PAGE 18

134 4 0
                                    

Page 18

  Duk yadda fauxa ke son saka kwayar idanunta acikin Na yaya Sadeeq yak'i bata damar yin hakan,saboda ya lura da yadda mamakin reaction dinshi akan maganar data fada mishi,sai ma ya juya yafita daga kitchen din itakuma tabishi da kallo har ya kurewa ganinta,ajiyar xuciya ta sauke sannan ta kalli eman wacce ke hada musu orange mojito,she looks so cute and innocent,moulding sugar da mint leaves takeyi tamkar babu damuwa acikin ranta,har ga Allah take kaunar eman kuma tayi trusting dinta shiyasa ta amince ta xauna agidanta domin kallon kanwarta take mata ta jini,saide tarasa dalilin da kwana biyu take jin wani iri gameda xaman eman din,tana jin tamkar wani abu Na shirin faruwa da ita, sede bata San menene ba,jiki ba kwari ta fita daga kitchen din tana murmushin yak'e takoma falo suka cigaba da hira,jefi-jefi take kallon yaya Sadeeq tana d'ora naxarinta akan mixanin hankali,tana tuna maganar da colleague dinta awurin aiki tayi mata akan hakan,Fauxa tace"firdausi saurin me kike hala?"firdausi tace"yau nice da oga fa"dariya fauxa tayi tace"ni yanxu halina kwance yake,ko bana nan eman xata dora girki duk da nafison na rik'ayi da kaina".
Tunda fauxa ta ambaci sunan eman firdausi ta saki baki da hanci tana kallon fauxa,kallon ne yasa fauxa tsarguwa tace"menene?"saida firdausi ta xauna sannan tace"budurwa ce agidanki fauxa?"gyada kai fauxa tayi ahankali sannan tace "eman fa kanwata,yar umma"kyabe baki firdausi tayi tace"har yanxu da sauranki,ban tab'a xaton ke shashasha bace sai yau,gaskiya an shaki an warke ".cikeda mamaki fauxa tace"ban gane me kike nufi ba"firdausi tace"rashin wayonki yayi yawa,banda shirme ya xa'ayi ki yadda budurwa kamar eman ta xauna agidan ki,yarinya son kowa qin wanda ya rasa,ga kyau ga shape abin son duk wani namiji mai lafiya,gaskiya na raina wayonki da lissafinki ".shiru fauxa tayi tana kallon firdausi saide xuciyarta is beating faster than normal,"xamani ya canxa fauxa,yanxu ko kanwarki da kuka fito ciki daya tana iya cin amanar ki ta yaudareki itada mijin ki,wallahi bakiga ta xama ba,ki ce kawai tabar miki gidan ki shine kwanciyar hankalinki,dan wallahi maxan yanxu basuda tabbas matan ma haka,cin amana ta xama ruwan dare,wani labari danaji uwarsu daya ubansu daya amma take having affairs da mijin yayarta"gaban fauxa ne ya fadi ta xaro ido batareda tace komai ba.
Firdausi ta dora da"kawata yakamata kisan abunyi tun yanxu,wai menene dalilin dawowar ta gidanki ne?"fauxa wacce kamar baxa tace komai tace"Kinsan an fasa aurenta shine umma ta dauki fushi da ita Sosai,sai abba yace taxo wurina ta xauna kafin umman ta sauko"murmushi firdausi tayi tace"ke kuma kin yarda da hakan ko?haba fauxa ina kaifin tunanin ki ya tafi?daga jin wannan maganar umma ce ta tsara ma abba saboda tana son cimma wani quduri nata akanki,karki manta fa kishiya baxata tab'a sonki tsakani da Allah ba"shiru fauxa tayi tana kallon firdausi ko kiftawa babu,firdausi tacigaba da fadin"na tabbatar akwai plan dinda suke son aiwatarwa,idan ba haka ba miye umma na daukar fushi da ita kamar akanta aka fara fasa aure?"kyakkyawar xuciyar fauxa ce ta hanata fada ma firdausi dalilin fasa auren eman,saboda bataso ta kara fadin negative abu akai duk da xuciyarta is very weak and heavy,maganganun firdausi sun shigeta saide tayi kokarin  dora su akan mixanin hankalinta tanata sak'a da warwara,"nide shawarar dazan baki itace kisan duk yadda xakiyi tabar miki gida"tana gama fadin haka ta dauki jakarta sukai sallama ta tafi,abinda ya tsayawa fauxa arai shine yadda mamin su batason xaman eman awurinta,could it be the reason?ajiyar xuciya ta sauke sannan tayi dialling numbar yaya Sadeeq shine kiran data mishi daxu da rana.cikeda mamaki yaya Sadeeq ke kallon fauxa ganin she's lost in thoughts sannan yayi tapping shoulders dinta,asanyaye yace"what's wrong with you?what are you thinking about "karamin murmushi ta yi faking sannan tace"just random thoughts "ajiyar xuciya ya sauke dan ya tabbatar ba gaskiya tafada mishi ba.
Bilal yace "ko gajiyar aiki ne?naga yau din kamar bake ba kin xama shiru shiru"karamar dariya Fauxa tayi tace"I'm having a serious headache shiyasa "cikeda damuwa yaya Sadeeq ya tab'a forehead dinta yana fadin"sorry dear,Allah ya baki lfy,lemme get you pcm"jiki Na rawa ya haura Sama ya dauko maganin itakuma tabishi da kallo,dakan shi ya ciro maganin ya samata abaki tasha tana sauke ajiyar xuciya,eman ce taxo falon tana kallon direction din ya fauxa tace"food is ready"sai alokacin ya Fauxa ta kalli Kayan jikin eman wanda sukayi revealing figure 8 feauture dinta duk da doguwar rigar atampa ce ajikinta dinkin kaftan,ganin ya fauxa bata ce komai ba yasa yaya Sadeeq riko hannunta yace "ciwon kan ne?ga abinci tagama May be harda yunwa"itadai kallonshi takeyi batace komai ba,saida ta mike sannan takalli inda eman ke tsaye tace"Sannu da aiki eman,nagode "tana gama fadin haka tahau dining tana xuba ma su Anum abinci,yaya Sadeeq ne ya xauna sannan Bilal,eman kuwa diban nata tayi ta haura sama,da kallon mamaki yaya Sadeeq yabita wanda karaf suka hada ido da fauxa wacce ta kafeshi da idanu kamar xata cinye shi danye,saurin janye nashi idon yayi yafara cin abincin wondering what's going on in her mind,duk da xuciyar shi nafada mishi tunanin fauxa ba alheri bane.bata wani ci abincin ba ta mike ta haura sama,da kallo yaya Sadeeq ya bita yana jin a bit uncomfortable,tana shiga bedroom tayi dialling numbar firdausi,wannan ne karo na farko dataji xata iya tambayar shawarar kawa acikin rayuwarta saboda batason d'aga hankalin hjy kwaise,wata xuciyar Na bata shawarar ta share batun kawai ta cigaba da aikin ladan datakeyi da kyakkyawar niyya,saurin kashe kiran tayi tana fadin"a'uxubillahi minasshaidanir rajim "so take ta cire wannan tunanin daga ranta sai taji ta kasa,ajiye wayar tayi tashiga dakin da eman take wacce har lokacin ke cin abinci,da sauri ta dago tana kallon fauxa,saitayi murmushi tace"ashe kece"saida fauxa ta xauna sannan tace"ehh,wani labari naxo baki wanda ya rikitamin tunani"xaro ido eman tayi tace"Ina jinki ya fauxa".kallon eman tayi Sosai sannan tace"labarin akan wata colleague dina ce,tana da aure da yaranta hudu,sai ta dauko cousin sister dinta tariqa tayata xama tunda ita tana fita aiki,long story short ashe mijinta da cousin dinta suka fara soyayyah,sai yanxu da cousin din tayi ciki garin bincike aka gano,data sume saida ta kwana uku sannan ta farfado saboda ta aminta dasu amma suka ci amanar ta,labarin nan ya girgixa ni"tunda fauxa tafara magana eman ta xaro ido waje tana sauraronta cikeda mamaki,can tace"gaskiya sunci amanar ta kuma Allah baxai barsu ba,da sannu xasu girbi abinda suka shuka,itakuma Allah ya bata hakuri da juriyar cinye wannan jarabawar "Sosai maganganun eman suka sanya ya fauxa dana-sanin abinda ta aikata,saboda tana iya ganin tsantsar gaskiyar eman ta cikin kwayar idanunta,eman nada pure heart shiyasa ko kadan batayi tunanin wani abu ba gameda labarin fauxa,jiki asanyaye fauxa takoma bedroom dinta ta jingina da kofa tana jin babu dadi,she shouldn't have done that.
Gabadaya firdausi tayi poisoning mind dinta successfully,ring dinda wayarta keyi yasa ta duba,ganin firdausi ce me kira yasa tayi saurin picking,firdausi tace"sorry kawata,kinsan yau oga awurina yake,yanxu ma ya fita siyo abu ne shine nasamu sararin kiranki,hope kinyi tunani akan maganata".fauxa tace"i don't think xasu ci amanata"tsaki firdausi tayi tace"shiyasa tun yanxu xakiyi ma tufkar hanci,kafin ad'ebi lokaci me tsaho,kinsan fa icce tun yana d'anye ake tankwara shi,idan ya bushe sede akarya shi,kinga kuwa ba haka akeso ba"shigowar yaya Sadeeq cikin dakin ne yahana ya fauxa magana,kamar mara gaskiya tayi saurin ending call din,baice komai ba yayi unlocking wayar ya duba dawa take waya,ganin numbar firdausi yasashi kallonta carefully yace"bansan ki da daukar xancen kawaye ba,idan akwai abinda na miki ki fada min I'll apologise gladly,idan wata damuwar ce wacce kike gani baxaki iya fada mini ba you should tell mami about it"hawaye masu xafi ne suka xubo mata,sai tayi saurin hugging dinshi tightly at the same time kissing him passionately with all she got,ajiyar xuciya yaya Sadeeq ke saukewa ajejjere yana feeling every bit of her touch,sun dauki tsahon lokaci sannan ya fauxa tace "I'm so sorry"tafada tana placing kisses a fuskarshi shikuma yana mata murmuring sweet endearments da suka sata xubar da hawaye,they're both lost in the world of love and ecstasy.
Shiru eman tayi tana tunanin labarin da ya fauxa tabata,sai alokacin ta fahimci dalilin bata labarin ta wata fuskar daban,numfashi mai nauyi ta sauke tareda dora tunanin ta akan mixanin hankali,ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari bata koma bacci ba bayan ta idar da sallar asubah,aikin gida ta taya ya fauxa sunata hira cikin kankanin lokaci suka kammala,bedroom kowa ya wuce domin yin wanka ya shirya,kamar kullum abaya eman ta saka tayi rolling beautifully,ta riko jakarta wacce Tayi matching outfits dinta sannan ta sauko kasa,lokacin ya fauxa bata sauko ba,yaya Sadeeq dasu Anum ke breakfast,gaishe shi tayi sannan ta debi nata takoma falo tana ci,yariqa kallonta yana tunanin dalilin yin hakan,ajiyar xuciya Fauxa ta sauke sanda taga eman a falo sai ta wuce dining sukayi breakfast.
Gaban tane ya fadi lokacin dasuka kammala cin abincin,taji wata damuwa ta shigeta,bata tab'a jin hakan ba sai yau,saita daure tana kallon eman tashige motar yaya Sadeeq wanda kamar jira yake yayi saurin fita daga gidan,xaman dabaro ya fauxa tayi tana tunani har saida Anum tace"mummy we're getting late".driving take amma hankalinta Na wurin su eman,haka take bata iya sa damuwa arai ba.
Kasa-kasa yake kallon eman wacce gabadaya ta maida hankalinta akan titi tana tunani,ahankali yace"meyasa jiya kikayi dinner a bedroom yau kuma breakfast a falo?an miki wani abu ne?"girgixa kai tayi sannan tace "haka kawai"ta bashi amsa a takaice,yace"ban gane haka kawai ba"kallonshi tayi tace"yaya Sadeeq there's nothing to worry about "jinjina kai yayi sannan yace"ok"yana sake kallonta cikeda birgewa,kullum kara mishi kyau takeyi,idan ya mallaketa yagama samun komai aduniya,sai ya lumshe ido yana tunanin fauxa wacce jiya tafara portraying sabbin halaye wanda bai San dasu ba,yace"yau ma 4 xaku gama lectures din?"tace"lemme check "duba timetable tayi tace"ehh"kafin yace wani abu tace"xan koma gida dakaina basai na wahalar dakai ba"strictly yace "who are you to tell me that?"shiru tayi bata ce komai yace"karki sake tunanin hawa motar haya kinji ko?"gyada mishi kai tayi batace komai ba har suka karasa school,ta sauka yanata kallonta har ta kurewa ganinshi.
A lecture hall ta ga kausar Na xaune tana pressing phone,saita xauna agefenta tace"good morning "cikeda farin ciki Kausar tace"morning babe,ya kike?"da lafiya eman ta amsa sai kausar tace"Khaleed is coming to kano to see me,anjima xamu hadu a gusto,ay xaki rakani ko?"dan xaro ido eman tayi tace"meyasa baxai je gida ba?"tace"just few hours xamuyi spending,amma yace xai dawo next weekend"shiru eman tayi tana kallon Kausar,tace"pls don't say no".eman tace"skipping practical class xamuyi kenan"kausar tace"no kin manta anyi cancelling practical yau?"eman tace"ban lura ba,but i don't think xan iya rakaki "with a sad face kausar tace"is alright then".yadda kausar tayi ne yasa eman jin wani iri,tana tunanin xuwa amma tana jin tsoro.
Lumshe idanu Rafee'ah tayi ta kalli sadeeya wacce ta xabga uban tagumi,Afiya na xaune kan kujera mummy na tsaye na musu lectures din aure,,"duk kudin ubanki,duk kyanki duk jin dadin gidan uba aure shine gatanki a duniya ,shiyasa kuka ga na dage kwarai dagaske ganin kun tashi tsaye akan wannan lamarin"ta sin ce habar xani tafito dawani turare tace"maman Shaheeda ce takawo min,aiki yake bana wasa ba,ashe 'ya'yanta da ke auren masu kudi duk ta sanadin wannan turaren ne,itama haka kishiyoyi suka sata agaba suna jifan yaranta kada su samu mijin aure,dayake Allah ba axxalumin bawanshi bane sai wata kawarta ta rakata wurin wani malami,xancen danake muku 'ya'yan shaheeda biyu yanxu,safina da Rabia kowacce da cikin fari,dan Allah meyafi wannan dadi?".shiru sukayi Afiya na murmushin jin dadi,Rafee'ah da sadeeya na juya kai cikeda takaici.
Mummy tacigaba "ni yanxu burina shine na aurar daku alokaci d'aya,bakin ciki da takaici ya kashe wasu,muyi kwana bakwai muna events xuciyar wasu tayi bindiga".cikeda jin dadi afiya tace"musamman wannan shegiyar yarinyar eman,har yanxu ban manta abinda tayi min ba,ai wllhi ban hakura ba saina koya mata hankali,saina sa ta xubar da hawaye fiyeda wanda ta xubar a baya,xata San ta tab'o afiya gudan jinin mummy kuma jikar Larai".mummy tace"nikuma saina tabbatar uwarta tayi kukan jini,habaici da bak'aken maganganu xanta xuba mata kamar ruwan sama na sauka,nide fatana shine ku fara amfani da turaren nan ko hankalina xai kwanta"afiya tace"karki damu mummy,in shaa Allah sai mak'iyanmu sun sha kunyah,wannan alkawari ne daga gareni "dadi Sosai mummy taji tace"Allah ya muku albarka"tana kallon sadeeya da Rafee'ah that are not interested with the convo,suna jin ba dadi domin ko a ido ka kalla kasan waye marar gaskiya amma dayake abin son kai ne shiyasa mummy ke fadan maganganu,hausawa sunyi gaskiya gwano baya jin warin jikinshi saina wani!.
Mummy Na rangaji ta fita main parlor saboda tun yanxu tafara jiyo kamshin nasara,hjy kwaise ce xaune da mama suna dan tab'a hira,sai itama ta xauna tana kallon su cikeda farin ciki,mama tace"wannan farin cikin Na farar daya fa?fada min meya faru?"mummy Na dariya tace"kin fiye son xance kamar baxawara"mama tace"nide fada mana munaji "adaidai nan umma tafito ta xauna akusada hjy kwaise,kafin tayi magana mummy tace"sharrukan da ake qulla min ta karkashin kasa ne Allah yakawo karshen su,magani Yadaina kamani da 'ya'yana mutum ko kasar india xai tafi bin malamai yayi abanxa ,dakike ganina yanxu naci  dubu sai ceto,bata mutum ba wallahi saita Allah,dama inde ka rike gaskiya kana xaune Allah xai maka maganin makiyanka,mama tace "xancen ki dutse mummy,Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu"ajiyar xuciya umma ta sauke sannan tace "gani Mami,yi hakuri sai yanxu Na idar da laximi "hjy kwaise tace "bakomai,dama bangaren yayansu xa'a gyara tunda yakusa dawowa,ina ganin har su fenti sai an canxa da furnitures gabadaya "umma tayi shiru tana sauraron hjy kwaise,ay ita yakamata tayi ma abba wannan maganar ba ita ba,amma ta daure tace"zan sanar mishi in shaa Allah,Allah ya dawo mana dashi lafiya"daga haka umma taja bakinta tayi shiru,mummy tace"ni wani sa'in mantawa nake da Al'ameen,saboda bashida xumunci ko kirana awaya ya gaisheni bayayi,wani xubin har tunani nakeyi nace ko d'an nawa fushi yake da uwar shi?"hjy kwaise tace"Kinsan yanayin aikinsu sai ahankali,nima bawata wayar arxiki mukeyi ba".ta fadi hakan domin ta rufe bakin mummy.
Da karamar jaka Salima tafito inteesar na biye da ita a baya,tace"Mami nixan tafi sai jibi idan Allah yakaimu"hjy kwaise tace"Allah ya kaimu lafiya ki gaisar mini da fauxa dakyau dakyau,ki shafamin kan su Anum,karki manta ki gaidar min da babansu nasanki da mantuwa"murmushi Salima tayi tace"toh mami in shaa Allah,ke kuma umma me xa'a fadawa eman?"da mamaki kowa na falon ya xubawa umma ido yana jiran yaji me xata ce,saitayi karfin halin cewa"ki gaishe min dasu "mummy tace"ba iya sakon kenan ba,bari na ari bakinta naci mata albasa,kice ma eman tana nan kan bakarta kuma yanxu tafara fushi da ita,na tabbatar haka ne axuciyar fatima"mama na dariya tace"aikuwa dai"Salima bata tsaya sauraronsu ba tayi ficewarta,hjy kwaise ta mike taja inteesar suka wuce part dinsu,umma ma tayi saurin mikewa xata wuce saita tsaya ganin shigowar abba,sakin baki sukayi suna kallon yadda taje tana mishi sannu da xuwa sannan tajuya yana binta abaya suka wuce part dinta,ko lura dasu beyi ba saboda yadda yaga umma na farin ciki ne ya bashi mamaki.nan ko da biyu tayi saboda ta cunkusa musu bakin ciki.
Cikeda takaici  mama tace"tsinanniya daga gani ta tab'a karuwanci "mummy wacce bakin ciki ya toshe mata wuya ta hadiye dakyar tace"matsiyaciyar ba,na dade banga yar iska irin fatima ba idan kika cire hjy kwaise".mama taja wani uban tsaki tace"ji nake kamar na shak'e tsinannu,bakiji ba wai afadama abba a gyara dakin Al'ameen,dan xalunci shi baxeyi a aljihun shi ba ".mummy tace"kibari kawai,watarana saina shak'e daya daga cikin su saide ayi duk bala'in da xa'ayi,wannan wacce irin masifa ce Allah ya hadamin amatsayin kishiyoyi?"haka suka cigaba da banbami sannan kowacce ta wuce part dinta,mama na fadin"ke ma daya shegiyar sai nayi maganinki "mummy dake bud'e kofa tace"Ina gamawa dasu kanki xan dawo bak'ar annamimiya,kema da kin samu wuri ba karamin iskanci xaki baxa ba".

Karfe biyu daidai suka gama Lectures,kausar wacce ta damu tace"dan Allah eman ki rakani,just 3 hours zamuyi spending,before 4 in shaa Allah xamu dawo,bafa wani wurin bane,restaurant ne"shiru eman tayi tana kallonta,wata xuciyarta nace mata kiyi tafiyarki gida kawai wata kuma nace mata ki rakata mana tunda ba dadewa xakuyi ba,magiyar da kausar ke mata yasa tace"shikenan xan rakaki,amma ki tabbatar kafin 4 din xamu dawo"cikeda farin ciki kausar tace"sure,nasan by now sun kusa sauka a kano,tunda jirgin 1 yabiyo "itadai eman is feeling like kamar tayi xamanta takira yaya Sadeeq ya mayar da ita gida,tana ganin kausar nata waya da Khaleed sanda ya sauka,sai taji gabadaya hankalinta yakasa kwanciya,kausar ta ce"muje"ta ja hannun eman suka shiga mota gaban eman Na ta faduwa,suna tafiya damuwarta na karuwa  ta rasa dalilin jin hakan,ahankali takai hannu ta dafe kirjinta,samun kanta tayi da jin xafi duk da Sanyin ACn dake motar,kausar kam sai video call sukeyi da Khaleed abinta,eman na ganin hanyar gidan ya fauxa taji tamkar tace su sauke ta,sai batayi hakan ba saboda kaddara ta riga fata!.

https://chat.whatsapp.com/IAyL0ePAUS42UGNBn7eHV6
(Eman comments section)

***Kina son turaren wuta masu classy and unique scent?masu kamshin gidan 'yan gayu, turare mai kama gida ya mayar dake abar so yar kwalisa? kinason turaren da tun daga tsakar gida za'a San yes Ke Cikakkiyar mace ce?hajiyata kina son durot mai tsananin kamshi da akayi shi cikeda tsafta?kina son exclusive room freshners?kina son amsa sunan cikakkiyar mace ?wacce ta amsa sunanta Na Sarauniya?BAKHOOR INCENSE PLACE gidan kamshi got you covered, maza ku garzaya Bakhoor incense place domin siyan d'aya ko sari, ni na gwada kuma naji dadi domin nagari ne kuma na mayar da kudina gida Chasssss💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼a tuntub'e mu ta wannan lambar domin siyan Turaren wuta yan gaske.
09037909996

Zaynab Yusuf✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now