PAGE 03

193 4 0
                                    

Eman...🥀

https://arewabooks.com/book?id=64a568cb8194f8956681682b

Episode 3

    I couldn't say a word,saina bita da rakiyar idanu har ta fice daga dakin,jiki asake nakoma Na zauna shirim ina sak'a da warwara,alokaci daya Na tsinci kaina cikin sabon tashin hankali,saboda babban burina shine zamtowa matar Aliyu,it's my dream tun ranar damuka had'u,I can't afford to lose him,my life will be incomplete without him,na tabbatar rashin Aliyu a kusa dani will make my life miserable,he's my happiness,my peace and comfort zone,sosai zuciyata ke azalzalata akan na karba wayata wurin umma,i really want to know his stand akan abinda ya faru,even though I'm quite sure yana cikin mawuyacin hali but Aliyu will never abandon me even in his wildest dreams,na tabbatar baze tab'a matsawa daga gefena ba matukar yana raye.

But why am i feeling scared and restless?zuciyata ta kasa samun nutsuwa akan maganar aurenmu,ina ji ajikina tamkar wani mugun abu ne zai kara faruwa dani,domin aduk lokacin da mutum ya sab'awa iyayen shi sakamakon baze mishi  kyau ba,take me as an example,ban duba rayuwar k'unci da bakin cikin da umma tayi ba agidan babana,gashi abinda yafaru dani na kokarin dakushe mata farin cikin data samu agidan Abba,da ace na bi maganar umma da haka bata faru ba,k'addarace ta fitar dani alokacin da umma ta zana mini layin shamaki,fitar data jawo mini bala'i da masifa take kokarin tarwatsa mini rayuwata,just one mistake but my life is crumbling.I couldn't control my tears,saboda shi kadai ne idan nayi nake samun relief,i really want to discuss about my problems with umma,amma banda wannan right din kamar yadda ta fad'a,na lalata yar siririyar alaqar data rage tsakaninmu,dama can babu wata shakuwa mai karfi,umma uwa ce agareni amma Sam babu fahimtar juna atsakanin mu,bazan ce komai akan babana ba wanda nazame mishi tamkar kwallon mangoro wanda yake alla alla ya wurgar don ya huta da k'udaje,rubuce take a kundun kaddarata bana sahun masu sa'a arayuwa,duk wani abu dazai zama silar farin cikina I end of losing it,that is my destiny!.

Shigowar Salima da inteesar ne yasa na d'ago jajayen idanuna ina kallon su,wata azababbiyar kunyah ce ta lullubeni,sainayi saurin saukar da kaina k'asa domin bazan iya cigaba da had'a ido dasu ba,Salima ce ta zauna agefen dama inteesar ana hagu,one look din dana musu naga tsantsar tausayina a kwayar idanunsu,salima ce ta riqo hannuna tace

"Eman whatever happens you're my sister,kin zamto yar uwarmu ta jini,abu mafi muhimmanci shine ka aikata kuskure kuma kayi realising cewar yes I made a mistake shima rahama ce,bana bin boka ba'a buga min k'asa amma na tabbatar bazaki aikata abinda akace kinyi ba,idan kuwa ya kasance dagaske ne bazan daina mamaki ba har karshen rayuwata,domin Tabbas jarabta ce daga Allah,Eman kinada tarbiyya daidai misali,burin kowacce uwa,held your head high kidena sunkuyar da kanki k'asa cikin kunyah matukar you're innocent saboda the truth shall always prevail,ita gaskiya d'aya ce".!

Ajiyar zuciyah ta sauke sannan tacigaba da fadin"karkiyi overthinking akan komai,kibar lamarin ki awurin Allah batareda damuwa ba ko fargaba,sannan ki karbi duk wani yanayi da kika tsinci kanki da hannu bibbiyu kisa aranki they're part of your destiny,Eman duk rintsi duk wuya kicigaba da addua da niyyar Allah shine me komai,asannu zai kawo haske cikin lamarin ki".

Hannu biyu nasa na rungume Salima iya k'arfina,ta zame min big sister dinda na rasa long time ago,Allah yajikan sabeeha yasa ta huta,Salima always reminds me of my sister sabeeha wacce rasuwar ta is still fresh in my mind,tasha baqar wahala kafin takoma ga Allah.inteesar ce ta katse mini gajeran tunanina ta hanyar cewa

"Eman you're my sister no matter what happens,no matter what life throws at you,we'll always be there for you ".kukan danake riqewa ne ya kufce mini,na rungumesu iya karfina ina fadin

"Nagode,nagode,nagode".

Salima tace"inteesar zubo mana abinci,tun breakfast ban kara cin komai ba,Na tabbatar Eman ma najin yunwar".da toh ta amsa sannan ta fice,a main kitchen ta tarar da mummy a zaune tana ordering workers suna zuzzuba abinci,ta kalli inteesar tace

EMAANWhere stories live. Discover now