PART 23

109 4 0
                                    

EMAN....PAGE 23

  Tun da yafara magana ta ji wani xaxxafan xaxxabi ya rufeta,banda rawa ba abinda jikinta keyi,xuciyarta cikeda tsananin damuwa da tashin hankali,bata tab'a tsintar kanta cikin  wannan tashin hankalin ba,ko lokacin da aka fasa aurenta da Aliyu bataji irin  wannan damuwar ba me kokarin tarwatsa mata xuciya,she couldn't believe her hears masu jiyo mata kalaman sadeeq masu kama da digar ruwan dalma acikin kunnenta,nor could she believe her eyes wanda yake hasko mata yaya Sadeeq on his knees agabanta yana rokar ta abinda ko sama da kasa xasu had'e she'll never accept,gumi ke xubo mata kamar an watsa mata ruwan xafi,idanunta kuwa sunyi jaa ga hawaye masu xafi suna gangarowa,wani irin tashin hankali ne wannan?wace irin kaddara ce wannan?ji tayi kirjinta yayi mata nauyi gawani xafi dayake mata kamar an cinna mishi wuta,bakinta yayi nauyin dako motsin kirki takasa yi balle tayi magana,sumewa take son yi amma hakan ya gagara,ajiyar zuciya ya sauke ajejjere sannan yacigaba da fadin
"I can understand what's going through your mind at the moment,domin ko ni I couldn't believe my heart dafarko,nayi kokarin cire ki daga cikin xuciyata amma abun ya gagara,maimakon nasamu sauki sai yakasance kullum sabon sonki ne ke kara shiga xuciyata,kullum ina cikin damuwar ya xanyi da wannan lamarin,saboda nasan baxai tab'a xama me sauki ba awurin mu,nayi kokarin birne sonki acikin raina  amma the more I force myself to forget you the more kaunarki ke kara wahalar dani,inajin baxan iya cigaba da rayuwa ba without you,trust me wannan ne last option din daya rage mini,da ace akwai wani better option din I'll go for it,saide ahalin dana tsinci kaina fada miki abinda ke cikin raina shine daidai,domin nagaji da wahalar da zuciyata,I'm so tired eman,xuciyata na bukatar hutu da nutsuwa,sannan baxata samun hakan ba sai daga wurinki".at this point eman ta daina apprehending abinda Sadeeq ke fada mata,anya yana cikin hankalinshi?kodai shaye shaye yafara shiyasa yake  fada mata wa'innan maganganun masu kamada almara,sai kace a shirin wasa kwaikwayo,tana cikin wannan tunanin taji yace"ki taimakeni eman kamar yadda Allah ya taimake ki,kiji tausayina sannan kisa aranki wannan abun bayin kaina bane yin Allah ne,I can't do anything about it,ki tallafeni eman ki rik'eni da hannu biyu,ki amince da kaunar danake miki dan Allah,wallahi my life is useless without you,bansan wani hali xan shiga ba idan kika ce a'a,Dan Allah find a small spot acikin xuciyarki for me,don't reject me pls".kuka kawai eman tafashe dashi mai tsananin karfi da sauti sannan da dukkan xuciyarta kamar wacce takeson amayo gabadaya damuwar dake xuciyarta,wani irin bala'i ne wannan ya risketa?ita shikenan baxa tayi rayuwarta kamar yadda kowa keyi ba cikin farin ciki?why is life being so difficult for her?da karfin gaske Sadeeq ke son jefata cikin bala'i da masifa,in ba haka ba miye ma'anar abinda yake fada mata,cikeda axaba take tapping cinyoyinta idan ma bacci take ta farka daga wannan mummunan mafarkin,sai daya goge hawayen dake xubo mishi sannan yace"take it easy on yourself eman, duk abinda kikeji yanxu nafi ki jinsa,for a long time nake dawainiya da sanki acikin xuciyata,i consult few people akan wannan maganar,ciki harda malamai,babu wanda ya fada mini haramcin hakan,meyasa xamu bar Halas dan kunyah?"kallonshi kawai take da tsananin mamaki tana cigaba da kuka kamar wacce uwarta ta mutu,ya runtse ido yana jin saukar hawayenta kamar xubar garwashi acikin xuciyar shi,yace"stop crying pls,wallahi I'm also feeling your pain,ki barni da abinda ke damuna pls karki karamin da kukan ki,I mean what I'm saying eman,dan Allah kiyi shiru".sakin baki tayi tana kallonshi sede har lokacin bata daina kukan ba,yaya Sadeeq na cikin hankalinshi kuwa?yasan me yake fada mata?ya daure yace"wipe your tears eman,bana son ganin ki ciki damuwa,dan Allah kibar kukan nan".zuwa yanxu ta tabbatar da gaske komai yake faruwa,sannan dagaske Sadeeq Na kaunar ta,domin tana iya kallon hakan ta cikin idan shi,ahankali kuma asanyaye ta samu damar cewa"inde dagaske kana sona kuma kana kaunata kuma kai me son farin cikina ne ka rabu dani,ka manta dani,ka cire eman acikin babin rayuwarka,kasa aranka tamkar bana duniyar gabadaya,ni kuma in shaa Allah daga yau baxan sake kwana a gidanka ba har gaba da abada,sannan ba lallai na sake bari wani abu yahadamu ba,ko ahanya idan Na hango ka xan canxa wata,xan guje ma haduwa dakai yaya Sadeeq,sannnan ina fatan Allah xai shiga lamarinka ya cire maka kaunata daga cikin xuciyar ka,nagode Sosai da taimakon da kuka mini,Allah ya saka da alheri ya jibanci lamuranku ".tana kaiwa nan ta mike cikin hanxari ko ganin gabanta batayi Sosai, sadeeq  yayi saurin riko gefen hijab dinta,still yana durkushe agabanta kamar sabon maroki ko kuma mabaraci yace"eman karki min haka,don't punish me this way,karki hukunta xuciyar da babu komai cikinta sai kaunar ki,don't do this to me dan Allah,ki tsaya ki saurareni xaki fahimceni"fixge hijab dinta tayi ta tsallake shi tawuce xuciyar ta kamar xatayi bindiga ta haura sama,shikuma ya yi xaman dab'aro yana fashewa da kuka mai ciwo mai tab'a xuciyar mai sauraro,da ace agabanta yake kukan da k'ila ta tausaya mishi.ganin kuka baxai mishi maganin matsalar shiba yasa ya Mike jiki ba kwari ya haura saman shima,dakin datake yake kallo yana jin xuciyar shi Na luguden daka,sai ya shiga bedroom dinshi ya daura alwala ya gabatar da nafila yana rokon Allah ya kawo mishi dauki acikin wannan lamarin,karatun Al-Qur'an dayayi ya yaye mishi kaso mai yawa na damuwar shi,dama shi Al-Qur'ani waraka ne.
Tana shiga dakin ta fada saman gado tana sake fashewa da matsanancin kuka me karya xuciyar me sauraro,tana tuna dinbin alherin da yaya Sadeeq yayi mata arayuwa,da ace wani abun ne daban sai inda karfinta yakare wurin cikar burinshi,da ace wani abun ne daban xata jajirce ta tsaya mishi tsayin daka har sai ya mallaki abun,amma wannan lamarin is beyond her,yafi karfin tunaninta da shallow reasoning dinta,idan xataci amanar kowa bai kamata taci amanar Fauxa ba,wacce ta xame mata bango abar jingina kuma tudu na dafawa,fauxa ce ta karbeta da hannu bibbiyu alokacin dako wacce tahaifeta bata kaunar sanya idanu akanta,fauxa ce ta tsaya tsayin daka ta tabbatar da little farin cikin datake ciki ayanxu,ta riqeta ta kaunace ta take mu'amalantar ta kamar kanwarta ta jini,fauxa ta xamto wani bangare na rayuwarta wanda baxata iya bada labarinta batare dashi ba,kuka takeyi Sosai domin Sadeeq ya bata tausayi sannan she can feel and understand his pain,ta tabbatar da gasken gaske yake kaunarta wallahi,ta runtse idanu tanajin ta kamar asaman gajimare,kanta sai juyawa yake asannu kuma ya dawo daidai,tarasa me xatayi adaidai wannan lokacin,ta tabbatar harda xaman ta agidan ya k'ara rura wutar sonta axuciyar yaya Sadeeq,dama ace she can went back in time da wallahi baxata yarda taxo gidan ba,koda kuwa tsirenta umma xata riqayi,xata jure ma kowacce wahala tunda tasan duk tsanani duk wuya bawa baya dawwama acikin bakin ciki,mikewa tayi kafarta na hardewa tafara hankado kayanta dake shirye acikin press,tana jin baxata sake minti 20 acikin gidan ba,xata koma wurin umma ne saide duk abinda zai faru ya faru,sannan tayi alkawarin baxata fadi dalilin komawarta ba koda ace abba ne ya tambaya tunda shine yace takoma gidan,wata xuciyar tace ko gidan babanki xakije?sai da gabanta ya fadi data tuno dashi,tana girgixa kai hawaye na xubo mata, tasan babanta baxai taba accepting dinta ba,not at this point,batada option din daya wuce komawa wurin umma tunda dai itace ta haife ta itace tafi kowa sanin yadda xatayi da ita,idan ma wani wurin xata kaita ta xauna ita wannan ba damuwar ta bane,damuwarta itace baxata sake kwanan gidan fauxa ba.
Asanyaye ya bud'e kofar yana kallon yadda ta watso kayanta daga cikin press,tana tura su cikin akwati tana kuka,gyara tsayuwar shi yayi sannan ya rungume hannu akirji sai kallonta yake,itakam har lokacin batasan da shigowar shi ba,ranshi ne yayi mugun b'aci yana tunanin ina hankalin eman ya tafi?uban me xata je gidan ta fada musu abirkice haka?yace"what do you think you're doing?"gabanta ne yafadi ta juyo da sauri tana kallon shi,yace"this isn't the right thing to do kuma wallahi baxan bari kiyi abinda bai kamata ba,inde baso kike komai ya lalace ba,I promise you idan kika sanya kafa kika tafi a halin dakike ciki nikuma baxanyi kasa a gwiwa ba saina fadama Abba dalilin komawar ki,xance mishi akan nace ina sonki ne Kuma aurenki xanyi".ta dade tana mamakin Sadeeq kafin tayi cilli da rigar dake hannunta ta silale akasa tana kuka yace"kinga shi Namiji ne na tabbatar xai fahimceni,sannan ki tashi ki gyara kayanki da fuskarki kafin dawowar fauxa idan tadawo ta fahimci wani abu daga gareki you left me with no choice dole zan fada mata gaskiya ne,and lastly ki xauna kiyi tunani mai zurfin akan soyayyah ta,karki xo daga baya kina dana sani idan mai afkuwa ta afku,xaki koma ga Allah kina me danasanin wannan decision din naki,sannan Na tabbatar fauxa dasu Anum baxasu yafe miki ba."yacigaba "ki share hawayen ki eman,domin baxan tab'a hakura dake ba koda ke baxaki so ni ba,son dana ke miki ya ishemu,and I'll make sure nasamu cikar burina"yana kammala fadin haka ya juya ya fita ya bar eman da baki abude saboda tsananin mamakin shi.

EMAANWhere stories live. Discover now