ciki,idan har xaki maida komai ba komai ba who am i daxan cigaba da rayuwa cikin bakin ciki da damuwa?"da Mamaki Eman ke kallon Fauxa batareda tace komai ba,fauxa tacigaba da cewa"har yanzu Sadeeq is going through a lot akan yarinyar daya fada min yana bala'in so,wannan kalmar kaɗai tana sani cikin tashin hankali Eman,imagine fa wai ni Sadeeq yafada ma hakan,aranar na tabbatar da yana masifar sonta kuma babu abinda baxe yiba akanta,wallahi Eman babu feeling din dayakai wannan tashin hankali,wai mijinka yafada maka cewar he's loving somebody else,kinsan me ke bani ƙwarin gwiwa?"asanyaye Eman ta girgixa kai alamar a'a,fauxa tacigaba da cewa"alameen ne my number one support,wanda ya tsaya mini acikin wannan lamarin yake iya bakin ƙoƙarin shi,sai kuma ke dakika xame mini tamkar madubi na dubawa,idan na kalli rayuwarki da abubuwan dakikayi passing through sai naji tawa damuwar kaɗan ce,idan har kin cigaba da rayuwa meyasa ni baxan cigaba ba?idan kina smiling with a heavy heart me cikeda bakin ciki meyasa ni baxanyi ba,arayuwata kin xame min tamkar role model,wacce nake duba agareta acikin rayuwata,da ƙananun shekarunki kikayi passing through alot of unbearable pain yet bakiyi kasa a gwiwa ba kikayi overcoming komai,duk ba'a lokaci ɗaya hakan ya faru ba,but still kinyi abinda ba kowa zai iya yin hakan ba,with xero support from Umma"murmushi Eman tayi trying very hard kada ta fashe da kuka,tace"Ya fauxa i can imagine your pain koda kuwa ba duka ba,amma I can imagine some part of it,idan kikayi tunani hanyar da alameen ya ɗoraki akai is the best way,meyasa xaki damu da sanin wacce yaya Sadeeq keso?wannan ba damuwar ki bace aganina,fatana shine koma wacece Allah yasa tagari ce,burina kuma shine ku kasance tare ku biyu abinku har tashin duniya"murmushi Fauxa tayi mai haɗe da hawaye,kwana biyun man dasuka wuce ta sauko Sosai sannan ta cire damuwar Sadeeq daga ranta,inde tana son tacigaba da walwala da farin ciki saita cire damuwar mijinta na soyayyah da wata acikin ranta,(know this and know peace!)tace"ko jiya danayi magana da alameen ya tabbatar min da cewar baxai bar Sadeeq yaƙara aure ba,hakan bai kwanta min ba Eman,Allah ne fa ya bashi damar yin hakan,meyasa xamu hanashi?nasan i might be too emotional atimes amma hakan baxai sa na manta da sanin yakamata ba"Eman dake cire abayar jikinta tace"alameen nada gaskiya,ko ni da akwai hanyar da xanbi saina hana amiki kishiya"murmushi sukayi atare Fauxa na jin daɗin ganin yadda Eman ta warware taxama kamar ba ita ba......yana shiga parlon shi ya kwanta akan kujera ya Mike kafa tareda lumshe idanu kamar me yin bacci,kuma ba baccin yakeyi ba tunani ne yasha kanshi,yanada ayyuka masu yawa a London,anan gida nigeria ma ya xama very busy kasancewar shi versatile business man,ga kuma ginin gidanshi wanda sai jiya aka kammala,gidan is very dear to his heart saboda Yasmeen ce ta xaɓi komai da komai da yadda gidan xai kasance,har ma da furnitures ɗin da xasu xuba gabadaya yayi order dinsu,shigowar Hajiya kwaise ce tasa ya buɗe ido ahankali sannan ya Miƙe zaune yana kallonta,xama tayi sannan tace "kasan dai ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi ko???,abinda kayi baka kyauta ba"wani bakin ciki ne ya tokare mishi xuciya,yace"dan Allah mami kada kimin maganar ta"xaro ido tayi tace"nifa ban gane wannan tsanar dakake mata ba,what's between you two?tsanar ma akwai dalilinta saboda alokacin baya babu ruwanka da ita shiri kukeyi sosai"maida idanshi yayi ya lumshe batareda yace komai ba,tace"magana nake maka kayi min shiru"bude idanunshi yayi akaro na biyu sannan yace"Mami it's nothing "yafada cikeda kosawa,kallonshi tayi keenly sannan tace"daxu kana min maganar gida mummy tashigo,ina jinka"asanyaye yace"an kammala,yaushe kike da time na kaiki ki gani?"cikeda farin ciki tace"ma shaa Allah alhamdulillah "tafada tana sakin ƙayataccen murmushi,so take ta mishi maganar Yusrah ƴar wajen ƙanwarta hajiya fanta amma ta rasa ta hanyar da xata ɓullo mishi,can dai tace"dole na gyara glasses ɗina na xabo maka mata"dan waro ido yayi yace"Noo need mami,i have someone "shiru tayi tana kallonshi,saboda a son ranta ya auri ƴar uwarta kuma jininta,amma tsananin son datake mishi baxai sa ta mishi dole ba,tace"toh ma shaa Allah,yaushe za'a kawo min ita?"kanshi ne gabadaya ya kulle,can dai yace"very soon"Tace "Allah ya kaimu,bayan la'asar sai muje gidan"da toh ya amsa yana jin kanshi kamar xai tarwatse saboda damuwa.A Lameedo crescent gidan nashi yake,tun daga waje xaka san ya kashe kuɗi masu yawa wurin ginawa,gashi da girma Sosai,tunda aka buɗe gate hjy kwaise ta saki baki tana kallon gidan,wani mahaukacin duplex alameen ya gina wanda haɗuwar shi ya wuce misali,abun dai sai wanda yagani,ta kalli alameen sannan ta kalli gidan wanda xaifi kyau a misaltashi da aljannar duniya,tun kafin ma akawo furniture's kenan,saida ya kaita kowani lungu da sako na gidan sannan suka koma gida tanata farin ciki domin dole maqiya su girgixa idan suka ga gidan,dole duniya ta shaida cewar ɗanta alameen is super rich,kuma kuɗinshi sun wuce yadda ake tunani.....daga can nesa alameen ya hango wata sabuwar benz mai kyau lokacin babu kowa a compound din,a main parlour suka tarar da  Salima,Fauxa,Eman,Afiya,Inteesar,Rafee'ah,gabaɗaya ƴan matan gidan na xaune suna kallon Salima me cewa"jiya da daddare ya kawo min "mummy dake tsaye agefe taji wani bakin ciki ya tokare mata wuya,motar 15m mijin Salima ya saya mata,hajiya kwaise kuwa kamar ta xuba ruwa aƙasa tasha farin ciki,saboda Allah yagama yimata komai arayuwa,batace komai ba ta xauna Salima tayi saurin gaisheta sannan tafada mata this good news,saida alameen yayi congratulating dinta sannan ya shiga part dinshi,mummy wacce takaici ya cika mata xuciya ta saki siririn tsaki saboda ba haka taso ba,so tayi azauna ayi analysis din lefen Afiya da adadin kudin da aka kashe amma babu wanda ya damu,kowa maganar motar Salima yakeyi,hakan ne ya tabbatar mata bata kasance cikin mutane masu sa'a ba arayuwa,da ace ƴar hajiya kwaise ko Umma aka kawo ma lefen afiya da sai an daɗe ana maganar,amma dayake na ƴarta ne Allah ya sanya alheri kawai sukace kowa ya kame bakinshi ya kulle.Da sallama fauxa tashiga gidanta tana mamakin jiwo kamshin girki na fitowa daga kitchen dinta,she couldn't believe her eyes ganin Sadeeq ne me dafa abinci,ƙaramin murmushi tayi tace"newest chef in town"ahankali ya juyo looking at her straight in the eyes yace"ba dole ba tunda kin bar mu da yunwa"dariya tayi tace"nafa ce kuyi order"yace "bilal ne yaxo mukaita hira ban lura da tafiyar lokaci ba"tana cire veil dinta tace"fatan dai bada yunwa su Anum suka kwanta ba"hararar wasa ya mata yace"da ita suka kwanta"tace"dole ayi punishing daddy"yace"saboda son kai ko?"ta girgixa kai batareda tace komai ba,ruwan sanyi ta dauko daga fridge tana sha tana kallon shi yana girkin,abubuwa masu yawa akanshi suna xarya acikin xuciyar ta,saurin kallon shi tayi lokacin dataji yace"Abba ya dawo kuwa?"ta girgixa kai ahankali sannan tace "a'a"yace"sai yaushe?"kalllonshi take attentively sannan tace"wace magana xaku tattauna da Abban ne?tun last week kake jiran dawowar shi,to ka kira shi awaya mana"murmushi yayi yace"no ba maganar waya bace"tace"is it about us?"xaro ido yayi yace"ko daya,in tayi wari xakiji "tabe baki tayi sannan ta fice daga kitchen din shikuma ya bita da kallo.washegarin Ranar da misalin karfe sha daya na safe yafita,direct gidan baban Eman ya tafi,securities basu barshi ya shiga ba saboda koda aka tambayi baban Eman cewa yayi baisan da xuwan kowa ba,Ammi ce dake gefen shi tace"idan emergency ne fa"shiru yayi for some seconds sannan yace"let him in"a main parlour aka ajiye Sadeeq wanda ya saki baki yana kallon gidan baban Eman daya gaji da haduwa,ashe ranar da suka zo baiga komai ba,kamar ma yanxu an kara gyarawa,gida ne kamar ka sace shi ka gudu,kallo daya yayi ma baban Eman yayi saurin sauke idon shi kasa,ya xamo daga kan kujera ya xauna saman carpet,baban Eman Alhaji Lameen Abdulfattah attajirin mai kudi ne mai cika ido da kwarjini,zama yayi yana kallon Sadeeq wanda yaji jikinshi yayi sanyi lokaci daya,can dai ya gaishe shi, ahankali baban Eman ya amsa saboda shi mutum ne that's not friendly at all,idan kaga yana murmushi to da Ammi ne ko kuma 2 of his kids excluding Eman,bakin Sadeeq na rawa yace"dama naxo ne muyi magana"baban Eman yace"I'm listening,maganar me?"yadda baban Eman yayi maganar saida gaban Sadeeq ya fadi,can dai yace"my uncle is on his way" baban Eman ya maimaita kalaman sadeeq sannan yace"and so?"at this point Sadeeq yagama kaiwa karshe wurin rikicewa,Ammi ce ta sauko tana kallon Sadeeq xaune akasa kamar wani ɗan maula tace"ka yi bako "without twice thought baban Eman yace"a shigo dashi"sassanyar ajiyar xuciya sadeeq ya sauke lokacin da uncle dinshi ya shigo,suka gaisa da baban Eman sannan ya ce"Sadeeq dan yayana ne uwa daya uba daya,wanda yakasance mai kaunar ɗiyar ka Eman ba don komai ba sai dan niyyar aurenta daya dauka,shine yazo min da maganar nikuma nace abinda xa'ayi shine muxo nan mu karbi permission awurinka"carefully baban Eman ke kallon Sadeeq yana auna shi a ma'auni sannan yace"ya akai kasan ni ne babanta?"Uncle din Sadeeq ne yace"kasan shi lamarin rayuwa sometimes akwai rikitarwa,mijin yar wajen Alhaji Abdulhameed Safana ne marikin Eman"xaro ido baban Eman yayi yace"what! Are you both out of your senses?ni xaku kawo ma maganar banxa irin wannan?"sassauta murya uncle din Sadeeq yayi yace"we just want your permission "shiru baban Eman yayi can yace"you both should get out of my house "yafada tareda mikewa tsaye,"kuje can wurin alhaji Safana saboda banida lokacin wannan maganar"yana kaiwa nan ya haye sama abinshi yana ma su Sadeeq kallon ƴan shaye-shaye,banda hauka me suka gama fada mishi yanxu?jiki ba kwari Sadeeq yakoma gida bayan uban fadan daya sha awurin Uncle dinshi wanda ya hanashi hakan tun akaron farko,daga karshe yace"xan baka shawara idan xaka dauka,ka hakura da Yarinyar nan saboda shigowarta cikin rayuwarka ba alheri bane,idan ka dage kuma wallahi saika rasa kowa in the process sannan ba lalle ka sameta ba daga karshe,kaga ka ɓata relationships masu yawa kuma ba biyan bukata"daga haka Uncle din sadeeq bai sake cewa komai ba,cikeda ƙunar xuciya sadeeq ke tunanin Abba is the only option daya rage mishi,kamar ma ya manta Abba shine mahaifin fauxa(Sadeeq namu🥴).Eman na kwance a bedroom dinta Umma tashigo,hakan yasa ta mike xaune tana sakin murmushi,Umma ta xauna tareda kamo hannun Eman ta bude shi tana kallon fuskar Eman din,asanyaye ta saka latest iPhone acikin hannunta wacce tayi seizing bayan faruwar wancan al'amarin ,tace"here is your phone "cikeda farin ciki Eman ta rungume Umma tana cewa"thank you umma na "umma na murmushi tace"you're welcome kuma ki kiyaye Sosai,Allah ya miki albarka"tafada tana shafa kan Eman din wacce kamar ta tashi ta hau rawa da juyi saboda farin ciki,relationship dinta da Umma ya gyaru Sosai,koda haka aka barta an gama yi mata komai arayuwa,umma tace"breakfast is ready "atare suka fito falon,Hajjo na wurin Abba suna karyawa,Eman ta xauna tana cewa"wow umma,duk yanxu kikayi abincin nan?"Umma na murmushi tace"an fada miki kowa irin kine"dariya Eman tayi ta dauki samosa tanaci,sallamar hajiya kwaise ce tasa Eman kallon kofa,tagaishe ta tana cigaba da bubbude warmers,ankon Afiya ta kawo musu,na iyaye hudu haka ma na ƴammata hudu,umma tafito daga kitchen tana cewa"kiyi tasting pepper soup din kiji".sakin baki tayi tana kallon Umma,abu ne da basu taɓa gani ba,sun saba ganin Eman da Umma not so close,da fara'a Umma ta gaida hajiya kwaise sannan tace"an kawo ankon kenan "hajiya kwaise tace"Toh abune ake yinshi cikin hanxari,yanxu fa sauran kwana 10 kacal"jinjina kai umma tayi tace"Allah ya kaimu lokacin"daga nan bata sake cewa komai ba,Eman ce tace"Mami me xa'a xuba miki?"kallon Eman tayi tace"akoshe nake"tana mamakin yadda Eman din yau ta tambayeta kai tsaye,wanda alokacin baya gaisuwa ce kawai ke hadasu.Mikewa tayi jiki ba kwari takoma part dinta tana jin gabanta na faduwa,bata San meyasa these days takejin hakan ba idan ta ga Eman,xama tayi tana xurfafa tunani akan hakan,musamman yadda ta lura alameen ya tsani Eman gashi baya iya ɓoye hakan,ajiyar xuciya ta sauke tana amsa sallamar shi,sanye yake da wani yadi dark blue mai kyau,tace"Ina xuwa?"atakaice yace"meeting"daga haka ya juya yana jin jikinshi very weak lokacin daya tuna gobe Abba xai dawo which is his perfect opportunity da xai gabatar da plan dinshi to end this drama once and for all,tsayawa yayi cak yana runtse idanu,shi kaɗai yasan xafin da xuciyar shi ke mishi alokacin,asanyaye yacigaba da tafiya yana faɗawa kogin tunani,Eman wacce ta dauko jug full of orange juice daga main kitchen ce taxo wucewa suka ci karo juice din ya xube ajikinshi gabadaya,runtse ido yayi yana jin saukar lemun mai sanyi afatar jikinshi,ranshi ne yayi baƙiƙƙirin saboda ya tsani abu mai sanyi ya taɓa fatar jikinshi,ahankali ya buɗe ido tareda saukesu akan fuskar Eman wacce ta tsorata Sosai da ganinshi,tayi saurin ja baya ganin yana ƙoƙarin closing gap din dake tsakaninsu,wurga ido tafarayi saboda takai bango,sai kawai ta rungume hannayenta kamar hakan ne xai bata kariya,hannunshi ya dunƙule ya daki bango ta saitin fuskar ta,tayi saurin runtse ido xuciyrta kamar ta faso daga gangar jikinta,dakyar yake iya magana saboda tsanar ta dayayi"never in your life cross my path again"ya furta hakan tana jin dumin iskar dake fitowa daga bakinshi saboda tsananin masifa,billahi ji yake kamar ya kikkifa mata mari saboda takaici,tun last week suka samu saɓani da Yasmeen dakyar yau ya shawo kanta ta hakura,shine tabashi time dinda xata iya mishi spearing yau, kuma ta tabbatar mishi idan ya wuce lokacin baxata fito ba,agogon hannunshi ya kalla da idanunshi dasukayi jajir,Eman ta rigada ta bata komai,yanzu kafin ya sake wani wankan ya shirya wani qaton aiki ne,gashi gidan su Yasmeen din akwai ɗan nisa daga gidan su,part dinshi ya shiga kamar xai tashi sama saboda fushi,ya rufe kofar da karfin gaske,cire kayan yayi ya shiga wanka sai xabga tsaki yake,ya dade Sosai a toilet din sannan ya fito yana dialling numbar Yasmeen wacce ko takan shi bata bi ba,ya runtse idanu ahankali yana trying kiranta multiple times amma taki picking,kife wayar yayi xuciyar shi na ƙuna sanin cewar  ta sake yin fushi dashi.Wannan thought ɗinne yasa xuciyar shi papiltate for few seconds,saboda yadda Yasmeen keda wuyar saukowa idan tana fushi dashi,in the other hand shikuma baya son fushinta,hankalinshi tashi yakeyi baya samun nutsuwa har sai sun shirya,Allah kaɗai yasan adadin baƙin cikin da alameen yake ciki alokacin.taɓangaren Eman ajiyar xuciya ta sauke sanda ya wuce yana nishi kamar wani xaki,ta xaro ido tana mamakin yadda idan yayi fushi yake xama abun tsoro haka,hakika ta tsorata da ganinshi ahakan,jikin ta ba kwari ta dauki jug din takoma main kitchen aka sake xuba orange juice sannan takoma part din umma ta ajiye akan dining,har lokacin jikinta tsuma yakeyi,daki tashiga tareda rufe kofa ta jigina jikin kofar tana dafe xuciyarta wacce har lokacin ke bugawa da sauri,tana kissima yadda xata ƙaurace ma ganinshi tun kafin ya mata illa,saboda tsantsar tsanar ta take hangowa acikin idanunshi,wanda alokacin baya ba haka relationship dinsu yake ba,jarabar Sadeeq ce ta janyo mata wannan masifar,ta daɗe ahaka sannan tayi jarumtar fitowa waje,Hajjo tagani tana gyara ɗauri,tayi dariya tace"har yanxu gyara dauri kike hajjo?"tafada tana dariya ,hajjo tace"kwarai dagaske,sai ma kinganni da skirt a bikin afiya"riqe ciki Eman tayi tana dariya Umma tace"kiyi hakuri dan Allah,wani irin skirt kuma?"murmushi hajjo tayi tafita daga part din,umma takalli Eman dake dariya tace"kawo juice dinne tun daxu?"Eman tace"xubewa yayi saida akayi sabo"tabe baki umma tayi tace"kina abu sai kace karamar Yarinya "murmushi eman tayi without saying a single word,saide har lokacin kallon tsanar da alameen ke mata ne ya tsaya acikin xuciyarta.

Dedicated to my lovely Mum Ummu Faisak 💕💕

Zaynabyusuf✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now