PAGE 10

172 5 0
                                    

Eman..🥀

Page 10

Written by Zaynab Yusuf✍🏼

Sosai Yaya Sadeeq ya dinke fuska tamkar be san mecece  kalmar dariya ba bare yasan yadda ake yinta,ya mayar da duk wata nutsuwarshi ga abincin dayake ciki,kallo mai cikeda nazari Ya Fauza ke mishi,abinda bai cika faruwa bane a tsakaninsu,tasan yaya Sadeeq mutum ne mai hakuri,shiyasa reaction dinshi ya bata mamaki,saboda fushin daya dauka mai zafi ne,Sosai tazama very uncomfortable,sai ta langabar dakai tace"I'm so sorry baban Anum,bansan hakan zai b'ata maka rai ba".batareda ya dago ba yace "Fauza what are you trying to do?Kin manta halin da eman ke ciki ne?".saida ta girgiza kai sannan tace"ban manta ba,hakkinta nake son fita,bamu saniba ko zai sai samu karbuwa awajenta nan gaba,aganina halin data ke ciki ba dalili bane da zaisa ta daina kula samari,domin bamu San inda rana zata fad'i ba,ta yiwu tasamu miji a irin hakan".ahankali ya d'ago yana kallon ya Fauza sannan yace"Shikenan,kiyi duk abinda kike ganin ya dace,amma kafin nan ki kalli eman,amsar na shimfide asaman fuskarta,she's still hurt".dan waro idanu tayi,this is unlike her Sadeeq,meyasa zai dau fushi akan wannan karamar maganar wacce bata kai takawo ba?saita daure tace "fadamin yadda kake son ayi"kamar yana fad'a da wani abu acikin zuciyar shi haka yake ji,so yake ya danne abun amma ya kasa,kallon dayake mata yasa wani mugun tausayinta ya dirar mishi,irin kallon dayake mata alokuta mabanbanta,ajiyar zuciyah ta sauke alokacin da idonsu ya sark'e,yace"kiyi duk abinda kikaga ya dace".
Tace"me kakeso ayi?".yace "just block him anawa raayin".yafada frankly Saida tayi blocking sannan ta d'ago mishi wayar tana fadin "happy?"ahankali ya lumshe idanu ya gyada kai yana sakin dan karamin murmushi Na gefen baki wanda dashi gara babu,sai alokacin hankalin ya Fauza ya kwanta,ta sauke ajiyar zuciyah tana kallona,nima kallonta nakeyi ina mamakin abinda yafaru yanzu,meyasa Sukai gab da samun sab'ani akan abinda bai kai yakawo ba?ya Sadeeq ne ya katse mini gajeren tunanina sanda yace"let's get going,kar baccin su Anum yayi nisa".muna nan zaune yakai su mota one by one sannan yadawo suka jera shi da ya Fauza ,sune agabana hakan yasa naga yadda ya Fauza ta riko mishi hannu tareda dora kanta saman shoulders dinshi,shikuma yana squeezing fingers dinta ahankali,tace mishi"I'm sorry for what happened ".saurin dakatawa yayi tareda riqo fuskarta with so much love yace"shhhh,stop apologising,I'm sorry too kawai naga rashin dacewar hakan ne lura da yanayin da Eman ke ciki".yakarashe yana kissing din goshinta,da sauri na d'auke kaina tareda yin dogayen taku Na wuce su,mota Na shiga tareda zuba tagumi abin duniya ya taru ya mini yawa,tace "yawuce baby na,I love you".yace"I love you more than anything ".Sosai ta tsura mishi idanu tana jin shaukin son yaya Sadeeq na kara shigarta,ahankali cikin muryarta me cike da jan hankali tace"Ngd Allah Daya bani kai a matsayin miji wato uban ya'ya na hakika ina alfahari da kasancewar ka miji agareni,D'aya tamkar da dubu. Idan ina kuka ka share mini hawaye na. Yayin da nike cikin damuwa ka sani farinciki.Yayin da nike cikin fushi ka lallasheni.Hakika kai din na musamman ne a gareni sbd ka samar wa rayuwa ta kyakkyawan littafi wanda dinbin Al'umma zasu so su karanta shi a duniyar masoya. ina alfahari da kai kuma har abada bazan taba mantawa da mutum mai karamci irin ka ba.Thank you for being mine."
Kyakkyawan murmushi yasaki yanajin shaukin sonta na tsarga mishi tun daga tsakiyar kanshi har tafin kafafuwanshi,yana sonta so mai tsanani wanda bazai iya fasalta shi ba.
Yace"I love you more matata,kodai k'ani kike so ayima Asad yau?".dariya tayi tareda b'ata fuska tana dan bubbuga kafafunta,itada haihuwa ba nan kusa ba saita kara hutawa,duk wanda yasan Fauza yasan yar soyayyah ce ta asali,she's very romantic shiyasa Sadeeq ke kara sonta,tashiga cikin rashin ta mamaye rayuwar shi.Yace"mene ne burinki?"cikeda fara'a ta ce"burina ka zamto nawa ni kadai aduniya harma da lahira,zaka iya cika mini wannan burin?",lips dinta ya kama amaimakon ya bata amsa,ahankali yake kissing dinta passionately bai damu da awaje suke ba,sun dauki few minutes ahaka sannan ya Fauza tayi saurin matsar da fuskarta gefe tanajin kamar su dawwama ahaka,tace"naki wayon sai fa ka bani amsar tambayata".ya saki murmushi yace"sure amma sai munje gida,mu biyu cikin sirri zan baki amsar,kada ki damu har amsoshin tambayoyin da baki min ba duk zan amsa miki su".dariya maganar shi tabata,ya riko waist dinta suka shiga mota suna sakar ma juna kallon kauna.
Tadan juyo tace"sorry mun barku a mota".
Nace"bakomai "ahankali kamar me koyon magana,yaya Sadeeq yace"budurwar kauye an bud'e baki,dazu fa ko A batace mini ba haka naita surutu ni kadai, danaji ba amsa sai nakama gabana".b'ata fuska ya Fauza tayi tace"la la la! Mijin nawa kika baiwa banza ajiya?mijin Fauza guda?"tafada tana kanbama harshe,kallonta kawai nayi bance komai ba yaya Sadeeq yace"fad'a mata dai"yana fadin haka idanun mu suka sark'e ta mirror,nayi saurin sauke idanuna inajin wani iri,har yanzu ni me laifi ce kuma haka Ba zai tab'a goguwa ba har karshen rayuwata,ga mamakina sai muka kara hada ido akaro na biyu,nan ma nayi saurin sauke nawa kasa,shikuma ya kamo hannun Ya Fauza wacce ke danna waya yana pecking,abinda take so kenan saita ajiye wayar ta tattara gabadaya hankalinta da nutsuwarta ta damk'a mishi,ta juyo da jikinta Sosai tana sakar mishi wasu shegun kallo,yana pecking hannunta yace"zamu fada rami idan kika cigaba da min wannna kallon".saida tayi farrr da ido sannan tace"Allah ko?"sai ya saki baki yana kallonta,Ya Fauza na kashe shi da salonta,haka suka cigaba da zuba soyayyah ban san sunayi ba dayake na lumshe ido na saboda bana son mu kara hada ido dashi akaro na uku,muna zuwa gida nayi saurin Daukar Asad na shige ciki,veil dina na ajiye Sannan na zauna agefen gadon Asad ina cire mashi kaya,naji motsin shigowar mutum amma aduk tunanina ya Fauza ce,ban dago ba saida nagama cire mashi kayan,ganin ya Sadeeq ya kalmashe hannu akirji yana kallona yasa nayi saurin mikewa tsaye,mutumin da ada muke shiri Sosai amma yanzu bana iya ce mishi koda A saboda kunyar abinda yafaru dani.
Yace"surikata dama kinada karfi haka?".
Dakyar na iya kakalo side smile nayi batareda nace komai ba na dauko kayan baccin Asad,"yakamata ki manta da komai eman and start your life afresh"nan ma bance mishi komai ba,yace"kinsan me?"ya tambaya yana kafeni da ido, na girgiza kaina  ahankali alamar a'a shikuma yacigaba da cewa"zuciyata bata yarda da abinda akace kinyi ba,nasan ki farin sani,May be ma fiyeda yadda kika san kanki ,munyi maganar da Fauza,itama ta nuna mini hakan,dan haka feel free kinji yar budurwar kauye"yakarashe maganar cikeda barkwanci.Sai alokacin na iya daga ido na kalleshi,kwayar idanunshi suka sark'e acikin nawa,acan na hango tsantsar gaskiyar abinda bakin shi ke furtawa,hakan ya bashi damar cigaba da cewa"Kidaina damuwa Akan rabuwarku da Aliyu,kisa aranki haka Allah ya kaddara,dama can babu aure atsakanin ku".wasu zafafan hawaye ne suka zubo mini,na lumshe ido ina jin zafin kalaman shi,alokaci d'aya ya fama mini ciwon da har na mutu bazan manta ba,ciwon da Aliyu kadai keda maganinsa,ciwon da bazai tab'a warkewa ba acikin zuciyata,Aliyu is my life and everything,na rasashi dan haka rayuwata bazata sake zama daidai ba,"i didn't mean to hurt your feelings eman,wannan maganar tazama dole shiyasa na miki".bance komai ba saima karfi da kukan nawa ya k'ara,da gudu na bar dakin ina bangaje Ya Fauza,bansan nayi hakan ba,fadawa nayi saman gado bayan Na rufe kofata na cigaba da rera uban kuka wanda sam bana gajiya, ya zame mini jiki,ya zame mini bango abin jingina kuma tudu na dafawa.
Da kallon mamaki ya fauza ta bini,ta karasa dakin su Anum tana tambyar yaya Sadeeq abinda yafaru,cikeda tausayina yace"magana nai mata akan abinda yafaru shine tafara kuka,kiyi hakuri bansan haka zata d'auki lamarin ba".ajiyar zuciyah ya fauza ta sauke sannan ta karasa inda yake tsaye ta dora kanta akan chest dinshi tana tsananin tausaya mini.tace"eman na bani tausayi,tana bukatar wani akusa da ita,musamman ayanzu datake cikin gararin rayuwa,gashi aiki ya hanamu kula da ita yadda yakamata".asanyaye yace"the weekend starts tomorrow,sai muyi iya kokarinmu akanta,duk da gobe zamuje gida,su Salima an zama Amarya".
Cikeda damuwa ya Fauza tace"Allah sarki da tuni fa tareda eman zaayi".hugging dinta yayi tightly yace"dan Allah kidena damuwa,dama can basuda rabon kasancewa tare".ya dasa ma maganar digon aya.
Washegari basu koma bacci ba tun bayan sallar asubah,aikin gidan sukayi shida ya Fauza,ya rike baya yana cewa"gaskiya nagaji mai aiki zamu nemo"harara ta galla masa sannan tace"kabarni nayi abuna ban saka dole ba,dan haka ka daina min zancen mai aiki".yace"kishin ki yayi yawa,hardasu mai aiki".tace"dole nayi kishinka yaya Sadeeq "tafada tareda riqo shi suka fada kan 3seater,dariya suka fara  atare lokacin da yafara kissing dinta takoina,sun dade ahaka sannan ya dakata yana kallon kyakkyawar fuskar ta,wacce ta dauko kamannin hjy kwaise har ma taso tafi hjy kyau,fara ce sol irin farin shuwan asali,ga kyau,ga gashi,ga tsaho komai Allah ya bata daidai gwargwado.Tsaye nake agaban mirror ina kallon idona dasuka kumbura saboda tsananin kuka,na sake kallon fatar jikina mai matsakaicin fari,fara ce ni amma ba irin fari Sosai ba,sannan banida zarkad'eden hanci mai tsayi saide hancina ya dace da doguwar fuskata data dace da manyan manyan lulu eyes dina,bakina nada girma saidai ba can Sosai ba,za'a iya kirana da kyakkyawa saide ba irin kyan su Ya Fauza,Salima da inteesar ba wanda zakasan akwai tsatson larabawa ajininsu,zan fi dacewa a misaltani da 'ya'yan mummy wato Afiya,Rafee'ah da Sadeeya fulanin asali,dogon gashi kawai nafisu ,sun fini tsaho dan bazaa kirani da doguwa ba just fallen in the middle,niba doguwa bace Sosai,Allah ya azurtani da figure 8 feature,abinda zan iya cewa na musu zarra domin ni asalin qirar kalangu ce,saide banida wata qiba idan aka cire sama da qasan da Allah ya bani,Ya Fauza ce kawai mai shape a 'ya'yan hjy,'ya'yan mummy nada daidai nasu suma,yaran mama ne kamar paper haka suka tafi 1 abinsu.Duk da ina cikin damuwa hakan baisa na manta da kalmar da hausawa ke kira yakamata ba,tun jiya naso gyara gidan amma banida strength din yin aikin,dalilin daya sa Na tashi da wuri kenan domin Na tsaftace  gidan,dakin danake ciki nafarawa gyarawa na wanke toilet sannan na gyara falon sama,na share nayi mopping da goge goge,dakinsu Anum Na gyara duk da suna bacci Na wanke toilet sannan nafito,ahankali tamkar wacce kwai ya fashe mawa Nake saukowa daga staircase,saida nayi rabi sannan na hango ya Fauza da yaya Sadeeq dake kissing juna,kallo daya na musu na juya dakina,akallo d'ayan na ga sun gyara falon sai na shiga wanka,doguwar rigar atampa A shape nasa duk da takure ni dasukeyi,umma ke cewa ayi mini A shape saboda yanayin jikina,duk da haka kallo daya zaka mini kasan Allah yayi baiwar Halitta awurin,Sosai naji kewar umma Na shigewa cikin duk wata k'ofar gashi ta jikina,ina son kiranta nagaishe ta sannan nabata hakuri,ina son jin muryarta koda fada zata mini,sanin bazataji dadin kiran ba yasa na hakura,saina zauna nafara karatun Alqur'ani,wanda ya yaye mini kaso mai yawa na daga cikin damuwata.Karamar wayar ya fauza Na kalla akaro na biyu,ina mamakin rashin kirana da Aliyu beyiba bayan yasan nice Na kirashi,kenan ya yarda mommy ta zaba mishi matar?ya rabu da ita kenan?wani gunjin kuka ne ke kokarin kufce mini  amma na hana  zuciyata karaya tun yanzu,nifa idan ba Aliyu bane yafurta mini hakan dakanshi gani nake kamar alamarin wasa ne,sai na mike akaro na biyu na sauka kasa,lokacin su ya Fauza suna kitchen suna hada breakfast,shiga nayi na gaishesu cikeda girmamawa,atare suka juyo suna bina da kallon mamaki,sai suka ja bakinsu sukayi shiru amma sunji dadin yadda na sauko dan ra'ayin kaina,naso su bari nakarasa breakfast din suka hanani,saina koma falo ina kallon Tv duk da hankalina baya kai.Yaya Sadeeq ne ya ajiye mini plate full of French fries da omelette,sai tea da ketchup,"thank you"nafurta ahankali,Sosai yaya Sadeeq yaji dadin maganar danayi yace"budurwar kauye yau baki ya bud'e ".bance mishi komai ba sai ya juya yana fadin"Enjoy your meal".ajiyar zuciyah na sauke domin Na dade banga masu kirki ba irinsu ya Fauza da yaya Sadeeq,yadda suka dauki damuwata kamar tasu suke iya kokarin su ganin Na daina shiga damuwa,Tabbas dukkan tsanani yana tareda sauki,ya Fauza da yaya Sadeeq sun kafa wani babban jigo acikin rayuwata.
Kwance take akan royal blue color din gadonta wanda yakasance royal bed,wanda kallo daya zaka mishi kasan mai tsada ne na gaske,gajeren tunani tayi sannan ta jawo wayarta tayi dialling numbar Fauza,yau kwanan Eman uku agidan amma ita kadai tasan adadin damuwar Data shiga,suna cikin yin breakfast itada yaya Sadeeq wayar tafara ring,cikeda murna tai picking sannan ta gaida hjy,suna gama gaisuwar tace"kwanan eman uku yau,sai yaushe zata dawo kenan?".hjy kwaise ta tambaya,Ya Fauza tace"I have no idea,amma da dukkan alamu zata dan kwana biyu dan har yanzu lamarin nata babu wani sauki,ya umma fa?".
Tace"Allah yagani banasan zamanta awurinki Fauza,hankalina yakasa kwanciya".da mamaki ya Fauza tace"bakomai mami,ba abinda zai faru sai alheri,nida yaya Sadeeq ba fad'a garemu ba balle ace zamu isheta da masifa har asamu matsala,su Anum ma ce musu nayi batada lafiya Sosai bata son hayaniya,gaskiya babu matsala azaman mu sedai bazaa rasa ajizanci ba irin na dan adam,dama zaman tare ya gaji haka".haka ya fauza ta riqa toshe duk inda hjy zata bullo mata,daga karshe ta miqa wuya duk da K'asan ranta na wani tunanin Na daban.Kallon mamaki yake jifan ya Fauza dasu,saita sauke ajiyar zuciyah sanda yace"meya faru?"asanyaye tace"mami ce ta damu da zaman eman awurin mu,tana ganin kamar zata takura mana".gyada kai yayi tare da cewa"okay"tacigaba da fadin"nide banga wani abu ba domin eman tamkar kanwata ta jini na d'auke ta,duk da maganganun mami sun sanyaya mini jiki domin banason negative thoughts acikin rayuwata,banda overthinking irin na Mami mezai faru tohm?dama dole asamu sab'ani kuma zaman tare ya gaji hakan".zazzafan cuppocino coffee ya kurba batareda yace komai ba domin baida abin cewar ahalin dayake ciki yanzu,zuwan Anum yasa suka tattara hankalinsu da nutsuwar su suka mik'a mata,akan cinyar baban ta zauna tana zuba shagwaba son ranta,yaya Sadeeq ya shagwaba yaran Sosai,hakan baya rasa nasaba da masifar son  'ya'ya da Allah ya jarabce shi dashi,yana kaunar yara irin Sosai da Sosai,burinshi ya haifi kamar biyar ko shida saboda yabasu ingantacciyar rayuwa mai cikeda tsari.Cikeda damuwa mummy ke labarta ma aminiyarta Hajia Rasheeda halin datake ciki"ace burin yaran nan shine a mini dariya,gabadaya Sun baje basa wani motsin da zanji dadi arayuwata,abin takaici har su hudu amma kowacce babu wanda zata nuna amatsayin saurayi bare miji,sun tayar mini da hankali su kuma ko ajikinsu,Salima fa aure zatayi"da mamaki Hajia Rasheeda tace"Salima dai Salima k'anwar afiya da Rafee'ah,gaskiya lamarin nan akwai alamar tambaya,dan ba tun yanzu ba naso miki maganar sai na fasa,kinsan irin haka ba dadi ban san yadda zaki d'auke ta ba".cikeda alhini tace"kinji tashin hankalin danake ciki,ga abba dayake kokarin cire mini zani a kasuwa,gabadaya ya ajiye lamarina agefe,ta umma yakeyi wacce yarta ta janyo mata abin kunyah,bakiga yadda yake tarairayarta ba kamar zai maidata ciki".
Hajia Rasheeda tace"gaskiya kina ganin ganin rayuwa,ni rashin auren nan nasu yafi damuna,domin Abba idan da sabo yakamata ace kin saba,shima fa haka mukaita fama akanshi".
Tace"kede bari kawata ni kadai nasan me nake ji,zuciyata tafarfasa take tana k'una,enemies dina sai cigaba sukeyi nikuma ina nan stagnant zaune awuri daya".shigowar Rafee'ah ce tasa mummy kara jan firar saboda haushin da suke bata ba kadan bane,sa'ar su daya agidan yawa suke batason aji halin Datake ciki amma da surutun ta kadai ya ishesu su fitar da miji anata tunanin.Ta dade Sosai tana fadama Hajia Rasheeda halin datake ciki sannan ta katse wayar bayan Hjy Rasheeda tayi mata alkawari zuwa acikin kwana biyun nan  domin suyima tufkar hanci.
Rafee'ah dake tsugunne agaban mummy tace"kiyi hakuri mummy in shaa Allah Allah zai kawo mana,ki cigaba da mana addua".dogon tsaki mummy taja sannan tace "zancen kenan, Wai ke bakya gajiya da maimaita mini su?Kinsan fa ba tasiri zasuyi akaina ba gara ma kija tsumman bakinki kiyi shiru".
"Allah yabaki hakuri"cewar Rafee'ah tareda mikewa tafice,"nak'i na hakura mara kunyah fitsararra,Ana nuna muku gabas kuna bin yamma"haka mummy taita mita tana jin bakin ciki na saukar mata,shigowar da Salima tayi tagaisheta itace ta kara karfin wutar dake balbala acikin zuciyarta....





Kina son turaren wuta masu classy and unique scent?masu kamshin gidan 'yan gayu,turare mai kama gida ya mayar dake abar so yar kwalisa?kinason turaren da tun daga tsakar gida za'a San yes Ke Cikakkiyar mace ce?hajiyata kina son durot mai tsananin kamshi da akayi shi cikeda tsafta?kina son exclusive room freshners?kina son amsa sunan cikakkiyar mace wacce ta amsa sunanta Na Sarauniya?BAKHOOR INCENSE PLACE gidan kamshi got you covered,maza ku garzaya Bakhoor incense place domin siyan d'aya ko sari,ni na gwada kuma naji dadi domin nagari ne kuma na mayar da kudina gida Chasssss💃🏼💃🏼ku tuntubesu ta wannan lambar domin siyan Turaren wuta yan gaske.
09037909996

Zaynab Yusuf ✍🏼

EMAANWhere stories live. Discover now