PAGE 16

120 5 0
                                    

Page 16

    Ahankali hawaye ke xubowa daga idanun umma wacce maganganun anty habiba suka ratsa ta Sosai tace"eman bata min adalci ba sannan bata kyauta mini ba,ta mayar dani abar nuni agidan nan,nima ba'a son raina nake mata hakan ba,I just can't help it saboda tayi tarnishing image & reputation dinmu,ta toxarta ni acikin kishiyoyi".anty habiba tace"abinda kika kasa fahimta shine kaddarar eman ce ahaka,tun kafin xuwanta duniya Allah ya qadarta faruwar hakan acikin rayuwarta,muma amatsayin mu Na iyaye muna kuskure balle 'ya'yan cikin mu,sai mu dage sai yaran mu sun xama perfect while we as their parents are not even half of them,idan kika duba rayuwa gabadayanta trial and test ce,dole sai munyi hakuri kafin mu cimma nasara,kin manta rayuwar dakukayi agidan baban eman ne?ina hakurin ki Na wancan lokacin ya tafi?shifa yaro ba'a daukar fushi dashi Na lokaci mai tsaho,saboda hakan Na affecting rayuwar shi in one way or the other,eman needs your emotional support in her trying time,duk da hausawa sunce sanin hali yafi sanin kama,na tabbatar ba lallai kiyi abinda ya kamata ba,saide kiyi kuka ki share hawaye ki cigaba da tafiya akan turba mara kyau gameda eman,she's your daughter for crying out loud,meyasa akan eman ne hakurin ki yake karewa?nan kishiya xata faffada miki magana saide kiyi shiru ko kibar wajen,amma eman Na abu kadan saiki fita hayyacinki kifara fada mata maganganu that might affect her future why?"shiru umma tayi tana sharce hawaye,tasan abubuwan da anty habiba ke fada are nothing but the truth but she can't do anything about it.Shigowar abba ce tasa anty habiba xamewa ta xauna saman carpet,bayan sun gaisa ya kalli umma wacce har lokacin hawaye basu daina xubo mata ba,yace"hala maganar eman kukeyi?"anty habiba tace"maganar ce taxama dole,naga lamarin yayata sai kara xurfi yakeyi,kuma bai kamata ace mun xuba mata ido tana ma yar cikinta Haka ba".xama abba yayi wanda ya shiga cikin damuwar ganin umma tana kuka yace"bansan mecece matsalarta ba,ina fatan koma me nene Allah ya yaye mata yakawo mana karshenta cikin gaggawa ".anty habiba tace"Lamarin yaya fatima Na daure mini kai,zuwa yanxu yakamata ace ta sauko daga fushin datakeyi da eman,abinda yafaru fa kaddara ce amma takasa fahimtar hakan".Abba yace"nima dai nayita naxarin halayyar fatima,sede ina mata uxuri sannan nabata lokaci tayi clearing mind dinta kafin eman ta dawo,na tabbatar mata baxan xuba ido ba tacigaba da muxgunawa yarinya ko tausayinta bataji ,shine dalilin xuwan eman gidan fauxa amma lokacinta ya kusa karewa,eman takusa dawo wa gidan nan,in har fatima nason ganin fushina tayi kokarin muzgunawa eman tagani,I won't tolerate that "yana kaiwa nan ya miqe ya fita ran anty habiba yayi fari,maganganun abba sunyi mata dadi domin abubuwan umma sun fara yawa.
Dakinsu Rafee'ah mummy tashiga tana fadin"wai ina sadeeyar take?"Rafee'ah dake waya da sayyid kasa kasa tayi saurin kashe wayar tana kallon mummy cikin rashin gaskiya,mummy wacce kallo daya ta mata ta tabbatar da sayyid take waya saboda mara gaskiya ko aruwa gumi yake,cikeda takaici tace"ban isa nafada miki kiji ba ko?sannan baki daina kula matsiyacin yaron nan ba ko?saboda kin rainani bakya ganina da gashi,wato kin riqa kin xama rikakkiyar kubewa right?"hawaye ne suka xubo ma Rafee'ah,tayi shiru tana sauraron maganganun da mummy ke fada marasa dadi,"ki rasa wanda xaki kawo gidan nan sai matsiyaci dan matsiyata saboda ban isa dake ba, nace ki daina kulashi kin k'i,me kikeso dani ne arayuwar nan?so kike bakin cikinku yayi ajalina?kun saka ni agaba kowacce takai munxalin aure amma babu saurayin arxiki".baki Na rawa Rafee'ah tace"dan Allah mummy kiyi hakuri".mummy tace"niba hakurinki nake bukata ba Rafee'ah,so nake ki tashi tsaye ki fahimci abinda nake son nuna miki,rayuwar nan ta canxa,yanxu ba kamar da bane da samari ke bin'yan mata,a wannan lokacin sai kin tashi tsaye kin dage sannan xaki samu,ki bud'e kunnuwanki dakyau ki saurareni "
"Duk duniya banida kamarku sannan babu wacce takaini son ganin cigaban ku,babban burina shine ku samu maxaje kuyi aurenku kuma ku huta kuji dadi,Amma hakan baxai yiwu ba sai kuma kun tashi tsaye kunyi kamar kunayi,abu nafarko shine inde bakya son ganin bacin raina kidaina kula matsiyacin yaron can,kiyi blocking Dinsa ki hada harda report,bana son ki sake kula shi koda amafarki,na biyu shine ki bud'e idanunki ki kalla wanda Eman ta kawo xata aura,duk da auran be yiwu ba amma Aliyu dan mukhtar marshal shahararren mai kudi ne wanda a kano an san da xaman shi,ki hanga ki sake kallon mijin da Salima xata aure shima dan hamshakin mai kudi ne,ki kalli fauxa wani irin jin dadi ta rasa,haka mariya wacce gabadaya xaman nigeria yayi musu kadan suna dubai suna cin duniyar su da tsinke,fisabilillahi har sai Na xauna ina nuna miki kalar mijin daxaki kawo gidan nan?Afiya ce kawai ke fahimta ta amma ku gani kuke na dameku da masifa,yanxu babban tashin hankalina shine inteesar tasamu miji ko kuma eman ta dawo gidan nan kuna nan xaune xata sake samun wani mijin,an fada miki haka iyayensu mata suka rungume hannu suka tankwashe kafafu,an fada miki haka kawai 'ya'yan hjy kwaise suke samun miji nagani na fada?Toh bari kiji anyi ittik'afi babu yaren daya kai shuwa arab bin bokaye da malaman tsibbu,tun su fauxa Na yara take tsuma su shiyasa yanxu abubuwan ke xuwar musu da sauki,duk da nasan wannan sakaci na ne kuma nayi alqawarin gyarawa kuma sai kun gyara ,dole sai mun hada karfi da karfe kafin mu cimma nasara".ajiyar xuciya Rafee'ah ta sauke batareda tace komai ba mummy tafita daga dakin tana fadin "ina xuwa "bedroom dinta takoma takira lambar aminiyarta wacce afarko tabata shawarar hadawa da bokaye tak'i,amma ayanxu tana jin xata iya komai domin samun daidaito arayuwar'ya'yanta.
Kausar ce ta kalli eman wacce hankalinta yayi nisa da inda suke tace"aren't we going to the cafeteria?"eman tace"sorry natafi tunani ne"Kausar tace"you should take it easy eman,everything happens for a reason,there's reason for and behind everything "asanyaye eman tace"thank you Kausar "lousiana pasta sukayi order da Oreo milkshake,Kausar dake kallon eman tana cakalar abincin tace"dan Allah kidaina sa damuwa acikin ranki,Allah yana gani kuma baya bacci shine xai miki maganin damuwarki ".
Eman tace"nagode Kausar"tana jin son Kausar na kara shigar ta,domin Kausar is the most understanding person she has ever come acrossed,babu ruwanta da poking nose  a lamarin mutum no matter how close you're sannan xata xauna tabaka shawara mai kyau idan ka bukaci hakan daga wurinta,she's indeed a friend in need wanda sukayi karanci a wannan xamanin,tace"eman nifa I've problem with medicinal chemistry,musamman drug synthesis "murmushi eman tayi tace"karki damu in shaa Allah yau zan fara koya miki,abun bawani wahala kawai maida hankali xakiyi "Kausar tace"awurinki gifted ne babu wahala,kede kinji dadi karatu baya baki wahala"haka suka cigaba da firar karatu sannan sukai sallah suka wuce practical class,yau karfe hudu sukayi closing,sai eman Tayi dialling numbar yaya Sadeeq domin tafada mishi xata wuce gida,shiru yayi yana sauraronta sannan yace"ban amince ki hau motar haya ba,kijira yanxu xanxo "yana kaiwa nan ya kashe wayar,saita bi wayar da kallon mamaki kamar shi take kallo,Kausar tace"dama nafada miki,baxai yarda kihau commercial ride ba,shiyasa nace xamuyi dropping dinki but you said no".
Eman tace"yace yanxu xaixo you can leave"hararar wasa kausar ta ma eman sannan tace "I'm going nowhere har sai yaxo ".suna cikin hira wayarta tayi ring,duk da kausar tayi mamakin ganinta da karamar waya amma batace komai ba,she believed if eman wants her to know the reason xata fada mata without asking,sallama sukayi kausar tashiga motarsu,eman tashiga motar yaya Sadeeq wanda ya hade rai,da dan mamaki ta kalle shi sai kuma ta mayar da kanta titi tana kallon moving vehicles,ganin ya dauki wata hanyar yasa taxaro ido tana kallon shi akaro na biyu,shima kallonta yake kasa kasa yana driving hankali kwance,tana son tambayar shi inda xasuje amma takasa,adaidai peristatal dinsu ya tsaya sannan yayi parking,still tana kallon shi cikeda mamaki,meya sa xai kawota wurin aikinshi?asanyaye yace"if you're done thinking xaki iya fitowa"jiki ba kwari ta fito tana bin bayanshi har su ka karasa office dinshi wanda haduwar shi ya tafi da imanin eman,ga pictures dinshi da ya fauxa dasu Anum,baki ta bud'e cikeda mamaki sanda taga old picture dinta awurin,wanda gabadaya ya manta dashi,ta kalleshi straight in the eye cikeda mamaki,me hotanta keyi a office din yaya Sadeeq?itace tambayar da xuciyarta ke mata,yayinda idonta ke watsa mishi tambayar da xuciyarta ke mata tana mishi kallon tuhuma....

Ya'll should manage this evening post babu yawa,kunsan har yanxu patient ce 🥹naga mssgs dinku I'll go through them in shaa Allah,thank you.
Zaynab Yusuf ✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now