PAGE 35

119 3 0
                                    

EMAAN........PAGE 35

Fauxa dake kwance ajikin Eman ce ta ɗago asanyaye tana kallonta carefully and attentively,tsantsar damuwa tagani shimfiɗe akan fuskar Eman,ga idanunta sun rine saboda kuka,gently take murxa hannun Eman dake rawa,tace"she'll be fine in shaa Allah"ajiyar xuciya Eman ta sauke sannan tace "we hope so,how's yaya Sadeeq doing?"hawayene masu xafi suka gangarowa Fauxa,tafara kuka instead of answering Emans question,can tace"he's not feeling better Eman,kullum da tunaninta yake kwana yake tashi,hakan na breaking heart dina but i don't know what to do"Eman tace"Allah ya bashi lafiya"ta fada atakaice tana jin tausayin Fauxa na ratsa xuciyarta,murmushi Fauxa tayi batareda tace komai ba,irin murmushin da hausawa ke ma laƙabi da kafi kuka ciwo,kallo ɗaya xaka mata kasan something is wrong with her,with a trembling voice tace"nikuma tawa ƙaddarar kenan".kallonta Eman ta dinga yi as if wanting to figure out something,tace"khair in shaa Allah"Fitowar Abba ce tasa Fauxa saurin goge hawayen dake xubo mata,ta gaisheshi cikeda girmamawa ,ya amsa yana tambayar"what are you doing here?"muryarta na rawa tace"Sadeeq passed out shine na kawoshi".cikeda damuwa Abba yace"Subhanallahi how comes?hope he's feeling better "shiru ta mishi tana kallon alameen wanda yake closing gap dinsu,ya matso kusa da Abba yana cewa"ga ward ɗin da yake can"yafaɗa tareda shigema Abba gaba,cikin rashin kuxari Sadeeq ya lumshe idanu thinking about alot of things,ayanzu he's feeling okay,ciwon kai ne kadai ke damunshi,gaban shine ya fadi sanda idanunshi suka sauka akan fuskar alameen,saboda yasan xuwan nashi ba alheri bane,yaxo ne kawai ya ƙara mishi damuwa akan sauran abubuwan dake damun xuciyar shi,saurin kawar da kanshi yayi gefe yana jin xuciyar shi na mishi xafi,yadda alameen ke trying hard to ruin his life ne ke bashi mamaki,gashi babu ɗigon imani acikin xuciyar shi,duk me tausayi idan ya kalli Sadeeq sai ya xubar mishi da hawaye,ya rame sosai kamar ba shi ba,tsayawa alameen yayi agaban Sadeeq yana sakin munafukin murmushi yace"ya jikin?"murya can kasa Sadeeq yace"what do you want?"alameen yace"Allah ya kara sauki,ga Abba yaxo duba ka" kallon banxa Sadeeq ya watsa ma alameen,sannan ya juya ya kalli gefen da Abba ke tsaye ya rungume hannu akirji yana kallonshi,yana kokarin mikewa xaune alameen yayi saurin mayar dashi ya kwantar yana cewa"you don't have to,just focus on getting better "yafada yana kallon Sadeeq straight in the eyes,asanyaye Sadeeq ya gaida Abba,ya amsa yana tambayar shi"ya jikin?meke damunka?"kallon alameen Sadeeq yayi atakaice yace"Bp na ne ya tashi"dan xaro ido Abba yayi yace"Bp?"ya maimata cikeda mamaki,alameen yace"damuwar aiki yasa aranshi,I've told him times without number damuwa bazata mishi maganin problems dinshi ba,dama haka mutane suke da hassada,tun da aka bashi multi million contract shikenan suka sashi agaba"Abba yace"Subhanallahi,wasu mutanen babu Allah aransu,Allah ya baka lafiya ya kareka daga sharrin su"da Amin Sadeeq ya amsa yana kallon alameen cikeda tsana,ji yake kamar ya shake alameen ya huta,alameen ya xauna yana tambayar "hope you're feeling better "yafada yana kallon Abba dake fita daga ward din,atsanake yake kallon Sadeeq sannan yace"this is just the beginning,kayi tunanin bansan abinda ke cikin xuciyarka bane?"yayi murmushi sannan yace"I'll always be 10 steps ahead of you fool"yana gama fadin haka ya fita daga ward din walking majestically,Sadeeq ya bishi da wani irin Kallo assuring himself dole ya tashi tsaye domin cimma burinshi,he won't allow alameen to defeat him,that he promise himself!.Abba ne ya biya both Sadeeqs and Ummas Bill,Eman was trying very hard ta tsaya akan ƙafafuwanta saboda yadda sukayi mata nauyi dakuma tsami ta shiga ward din da umma ke ciki,axaune taga Umma ta jingina kanta da bango tana kallon wuri daya alamar tunani takeyi,ajiyar xuciya ta sauke ganin Umma is doing okay,agefenta ta xauna tana ta kallon Umma dake kallonta itama,Sallamar alameen ce ta sauka akunnen Eman,ta dago da kanta asanyaye tana kallonshi xuciyarta na bugawa da sauri da sauri,saide kallo daya ta mishi ta dauke kai saboda yadda ya hade rai kamar bai taba dariya ba,ya sassauta murya sannan yace"Umma ya jiki?"murmushi Umma tayi tace"Alhamdulillah naji sauki"yace"Allah kara sauki"atakaice sannan ya fita daga ward din,Umma aka fara sallama after few minutes aka sallami Sadeeq,atare suka fito compound din asibitin,Sadeeq dake trying very hard kada ya kalli gefen da Eman take amma ya kasa,ya kwana biyu baiyi gamdaƙatar da kyakkyawar fuskarta ba mai sashi cikin farin ciki da nutsuwa,ta gefen ido yake kallonta kasa-kasa yana son ya mata magana,ganin ta d'auke kai daga kallonshi yasa shi sauke ajiyar xuciya,he knows right soyayyar Eman jarabta ce agareshi,ada datake kula shi ya na ɗan samu nutsuwa da kwanciyar hankali,banda ayanzu dayake jin opposite din hakan,wata banxar harara alameen ke watsa ma Sadeeq,yana ganin moves din Sadeeq da irin kallon dayake ma Eman,bayan sun gama sallama da fatan samun lafiya ga Sadeeq da Umma kowa ya shiga motar shi,saide har lokacin Sadeeq bai daina kallon gefen da Eman take ba,ya sauke ajiyar xuciya yana kallon titi,har suka je gida baiyi magana ba,ita ma Fauxa batace mishi komai ba,kowa da tunanin dake ranshi.Da mamaki Eman ke kallon Anty Habiba ta xabga uban tagumi tana kallon enlargement picture din Umma,sallamar Umma ce tadawo da ita daga duniyar tunanin data fada,ta kalli Umma cikeda damuwa tace"ya jikin?"xama Umma tayi tana sauke numfashi tace"da sauki"anty habiba tace"Allah ya kara sauki,typhoid dinne?"gyada mata kai kawai Umma tayi batareda tace komai ba,ta kalli gefen da Eman ke xaune tana kallon both of them,bayan sun gaisa Eman tashiga bandaki ta hada mata ruwan wanka,a bedroom ta tarar da Umma da anty Habiba wanda shigowar su ciki kenan,tace"Umma shiga kiyi wanka"umma dake cire hijab tace"toh "Eman tafita daga dakin xuwa kitchen,swallow tayi ma umma da vegetable soup,tana gamawa tashiga toilet tayi wanka saboda uban gumin data yi,tana cikin gyara dining Musaddiq yashigo yana cewa"anty Eman Abba nakira"samun kanta tayi da faduwar gaba,tace ma yaron"ok"sannan tashiga dakinta ta dauko dogon hijab har kasa tafita,a main parlour suka hadu da Afiya wacce kana kallonta kasan bata cikin nutsuwarta ,taci uban kuka kamar idanunta xasu fito waje,kallon juna sukayi Afiya tasaki siririn tsaki,Eman ma ta sakar mata tsaki domin tayi alkawarin bazata sake raga ma Afiya ba acikin gidan,kafaɗar Eman ta janyo baya tana watsa mata kallon tsana tace"uban wa kike me tsaki?"Eman tace"Uban wanda ya tsargu "cikeda hargagi Afiya ke cewa"kan bala'i ni kika xaga?wallahi saina ga uban daya tsaya miki a garin nan,saina koya miki hankali,sai na nuna miki yar iska ce ni ta gaske "atsanake Eman tace"nikuma zan nuna miki ni me hankali ce da tarbiyya"dariya Afiya tayi tace"tarbiyya my foot,har kinada bakin ambatar kalmar tarbiyya?wacce tagama yawan iskancinta agarin nan,babu hotels da clubs din da baki je ba,idan kin manta bari na tuna miki dalilin fasa aurenki da Aliyu ".saurin dakatar da ita Eman tayi tace"not a single word against my character ".dariya maganar Eman taba Afiya tace"character manya,karki manta I still have those pictures of you"saurin runtse idanu Eman tayi jin Afiya na fama mata tsohon ciwon data birne acikin xuciyrta,Afiya tace"I'll use them against you Eman har tashin duniya,keda aure sai a lahira idan anayi,zan cigaba da amfani da pictures dinki ina lalata duk wata maganar aurenki,that I promise you,sai kinyi dana sanin sani na arayuwarki "cikeda karfin Hali Eman tace"we shall see,nikuma xan shayar dake ruwan mamaki,just wait and watch"Afiya tace"you should wait and watch abinda zan miki Eman,kin shigo gonata dan haka you'll pay for the consequences "Eman tace"xamu ga wanda xaiyi hakan tsakanina dake banxa kawai boyfriend snatcher,taxi no garage,magana dake ma bata lokaci ne dakuma xubar mada kai mutunci".Afiya tace"dani dake xamuga wacce duniya xata ma shaidar hakan"ko tsayawa sauraronta Eman batayi ba tawuce part din Abba xuciyrta na tafarfasa,kwafa Afiya tayi tana cin mugayen alwashi akan Eman.da sallama tashiga falon wanda baka jin karar komai sai AC,gabanta ne ya fadi sanda taga alameen xaune agefen Abba,ta xauna asaman carpet bakinta na rawa tace"Abba gani"yana murmushi yace"Eman tashi ki xauna "yana nuna mata saman kujera,xama tayi tana massaging hannayenta ga tarin damuwa dake cikin xuciyarta,Afiya tayi nasarar dawo mata da tunanin abinda ta cire daga babin rayuwarta,hawaye ne suka cika mata idanu,akan Auren Aliyu aka lalata mata image,aka xubar mata da mutunci da qima a idon mutane,Abba yace"kina jina?"asanyaye ta gyada mishi kai hawaye na zubo mata,yace"alameen yaxo min da magana mai girma atsakanin ku,yaxo min da maganar Aure,hakan ya min dadi fiyeda misali saboda babban burina shine na aurar dake ga wanda ya cancanta,kuma Alhamdulillah alameen ya cancanta fiyeda yadda ake xato da tsammani,saide duk da haka ina so naji ta bakinki,shin kin amince da auren nashi?"ahankali Eman ta lumshe idanu tareda budewa suka sauka asaman fuskar alameen wacce babu d'igon rahma asaman ta ,wani mugun kallo yake wurga mata na xallar kiyayyah,Ganin tayi shiru yasa Abba cewa"I'm listening Eman,kin amince ko kuma a'a"bakinta na rawa Sosai yayinda hawaye ke xubo mata tace"na amince"tana ji kamar ana barbaɗa mata barkono acikin xuciyar ta,dalili biyu ne yasa ta amince da auren alameen,nafarko shine yaya Sadeeq wanda take so ya cireta daga cikin rayuwar shi gabadaya,domin soyayyar shi agareta Babbar masifa ce da tashin hankali wacce baxata haifar musu da ɗa mai ido ba,dalili na biyu kuma Afiya ce da kuma duk wanda yakeda sa hannu akan fasa aurenta da Aliyu,dama auren ne basaso tayi,shiyasa tayi amfani da wannan damar domin girgixa xukatan makiyanta,kafin xuwan lokacin da xata yanke hukunci akan auren nasu domin babu yadda xa'ayi su dawwama akarkashin inuwa daya,that's impossible saboda itama yanxu tafara jin kiyayyar shi acikin xuciyar ta da ruhinta .cikeda farin ciki Abba yace"Allah ya muku Albarka,Allah ya albarkaci aurenku ya axurtaku da xuri'a dayyiba "yacigaba da cewa"nayi magana da Alhaji Muhammad (elder brother din Abba dake gombe)sun ce xasu xo shida Uncles dina guda uku domin adaura auren bayan sallar azahar din gobe"ya kalli gefen Eman sannan yace"bance ki  fada ma kowa wannan maganar ba,kina jina?"asanyaye Eman ta gyada mishi kai batareda cewa komai ba,Abba yace"maganar lefe da duk wani abu xai yi miki in shaa Allah,yace baya son taro amma inason naji naki ra'ayin,idan kinaso sai ahada ayi dana afiya"saurin girgixa kai tayi tace"banaso"Abba yace"ok,xaki iya tafiya"mikewa tayi tafita daga part din Abba tana jin jiri yana dibar ta,tayi saurin xama a main parlour hawaye masu xafi suna zubo mata, tasan she's very unfortunate in life shiyasa kullum take cikin bakin ciki da damuwa,ta manta yaushe rabon datayi dariya,May be she's not meant to be happy in this life,goge hawayen tayi takoma part din Umma,lokacin suna xaune suna cin Abinci,Umma tace"Ina kikaje?"asanyaye Eman tace"Abba ne ya kirani "daga haka bata sake cewa komai ba tashiga bedroom dinta tayi locking tareda fadawa saman gado ta fashe da matsanancin kuka mai karya xuciyar mai sauraro,kuka takeyi da iya karfin ta wanda yake fitowa daga kasan xuciyrt me balbala da wuta,ta dade tana kukan kafin wani wahalallan bacci ya dauketa.Cikeda damuwa alameen yakoma part dinshi yana jin kirjinshi na mishi nauyi,babban tashin hankalinshi shine yadda Mami zata dauki maganar auren shi da Eman,ganin Eman kadai a part dinshi na tayar mata da hankali balle taji an daura mishi aure da Yarinyar,Sosai ya shiga cikin damuwa gumi na karyo mishi takoina,sallamar Mami ce tasa gabanshi ya yanke ya fadi,ya kalleta kamar marar gaskiya sai xaro ido yakeyi,xama tayi tana kallon shi keenly tace"meke damunka?"atakaice yace"bakomai"tare da kawar da kallonshi daga gareta,Numfashi mai nauyi ta sauke sannan tace "ni xaka kalla tsabar idona kamin karya alameen?"runtse idanu yayi yana jin saukar maganar tata kamar saukar ruwan xafi acikin xuciyar shi,tace"bana son iskanci,kafada min meke damunka"dan xaro ido yayi yace"I'm having a severe headache "cikeda damuwa ta tab'a wuyan shi to feel his temperature even though bata yarda da maganar shi ba,wani abu ne keta xarya acikin ranta yahanata nutsuwa,ji take kamar wani abu na shirin faruwa da ita,tace"anya kuwa?mecece damuwarka bayan haka?"shiru yayi yana kallonta cikeda mamaki,saboda Mami mutum ce me saurin d'ago mutum shiyasa taxama restless,he's quite sure jikin tane ke bata wani abu is going to happen which is true,Shide fatan shi Allah yasa tayi overcoming situation din,ta dade Sosai sannan takoma part dinta jiki asanyaye kamar ba energetic hajiya kwaise ba,gabadaya jikinta yayi la'asar gwiwoyinta sunyi sanyi.da kallo yabita har ta kurema ganin shi,ya sauke ajiyar xuciya yana kallon kiran yasmeen saide babu halin dagawa,itama kamar tasan abinda zai faru sai kiranshi takeyi which is unlike her.Kashe wayar yayi tareda kifeta ya kwanta yana kallon POP yana tunani,yadda yaga rana haka yaga dare yakasa rufe idanunshi na second daya saboda damuwa,tabangaren Eman kwana tayi tana kuka wanda ya saukar mata da headache mai tsananin da fever,jikinta yayi bala'in xafi hakoranta sai bugar juna suke suna bada wani irin sauti,kallo daya zaka mata ka xubar da hawayen tausayi,tabangaren  Umma ma yadda taga rana haka taga dare,ciwo ne ya taso mata sosai adaren kamar jiya,ga mamakinta kuma asubah nayi taji tafara samun sauki,Abba kuwa baccin shi yasha mai dadi saboda murna da farin ciki,cikeda damuwa Fauxa da Sadeeq suka kwanta kowa ya kalli bangare daya sun kasa bacci,kowanne da tunanin dake ranshi,akarshe Sadeeq ya yanke hukuncin fadama fauxa gaskiya idan gari ya waye,sannan xai je har gida ya sanar ma Abba halin da yake ciki,yasan Abba mutumin kirki and the most understanding person ever,definitely xaiyi reasoning dinshi.hakika wannan daren ya kafa mummunan gurbi axukata masu yawa,domin hajiya kwaise juyi kawai takeyi tarasa dalilin shigarta damuwa mai tsanani babu gaira babu dalili!.....Hausawa sukace rana bata karya saide uwar diya taji kunyah,asanyaye Sadeeq yake kallon Fauxa wacce fitowarta kenan daga wanka,fuskarta ahade take shafa mai da tunani masu yawa,Sadeeq ne yayi karfin halin xama agefenta tareda riqo hannunta,can kuma ya durkusa akasa yana kallon fuskarta wacce already taciko da ruwan hawaye,shima hawayen yaji yana xubo mishi,but he can't hide his pain and feelings anymore,yace"I'm sorry fauxa..."sai kuma yayi shiru yana kallon yadda ta fashe da matsanancin kuka,saurin rungumeta yayi yana jin tausyinta na ratsa shi,but he can't help it,dole tasan gaskiyar abinda ke faruwa,murya very low yace"kiyi hakuri Fauxa,nasan ban kyauta miki ba,like I always said ban taba tunanin I'll love someone else ba apart from you,ban taba tunanin hakan ba koda kuwa amafarki amma kana naka Allah yana nashi,kuma Na Allah shine daidai,dan haka I want you to accept this with good faith,you're my first love kuma babu abinda xai canza hakan,ina kaunarki fiyeda yadda kike xato da tsammani,inason ki ajiye hakan acikin ranki,kada ki yadda da abubuwan da mutane xasu fada miki,wallahi ina sonki fiyeda yadda nake son kaina..."dakatar dashi tayi tahanyar cewa"go straight to the point "numfashi mai nauyi ya sauke sannan yace"ki shirya xamuje wurin Abba,xai miki bayanin koma menene"da mamaki ta dinga kallon shi tace"Abbana kuma?meya hada Abba da wannan maganar ?"shiru ya mata saide har lokacin yayi wrapping hannunshi tightly da jikinta,tace"I'm asking you,miye hadin Abbana da buduwarka?"nan ma shiru yayi mata,ta bude baki xata kuma tambayar shi for the third time yayi saurin rufe bakinta with his lips trying to give her a deep snog, hankade shi tayi gefe tana mishi wani irin kallo masu ma'ana da yawa,tana kuka tace"tell me Sadeeq,meyasa Abba ne zai fada min wacce kake so?!!"tana ihu da iya karfinta,jijiyoyin kanta sun mimmike jikinta na rawa,toilet xai shiga tayi saurin shan gaban shi tana cewa"why are you silent?kafada min miye hadin Yarinyar da Abbana?what's my relationship with her?"ta tambaya tana sake rushewa da kuka tana cewa"speak up Sadeeq,mecece alaqa ta da ita"ta fada da karfi tana kuka,rikicewa yayi yana riqo ta tana xillewa,tace"stop touching me sadeeq,don't you dare do that again"tafada tana xaro ido waje,with so much rage and anger take maganar,wuyan rigarshi ta damke tana cewa"tell me my relationship with her,fada min alaqa ta da Yarinyar,cos there's no way I'm not related to her,cin amanar daxaka min kenan Sadeeq?duk irin soyayyar dana nuna maka,duk dinbin kaunar danake maka,duk sacrifices din dana maka arayuwa ta wannan hanyar xaka saka min??..."shiru tayi tana jin Numfashin ta yana sama,ta fadi kasa tana maida numfashi dakyar,saurin rikota yayi yana cewa"calm down fauxa"da dukkan karfin da Allah ya bata ta hankade shi can gefe kasancewar baida lafiya babu wani strength atare dashi,kuka takeyi Sosai tana cewa"dama sun fada mini namiji ba dan goyo bane,amma na banxatar da maganar su,gashi tun ba'aje koina ba you betrayed me,now tell me wacece?ya sunanta?"tafada tana tashi tsaye without minding towel dinta dake yashe akasa,kanta ya barbaje jikinta sai rawa yake,key din kofar ta cire ta rufeshi ta waje sannan ta sauka kasa xuwa kitchen,wata yar madaidaiciyar wuk'a ta dauko ta koma dakin,gaban Sadeeq ne yayi mummunan faduwa ganinta da wuka tana pointing dinshi,stammering din dole yafara"fafffauxxxa...."ya ambaci sunan dakyar wasu munafukan gumi suna karyo mishi,wurga mishi wukar tayi tafadi daidai saitin kafafuwanshi sannan tace "use this knife and kill me after telling who the girl is"tafada xuciyarta na kekashewa,ya kalleta ya kalli wukar sannan ya dauki wukar ya ajiye agefe,bai taba tunanin haka notin kan fauxa ke kuncewa ba idan tana fushi,gaban shi sai faduwa yake jikinshi na rawa,ya dauki towel dinta yace"sa wannan first ".wani mugun kallo ta wurga mishi sannan tace "kafada min sunanta nace!!!!"tafada hakan da karfin gaske tana riqe kanta tareda sulalewa kasa tana cigaba da dirxar kuka,atsorace ya karasa inda take yana cewa"I'm sorry fauxa,I'm sorry fauxa"hannunshi na rawa ya jawota jikinshi hugging her tightly tareda fashewa da kuka mai tsanani,kukan tausayin fauxa yakeyi ganin taxama kamar sabuwar mahaukaciya tun kafin tasan wacce yake so din,ya xatayi kenan idan taji Eman ce?sosai take kokawar kwace kanta daga jikinshi amma hakan ya gagara,saboda karfin daya samata bana wasa bane ya riqeta gam ajikinshi,even at that moment he was trying really hard to get close to her,lamarin daya girgixa Fauxa kenan for the first time taji haushin shi mara misaltuwa acikin xuciyarta,tayi kuka,tayi cixo tayi ihu hardasu xagi amma ko gexau Sadeeq wasn't listening to her,Shide burinshi shine ya rage mata radadin dake cikin xuciyarta,kuma hakan dayakeyi is the best way dayake wiping away fauxas anger,saide unfortunately awannan ranar jitayi kamar yana kara rura wutar dake balbala acikin xuciyrta,sun dauki lokaci mai tsaho ahaka,tun fauxa na kuka har ta daina,ta cigaba da sauke ajiyar zuciya wani matsanancin ciwon kai yana saukar mata,ta gefen idanu wani karamin hawaye yake xubo mata,idanunta sunyi nauyi sai kallon fuskar Sadeeq takeyi taga shima bawai yana cikin hayyacinshi bane,ta runtse idanu tana jin wata gajiya na saukar mata gashi jiya batayi bacci ba,Jiki asanyaye ya dauketa kamar baby zuwa cikin bandaki ya mata wanka sai kallonshi take tana hawaye,ga mamakinta taga ya dauko mata wata doguwar rigar Abaya da veil, har yanzu yana kan bakarshi na xuwa wurin Abba kenan?after all abubuwan data yi yanxu he still have the audacity and nerves din ciro mata kaya har dasu veil,alokacin ta tabbatar da Sadeeq is madly in love with the girl wacce ta tabbatar tana da alaqa da ita,wasu xafafan hawayene suke xubo mata,abu daya ne yasa xata bishi sai don sanin wacece yarinyar,amma tayi alkawarin rabuwa da Sadeeq koda hakan xai xama ajalinta,he didn't deserve her,yana samata kaya take wannan tunanin har ya kammala shima ya shirya,murya adashe tace"pack my things Sadeeq "da mamaki ya juyo yana kallonta,tace"kana tunanin xan cigaba da xaman aure dakai after finding out who the girl is?"tacigaba da cewa"aure ya kare tsakanina da kai the moment Abba ya fada min whoever the girl is "ta gyada mishi kai alamar tabbatarwa,xama yayi agefen gado tareda riqe kanshi,me fauxa take nufi da hakan?kenan xab'a xaiyi tsakanin ita ko Eman?wasu gumi ne suka xubo mishi,ya rasa yadda xaiyi alokacin,he love them both with all his heart and soul,tayaya xai iya xab'ar daya acikinsu????????????????Xuwan su Alhaji Muhammad da kawu Mallam ne ya daure ma kowa kai,hajjo dasuka tattauna maganar da ita sai farin ciki takeyi, itama taso yima Abba xancen sai kuma tafasa sanin halin yaran xamani,amma wannan hadin yayi mata babu karya,sabuwar atamfarta tasa ta kashe dauri sai washe hakora take,hajiya kwaise dake gabatar mata da breakfast sai kallonta take,can dai ta kasa hakuri tace"meke faruwa hajjo?naga su kawu mallam sunyi xuwan baxata,gashi  sai farin ciki kikeyi har da sa sabon kaya"murmushi hajjo tayi tace"ke kwaise ki rufani ki saya ni,na mutu maxa sukaini ba mata ba,ashe duk abinda nakeyi agidan nan idonki na kai"murmushin yak'e Mami tayi tace"ba haka bane hajjo"hajjo tace"to yaya ne?"ganin baxata ji wata magana daga bakin hajjo ba yasa takama bakinta tayi shiru saide har lokacin tana cikin damuwa mai tsanani,jiki ba kwari ta fita daga part din,hajjo ta rakata dawani mugun kallo.....part dinta takoma tana safa da marwa,tunani ya sha kanta Sosai tana mamakin meke faruwa agidan wanda batada masaniya akai,can dai ta mike tashiga part din alameen wanda ke kwance har lokacin saboda xaxxabin daya rufeshi,yana kwance ya rufe kanshi cikin duvet yana sauke ajiyar xuciya ahankali,bedroom dinshi tashiga tana cewa"hala wani daren xa'a sake maka???".sai kuma tayi shiru tana kallon yadda ya shige cikin duvet kamar dai ba lafiya ba,da sauri ta janye duvet din tana kallon fuskar shi dake fitar da k'ananun gumi,tace"what's wrong with you?"tana shafa forehead dinshi,sosai taji xafi ta xaro ido tana cewa"sannu dear,meke damunka?"shiru yayi baice komai ba tashiga toilet ta hada mishi ruwan wanka,sosai yaji dadin wankan yafito har lokacin tana dakin,xama yayi yana kallonta ganin ta nutsa cikin kogin tunani,ya kalli gefenta data ajiye qaton tray mai d'auke da breakfast,asanyaye yace"mami tunanin me kikeyi?"kallonshi tayi tace"how are you feeling?"yace"better,tell me mami meke damunki?"ajiyar xuciya ta sauke sannan tace"your paternal uncles are here,ni nasan akwai abinda ke faruwa wanda banida masaniya akai"lumshe idanu yayi yana jin babu dadi aranshi,ji yake kamar ya fada mata sai kuma ya fasa ya ce"khair in shaa Allah"jijjiga kai tayi asanyaye tace"have your breakfast "tana nuna mishi tray din,ko kadan baya jin yunwa saboda yayi loosing appetite dinshi gabadaya saboda damuwa da bakin ciki,ji yayi cikin shi ya cushe kamar an jefa mishi dutse aciki,ganin yadda ta damu yasa yace"ok mami "yafada hakan yana bude press dinshi itakuma tafita daga dakin domin bashi damar shiryawa,cikin wasu black kaftan ya shirya kamar yadda xuciyar take bakikkirin haka yau ma take bakikkirin agareshi,baxai taba mantawa da wannan ranar ba mai cikeda bakin ciki arayuwar shi .ko kallon gefen da tray din yake baiyi ba ya fita daga part dinshi jiki ba kwari,gabadaya ya rasa kuxarin shi,parlorn Abba ya shiga da sallama,suka gaisa da Abba da uncles dinshi,ya xauna acan gefe yana sauke numfashi da karfi yana tunanin is he doing the right thing?xuciyar shi tayi mishi tambayar da shi kanshi baida amsar ta,maganganu  suka tattauna sannan suka yanke hukuncin daura auren bayan an idar da sallar azahar domin lokacin karfe sha daya ne na safe.hajiya kwaise dake lab'e ajikin kofar parlorn ta buga siririn tsaki domin babu abinda take iya jiyowa kasancewar kasa-kasa suke magana kamar munafukai,a main parlor ta zauna tana jiran fitowar alameen domin jin abinda ke faruwa.Umma ce ke Kallon Eman asanyaye wacce ke kakkkarwa cikin bargo,jikinta kamar garwashi saboda tsananin xafi,itama ba lafiyar gareta ba balle tayi ma Eman din wanka duk da tasan hakan xai taimaka mata sosai,tea mai kauri daya sha madara ta sa musaddiq ya hada ma Eman,dakyar ta mikar da ita xaune har lokacin Eman rawar sanyi takeyi,Umma takai cup din bakinta tana cewa"drink pls"ahankali Eman ke shan shayin har ta shanye gabadaya gumi nata xubo mata,cikeda dauriya Umma ta hada mata ruwan wanka sannan ta taimaka mata xuwa bandakin,kujera tasa musaddiq ya kawo mata har cikin toilet dan baxata iya tsayuwar ba,axaune tayi ma Eman wanka tadaura mata towel sannan ta kwantar da ita agefen gado,riga mai kauri tasa mata sannan ta bata magani ta rufeta da bargo,xama tayi tana sauke ajiyar xuciya saboda nauyin da kirjinta ya mata,tana ta sauke numfashi ahankali tana jin kamar xai tarwatse saboda axabar dayake mata .Nasiha mai ratsa jiki sukayi ma alameen wanda gabadaya ba sauraronsu yakeyi ba,he was lost in thoughts,Mami da yasmeen ne makale acikin xuciyar shi,yana tunanin yadda Mami xatayi reacting saida gabanshi ya fadi,ya tabbatar she won't take it lightly with him,sun dauki 40minutes kafin ya mike jiki asanyaye ya koma part dinshi kamar yadda su Abba suka umarce shi lokacin karfe 12 saura,ganin Mami xaune afalon shi yasa shi runtse idanu,ji yayi kamar ya koma saide kafin yayi hakan suka hada ido,babu yadda ya iya dole ya xauna yana faking smile yace"Sannu da hutawa mami "tace"Yawwa,tell me what are you discussing about?"shiru yayi nawani lokaci sannan yace"nasiha suka min"ta maimata kalmar nasiha sannan tace "ban gane nasiha ba"goge gumin daya xubo mishi yayi yace"nasiha dai dakika sani mami,ta bin iyaye dakuma xamantakewa "daga haka bai sake cewa komai ba,ya lumshe idanu yana jin so many things going through his mind,yana nan xaune aka kira sallar axahar,gaban shi ne yayi mummunan faduwa lokacin dayaji ana kiran sallar,turkashi! Ya ambata gumi suna wanke mishi fuska,dakyar ya Mike yayi alwala suka fita xuwa masallaci,ga mamakin shi yaga motar Sadeeq a compound dinsu,kafin yagama digesting hakan ya hango Abba da Sadeeq a tsaye suna magana,gaban shine yayi mummunan faduwa,ya nufesu da sauri saide kafin yakarasa suka fara tafiya xuwa masallacin yana bin su a baya,su Abba da kawu Mallam na daga gaba-gaba a jam'i,Ana idarwa kawu mallam ya yafada ma Liman akwai daurin aure,babu bata lokaci aka daura Auren Fatima Lameen Abdulfattah da Muhammad Alameen Abdulhameed Abubakar Safana akan sadaki naira dubu dari biyar,wanda Abba dakanshi ya bayar da kudin,Sadeeq dake baya ya riqe kai yana jin kamar an bude brain dinshi ana daka aciki,duhu ne ya mamaye mishi idanu,ya yanke jiki ya fadi tareda sakin wata iriyar firgitaciyyar kara,da sauri attention ya dawo kan Sadeeq wanda baya numfashi,kawu mallam yace"get the car,he isn't breathing "!.......



Dedicated to my lovely Mum Ummu faisak💕💕

Zaynab Yusuf✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now