PAGE 41

100 4 0
                                    

EMAAN......PAGE 41

   Umma dake kallon emaan ko ƙiftawa babu tace"May Allah the most high continue to guide and protect you daughter,Allah ya miki albarka...."emaan was speechless alokacin,hakan yasa hawaye masu xafi suka xubo mata,these words are her favourite words aduniya,kuma akullum burinta shine ta riƙa ji suna fitowa daga bakin umma 24/7 which she believed they'll change her life for the better,ƙaramin murmushi tayi wanda ya fito da tsantsar kyanta,dimples ɗinta ne suka lotsa ciki dasuka kara ma fuskar ta kyau fiyeda misali,takalli umma da manyan idanunta wanda suka cika da ruwan hawaye,tace"thank you umma"umma tace"don't thank me emaan,wannan kalaman haƙƙinki ne danayi depriving for good 22 years,daga haihuwar ki xuwa yanxu kenan,I'm sorry daughter,I'm sorry for everything...."ta fada tana riƙo hannayen emaan masu kyan kallo,emaan couldn't control her tears,first time in so many years taji a bit of farin ciki acikin xuciyar ta,bata ce komai ba illa shigewa jikin umma datayi tana sauke ajiyar xuciya,tana jin ɗumin jikin mahaifiyarta wanda bata samu damar ji ba alokacin ƙuruciya,hakan yasa umma tayi wrapping hannayenta ajikin emaan hawaye masu xafi na xubo mata domin lokaci ne daya kamata su sake shakuwa da juna,lokaci ne daya kamata su ƙara fahimtar juna,umma tace"it's okay emaan,stop crying kinji ko?"asanyaye emaan ta gyada kai feeling a bit different,babu soyayyar data kai ta uwa da ɗa aduniya,it's the purest form of love ever,umma ce tayi breaking hugg din tana cewa"nasa habiba tayi depositing kudin da babanki ya baki into your bank account...."gyada kai emaan tayi tace"umma har yanxu fushi yake dani..."runtse idanu umma tayi tace"enough emaan,je ki fara hada kayan naki kinji?"mikewa tayi jiki asanyaye tashiga bedroom,umma ta fashe da matsanancin kuka mai karya xuciyar me sauraro,tasan relationship din emaan da babanta baxai taba gyaruwa ba,Lameen baxai taɓa canxawa ba sannan baxai ƙaunaci emaan ba kamar yadda yake ƙaunar Sultana da Ali,she's a victim of forced marriage wanda take ɗanɗanar xafin shi har yanxu.asanyaye emaan ke haɗa documents dinta,tana yi hawaye suna xubo mata,she's just imagining irin rayuwar da xatayi a London tare da alameen wanda yayi detesting dinta beyond imagination,tana hangoma kanta bakar wahala mara misaltuwa,tana hango ma kanta bakin ciki wanda yafi na yanxu datake ciki,saboda dalilin aurenta da yayi kenan domin ya ƙunsa mata takaici ya jefa rayuwar ta cikin matsala,goge hawayen tayi dalilin shigowa dakin da akayi,ta ɗaga ido tana kallon kausar cikeda mamaki taga murmushi mai kayatarwa asaman fuskar ta,wasu hawayen taji sun sake xubo mata,she'll surely miss her friend,xama kausar tayi with excitement tace"you like the surprise?"gyada kai emaan tayi still tears na dropping from her fluffy eyes,kausar tace"Mrs  kuka shine sunan daya dace dake"goge hawayen emaan tayi tace"thank you for coming "kausar tace"yanxu umma ke fadamin good news,I'm so happy for you kawata,Allah ya sanya alheri,even though xanyi missing dinki Sosai "kallonta emaan keyi can tace"I'll miss you more"daga haka taje kitchen ta hado ma kausar drinks dasu snacks,kausar na snacking tana gisting emaan akan abubuwa dayawa,emaan saide ta xaro ido idan abun mamaki ne ko kuma ta yi karamin murmushi idan abun dariya ne,na hawaye kuma ta xubar da fiyeda misali tunda xubar hawaye is her favourite thing to do,kausar ce tayi assisting dinta suka hada every important thing din ta,Umma tashigo dakin with smile all over her face sannan tace"lunch is ready".a parlorn umma suka ci abincin even though emaan bawani ci tayi ba,kasancewarta picky eater kuma batada cin abinci Sosai,umma ta kalli ɗan abinda taci tace"wa kika bar ma sauran?"marairaice fuska emaan tayi tace"I'm full"kallonta kawai umma tayi tace ma kausar"don't mind your silly friend,ki ci abinci ki Sosai kinji ko"gyada kai kausar tayi tana sakin karamin murmushi,itadai emaan na xaune saman kujera tana aikin tunani.Five days after Umma tashigo dakin emaan jiki asanyaye tanata kallon emaan wacce ta rame Sosai,ga damuwa mai yawa atattare da ita,most times xaka sameta ta xurma cikin duniyar tunani musamman yanxu da sauran kwana biyu tafiyarta.misalin k'arfe 9 ne na daren Friday,xama umma tayi tace"emaan"dagowa emaan tayi tana kallon umma saide anyi sa'a babu hawaye akan fuskarta,ajiyar xuciya umma ta sauke sannan tace"Abba na kiranki"daga haka ta janyo dogon hijab ta ba emaan tasaka sannan ta rike mata hannu suka shiga parlorn Abba wanda bakajin motsin komai sai karar Ac kamar babu kowa aciki,ga mamakinta kuma taga Abba da hajjo na xaune agefe daya,dayan gefen kuma Mami na xaune ta hade rai tana kallon direction dinda Abba yake,xama Umma tayi asaman kujera emaan kuma ta xauna akasa yayinda gabanta ke tsananta faduwa,batasan meyasa take having strange feelings ba idan taga Mami,tana tsintar kanta cikin firgici da damuwa mara misaltuwa koda hada ido suka yi bisa kuskure,wani tsoron mami ne ke shigar ta dagasken gaske,saboda dama can mami is not that friendly with her balle yanxu da abubuwa suka faru...gyaran murya Abba yayi yace"emaan kina jina?"gyada kai emaan tayi hawaye na sauko mata,Abba yace"na aminta da tarbiyyar da muka baki,nasan baxaki watsa mana kasa a ido ba,nasan what you're capable of doing dakuma wanda baxaki iya ba,na sanki da gaskiya da rikon amana,hakaxalika ban sanki da karya ba da rashin gaskiya,akullum ina farin cikin kasancewar ki ƴa agareni,I'm very proud to call you my daughter,nasan baxaki bani kunyah ba emaan,amma inason ki dage fiyeda yadda nasanki da jajircewa akan abu,kiyi hakuri ki xauna da mijinki lafiya,ki mishi biyayyah daidai gwargwadon ikonki,Fatima tayi kokarin nuna miki example yanxu xamu ga kin dauka ko kuma watsi kikayi da su,amma inada yaƙinin kin dauka kuma xakiyi fiyeda yadda take min,idan kinsamu kanki cikin matsala don't hesitate to call me,know that I'll always be there for you,har ixuwa ranar da Allah xai dauki raina..."kuka emaan keyi mara sauti tana jin maganganun Abba suna ratsa xuciyar ta,hajjo ta ɗora da cewa"kamar yadda abdulhameed yafaɗa mun yaba ƙwarai da hankalinki dakuma tarbiyyar ki,nasan baxamu samu matsala dake ba,tuntuni nafaɗa ma Abbanku idan aka samu matsala toh daga wurin alameen ne,saboda shine baya ganin kowa da gashi ya raina kowa,ko ni dakike gani sai nayi mishi da gaske yake shiga taitayinsa,magana kaɗan xakuyi kaji ya danno maka xagi wai shi bature,to nabi mango park da gudu ba wando ƙarewar turanci"wani kallo Mami tayima hajjo tana jin baƙin ciki mara misaltuwa yana shaƙe mata wuya,hajjo tace"kalleni dakyau kwaise,baki dai Allah ya tsaga yaba kowa idan abinda na faɗi bai miki ba kina iya gyarawa"cikeda takaici mami tace "ni banida abin faɗe balle na gyara ma wani"hajjo tayi murmushi tace"ga maganganu nan cike da bakinki, ki fada kar su kashe ki"murmushi Abba yayi yace"idan kwaise nada magana kiyi, emaan kamar ƴa take awurinki,ke me mata nasiha ce adaidai wannan gaɓar daxata fara sabuwar rayuwa"shiru mami tayi without saying a single word,Abba ya kalli emaan yace"flight dinki gobe na dare ne,amma ki shirya 6 hours before departure,kinga tun da yamma xamu je airport "daga haka emaan ta mike jiki asanyaye takoma part dinsu har lokacin kuka takeyi...hajjo tace"Allah sarki rayuwa,Allah ya ƙaddara saduwar mu"da amin Abba ya amsa yana jin wani iri acikin ranshi.Hajjo tace"kira min alameen nayi mishi tatass,xuge shi xanyi kamar xogale akan yarinyar mutane,ka sanshi dai da baƙin hali"murmushi Abba yayi yace"yanxu kuwa xan kirashi,baƙin hali kuma da kike magana ai baxai mata ba tunda shi yaxo nan kamar xaiyi kuka yana neman aurenta"takaici ne yasa hajiya kwaise galla ma bango harara,hajjo dake kallonta tace"saide ayi ma bango,saboda ɗana yafi ƙarfin a harareshi ballantana ni"Shide Abba murmushi yakeyi har lokacin da alameen yayi picking wayar,murya can kasa ya gaida Abba,hajjo tace"kaga irin rainin ko?ko takaina baibi ba balle ya gaisheni"alameen yace"hajjo ikon Allah ai bansan kuna kusa ba"asanyaye Abba ya gyada mata kai tace"to ya kake?ya aikin kuma"yace"alhamdulillah hajjo,nayi kewar ki"tabe baki hajjo tayi tace"ba wannan maganar na kira muyi ba,nakira ne na ja maka kunne akan ƴar mutane,ka dubi girman Allah ka riqe amanar da muka damka maka da hannu bibbiyu,kaga rayuwar emaan abar tausayi ce,yanxu ne yakamata taji dadi agidan miji,ka riketa da mutunci kana jina ko?idan ba haka ba?".asanyaye yace"idan ba haka ba sai me?"hajjo tace"har garin xanxo naci maka mutunci"tayi ƴar dariya sannan tace"ka dai ji abinda na fada maka"murmushi yayi yace"Toh hajjo naji "tace"Allah ya maka albarka"daga haka ta mike tabar part din,saida Abba ya mishi nasiha sannan ya kashe wayar yana kallon Mami wacce damuwa ta cika ma xuciya,murya atausashe yace"calm down Fatima"kallon shi tayi tana mamakin kiranta dayayi da asalin sunanta,yacigaba da cewa"I totally understand you Fatima,you might not like this marriage and that's okay,abu daya ne bana so kiyi shine kisa damuwa acikin ranki na babu gaira babu dalili,I promise you xakiyi alfahari da auren nan"hawayen datake kokarin dakatarwa ne suka xubo mata,jikin Abba ne yayi sanyi yanata kallon ta saide bai sake cewa komai ba.suna shiga parlorn umma ta kalli emaan tace"kin daiji abinda Abba ya fada miki"asanyaye emaan ta gyada kai batace komai ba taxauna tana kallon anty habiba wacce xuwanta gidan kenan,tace"Anty ina yini?"murmushi anty habiba tayi tace"lafiya kalau amarya"umma ta xauna tana cewa"ashe xakixo din,nayi tunanin sai gobe"girgixa kai anty habiba tayi tace "a'a,ina son muyi magana Sosai da emaan ne,kinsan xa'a dade ba'a hadu ba"asanyaye umma ta gyada kai tana jin babu dadi acikin ranta,xatayi missing ƴarta beyond imagination,emaan dai na xaune tana ta kallonsu without saying a single word,anty habiba tace"banki ne suka bata min lokaci,daga nan kuma nashiga kasuwa"umma tace"bari nasa saliha ta kawo miki abinci"daga haka ta fita daga parlorn xuwa main kitchen,anty habiba ta kalli emaan tace"dawo nan "tana nuna mata gefenta,xama emaan tayi tana saukar da idonta kasa,hawayen dake makale a idonta suka gangaro,anty habiba tace"rayuwar duniya sai da hakuri emaan,you've been through alot arayuwa,ina da yaƙinin yanxu ne lokacin daxaki samu eternal happiness,amma saikin kwantar da hankalinki kinji ko"ko motsin kirki emaan batayi ba balle tayi magana,banda hawaye babu abinda ke fita daga idanunta,anty habiba tace "ki share hawayenki emaan and listen to me carefully,kinga dai auren nan shine gatanki aduniya,ki rike shi hannu bibbiyu ,nasan babu soyayyah atsakanin ku amma tunda kikaga hakan ta faru Allah xai Daidaita tsakanin ku,lastly ki dage da addua"sai alokacin emaan ta gyada mata kai asanyaye sannan ta goge hawayen domin baxasu fahimci halin datake ciki ba,baxasu taba fahimtar hakan ba.shigowar saliha da umma ne yasa emaan mikewa ta shige bedroom dinta tareda kwanciya akan gado tana cigaba da tunani....sai past 11 anty habiba tashigo dakin ta tarar da emaan ta lumshe idanu,ba bacci takeyi ba magana ce bata so amata ,wannan daren ne yakasance dare mafi tsayi arayuwar emaan,yadda taga rana haka taga dare,wani xaxxabi ne taji yana saukar mata ga wani headache dake ɗaure mata kai,lafiyayyan breakfast anty habiba ta shirya ma emaan,umma tace"masu ƴa kenan"murmushi anty habiba tayi tace"ke kuwa umma tafiya fa xatayi can wata uwa duniya "nan da nan mood din umma ya canxa,ta sauke ajiyar xuciya tana kallon emaan wacce tafito daga dakinta jiki asanyaye,tayi rau-rau da fuska kadan take jira ta fashe da kuka,haka ne yasa umma da anty habiba suka tsare gida saboda kada emaan tayi breaking down,bayan sun kammala breakfast anty habiba ta sake yima emaan nasiha mai ratsa jiki,anan emaan ta fashe da kuka mai tsanani da ciwo,tanajin kamar xata rabu dawani bangare na jikinta.....karfe hudu na yamma bayan sallar la'asar Anty habiba ta taimaka ma emaan tashirya cikin wata black abaya mai kyau,ta ajiye mata maroon sling bag da maroon flate Hermès shoes,suka fito parlour saliha na rike da trolleys dinta guda biyu,tana kallon umma dake xaune a falo ta fashe da kuka,idanun umma suka ciko da kwalla suka rungume for few seconds sannan umma tace"Allah ya tsare,Allah ya kiyaye hanya"daga haka ta koma ta xauna,anty habiba na rike da ita suka shiga part din Mami,a parlor suka tarar da ita tareda dasu inteesar wacce tayi  narai-narai da ido kamar xatayi kuka,ciki-ciki Mami ta amsa sallamar sannan suka wuce wurin mama da mummy da kamar xuciyar ta xata fashe saboda bakin ciki....a motar Abba aka saka kayan dayake shine zai kaita Airport din,xuwa yanxu kuka take Sosai kamar ranta xai bar gangar jikinta,tana jin kamar baxasu sake haduwa ba.tafiyar minti arabain ce ta kaisu airport,saida Abba ya tabbatar tagama check in sannan ya tafi, ta sake fitowa suyi sallama taga yatafi ,hakan ne yasa wasu hawaye suka sake xubo mata,jiki asanyaye ta shiga departure ta xauna a first class lounge,har lokacin hawaye nata racing daga idanunta kasancewar this is the first time daxata yi tafiya ita kadai kuma me nisa,takardar da Abba ya bata ta bude,cikeda mamaki taga atm card sai address din alameen na Uk,even though yayi tunanin they're in contact tunda dai bashi ne ya hada su balle yayi wani tunani na daban ,tana xaune wasu hadaddun couples suka xauna sunata hira gwanin ban sha'awa,lokaci-lokaci emaan ke kallonsu sede har lokacin babu wanda yace ma kowa komai,kafin suyi takeoff saida Abba yakirata suka sakeyin sallama,umma dake gefen shi ta amshi wayar sukayi magana sannan emaan tasa wayar a flight mode...few minutes after qatar airways ya tashi from kano to abuja then to lagos daga nan suka fara asalin tafiyar tasu xuwa birnin London.....6 hours later jirgin ya sauka a Heathrow international airport,emaan tafito jiki asanyaye tana jin kanta na sara mata,ga wata fargaba data darsu acikin xuciyar ta ta musamman,after immigration check emaan ta wuce wurin luggage dinta, gabanta ne ya fadi lokacin data tuna inda taxo kuma wurin wanda taxo,jiki asanyaye ta fita daga arrivals tasamu wuri taxauna kamar wata marainiya,yunwa taji tanaji saboda bata ci abincin cikin jirgi Sosai ba,kamar ance ta juya taga McDonald's hakan yasa ta sauke ajiyar xuciya,xuwa tayi tasayi chips da burger da drink taci sannan tafara tunanin yadda xatayi,ita ahalin datake ciki batada numbar shi,idan ma tana da numbar kiranshi xatayi???ita data taho ai shi yakamata ya neme ta,xama tayi tanata tunani,bata son xuwa gidan dakanta for her personal reasons tunda Abba ya bata address for emergency purpose,tagumi ta xabga tana kallon different people from different continents,wayarta dake ring takalla,ta duba taga sunan Abba,ajiyar xuciya ta sauke sannan tayi picking,bayan sun gaisa yace"by now kun isa gida ko?"ta girgiza kai ahankali tace"a'a"cikeda mamaki Abba yace"ban gane a'a ba"shiru tayi can tace"bai karaso ba"tana gama fadin haka taji Abba ya kashe wayar ya kira alameen wanda lokacin yake baccinsa hankali kwance,ya manta shaf da xuwanta kuma shine ya tura ma Abba ticket din,god knows ko kallon ticket din baiyi ba balle yasan date dinda aka saka tunda xabi suka bashi yace susa duk wanda sukeso,Abba yace"Wai kana ina ne?tun daxu tana jiranka a airport "bude ido yayi sannan yace"Ina hanya Abba"daga haka ya ajiye wayar ya cigaba da baccinsa dan bega dalilin daxai hana kanshi bacci ba saboda emaan,yarinyar daya tsana fiyeda misali,after like 15 minutes Abba ya sake kiranta,cikeda damuwa tace mishi"Abba yaxo"tafada hakan saboda ta kwantar musu da hankali,daga nan Abba bai sake kira ba,tun tana xaman jiranshi harta mike tsaye saboda yadda kafafuwanta ke mata ciwo,can ta rike ƙugu tana jin bayanta yana amsawa,wasa-wasa taga anyi axahar baixo ba suda suka sauka early in the morning,toilet tashiga tayi alwala tayi sallah tana jin xaxxabi yana dawo mata,haka tacigaba da xama har karfe uku sannan ta shiga kfc tasiya abinci saboda yunwar data fara ji,har kuma ta kammala bai xo ba,tana nan xaune a arrivals wasa-wasa har yamma tayi,xuwa yanxu tasan intentionally yayi hakan,ta hadiye wani abu mai tauri xuciyarta na suya,bata sake yadda alameen baida imani ba saida ta idar da sallar isha,xuwa lokacin hawaye masu xafi suka gangaro mata,tana jin tsanar shi na sake shigarta,itakuma tayi alkawarin baxata taba zuwa gidan dakanta ba,xuwa safiya idan baixo ba return ticket xata siya ta koma gida abinda ta yanke shawarar yi kenan....tana cikin wannan tunanin taga inuwar mutum tsaye agabanta,kamar ance ta daga ido taga alameen tsaye ya rungume hannu akirji yana kallonta da fuskar shi cikeda rashin fara'a,saurin saukar da fuskarta tayi,ga mamakinta taga ya juya yana tafiya majestically,ganin dagaske tafiyar yakeyi yasa tayi saurin mikewa tabi bayanshi tana jan trolleys dinta abin tausayi,shiga motar shi yayi ya xauna ya na pressing phone,taɓa booth tayi taji shi arufe,hakan yasa ta bude back door ta xuba trolleys din aciki,saida ya tabbatar ta gama ajiye su sannan ya juyo ahankali yana yi mata wani irin kallo na rashin mutumci,atsanake yafurta"get those filthy trolleys of yours out of my ride"yana kaiwa nan ya bude mata booth,wani irin bakin ciki ne ya mamaye mata xuciya,saboda ta gaji iya gajiya,amma dayake alameen is heartless ko ajikin shi,bata da yadda xatayi ta mayar da trolleys din cikin booth sannan ta xauna,ko gama rufe motar batayi ba ya figesu da shegen gudu suka bar airport din,ajiyar xuciya ta sauke tana kallon birnin london mai kyau da tsari,ahaka har suka karasa unguwar su mai suna Knightsbridge,unguwar data kasance one of poshest area aduniya gabadaya bama a iya birnin london ba,a gaban wani rantsastsan gida ya tsaya gate din ya bude kanshi da kanshi,a parking lot yayi parking,emaan ta fito jiki asanyaye tana kallon pool din dake gefe,gidan yayi masifar haduwa,ko second daya bai sakeyi awurin ba ya shige ciki ya barta awurin bayan ya bud'e mata booth,jiki asanyaye ta fito da trolleys din sannan tashiga cikin gidan tana dan waro ido,saboda yadda gidan ya tsaru abu ne mai wuyar misaltuwa,bata ganshi a parlour dinba wanda iya shi ya isa ya tafi da xuciyar mai karatu,daga gefe staircase ne mai masifar kyau wanda zai kaika saman gidan,xama tayi a parlor saboda batasan inda xata shiga ba,saide ga mamakinta taga har past 11 baixo ya nuna mata dakin da xata xauna ba,mikewa tayi jiki asanyaye tafara bude kofofin gidan,na farko wani hadaddan kitchen tagani,rufewa tayi ta sake bude wata kofar taga toilet ne,iya kofofin dake parlon kenan,daga kitchen sai store sai toilet sai dining,bedrooms na sama kenan tafada hakan acikin xuciyar ta,ganin bashida niyyar fitowa lokacin 12 na dare yayi yasa ta hau saman asanyaye,nan ma wani breathtaking parlor tagani saidai bai kai na kasan girma ba,sai kuma taga taga kofofi guda uku,saida taja dogon numfashi sannan ta bud'e kofar farko,idanunta suka sauka acikin dakin,arikice ta xaro ido jikinta yana rawa,tana jin numfashin ta nayin sama da kasa yana sauka dakyar saboda tsananin tsoro.......


Zaynabyusuf✍🏼💕
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now