PAGE 12

140 4 0
                                    

Eman...🥀

Page 12

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

   Cikeda damuwa ya Fauza ke kallon yaya Sadeeq wanda ke cakalar abinci,ko loma daya yakasa yi,duk da ya tattara hankalinshi da nutsuwa awuri daya yana kallon abincin,itama sai takasa cin abincin ta tsaya tana kallon shi,har wata rama yayi kwana biyun nan,ta rasa me ke damunshi arayuwa da zai fitar dashi daga cikin hayyacinshi haka,ajiyar zuciyah ta sauke zuciyarta na k'ara yin rauni akan lamarin,saboda yaya Sadeeq mutum ne da baya b'oye mata damuwar shi ko kadan,yana bayyana mata halin dayake ciki tun kafin ta tambaye shi,amma tana mamakin yanzu dayake rufe mata damuwar shi,tana lura da abubuwan dayakeyi wanda a iya fuska suka tsaya basu k'arasa zuci ba,this is the first time da hakan ke faruwa acikin rayuwar aurensu,shiyasa ya Fauza ta shiga damuwa mai tsanani,murya asarke tace"yaya Sadeeq..."sai kuma tayi shiru ta rasa me zatace mishi,ta kalli gefen danake nima bawani cin abincin nakeyi ba,saita langabar da kai tace"ke ma cikin damuwar zaki sani eman?why are you not eating?"wani irin tausayinta ne ya saukar mini,na fara cin abincin ba don ina so ba,saita juyar da kallonta zuwa ga yaya Sadeeq wanda still yake kallon abincin amma tunani ya sha kanshi,kenan baiji maganarta ta farko ba,Damuwar dayake ciki Na tayar mata da hankali,tana sanyata cikin tunani da damuwa mai tsanani,hannun shi ta riko tana kallon shi da idanunta wanda suka cika da ruwan hawaye,sai alokacin ya d'ago tareda zuba mata jajayen idanunshi wanda suka k'ankance,wani irin tausayinta ne ke ratsa shi,yasan yadda Fauza ta mayar da damuwar shi tata,yasan yadda yake acikin zuciyarta,shi din mai girma ne da daraja awurinta,amma tayaya zai fada mata asalin damuwar shi?ta wacce hanya zai fahimtar da ita?da wani bakin zai fad'a mata cewar Son eman ne yajefa shi cikin halin dayake ciki wanda bashida ikon fitar da kanshi?ta yaya zai fada mata damuwar shi bayan yasan babban tashin hankali zaayi idan ta San cewar son eman yakeyi,so mai tsanani wanda yake tunanin bazai iya karasa rayuwar shi cikin farin ciki batareda ita ba,yasan tsananin kishin Fauza bazata tab'a saurarenshi ba,ajiye tsananin kishin Fauza agefe,babu wacce zata saurareshi da wannan batu mai kama da cin amana da yaudara,shi kanshi bai San yadda akai ya fad'a cikin wannan tashin hankalin ba me barazana da farin cikin shi harma da lafiyar shi,ya kasa sukuni yarasa inda zai tsoma ranshi yaji dadi saboda yasan ko sama da k'asa zasu had'e eman bazata tab'a amince ma soyayyar shi ba,haka zalika zai lalata karamar fahimtar  dake tsakanin hajiya kwaise da umma,uwa uba eman wacce take a d'ofane acikin gidan wacce batada kowa dakuma mataimaki sai Allah,yasan abubuwa dayawa marasa dadi ne zasu faru,shiyasa tun farko baida niyyar fadama kowa wannnan maganar,ya birneta amatsayin sirri acikin zuciyar shi,sede hakan yak'i yiwuwa saboda masifar damuwar daya shiga ta wannan dalilin,baya iya baccin kirki,baya iya cin abinci,ya canza ma matar shi da 'ya'yan shi akan lamarin da idan ya fito fili zai rasa kowa ne,domin ya tabbatar baida koda 1% na mallakar eman,wannan tunanin Na k'ara d'aga mishi hankali domin son Eman yake da gasken gaske.
"Meke damunka ne?kwana biyu gabadaya ka canza"cewar ya Fauza wacce muryarta ke rawa alamar tana gab da fashewa da kuka,this is unlike her Sadeeq,wannan Sadeeq din takasa gane kanshi,ahankali yafurta"zan miki bayani,amma ba yanzu ba"tasan za'a yi hakan,saita tashi da sauri ta shige bedroom dinta tana fashewa da kuka mai tsanani,wai yau Sadeeq dinta ke b'oye mata damuwa,she can't take it anymore,wayarta dake gefe ta jawo tayi dialling numbar hjy kwaise,hjy Na ganin kiran Saida gabanta ya fad'i,dama kwana biyun nan tana cikin damuwar halin da Fauza ke ciki,tunda eman taje gidan Fauza ta rasa nutsuwar ta,saide babu yadda zatayi da umarnin abba,amma da tuni taje da kanta tafitar da eman da k'arfin tsiya,"Hello mami "Fauza ta furta cikin muryar kuka,zuciyar hjy kwaise ce tayi tsalle tamkar zata faso daga gangar jikinta,tayi saurin zama tanajin kafafunta bazasu cigaba da iya daukarta ba,arayuwa tana bala'in son yaranta wanda kowa yasani,bata iya b'oye sansu agaban kowa shiyasa take tsananin kula dasu bata bari su shiga cikin damuwa bare azo gab'ar da fauza ke kai wato su zubar da hawaye akan wani abu ,Fauza dinta ce ke zubar da hawaye??,innalillahi wainna ilaihi raji'un,tafurta afili kuma da karfi Salima da inteesar suka waro ido suna kallon maminsu wacce tsantsar tashin hankali ya bayyana asaman fuskarta."Fauza kuka kikeyi?"hjy kwaise ta tambaya with a broken heart, Ya Fauza ta k'ara fashewa da kuka mai karfi tana fadin"I can't take it anymore mami".gaban hjy ne yayi mummunan faduwa,bakinta Na rawa tace"what are you talking about Fauza?".ajiyar zuciyah Fauza ke saukewa ajejjere sannan tace"Ya Sadeeq is in pain,yana cikin damuwa,amma nakasa gane meke damunshi,yak'i fad'a mini".duk da maganar fauza bamai tayar da hankali bace saida hjy taji wani iri,magana ce wacce  ba saita kawo ma hjyr ba amma tayi raising dinsu akan wannan turbar ,sai sun fad'a mata kome k'ank'antar matsala,asanyaye hjy tace"shiyasa banso zaman eman ba awurinki,kinsan ita haka take duk inda ta sanya kafa sai an samu matsala,kuma inada yak'inin itace tai mishi wani abun ko kuma yagaji da zamanta awurinku,ki saurareni da kyau Fauza,Sadeeq babban gatan kine aduniya idan aka cire ni,ki tashi kisan yadda zaki sa eman ta dawo gida,Na tabbatar akanta ne tunda bai taba miki haka ba sai yanzu,bawan Allah ay yayi kokari,bansan dalilin abba nayin haka ba amma yanzu dole kisa ta had'a kayanta babba da karami ta dawo gida,zanyi ma abba bayani domin sauk'ak'a lamarin".
Da sauri ya Fauza tace"a'a mami,miye had'inshi da eman dazai shiga damuwa saboda ita,Yarinyar da ko magana bata fiye yiba,kullum tana cikin d'aki sai munyi dagaske take fitowa falo,tsakani da Allah ina jin dadin zama da eman kuma Na tabbatar damuwar shi ba akan zamanta bane,wani abun ne Na daban wanda yakasa fada mini".tacigaba da fadin"dan Allah karki  ce ma Abba komai akai,danni Na canza shawara ma, anan wurina zata cigaba da zama har Allah ya kawo mata miji".
Cikeda fada hjy kwaise tace"mahaukaciyar ina ce ke Fauza?ina tunanin ki yatafi?bari kiji ko kina so ko bakya so sai eman tabar gidanki,yanzu ina cikin hidimar bikin Salima amma ina kammalawa zan juyo takanki,gobe kizo da wuri".tana gama fadin haka ta kashe wayar,ya fauza ta rike kai cikeda damuwa,meyasa Mami take dragging eman cikin maganar?ina ruwan damuwar Sadeeq da eman?? shine abinda takasa ganewa kuma yake daure mata kai.
Tashin ya Fauza yayi daidai da miqewa ta tsaye ina Binta da rakiyar idanu,sai Na mayar da kallona zuwa fuskar yaya Sadeeq wacce tayi wani irin jaa,kallona yakeyi k'asa kasa without blinking his eyes,sai naji wani mugun tausayin shi ya kama mini zuciya,naji zuciyata na son sanin damuwar shi koda kuwa banida abin magance masa ita,saboda damuwar shi ta shafi gidan gabadaya,haka rashin walwalar shi ma tayi affecting kowa nagidan musamman yaya Fauza,wacce nakejin zan iya mata komai aduniya.ahankali kuma asanyaye nace"tunani bazai maka maganin damuwarka ba yaya Sadeeq,saide ya janyo maka wani ciwo na daban,I believe na shiga cikin jarabawar rayuwa masu tsauri,dan haka all will be fine shine abinda zan fada maka,kayi hakuri kadaina tunanin nan domin bazai samar maka mafita ba anawa ganin,addua zamu dage Dayi kuma dan Allah kaje wurin ya Fauza,she need you at the moment "na fada in a pleading tone,kallona kawai yakeyi without saying a single word,wanda hakan yasa nayi tunanin ba lallai yaji abinda na fad'a ba domin he's lost in thoughts,lost in the world of his own memories,saina juya nashiga dakin ta,akwance Na tarar da ita ta juyawa kofa baya,da sauri ta juyo atunaninta yaya Sadeeq ne,saita sauke ajiyar zuciyah with a disappointment look amma tayi kokarin sakar mini karamin murmushi,zama nayi na riko  hannunta ina murzawa ahankali with so much care,kafin nayi magana tace"bansan meyasa yaya Sadeeq ya zab'i wannan hanyar ba acikin zaman aurenmu,wacce bazata kaimu ga madakata mai kyau ba,kuma ni bai saba mini irin haka ba"tafada zafafan hawaye na zubo mata,dayan hannuna nasa na goge mata hawayen sannan nace"kiyi hakuri ya fauza"saboda ban San me zance mata ba,nima I'm lost just like her,asanyaye ta gyada mini kai sannan tace"thank you eman"jiki na ne yayi sanyi Sosai,wani bangare na  zuciyata is feeling guilty,kamar nasan asanadiyya ta hakan ke faruwa dasu,shigowar yaya Sadeeq ce tasa Na mike ina kallonshi yayi wani iri,na fita daga dakin wondering what's wrong with him,kodai wani ciwon ne ya kamashi?na tambaya kaina lokacin dana shiga dakina ina jin guilty conscience na kamani,bansan meyasa nake having this kind of feeling ba.
Baice komai ba ya zauna tareda d'ora kanshi acinyar fauza,batai k'asa a gwiwa ba tafara shafa mishi gashin kanshi wanda ya kwanta luf,cikeda tsananin mamaki ta tab'o ruwan hawaye akan cheeks din shi,ta furta "kuka?"jikinta na wani irin rawa kamar mazari,tayi saurin dago da fuskar shi mai zubar da hawaye,bakin ta nawani irin rawa take fadin"kuka yaya Sadeeq?contract din aka hana?"ta tambaya even though tasan damuwar shi tafi karfin ta contract,tabangaren shi kuwa hawaye ne kadai yakeyi ya samu sassauci,even though yana danne zuciyar shi da karfin tsiya,ya runtse idanu yana jin bai kyautawa ya Fauza ba ko kadan,bata cancanci hka daga gareshi ba,shima be  San lokacin da son eman ya mamaye mishi zuciya ba yake kokarin kwantar dashi a gadon asibiti,asanyaye yace"Fauza calm down,magana zamuyi"tana share hawaye tace "Ina jinka".yace"kiyi hakuri kinji"gyada kai ya Fauza tayi shikuma ya cigaba da fadin"nayi alqawarin zan fada miki amma ba yanzu ba,dan haka kidaina damun kanki akan abinda ke damuna,nima zanyi kokarin kiyaye kaina daga shiga damuwa,kisani komai ze faru ina sonki,ina sonki,ina sonki Fauza ".daga haka ya rungumeta iya karfin shi tausayintane yasa Sosai yau din yayi kokarin being intimate with her saboda ta samu saukin rad'ad'in da take ji.
Washegari da less damuwa Fauza ta tashi,ranta ya saki saboda ta aminta da maganar yaya Sadeeq tunda har alqawari yamata,zata cigaba da binshi ahankali har lokacin da zai bayyana mata komai,sannan zatayi iya bakin kokarinta ganin bata bar shi shi kadai ba bare ya riqa unnecessary tunani,shima ba yabo ba fallasa ya tashi unlike yesterday,hakan ya kara yima ya Fauza dad'i,tana masifar kaunar bawan Allahn nan,domin tsantsar kirkinshi da iya mu'amala uwa uba son dayake mata da mutuntata dayakeyi is out of this world.
Afiya ce ta shigo falon mummy da mugun sauri har da tuntub'e da throw pillow,fuskarta d'auke da mamaki,baki asake take kallon mummy tana haki,mummy wacce yau ta tashi cikin tsananin farin ciki saboda bakon da Rafee'ah zatayi yasa take jinta cikin farin ciki mara misaltuwa,dole ta kara mikewa akan sadeeya tunda Rafee'ah ta samo nata wanda koda tsiya koda tsiya tsiya bazata bari ya kufce musu ba,tace"ke lafiyar ki meya faru?".cikeda tsantsar takaici Afiya tace"idan nafada miki abinda nagani na tabbatar sai zuciyar ki tayi bindiga,gara kizo muje ki ganema idonki".jikin mummy har rawa yake ta dauki mayafi Afiya ta shige mata gaba har suka karasa babban tsakar gidan su wanda yagaji da haduwa,Rafee'ah da saurayinta na cikin wani kebantaccen wuri wanda akaima kwalliya da transparent glass,kana iya ganin komai ta waje,anan yammatan gidan ke zance idan bukatar hakan ta taso,da hannu Afiya ta nuna ma Mummy sabuwar Lifan din da akayi parking,cikin rashin fahimta mummy tace"ban gane ba,mashin kike nuna min,shine abin mamakin?".ajiyar zuciyah Afiya ta sauke sannan tace "na bakon Rafee'ah ne fa,dashi yazo"wani irin duhu ne ya mamaye ma mummy idanu,ta kunduma wani uban zagi tana dukan kirjinta tace"ni Rafee'ah zata ma tonan silili acikin kishiyoyi?"afusace take tafiya zuciyar ta Na suya,wani irin bakin ciki ne wannan?Rafee'ah ta rasa wanda zata kawo mata sai talaka matsiyaci?me lifan saboda tsiya?ta karasa inda Rafee'ah ke zaune tana sakin karamin murmushi,kallon saurayin tayi wanda yaci farar jallabiyar shi mai wando fari,ya sanya black ordinary shoes da hular shi yar karama,fes fes dashi saide kallo daya zaka mishi kasan ba shida wadata,kayan jikin shi ne suka kara bakantawa mummy rai tace "ki kashe ni ki huta Rafee'ah,yanzu wannan matsiyacin zaki kawo har cikin gida?banda tsaurin ido irin nashi na marasa kunya me nasama yaci bare yabaiwa na kasa?".cikeda ladabi yace "barka da rana"dogon tsaki taja zuciyarta na wani irin turirin bakin ciki take"matsiyaci fita daga gidan,kada ka kara gigin dawowa ko ka kara kula mini yarinya wallahi saina sa an b'atar dakai b'acewa ta har abada,matsiyacin banza da dogon buri,banda hauka ina kai ina Rafee'ah yar masu kudi jikar masu kudi ga kyau ga ilimi?kema shashasha sakarya kika zauna kina bud'e mishi baki ke gaki ta kwarai".simi simi saurayin ya tayar da lifan dinshi yafita,ta jawo Rafee'ah kamar ta rufeta da duka saboda bakin ciki da takaici.atsakiyar falo ta watsar da ita tana huci,Allah yasota hjy kwaise dasu umma sun tafi kasuwa,mama ma tafita da yau taga masifar rayuwa,wani irin abin kunyah ne wannan?Ita data gama cika bakin sai an kalli wanda 'ya'yanta zasu aura shine Rafee'ah ta kawo mata mai Lifan,tace"duk abin nan danake yi is for you amma gani kuke kamar takura muku nakeyi,yanzu dan Allah wannan wani irin zagi ne?".Rafee'ah dake zubar da hawaye tace"saboda na faranta miki ne mummy,kullum kina cewa mu fito da miji ".ta juya kai cikeda bakin ciki tace"yanzu wannan ne mijin?wannan ne miji awurinki?akan wannan abin dakika mini gara ki dauki hannu ki zabga mini mari yafi min sauki".cikeda mamaki Rafee'ah tace"kada Allah ya nuna mini wannan ranar mummy,dan Allah kiyi hakuri".tace"bana tunanin zaki kara mini abinda zai bak'anta min rai fiyeda wannan,ke ko tsoron irin mutanen nan bakya ji,kila ma d'an damfara ne ko barawo ko kuma d'an fashi".afiya tace "gaskiya na dade banga mutum mai tsaurin ido ba irin shi,ko tsoron shigowa gidan nan beyi ba da Lifan,inda zaki San asalin matsiyaci ne Lifan din kenan garesa,ni wllhi gara mutum yazo mini akafa "mummy tayi saurin cewa"astagfirullah Allah ka raba bawa da wahala,ke kuma mara mutunci mai kaunar ganina acikin damuwa bari kiji,zamu sa kafar wando d'aya dake idan kika sake kula wancan matsiyacin".da Toh Rafee'ah ta amsa sannan ta shiga dakinsu,last 2weeks ta Had'u da Sayyid,masifar mummy ce tasa ta bashi numbarta amma sam bai kwanta mata ba sai ynzu da mummy tayi musu iyaka.
A layin dake gaban gidan su yayi parking,motar shi k'irar Range Rover na parke agefe,driver dinshi na ganin shi yayi saurin fitowa ya karba mukullin lifan din,shikuma ya shiga drivers seat yana kallon abokin shi kuma aminin shi mai suna Anwar,"an dace?"anwar ya tambaya with excitement,asanyaye Sayyid yace"Rafee'ah batada matsala,amma ansamu mishkila wurin mamanta"ajiyar zuciya anwar ya sauke ya ce "da sauki kenan"batareda sayyid yace komai ba yafara driving suka bar unguwar yana tunanin yadda dukiya tazama babbar jarabawa acikin rayuwar shi.
Da tunanin eman Bilal ya kwanta arai,hakan yasa shi lulawa duniyar mafarkinta,koda ya tashi tana mak'ale acikin ranshi,eman mutum ce mai shiga rai da kuma zuciyar mutane musamman a kallo nafarko dazaka mata saide  ka canza ra'ayi daga baya,kamar yadda mahaifinsu Alhaji Kabeer ya umarce shi k'arfe tara daidai ya shirya cikin kaftan dinshi mai kyan duba,interview zaije domin already an ajiye mishi slot din aiki,hira sukayi Sosai da HR din Finlak industries amaimakon interview me tsauri da akeyi,anan take aka ba Bilal aiki mai babban matsayi,yanzu zai mayar da duk wani tunanin shi ga Eman,wacce yakeda buri dakuma muradin aure,duk da ya lura tana da d'aga kai sannan miskila miskila ce,shi yayi alkawarin mallakar ta ta kowacce hanya domin bazai bari ta sub'uce mishi ba,saide zai k'ara bata lokaci takara hutawa kafin ya bayyana mata k'udurin shi,yayi wani murmushi Na gefen baki wanda hakan ya zamto mishi jiki.A halayyar zahiri bilal mutum ne mai cika ido da cikar Kamala,gashi yanada kyau daidai misali,ya iya flows da gayu shiyasa yammata suka mutu akanshi musamman a US da turawa ke cewa suna sonshi,hakan ne kara ma kanshi girma yanajin kanshi yakai kuma yakawo!.




Zaynab Yusuf✍🏼

EMAANWhere stories live. Discover now