PAGE 13

124 4 0
                                    

Page 13

Eman ce xaune  with bowl full of milky popcorn a saman cinyar ta,ta tattara nustuwarta gabadaya akan TV tana kallon her favourite Nigerian movie,saide if you look closely ba iya film din bane ya tafi da tunanin ta,she was lost in thoughts,lost in the world of her own memories,Yaya Sadeeq dake kallonta keenly ya lumshe idanu,yanajin damuwarta har tsakiyar xuciyar  shi da ruhinshi,babban burin shi is to make her happy duba ga yadda rayuwarta ta juya upside down acikin lokaci kalilan,gyara tsayuwarsa yayi yana tunanin umma wacce sam batasan kalmar da ake da kira k'addara ba,saboda wannan shine karo na uku daya ba umma hakuri on her behalf,amma gabadaya umma bata fahimce shi ba,har Yanxu bata sauko daga  inda tahau na fushi da eman ba,wanda dole xaiyi affecting rayuwar Yarinyar ,shi kuma baxai samu sukuni da nutsuwa ba har sai komai ya Daidaita acikin rayuwar ta,xama yayi yana kallon Tvn shima,adaidai lokacin da Joseph ke kallon Francis tana waya da Boss dinta at 11pm,abinda ya bakantawa Joseph rai kenan,tana ajiye wayar tayi cupping fuskar shi tace"sorry for keeping you waiting..."ya dakatar da ita kafin ta karasa"how much is your salary?"ya tambaya akaro nafarko arayuwar su,suprisingly tace"300k"yace"I'll give you 500k but you've to quit your job and I mean what I'm saying "yafada without giving her room to express her opinion,da mamaki francis ke kallon Joseph wanda ya riqo both hands dinta,he meant what he said,sannan ahankali making his way to her mouth kissing her passionately, gefen da eman take ya kalla wacce batasan da xaman shi awurin ba balle xazama uncomfortable,ita mamakinta ashe suma sunada kishi haka?sai lamarin ya burgeta matuka,domin tana son taga namiji Na nuna kishi akan matar shi,ahankali wannan tunanin ya jawo mata Aliyu cikin ranta,wanda take trying very hard to forget,duk da she's quite sure Aliyu ya mata nisa ayanxu,tamkar yadda sama taiwa kasa nisa,ajiyar xuciyah ta sauke sannan takalli left side of her,ganin yaya Sadeeq na kallonta yasa gabanta faduwa,at the same time kunya ta lullubeta,bata San iya adadin lokacin daya dauka ba xaune awurin,saitayi saurin sauke idanunta kasa tana murza not so tiny fingers dinta,baice komai ba haka sannan bai daina kallonta ba saboda shi kadai yasan sanyin da zuciyar shi ke Mishi alokacin,kallonta kadai Na sanyaya mishi xuciya yasa shi cikin jin dadi dakuma nishadi,yana masifar son Yarinyar nan,yana kaunarta with every fibre of his being,Ahankali yace "the movie is interesting right?"samun kanta tayi da kasa cewa komai,domin kunyar shi take ji dagasken gaske,"eman!"ya furta lyrically akaro na biyu yana cigaba da kallonta da idanunshi wanda suka cika da ruwa suna maiko,jin ya kira sunanta yasa ta dago kai ta kalleshi akaro na biyu,tayi dauriyar kallon shi straight in the eyes dukda xuciyarta Na dukan tara tara,yace"nayi ma umma magana for the third time ..."saurin xamewa tayi daga kan kujerar ta xauna saman carpet,jikinta yayi wani irin sanyi,idanunta sun ciko da ruwan hawaye,bakinta na rawa tace"har yanxu tana fushi dani ko?"ta tambaya innocently,yadda tayi maganar saida yaya Sadeeq yaji xuciyarshi tayi tsalle kamar zata fito waje,yace"a'a tafara saukowa,we should be more prayerful har lokacin daxata daina fushin gabadaya".hawayen datake kokarin dannewa ne suka xubo mata,saita runtse idanun tana jin xuciyar ta na mata zafi,why her ?ta yi tambayar da babu me amsa mata ita, ayanxu babban burinta umma ta yafe mata arayuwa,saukar da idanunshi yayi daga kallonta,saboda yadda xuciyar shi ke k'una,baxe iya resisting ganinta ba tana kuka ,batasan yadda kukan ta ke affecting dinshi ba,kukan ta Na tayar mishi da hankali,kukan ta Na nuna gaxawar shi acikin rayuwarta,kukan ta Na nuna har yanxu akwai sauran aiki gameda ita akanshi,even though he's trying his possible best,yanxu ma dakyar umma ta amince ta koma school saboda magiyar daya rinqa mata,Kamar baxai yi magana ba yace"gobe xakuyi resuming school right?"damuwar datake ciki bata hanata mamakin shi ba,ya akai yasani?murmushi yayi domin ya fahimci look din datake bashi yace"why are you surprised?".tace"why shouldn't I? Ashe kasan school dinda nake".yace"you're not serious,yanxu dame dame kike bukata?idan fauxa ta dawo sai muje shopping ".shiru tayi tana kallon tvn,zuciyarta na tunanin lokacin da umma tace ita da school har abada even though she's in her final year,yace "I'm listening "nan ma shiru tayi tarasa me xatace mishi,yaya Sadeeq is so down to earth,kirkinshi ya yi yawa,sai kawai tace"thank you amma umma tace i should forget school acikin babin rayuwata"cikeda jin dadi yace"you worth more eman,sannan karki damu xaki koma school munyi maganar da umma kuma ta amince"da d'an mamaki ta kalleshi tace"are you serious?"ya gyada kai alamar eh,tayi murmushin daya bayyana hakoranta saboda farin ciki,"thank you"ta kara maimaita mishi akaro na biyu,yaya Sadeeq has a very special place acikin xuciyar ta.
sallamar ya Fauxa ce ta katse mata tunani,ta daga kai tana kallon fuskar ta wacce ta ke murmushi ganin yaya Sadeeq ya saki jikinshi,ta xauna daf dashi kamar xata shige cikin sa take fadin"naji dadin ganinka ahaka"Yana murmushi yace"thanks to eman"bai san lokacin daya furta hakan ba,eman ta waro ido waje tana kallonsa,fauxa tace"Thank sis"tafada tana cupping fuskarshi tana kallonshi cikeda tsantsar kauna,for the first time dayaji wani iri saboda eman Na wajen,ya samu kanshi da tunanin hakan bai kamata ba saboda tsananin kaunar dayake mata,kafin yayi wani abu eman ta mike xata wuce sama,Ya Fauxa ta mika mata jakarta,tace"kai min daki".Shide yaya Sadeeq kallon eman yake har tabar falon sannan yayi saurin Daidaita kanshi,tana hawa staircase wayar fauxa tafara ring,fauxa tace "duba kiga waye"da d'an mamaki eman taga sunan Al'ameen ya fito,tace"its ameen".fauxa tace"pick the call kafin ya kashe,kinsan shi da anger issue,tun jiya nake kiranshi"asanyaye eman ta daga saide batace komai ba har lokacin data mika ma fauxa wayar,sai fauxa ta riqo hannunta alamar ta tsaya,daga can bangaren yace"ya kinyi picking kuma kinyi shiru,you know my tight schedules fauxa..."tana murmushi tace "afuwan dear,Eman picked the call yanzu tabani".yace"how are you doing?"ya tambaya ko sauraron karshen maganar fauxa beyi ba,"kowa na lafiya,yaushe ne dawowar taka?"yace"before salimas wedding,Mami tayita insisting "cikeda farin ciki tace"we can't wait to see you "yace"same dear,my regards to the kids "yayi shiru sannan yace"da babansu"ajiyar xuciya ta sauke mai nauyi,saboda batayi tunanin xai fada hakan ba,Sosai taji dadi tace"karka manta inform me kafin dawowarka ".yace "sure dear"haka sukai sallama fauxa sai dariya takeyi.
Yaya sadeeq yace"Kice munada babban bako,it's been long dayaxo"tace"yanxu dinma Mami ce ta mishi dole,kasan Al'ameen da rashin son mutane,hayaniya na saurin rikita shi gashi gidanmu gidan yawa,duk da yanxu aiki ne ya sashi agaba,he has a very tight schedule Kullum yana cikin  aiki"yaya Sadeeq yace"shi ai ya banbanta da 'yan gidanku,Sam baida hakuri,ga fushi da xuciya,wani irin baud'add'en mutum ne saide akwai kirki shiyasa Allah ya bud'e mishi hanyoyin samu,Al'ameen dinku fa Don ne"murmushi Fauxa tayi tace"xuciyarshi nabani tsoro,saboda bai iya fushi ba,idan ya hau babu me iya sauko dashi,shiyasa kowa ke kaffa kaffa ,kana ganin nice babba amma saide Na lallaba shi".murmushi yaya Sadeeq yayi yace"Dan Mami da abbansa ba".

EMAANWhere stories live. Discover now