PAGE 50

146 3 0
                                    

EMAAN......PAGE 50

Written by Zaynabyusuf✍🏼

   tunda suka shiga ward din fauxa ta haɗa kai da gwiwa take kuka mai karfi da ciwo wanda yake fitowa daga can ƙasan xuciyarta,gawani jiri dake ɗibarta wanda da atsaye take saiya xubar da ita,saboda it didn't seem possible to take the next breath but she realize she's surviving Sadeeqs death,she can't believe he's no more,mami dake gefenta tana matsar kwalla ce ta rungumeta sosai tana kallon Abba wanda jikinshi yayi sanyi kalau,babu komai axuciyoyinsu sai tausayin fauxa,but they can't do anything about it and that's the most painful part,babu yadda xasuyi saidai su cigaba da bata hakuri,Abba yace"Death is part of life that leaves people with memories.nothing can compensate for the loss of a loved one.Allah ya baki hakuri da juriyar cinye wannan jarabawar".bakin Mami na rawa tace "Amin"tausayin ƴarta na karya duk wata gaba ta jikinta,Allah kadai yasan me take ji acikin xuciyarta wacce babu komai cikinta sai bakin ciki da damuwa,allurar bacci sukayi ma fauxa ganin irin kukan da takeyi kuma tana bukatar hutu cox she miscarried the pregnancy,cikeda tsantsar damuwa mami tace"bansan da wani baki da kuma kalmar da xanyi ma fauxa bayani ba Abba,bansan ta yadda zan fada mata ba,my daughter is already in so much pain...."hawaye mai xafi ne ya xubo mata takasa karasa maganar,Abba dake gefenta ya dafa shoulders dinta yace"khair in shaa Allah,this too shall pass,amma kada ki fada mata for now"gyada kai mami tayi sabbin hawaye suna xubo mata,Abba yace"munyi magana da alameen daxu yace min suna Abuja,nasan by now sun karaso"gaban mami ne yayi mummunan faduwa sanda ta tuna da emaan,tsanar yarinyar na sake ninkuwa acikin xuciyarta,kasa magana tayi saboda takaici da bakin cikin emaan,ganin tayi shiru yasa yace"I'm hopeful akan future din fauxa,cox she's still young"wannan kalaman ne suka sake karya xuciyar mami,taji wani kuka mai karfi ya kwace mata wanda yake fitowa daga kasan xuciyarta,kukan tausayin ƴarta takeyi dakuma halin daxata shiga ciki kafin tayi move on da rayuwarta,saboda fauxa is still young balle ace ta rufe maganar aure daga babin rayuwarta,wannan lamarin ne ke breaking heart din mami into tiny pieces saidai ba yadda xasuyi,duk wani kuka da damuwa baxai dawo da Sadeeq ba,addua kadai ce gatan da xasu mishi sannan su sanya rislama hakuri da tawakkali acikin xuciyar su.... runtse idanu emaan tayi gabanta na tsananta faduwa sanda suka sauka a aminu kano international airport,wasu xafafan hawaye masu tsananin ciwo da radadi na xubo mata,abubuwa ne masu yawa ke xarya acikin xuciyarta,ga rasuwar Sadeeq wacce har lokacin take ganin kamar ba dagaske bane,ga damuwar dake addabar xuciyarta,ga kuma cikinta dake murdawa yana mata ciwo mai tsanani,nurain data hango from a far ne ya sa gabanta faduwa,ya kalleta keenly bayan sun gaisa da alameen yace"emaan are you okay?"tsaki alameen yayi yashiga mota,Nurain ya bishi da kallon mamaki yana kallon emaan dake rike da gefen cikinta,da kanshi ya bud'e mata kofa yana mata sannu sannan ya shiga yana kallon fuskar alameen wacce ke tamke kamar hadarin gabas,nurain yace" wani asibiti xamuje?"da mamaki alameen yace"ban gane asibiti ba"dan juyawa Nurain yayi yace"naga she's not okay...."kafin ya karasa magana alameen yace"take me home immediately ".jinjina kai nurain yayi yana mamakin alameen,calmly yake driving saidai hankalinshi gabadaya yana wurin emaan dake fitar da nishi masu nauyi tana sakin shesshekar kuka ahankali,saboda the pain is almost unbearable,juyawa yayi yakalleta yaga gumi sai xubo mata sukeyi,acikin kallo ɗaya daya mata ya lura she's going through a lot of pain,alameen was lost in thoughts,lost in the world of his own memories,ji yake kamar kanshi xai tarwatse saboda damuwa,gefe daya yana cikin fargaba mai tsanani domin yasan mami will disturb the hell out of him akan sai ya saki emaan adaidai wannan gabar wacce yake ganin ba haka yakamata yayi ba,kuma baxai yi hakan ba no matter the circumstance,he'll divorce emaan alokacin daya gamsu cewar ta ɗanɗana kuɗarta,duk da ayanxu mafi rinjaye acikin xuciyar shi na bashi shawarar yacigaba da xama da ita yana gana mata axaba for the rest of their lives,dan haka maganar saki ayanxu bata taso ba,and he's not going to divorce emaan no matter how hard mami will try,he's not divorcing emaan not at this point,that he assured himself....tafiyar minti talatin sukayi suka karasa gida,xuciyar Nurain cikeda tausayin emaan,juyowa yayi asanyaye bayan yayi parking ya ce"go and have some rest anjima sai muje asibiti"gyada mishi kai kawai tayi sabbin hawaye suna sake xubo mata,alameen kuwa ko second daya bai kara ba acikin motar ya fita yana kallon compound dinsu da mutane jefi-jefi ke kaiwa da komowa,runtse idanunshi yayi tareda sauke deep breath sannan ya wuce part dinshi,Nurain ne ya bud'e ma emaan kofa yana mata sannu,fortunately bata tarar da fuskar sani ba a main parlour hakan yasa ta sauke ajiyar xuciya ta nufi part din umma tana rike da gefen cikinta,kuma har lokacin bata daina kuka ba,tsayawa umma tayi cak gabanta yana tsananta faduwa lokacin da idanunta suka sauka akan emaan,wani abu mai kaifi taji yana tsarga mata daga kanta har ixuwa tafin kafafuwanta,ga wani sharp pain dake ratsa xuciyar ta,takasa motsawa balle ta iya amsa gaisuwar da emaan ke mata awahalce,asanyaye kuma ahankali emaan ta rungume umma tana sake fashewa da kuka mai ciwo,umma jitayi kafafuwanta sun fara rawa gefe daya kuma ruwan hawaye sun cika mata idanu saboda harga Allah kuma har axuciyar ta bataji dadin ganin emaan acikin wannan yanayin ba,saurin zaunar da emaan tayi tana kallonta keenly tace"whats wrong with you?"Sosai emaan take kuka tace"cikina umma".gaban umma ne ya sake faduwa tace"meya samu cikin naki??"kuka emaan tacigaba dayi instead of answering ummas question,sai kawai umma ta mike xuciyarta na mata xafi da radadi,bandaki tashiga ta hada ma emaan ruwan wanka sannan ta dawo parlon tana kallon yadda emaan ke juye-juye asaman kujera,wasu hawaye ne suka xubo mata tayi saurin goge su sannan ta taimaka ma emaan tayi wanka wanda hakan yasa taji dadin jikinta Sosai,agadon umma ta kwanta tana jin saukin cikin nata yayinda umma tashiga tahada musu light breakfast itada alameen,acikin tray ɗaya ta hada mishi nashi sannan ta nufi part dinshi,bakinta dauke da sallama tashiga fortunately lokacin yayi wanka har ma ya canxa kaya,dube-duben car key dinshi yakeyi tashiga,dagowa yayi da sauri yana kallonta xuciyar shi babu dadi,baiso ta rigashi xuwa inda yake ba,koba komai umma is a very nice person kuma kamar uwa take awurinshi,saida ya russuna sannan ya gaisheta ta amsa tana kallonshi closely inda ta fahimci shima yana cikin damuwa mai tsanani,ajiye tray din tayi tace"ga breakfast "kallon tray din yayi ya kalleta domin cikinshi ya cunkushe baya tunanin xai iya cin abinci alokacin,kafin yayi magana tace"ya Karin hakurin mu?sai kuka ji wannan mummunan labarin,fatan mu Allah ya mishi rahama yasa yana aljannah"runtse idanu alameen yayi yace"Amin umma,nagode Sosai "tana fita daga parlon tace"make sure kaci abinci kafin ka fita"bata tsaya jin amsar shiba ta koma part dinta domin hankalinta ya koma wurin emaan,xama tayi agefen gadon tana kallon emaan wacce har lokacin ke xubarda hawaye tace"kin dade kina ciwon cikin ne?"girgixa kai emaan tayi tace"a'a"umma tace"me suka ce a asibiti?"shiru emaan tayi sabbin hawaye suna xubo mata,umma tace"Ina miki magana kinyi shiru"riko hannun umma tayi tace"bugewa nayi jiya,ban samu xuwa asibiti ba muka taho"cikeda damuwa umma tace"Tashi kici abinci sai muje asibitin"girgiza kai emaan tayi hawaye yana zubo mata tace"bazan iya ci ba"hankalin umma ne ya tashi,tasa dogon hijab sannan tasama emaan ta figi jakarta da car key sannan ta taimaka ma emaan ta mike tana rike da ita suka fito har main parlour,adaidai nan suka ci karo da alameen wanda shima ya fito xai fita,ganin su yasa ya tsaya cak yana jin nauyin umma na shigar shi,domin ko mutuwa na kunyar idon mahaifi,wannan dalilin ne yasa ya kalli emaan ya ce"cikin ne har yanxu?"da mamaki ta dago tana kallon fuskar alameen,domin ya shayar da ita ruwan mamaki fiyeda misali,cikeda girmamawa yace"umma bari na kaita asibitin,basai munyi stressing dinki ba"yafada saboda baxai iya wulakanta emaan agaban umma ba,Sosai hakan yayi ma umma dadi taji damuwar datake ciki na raguwa,tace mishi"dama akwai masu xuwa ta'axiyya kuma kaga mami suna asibiti sai anjima xa'a sallamosu "jinjina kai alameen yayi yasa hannu ahankali ya jawo emaan daga jikin umma ya mayar da ita jikinshi,alokaci daya suka sauke wata deep ajiyar zuciya,kanta ya dora akirjin shi yana tafiya da ita ahankali yayinda emaan tayi suman tsaye saboda mamakin wannan lamarin,shima ta bangaren shi wani xafi yakeji even though yana jin wani irin al'amari ajikinshi,like this is the first time daya taba kwantar da mace akirjinshi,Ahankali yake takawa yana jin takaici yana lullube shi,har kuma suka karasa wurin motar ahankali suke tafiya,adaidai back door ya tsayar da ita carefully saboda yana ji ajikinshi umma is looking from a distance,hakan yasa ya bude mata motar tashiga mamakin alameen na kashe ta,baki ta bude wangalau tana kallon ikon Allah,me alameen ke nufi da hakan?itace tambayar da batada amsarta,driving yake calmly saide xuciyar shi cike take da damuwa mai tsanani,Tafiyar minti ashirin da biyar sukayi suka karasa asibitin,ya juyo akaikaice yana kallonta ganin har lokacin bata motsa ba balle yasa ran xata sauka daga motar,afusace yace"get out!"yadda yayi maganar saida ya daki xuciyar emaan,dama tasan xa'a rina,ahankali ta sauko jikinta asanyaye ta fito daga motar tana dafe cikinta,shikuma yasanya dior glasses dinshi yana tafiya majestically xuwa cikin asibitin,emaan kuma na binshi abaya ahankali tana matse kwalla,dayake expensive private hospital ne babu mutane dayawa aciki,hakan yasa nurses suka taso da sauri suna rike emaan wacce takai kololuwar galabaita,emergency suka shiga da ita shikuma ya xauna a reception yana tunanin dake damun xuciyar shi,Sosai aka duba emaan aka mata duk wani abu daya kayamata,kuma alhamdulillah taji sauki fiyeda misali,xama yayi yana facing dr Anthony daya kirashi,ya kalli alameen carefully sannan yace"ya akai ta buge sosai haka?sauran kadan tafara internal bleeding fa,ka gode ma Allah domin matarka ta tsallake rijiya da baya,dan haka dole akula da ita sosai sannan akula da shan maganinta"kallon dr anthony kawai yakeyi amma ko kadan ba saurararsa yakeyi ba,yasan dai magana dr Anthony keyi amma ko kashe shi xa'ayi baxe iya maimaita abinda yafada ba,fita yayi bayan ya gama magana ya wuce pharmacy da prescription din da suka bashi,bai wani dade ba ya gama siyan maganin sannan ya koma emergency inda emaan ke kwance tana maida numfashi ahankali,xuwa lokacin ta daina kuka haka kuma cikin nata ya daina ciwo,tunda yashigo ta kafe shi da idanu tana jefa mishi kallon tsana,wallahi kiyayyar shi take ji acikin xuciyrta fiyeda misali,saboda damkar daya mata ne yakusa mata illa abanxa a hofi,shima irin kallon datake mishi yake mata,bai ce komai ba illa ajiye drugs din dayayi agefenta ya juya yafara tafiya sai kuma ya sake juyowa yana kallonta,itama har lokacin shi take kallo,kalmashe hannu yayi akirji sannan ahankali ya furta"kina tunanin banida abin yi ne da xaki kwanta kina kallona instead of you to get your filthy body up?"yafada yana fesa mata xaxxafar iskar bakinshi,runtse idanu tayi tana kokarin mikewa xaune without saying a single word,but she's feeling very weak alokacin,wata nurse ce tashigo tana yi ma emaan sannu sannan ta dago da ita xaune tace"Saifa ka taimaka mata,saboda jikinta babu karfi"wani kallo ya wurga ma nurse din baice komai ba,nurse din ce ta taimaka ma emaan ta mike sannan takaita har gaban alameen,emaan dake runtse idanu tana jin dan xafi-xafi tayi saurin dafe bango domin  bata bukatar taimakonshi,cikeda dauriya take takawa tana runtse idanu sabbin hawaye suna xubo mata,dafarko baiyi niyyar riketa ba sai kuma ya fuxgo ta ta fado jikinshi yana sake tamke fuska,kokarin kwace jikinta tafara yi tana mutsu-mutsu ajikinshi wanda hakan yasa alameen ya xaro manyan idanunshi yana kallon fuskar emaan,ita kawai so take ya saketa,dan haka axafafe yace"ki nutsu before I lose it,idan nayi gaba baxan dawo ba,kinsan dai I don't care about you at all,so hakan baxai min wahala ba".sai alokacin ta daga fararen idanunta da suka koma jaa tana kallon shi,shima ita yake kallo alokacin,samun kansu sukayi starring at each other with ultimate hatred,shine yafara janye idanunshi yana janta da karfi har suka karasa parking space,ajiyar xuciya ta sauke sannan ta shiga motar shima ya shiga yana driving saidai hankalinshi gabadaya na wurin mami da fauxa....Mami ce ta ruko fauxa wacce har lokacin take kuka mai taba xuciyar me sauraro,Mami da Abba sai lallashinta sukeyi har suka fito compound din asibitin,Nurain ne yake driving Abba Na xaune agaba sai mami da fauxa abaya,fauxa na kwance akan laps din mami tana kuka kamar ranta xai fita,ahaka suka karasa gida kowa da tunanin dake ranshi,musamman mami dake alla-alla su karasa gidan domin tasamu xama da alameen,a main parlo suka tarar da umma tana xaune da wasu baki wanda suka kasance neighbors din Fauxa,kallo daya suka mata idanunsu ya ciko da ruwan hawaye,xaunar da ita sukayi a parlon tana karbar gaisuwa tana jin kamar xuciyarta xata tarwatse,dan haka ta mike jiri na dibarta ta wuce part din mami,da kallon tausayi kowa ya bi fauxa wasu na girgixa kai alamar tausayi,tafiyar minti ashirin da biyar ta dawo da su emaan gida,ahankali ya juya yana kallon emaan dake baccin ta peacefully dama dr Anthony yafada mishi xasu mata allurar saboda tasamu enough rest,fitowa yayi daga motar ya bude back seat yana dukan kujerar da karfin gaske,saide ko motsi emaan batayi ba kuma gashi tanata sauke ajiyar zuciyah,ya dade Sosai awurin without knowing what to do,yasan it doesn't make sense ya shiga gidan yace suxo su dauketa,afterall kallon mijinta suke mishi,ji yayi kanshi ya sake daukan xafi ya rasa me xaiyi alokacin,Nurain ne yakaraso inda alameen yake yace"yaya hurry up Abba yana kiranka,I think something important xakuyi discussing "kai kawai alameen ya gyada ma nurain without saying a single word,saida ya sauke deep breath sannan yayi shahadar jawo ta ya rungume akan faffadan kirjinshi,emaan sake shigewa jikinshi tayi tana cigaba da baccinta abinta,sai kawai ya tsaya yana kallonta wani takaici na xuwar mishi wuya,sosai ya dauke ta irin rikon da akema baby ya shiga main parlor kanshi tsaye,babu damuwar ko xai hadu da wani acikin ranshi,bai lura da su mami dake xaune a parlon ba yashiga ciki,saidai yakai tsakiya sannan yajuya da sauri yana kallon hajjo daga saki salati tana tafa hannu,tace"ohh ni Hajjo me zan gani?"bai damu da maganar hajjo ba ya kalli gefen hagu inda mami tayi mutuwar xaune tana kallonshi har wani xaro ido takeyi jikinta na rawa kamar mazari,ga Numfashinta dake baraxanar seizing saboda tsananin firgici da tashin hankali,ta kasa gasgata abinda idanunta ke gani,emaan ce ajikin alameen dinta ya rungumeta kamar wanda xa'a kwace mishi ita,gabanta ne yayi mummunan faduwa ta wani runtse idanu hawayen dake makale a idanunta suka xubo suna gangarowa asaman cheeks dinta,hawayen mami ne yasa yaji jikinshi yayi sanyi domin yasan she'll think about so many things wanda ba haka bane,umma dake gefe ya kalla yaga ta sunkuyar da kanta kasa,mama da mummy sunyi wuri-wuri da ido suna kallon ikon Allah,musamman mummy wacce hakan ya mata dadi fiyeda misali,ji yayi jikinshi yayi sanyi yakasa motsawa daga inda yake,hajjo tace"bawan Allah tsayuwar me kakeyi har ynxu?dalla wuce da ita bangaren ka,dan ban shirya ganin abinda yafi karfina abangaren fatima ba"bai ce komai ba illa wucewa da yayi sumi-sumi kamar sabon munafiki,hankalinshi atashe yake saboda yasan mami is heartbroken,wani irin xafi xuciyar shi ke mishi ya nufi part din umma,hajjo ce tayi saurin shan gabanshi tace"hala kai kurma ne bakaji mena fada maka ba,cewa nayi kutafi can bangaren ka kuyi fitsarar acan"hade rai ya sakeyi xai shiga ta tsaya abakin kofar tace"kasan Allah baxaka ajiyeta anan ba,juya kutafi can dan ban shirya ganin abinda xai tayar min da hankali ba tsofai-tsofai dani kuke son lalata min ido"bai da option din daya wuce ya shiga part din shi yana jin takaicin hajjo na xuwar mishi wuya,yana shiga ya jefata saman kujera....komawa hajjo tayi taxauna tana kallon umma tace"dole ki sunkuyar da kai,abu dai babu tsari ya wani dauko ta kamar jinjira "sake sinne kai umma tayi batace komai ba,mami kuwa afusace ta mike jiri na neman kayar da ita ta shiga part dinta,xubewa tayi asaman kujera tana jin numfahsinta na kaiwa dakyar,shikenan alameen ya cuceta ya gama da rayuwarta,saide ko da me yake yawo sai ya saki emaan,wallahi baxai xauna da emaan ba,saide suyi duk bala'in da xasuyi,ashirye take awannan gabar domin baxata xuba ido ba su umma su shanye d'anta kamar yadda suka shanye Abba,that she promised herself...







*CHEF 👩🏽‍🍳 ZEEE ONLINE CLASS 2.0*

My fans kamar yadda kuka sani cooking is my passion,hasalima nafison girki fiyeda rubuta littafi,kunga kenan riba biyu xaku kwasa domin wannan class din will change your life for good,xan koyar daku enticing recipes fara Daga traditional cuisine's,continental cuisines,Arabian dishes,snacks da drinks a kudi kalilan,wanda suka shiga free class dina sunsan banxo da wasa ba,domin na shirya tsaff wurin kawo muku kalolin abinci masu dadi da tsayawa arai,ku garxaya ku shiga online class dina domin koyan kayatattun girkuna kala daban-daban..

Price-1k only

Pay into 6319878551 Zainab Yusuf

Fidelity bank and send your proof of payment via 09037909996



Zaynabyusuf aka chef zeee👩🏽‍🍳.

EMAANWhere stories live. Discover now