PAGE 26

111 2 0
                                    

EMAN....PAGE 26

  Bata ankara ba taji ya ce"give our love a chance,koda sau daya ne,idan hakan bai yi working out ba nikuma nayi miki alkawarin rabuwa dake har abada koda yin hakan xai xama dalilin d'auke war numfashina,amma I'll die a honourable death knowing that you've done something for our love,rashin amincewar ki is driving me nuts,I can't think straight, I don't care anymore,all I care about is you my love,all I care about is to have you Eman,na xo karshe,hakuri na ya k'are,is either you give us a chance ko kuma nabi wata hanyar ta daban,idan itama hanyar tak'i yiwuwa sai na hakura Na jirayi mutuwa ta!".idan ya ambaci mutuwa gabanta yana faduwa tana shiga cikin damuwa,hakan Na karya mata xuciya,yana sata xubar hawaye,xuciyarta na k'una,tana jin xafi aranta mara misaltuwa,this issue is very complicated,bata san yadda xatayi ba,bata san wurin wa xataje ba domin ya bata shawara,tana kuka take fadin"wace hanyar xaka bi?saboda baxan taba amincewa da son ka ba,baxan xama silar bakin cikin ya fauxa ba,amana batace haka ba,I don't want to ruin my relationships,yakamata ka fahimci hakan,I understand you amma ni ka kasa fahimta ta from my own perspective".Yace"na fahimce ki Eman,i really do,kece yakamata ki fahimci ba haram bane,tunda Allah bai haramta ba meyasa kike kokarin yin hakan?"ajiyar xuciya ya sauke yacigaba da fadin"nide nafada miki,kodai ki amince ko kuma nabi wata hanyar mai cikeda fasassun kwalab'e,gargada da kwaxaxxabo,saboda you left me with no choice ".wani irin xaro ido Eman tayi tace"kar ka min haka yaya Sadeeq,ka tausaya min,kaji k'aina dan Allah,wallahi baxan iya cin amanar ya Fauxa ba,I can't do that"yana mata wani irin kallo yace"shikenan,xan bi wata hanyar in shaa Allah"daga haka ya juya xai fita tayi saurin tsayawa agabanshi,kirjinta nawani hawa da sauka,tana kuka mai tab'a xuciyar mai sauraro,ta dunkule hannunta awuri daya tace"karka min haka,kada ka ruguje min abinda ya rage acikin rayuwata".yana kallonta keenly yace"then accept my love,it's that easy,abune mai sauki,duk fushin da iyayenmu xasuyi na lokaci kadan ne amma xasuyi mana abinda ran mu yakeso koda su basaso,kidena tunanin maganar mutane,Fauxa kuma xata karbi hakan amatsayin wani sashe na kaddararta,haka Allah ya qadarta so she'll find a way to make peace with it,nide abu daya nasani xanyi trying possible best dina to have you".bakinta na shaking take kallon yaya Sadeeq,tana mamakin kalamanshi,dama haka namiji yake idan yana son abu?yadda idanun yaya Sadeeq suka rufe ta tabbatar zai iya fadama Fauxa halin dayake ciki ko kuma someone close to him,ta runtse ido bata son hakan ya faru,batason kowa yasan da wannan maganar,tace"ka k'ara mini lokaci,xanyi tunanin abinyi "yana gyara tsayuwar shi yace"not anymore,xan fada ma fauxa halin dana ke ciki,saboda damuwar Hakan is eating me up,I'm feeling guilty at the moment,ban yi ma Fauxa adalci ba,ban kyauta mata ba,duk da ba haram bane amma hakan yana breaking xuciyata into tiny pieces,bazan iya cigaba da b'oye mata damuwata ba,xan fada mata komai Eman,nasan matata xata fahimceni saboda ita din me sona ce da kaunata da son ganin farin cikina,unlike you Eman you're not worthy of my love,baki cancanci soyayyar danake miki ba,it's just a one sided love,ko tausayina bakya ji,baki damu nayi rai ko kuma Na mutu ba,idan har akwai b'urb'ushin imani acikin xuciyarki you won't treat me this way "tana kuka take girgixa kai tace"da damuwarka kullum nake kwana nake tashi yaya Sadeeq,kullum ina cikin fargaba da xullumi,kana raina 24/7 tun ranar daka furta mini kalmar so,banida yadda xanyi ne,nayi tunanin abubuwa masu yawa yaya Sadeeq,wannan maganar ba karamar magana bace,xata lalata abubuwa masu yawa,nafarko xata lalata tsakaninka da ya fauxa,na biyu xata lalata tsakanina da ya fauxa,na uku xata lalata tsakanina da umma,tsakanin umma da mami,tsakanin Abba da umma,tsakanin Abba da mami saboda she'll blame him for bringing me here,tsakanina da sauran yan gidan,kana ganin inada sauran space din xama agidan su?dole nabar gidan su,idan na bari ina xanje?agaban idanka baba na ya koreni yace kada Na sake shigar mishi gida,idan haka tafaru wurin wa xanje?ina xan nufa?".runtse idanu yayi domin shima yayi wannan tunanin,ahankali yafurta" daura mana aure xa'ayi Eman,cikin Kwanaki kadan xan tabbatar da anyi hakan,kinga maganar cigaba da xama agidan wasu bata taso ba".sakin baki kawai tayi tana kallonshi ganin bai tsaya ya fahimci maganar taba,shi takanshi kawai yakeyi acikin wannan lamarin,baya duba ita halin daxata shiga,wace irin masifa ce wannan?yace"xanje nasha magani na kwanta,karfe 2 saiki shirya muje makeup din"yana gama fadin haka ya fita daga dakin yana tabbatar ma kanshi xai fada ma Fauxa ne kawai,duk abinda xai biyo baya kuma a shirye yake da tunkararsa!.Duk da yasan maganar nada girma,yana fatan samun courage din da xai iya kallon tsabar idon fauxa ya fada mata hakan,lamarin ne akwai rikitarwa,ya tabbatar da wata ce daban sai yafi mishi sauki,amma Eman fa,shima ya jinjina abun yana tunanin da wani idon xai kara kallon fauxa idan ya fada mata hakan,wata xaxxafar iska ya furxar domin faruwar hakan ya xama dole,sai dai yana fatan samun sauk'in lamarin awurin Allah.
Tunda yafita take kukan bakin ciki da takaici,har xuciyarta ta yi tauri idaniya suka daina xubar hawaye,tunanin mafita tafara yi,xuciyarta na bata shawarar ta amince mishi kawai shine maslaha,wata xuciyar na hanata aikata hakan,saide sashen farko yafi tsaya mata arai,yaya Sadeeq na tsananin sonta ta tabbatar da hakan,kodai ta bashi chance dinne suga me Allah xaiyi?ta girgixa kai tace baxe yiwu ba,dayar xuciyar tace idan fa wani abun yasameshi?kina tunanin Fauxa dasu Anum xasu yafe miki?kowa xai dora blame dinne akanki,kowa xaiga laifinki ne matukar hakan tafaru,kowanne bangare yanada nashi tashin hankalin amma wanne yafi sauki?wanne ne yafi girma?cin amana ko kuma asarar rai?sai kawai ta runtse idanu tana making final decision.
Kamar yadda sukayi jiya su Salima na tafiya wurin emgees yaya Sadeeq yafito jikinshi sanye da wata black color jallabiya,Eman na xaune afalon sama ta xabga uban tagumi,har ya karaso inda take xaune bata motsa ba,sai kawai ya tsaya yana kallon ta,idanunta sun fada saide sunyi haske,cute bakinta ya kalla wanda ta danne hakoranta biyu akai tana Dan cixawa ahankali,bai San lokacin da ya sauke wata banxar ajiyar xuciya ba,shifa kome tayi burgesa takeyi,asanyaye ta Dan motsa tana kallon gefen dayake tsaye,ta xuba mishi ido tana kallon shi carefully,tun daga gashin kanshi ixuwa idanunshi,hancinshi,bakin shi,kirjinshi har ixuwa kafafuwanshi dake sanye da bertozzi sandals,xuciyarta na raya mata kawai ta amince saboda yaya Sadeeq ba daga baya ba wurin kyau,haduwa,iya gayu gashi uwa uba yana mutuwar kaunarta.
Cikeda jin dadin irin kallon datake mishi yace"idan kin gama kallon nawa ki tashi mutafi time is going "yafada hakan even though shi bai k'i su dawwama ahaka ba,yana jin wani masifaffen dadi,wai yau Eman ce ke kallon shi haka,awani shagwabe tace"niba kallon ka nakeyi ba"ya dan bud'e baki tareda xaro ido yace"kodai kallon bai isheki ba xakice?"sai ya xauna agefenta yana fadin"xanso kiyita kallona Eman,bakisan dadin dana tsinci kaina aciki ba"yau ne karo na farko data kasa cire idanunta acikin nashi,koda yayi wannan maganar sai kawai ta gyara xama still tana kallon shi yace"nafada miki kina sona,meyasa kikeda tsoro ne?"rausayar da eye balls dinta tayi tace"ba tsoro bane,lamarin ne bai kamata ba"wannan kallon data mishi jiyayi kamar ya kwanta yayta ihun jin dadi,ya wani washe baki yana fadin"slowly but steady,you'll come running to me "sai
Yacigaba da fadin"nayi making mind dina,I'll tell fauxa about it"sai alokacin ta d'auke idanunta daga kallon shi sannan tace "idan hakan kake ganin yafi it's alright then,even though fauxa might not forgive us,wannan shine height of cin amana"itama alokacin tafison kawai ayi komai ya kare,dan tagaji iya gajiya,komai xai faru haka Allah ya kaddara,sai ta mike ya bi bayanta suka tafi,yana driving yana kallonta ga mamakinshi sai yaga suna yawan hada ido,sai ya kasa hakuri yace"Eman,dagaske kallona kikeyi?"
Tana kallon titi tace mishi"a'a"murmushi yayi yace"haka ne"baxai tuna ranar daya tsinci kanshi cikin irin wannan farin cikin ba,infact bai ma taba tsintar kanshi cikin hakan ba,jin kanshi yake over the top,wai yau shi Eman ke kallo kuma kallon ma ba normal kallon datake mishi ba,wallahi yakasa yadda da hakan,itama mamakin farin cikin dayakeyi take,tana ayyana ko Aliyu baya mata rabin son da Sadeeq ke mata,saide soyayyar sadeeq me cike da kalubale ce da hargitsa tunanin me tunani,ina ma ba mijin Fauxa bane shi,ina ma they're not somehow related,she'd have been the happiest girl ever dubaga rayuwarta mai cikeda bakin ciki mara fasaltuwa,ta tabbatar Sadeeq will worship the ground she walks on,Bata San meyasa she's feeling calm ba,tana ta tunane-tunane har suka karasa gidan dasukaje jiya,kamar a jiyan ma haka Sadeeq ya xauna acikin mota yana jiranta,tun da aka bud'e kofar gidan ya gyara xama yana kallonta,wani irin masifaffen kyau tayi fiyeda misali,ya saki wani kayataccen murmushi yana jin sonta har kasan xuciyar shi,xama tayi tana kallon shi,can tace"muje mana"sai alokacin ya sauke ajiyar xuciya yafara driving calmly,can yace"you look absolutely stunning Eman,kamar Na d'auke ki Na mayar cikin xuciyata,I love you baby girl"yafada yana sakar mata wani killer smile,lumshe idanu tayi tana jin kalamanshi har cikin xuciyarta,amma bata ce komai ba illa wasa data farayi da fingers dinta wanda suka sha lalle mai daukar hankali,kallon hannun yayi yaji dama kawai ya riqo hannun ya bata mad peck akan fingers dinta,sai yayi saurin kawar da tunanin daga ranshi har suka karasa gida,ta shirya cikin atamfa straight gown me daukar hankali,tayi kyau iya kyau fiyeda misali,tana xaune afalon kasa Sadeeq ya sauko sanye da sky blue din shadda wadda ta amshi jikinshi Sosai,yana sakar mata murmushi yake fadin "muje "yasata agaba yana binta abaya suka fita,ahankali yake tafiya kamar baya son xuwa,yana ta tunanin maxa xasu kalle mishi Eman dinshi,ranshi yayi mugun baci yana driving yana sakin kananun tsaki.
Fitowar shi daga toilet kenan wayar shi tafara ring,ya xauna yana kallon wayar yana sakin murmushi yana jin dadin kiran nata,yace"my Yasmeen,sai yanxu kikaga call dina"ta dayan bangaren tace"sorry babe, I wasn't close alokacin,kai ma kasan I won't ignore your call haka kawai"gyada kai yayi yace"sure babe,amma kibani few minutes pls,xan shirya ne yanxu nafito daga wanka"tace"Alright babe,May Allah bless their union"yace"Amin,ours is next ko?"tace"in shaa Allah "yace"gobe xa'a gama bikin kinga few days after xanyi ma Abba magana akan mu,I can't wait to make you my wife,that's my biggest wish "tace"I love you baby,talk later bye"tana fadin haka ta kashe wayar ya ajiye yana murmushi,yana bala'in son Yasmeen fiyeda misali,and the thought of making her his wife na kara mishi jin dadi.cikin wata maddd farar shadda ya shirya wacce ta amshi jikinshi sosai ,yayi wani irin kyau mai daukar hankali,koda yafito hjy kwaise na xaune tana jiranshi cikin wani rantsastsan lace mai shegen tsada wanda ya sha dinkin straight gown,gefenta umma ce wacce idan kayi mata kallo daya xakayi tunanin babbar yayar su Fauxa ce,anyi mata makeup tayi bala'in kyau,mummy da mama ma sunyi kyau daidai nasu,Tunda abba yashigo ya tsayar da idanunshi akan Umma,matar shi ta hudu kuma amaryar shi,kyan datayi yasa ko kallon gefen su mummy beyi ba yakarasa inda su umma suke,ya kalli hajiya kwaise yana murmushi yace"Al'ameen kaga mamanka saikace itace Amaryar"murmushin jin dadi hajiya kwaise tayi tace"kaji abba da tsokana"daga haka Abba be ce komai ba yakoma part dinshi,wannan abun ne ya tsaya ma mummy arai tace"yan kutumar uba"sannan ta juya takoma part dinta,lokacin su Sadeeya sun gama shiryawa sai kawai ta hada garwashi tafara turare su dashi,ba'ason ransu ba suka tsaya gasu hajiya can atsakar gida suna jiran fitowar ta,saida ta turare su dakyau sannan tace"Allah ya bada sa'a da nasara,Allah ya baku miji ayau dinnan,mai kudi wanda yagaji arxiki kuma mutumin kirki,in shaa Allah ayau dinnan xakuyi gam da katar!.tana kaiwa nan tafice da sauri Sadeeya da Rafee'ah suka bita da kallo,suna jin wani takaici yana tokare musu wuya.
At the same time suka shiga hall din,Kowacce budurwa tasaki baki tana kallon Al'ameen yana wani cin magani da hade rai,shifa Yasmeen ce kawai tasan dariyar shi sai yan gidan su,table dinsu hajiya kwaise,umma,mama,mummy da hajiya Fanta da wasu kawayen Hajiya kwaise daban,sai Table din Al'ameen,wanda su Sadeeq dasu Eman xasu xauna wanda Fauxa ce tayi musu reserving dinshi,su Anum na gefen Al'ameen yana musu pictures Sadeeq da Eman suka karaso wurin,gaisawa sukayi da Al'ameen Eman ta xauna sannan can tace"Ina yini?"dagowa yayi yana kallonta sannan can yace "lafiya"sannan yacigaba da pressing phone dinshi,Sadeeq da Al'ameen bawani shiri sukeyi ba dan haka babu me cema wani ci kanka awurin,saboda tun lokacin da xai auri fauxa Al'ameen ke tunanin son da take mishi yafi nashi,kamar ma itace me shisshige ma Sadeeq din,shikuma Al'ameen yana bala'in jin haushin hakan saboda fauxa is he favourite sister,yafi sonta fiyeda sauran siblings dinshi,jiki na rawa yake mata abubuwa cikin dadin rai da rashin gajiyawa,farin cikinta nashi ne haka ma bakin cikinta,shiyasa bata iya b'oye mishi komai na rayuwar ta.Sadeeq sai wasa yake da yaranshi yana musu pictures,Eman kuwa Na gefe tanata kallon Umma,can dai ta mike ta karasa table din,ta tsugunna tagaida Hajiya kwaise,kallonta hajiya kwaise keyi Sosai tana ayyana abubuwa masu yawa acikin ranta,can dai ta amsa,sai takoma wurin umma ta gaisheta,fuska asake umman ta amsa,kallo daya xaka musu kasan uwa da 'ya ne saboda kamar su daya,tsayawa tayi abayan uwar can tace"umma kinyi kyau"sai alokacin umma ta kalleta Sosai sannan tayi murmushi kawai,Eman tace"umma ina wayarki muyi hoto "wayar umma ta mika mata,eman ta karba tayi musu selfies masu kyau sannan takoma seat dinta tana murmushin jin dadi,wai yau umma ce ta yi mata murmushi har dayin hoto,tana dago ido idanun ta ya sark'e dana Al'ameen wanda shima ya dago ido alokacin,samun kanta tayi da k'in janye idanun nata shima ya tsare gida,Sadeeq na ganin haka gabanshi ya fadi,ya ji kamar ya shake Al'ameen ya huta saboda bakin ciki da takaici,atake idanunshi sukayi ja ko jin Anum dake magana bayayi,gabadaya alamarin ya rikitashi,xuwan fauxa ne yasa yayi saurin kallonta yana murmushi ganin kyan datayi,dama fauxa inde kyau ne lamba daya ce,ta bayan shi ta sakalo hannunta tana hade kansu tana sakin murmushi,Al'ameen ya kalleta yana mata pictures,can takoma wurin Eman tace mishi "snap us "nan ma yayi musu beautiful pictures sannan Fauxa tabar table din domin tarbar bakin hajiya kwaise,su Rafee'ah da sadeeya ne sukayi joining table din su Eman,Afiya kam Na can table din kusada abokan ango anata xuba iyayi saboda asamu shiga.
Xaman su awurin wasn't comfortable for Sadeeq saboda samarin dake kallon Eman,Al'ameen ma ya lura da hakan,sai dai ganin maxa akusa da ita ya hana su xuwa suyi mata magana,Sosai xuciyar Sadeeq ke kuna yana jin wani sabon takaici yana rufeshi,kishin Eman yake da gasken gaske,ya tsani kowani namiji yakalleta,suna nan xaune umma taxo table dinsu,ta kalli Eman sannan tace"tare xamu tafi gida"tana kaiwa nan tajuya tabar sadeeq da budadden baki,ji yayi kamar ta xabga mishi mari,me xataje gidan tayi??,sai ya nemi nutsuwar shi ya rasa can dai yace"idan kunje if you're done saiki kirani na maidaki gida"Al'ameen na danna waya sai tunanin shi ya tsaya cak,yayita maimaita kalaman Sadeeq din sai can ya dago yaga tabbas da Eman din yake,dama shi can baya san Sadeeq shiyasa abu kadan xaiyi yaji yaxo mishi wuya,dan ma dai bame magana bane da sunyita samun matsala,Shide yayi mamakin meyasa zai ce wai idan tagama xai je ya maida ta gidan fauxa,why is it that necessary for him,shiru yayi yanata tunani domin inde akan abinda ya shafi fauxa ne sai inda karfin shi ya kare,lokacin daxasu koma gida Mummy ta tura Eman gaban motar Al'ameen,sukuma suka shiga baya,Suman tsaye hajiya kwaise tayi data ga eman xaune agefen Al'ameen dinta,taji wata mummunar faduwar gaba,harga Allah bata kaunar Yarinyar ta riqa xuwa kusada d'anta,ita fa ko magana bata son ta hadasu,Sosai ta hade rai tashiga baya kusada umma taxauna xuciyarta na k'una da tafarfasa,ji take kamar ta cilla Eman waje daga cikin motar d'anta,banda hauka irin na Al'ameen meyasa bai dauko inteesar ba sai wata Eman,itafa ta gwammace ko yan uban shine ya dauko yafiye mata kwanciyar hankali koba komai yan uwanshi ne,idan bisa tsautsayi wani dan uwan Aliyu yagansu fa?ay mutuncin danta ya zube kenan tunda kallon banxa familyn su Aliyu kema eman,kallon rashin kamin kai.,alla alla take su karasa gida domin tayi ma Al'ameen iyaka da eman dan wallahi baxatayi tolerating yana shiga sabgar Yarinyar ba,shikam ko kallon gefen da eman din take baiyi ba balle ya mata magana dama can miskili ne but he's friendly,suna karasawa gida kowa ya shiga part dinshi,Hajiya kwaise taja Al'ameen bedroom dinshi tana mishi wani irin kallo,saida gabanshi ya fadi dan yayi tunanin wani babban abun aka mata.Ya ce"my dear Mami what happened "ya tambaya yana xaunar da ita agefen gado,soyayyar danta ce ke nukurkusar xuciyarta baxata iya mishi ihu ba,ahankali tace"meya kawo Eman cikin motar ka?nifa bana son kana shiga harkarta"da mamaki yake kallon hajiya kwaise can yace"you're funny Mami,I don't understand what you mean "tace"meyasa tashiga motar ka?"yace"umma ce tace tare xamu dawo,meya faru?"gaban hajiya kwaise ne ya fadi,wato Ta bayan fage umma ke shirin bullo mata kenan??,tayi wani murmushi domin inde tana numfashi baxata bari burin umma ya cika ba,Tabbas duniya babu gaskiya,abinda umma take shirin kulla mata kenan?me danta xaiyi da wata eman wacce aka buga mata tambarin iskanci?tayi siririn tsaki tana Allah wadai da halin umma,wato xaman da eman din keyi agidan 'yarta bai isa ba shine take kokarin turama Al'ameen ita?,toh anyi walkiya taganta kuma inde tana numfashi saita murkushe duk wani kudirin umma na munafurci.
Hajjo na xaune tana laximi Eman tashiga fuskarta dauke da murmushi,itama tana son tsohuwar saboda hajjo nada abin dariya,tana jin hajjo aranta Sosai,da sauri takarasa ta rungume hajjo tana fadin "Naji dadin ganin ki hajjo,jiya naxo kina bacci"hajjo tace"tafi can 'yar nema,tunda naxo nake tambayar ina kike?saida nayi ma Fatima kaca-kaca sannan tace xata turoki yau"murmushi Eman tayi tace"Allah sarki,muma munso kwana saiga yaya Sadeeq yaxo daukar mu "tab'e baki hajjo tayi tace"shi wannan banda lokacin shi tunda gaki kinxo,kullum kina raina,nace kila tana can tana damun kanta Akan Aliyu batasan in shaa Allah sai ta samu wanda yafi shi ba,kuma sai Allah ya wulakanta duk munafukin daya kulla miki wannan kulalliyar"hawayen farin cikine ya xubo ma Eman,hajjo na sonta fiyeda yadda takeson wasu daga cikin jikokin tama.hajjo tace "jibi in shaa Allah xaki hado kayanki babba da karami ki dawo kinji Emani,muyi xaman mu tunda nima xan dade,sai bayan bikin Al'ameen xan koma gombe".da dan mamaki eman tace"aure xaiyi dama?"hajjo tace "ehh haka muke sa rai"jinjina kai kawai eman tayi suka cigaba da hirar duniya.
Tunda suka bar hall din Sadeeq bai kara cewa komai ba saboda b'acin rai,yana driving kamar xai tashi sama,fauxa na lura da yanayin shi amma batace komai ba dan ta lura yana cikin fushi,gashi bai iya b'acin rai ba shiyasa tayi mishi shiru batace komai ba,suna xuwa gida ya bud'e motar afusace ya haura sama,da sauri tabi bayan shi tana jin xuciyrta na harbawa da sauri sauri,ruwan hawaye har sun cika mata ido,fauxa mutum ce mai rauni gashi tana masifar son Sadeeq,yana shiga bedroom dinshi yafada kan gado yana sauke wasu kalar ajiyar xuciya kamar yadda obsessed lovers keyi,suna ganin cewar sunada cikakken iko akan mutum,kitchen ta juya tashiga ta dauko honey sannan ta koma dakin nashi,ta xauna agefen gadon tareda dora kanshi akan cinyar ta tana dangwalo xumar tana turawa acikin bakinshi take fadin"haba mijina,waya tabamin kai kake fushi?tell me waye ya bata maka rai?"shiru yayi baice komai ba saide tausayinta daya cika mishi xuciya,ya Mike zaune yana kallonta,can ya riko hannunta sannan ya tsugunna agabanta yana murxa hannuwan hankali yace"Ina sonki fauxa,ina sonki ina sonki,dan Allah ki fahimce ni,kiji tausayina sannan kiji k'aina,ki dafa mini,ki tsaya mini akan hanya ta ta cikar buri"tunda yafara magana taji gabanta na faduwa,hankalinta ya tashi lokaci daya,hawaye Na xubo mata,shima hawayen yafara yi domin tabbas yanxu xai fada ma fauxa halin dayake ciki,xuciyarshi nawani bugawa da karfi yace"......!

Zaynab Yusuf ✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now