PAGE 52

125 6 0
                                    

EMAAN.....PAGE 52

Written by Zaynabyusuf✍🏼

   asanyaye umma tashigo dakin emaan tana kallonta keenly,emaan dake xaune agefen gado ta dago tana kallon umma,ajiyar xuciya umma ta sauke ganin emaan wasn't crying,tace"har yanxu baki shirya ba?"rolling eyes emaan tayi tace"umma kaya kawai xan sa"gyada mata kai umma tayi ta ce"hurry up,kin barshi yanata jiranki"emaan batace komai ba ta jawo black abayan data ciro daga press tasaka,rolling veil din tayi abinda bata fiye yiba kenan,ta feshe jikinta da turare mai sanyin kamshi sannan ta rataya sling bag datayi complementing dress dinta,tsayawa tayi tana kallon fuskarta a mirror,gani tayi she looks pale kasancewar baxata tuna ranar datayi applying powder ba ko lipstick balle kuma eyeliner,samun kanta tayi da karasawa daf da dresser din ta shafa powder wacce ta dace da fair skin color dinta,nude lipstick ta goga sannan ta sa kwalli tana gyara xaman gyalenta,samun kanta tayi da sakin karamin murmushi saboda ita kanta ta burge kanta saboda wani kyau na musamman ta yi,murmushi umma tayi data ga emaan wanda yafito daga can kasan xuciyarta,samun kanta tayi da xuba ma yarinyar idanu tana kallonta cikeda birgewa tace"you look beautiful daughter "murmushi emaan tayi batace komai ba,umma tace"from now henceforth haka xaki cigaba dayi,kinji ko?naji dadin yadda kikayi move on da rayuwarki like nothing happened,Allah ubangiji ya sanya dawwamamman farin ciki acikin rayuwar ki"cute smile emaan tayi tace"Amin umma na,sai mun dawo"ganin emaan very lively ne yasa hawaye suka taru a idanun umma,it's been long dataga emaan ahaka,hannu ta daga sama tace"Ya Allah ka daidaita rayuwar emaan,ka daidaita aurenta,ka sanya soyayyah,hakuri,kauna da tausayin junansu axukatansu.."tafada tana sakin kayataccen murmushi,ita kanta murna takeyi ganin yadda emaan ta murje yau din kamar ba ita ba...Afiya tagani xaune a main parlour sanye da wata fitted dress tana pressing wayarta,ko kallon gefen datake emaan batayi ba ta nufi part din mami gabanta na faduwa,yau sati uku kenan da rasuwar Sadeeq kuma yauce rana ta biyu da xata shiga part din tun xuwansu,kuma basu sake haduwa da fauxa ba tun faruwar wancan al'amarin,even though emaan tana son suyi magana ta fahimta da fauxan,da salllama ta shiga parlon xuciyarta na tsananta bugawa,idanunta basu sauka akan komai ba sai akan fuskar alameen dake xaune can gefe yana kallon direction dinda mami take,fauxa na kwance akan laps din mami yayinda su Anum keta guje-gujensu acikin parlon,kallo daya ta ma alameen ta tabbatar da baya cikin nutsuwar shi, sosai taga damuwa atattare dashi sai kawai ta tabe baki ta karasa ciki,Anum da Asad suka rungumeta suna cewa"oyoyo anty emaan,we miss you "rungume su tayi tana runtse idanu,hawayen dake makale a idonta suka gangaro suna sauka asaman cheeks dinta,kallon Anum takeyi saboda yadda yarinyar ke abubuwa kamar Sadeeq,kamar su daya da sadeeq hatta maganar su iri daya ce,saurin goge hawayen tayi ta dago idanunta suka sarke acikin na alameen,kallonta yake keenly cox she looks different kamar ba emaan din daya sani ba,warm breath ya furxar tareda d'auke idanunshi daga kanta,itakuma asanyaye ta gaida mami wacce ke kallonta akaikaice tana jin masifar haushin yarinyar data xame mata k'adangaren bakin tulu,ba dama tayi ma alameen xancen saki sai yace Abba na cikin maganar aurensu kuma almost everyday sai ya mishi maganar emaan din,kusan kullum sai Abba ya mishi nasiha akan ya riketa da amana da kuma mutunci,idan ta fahimce shi babu saki yanxu acikin tsarinsa,tana kallon emaan take wannan tunanin yayinda emaan ke kallon fuskar fauxa dake kallonta itama,abubuwa masu yawa ne ke yawo azuciyar fauxa dayake xuwa yanxu idaniya sun gaji da xubar da hawaye,haka xuciya tayi nauyi tafara karbar tawakkali,saidai kallo daya zaka mata kasan bata cikin cikakken hayyacinta,asanyaye emaan tace"pls ya fauxa I'd like to talk to you"ba mami ba hatta alameen kallon emaan yakeyi,lips dinta yake kallo yadda take magana ahankali cikeda nutsuwa ga voice dinta mai dadin sauraro ta dace sosai da ita,asanyaye fauxa ta mike xaune tace"say what you want to say emaan,mami dai mahaifiya tace,mijinki kuma brother na ne,xaki iya maganar ki agabansu".ajiyar xuciya emaan ta sauke sannan tace"I'm sorry for everything fauxa,I didn't mean to hurt you,all I did was for you trust me,wallahi ban tab'a cin amanar ki ba,kawai dai lokacin i was confused ne saboda yadda marigayi Sadeeq ke nuna min he can't live without me,tabbas ina matukar tausayin shi alokacin amma girmanki da qimarki awurina baxasu bari na amince mishi ba,he tried his possible best amma na ki bashi chance,i admit nayi kuskuren tsayawa na saurareshi amma wallahi daga nan babu wani abu atsakaninmu,but I'm so sorry for everything"wayarta ta ciro daga jaka tace"you can through his messages and all babu inda ya nuna cewar soyayyah nakeyi dashi,hasalima one sided love ne"kallonta kawai fauxa tayi without saying a single word,can kuma hawaye masu xafi suka fara xubo mata,tunda emaan tafara magana alameen ke kallonta closely,he can't tell dalilin dayasa maganganunta ke ratsa xuciyar shi,sai kawai ya mike yana cewa"mami xamuje gidan baban emaan,nasan Abba ya fada miki"gyada mishi kai tayi batace komai ba emaan ta mike tabi bayanshi suka fita,da kallon tsana mami ta bita ganin dagaske auren emaan da alameen ya dauru kuma babu ranar rabuwa,suna fitowa main parlor Afiya tayi saurin yafa mayafinta tace"ina bukatar lift yaya"without looking at her face yace"xo muje".kallonta emaan tayi batace komai ba har suka karasa parking space,da mamaki Afiya taga emaan tashiga front seat,shima alameen din kallonta yayi yaga gabadaya hankalinta baya kansu,hasalima wayar ta take pressing even though bawani abu me muhimmanci takeyi ba,lokaci-lokaci yake kallonta yana tunanin maganar datayi ma fauxa,sake kallonta yayi akaro na babu adadi yaga ta dago tana kallon shi itama,saboda tun dazu jikinta ke bata kallonta yakeyi wanda hakan ke sata xama very uncomfortable,da gayya ta wani dauke kai ta mayar kan titi ahaka suka karasa wani hadaddan saloon inda Afiya xataje kenan,sauka tayi daga motar tace"thank you yaya"gyada mata kai kawai yayi ya juya motar suka wuce gidan su emaan,tafiyar minti talatin sukayi suka karasa gidan.after all those security checks aka wangale musu gate suka shiga rantsastsan gidansu emaan,wanda kyanshi da tsarin shi ya wuce misali,ajere suka shiga main parlo kamar abun arxiki kowanne ya xauna da tunanin dake ranshi,baban emaan ne ya sauko yana sakin karamin murmushi lamarin daya ba emaan mamaki kenan ta bude baki tana kallon babanta,if she could remember babanta bai taba kallonta yayi dariya ba saidai taga yana ma wasu,agefenta ya xauna yana kallon ta ita da alameen din closely,ji yayi sun burge shi Sosai,cikeda girmamawa alameen ya gaida shi,baban emaan yace"alameen ka girma sosai,da ahanya naganka ay baxan gane kaba "murmushi kawai alameen yayi emaan ta russuna ta gaida baban nata,da murmushi ya amsa yana cewa"how are you doing?"wani masifaffen dadi ne ya mamaye mata xuciya,saboda wannan ne karo na farko da babanta ke mata magana da farin ciki da komai,hawaye ne suka sauko mata,babanta yayi saurin goge mata kuma ahankali yace"baxan sake xamtowa silar xubar hawayen ki ba emaan,that I promise you "xaro ido emaan tayi takasa yadda da kalaman babanta,hakan yasa baban emaan ya rungume ta iya karfinshi yana daya-sanin abubuwan daya mata abaya,tun xuwansu da Abba yafara jin hakan,saidai baisan ta inda xai fara gyara mistakes dinshi ba,masu aiki ne suka fara shigowa da varieties of drinks,snacks da abinci,kafin kace me sun cike tsakiyar parlon da kayan ciye-ciye,kallon alameen baban emaan yayi yace"feel at home son"sannan ya mike ya haura sama,kallon emaan alameen keyi dake goge hawayen farin ciki,tana dagowa idanunsu ya sark'e acikin na juna,looking at each other kowa da tunanin dake ranshi,saida baban emaan ya dawo sannan kowanne ya shiga taitayinsa,emaan tace"daddy ina su Sultana da Ali?"dan shiru yayi sai kuma yace"basa nan"ya fadi hakan atakaice,even though ta fahimci mood dinshi ya canxa amma bata ce komai ba,yace"daughter what would you like to eat?"hawaye ne suka xubo mata instead of answering him,yace"emaan banason kukan nan"saurin gyada mishi kai tayi tana sakin murmushi,shi dakanshi ya xuba musu abinci a babban plate with enough proteins,saman carpet suka xauna suna cin abincin from the same plate,even though alameen ya na jin kunya,baban emaan ne ya mishi dole dan haka babu yadda ya iya,emaan kuwa bakinta kasa rufuwa yayi saboda farin ciki,haka suka ci abincin cikeda farin ciki banda alameen dake random thoughts,masu aiki ne sukayi clearing parlon leaving fruits da juices behind,ahankali baban emaan ya riko hannunta yace"try to call emaan,where's your phone?"mika mishi wayar tayi yasa numbarshi with a broken heart yayi dialling sannan yayi saving numbers dinta guda biyu,na nigeria dana Uk,Shide alameen kallon su yakeyi without saying a single word,sama baban emaan ya sake hawa ya sauko da wani envelope wanda kana gani kasan kudi ne masu yawa aciki,alameen ya ba daga farko yaki karba sai kawai yaba emaan yace"ki bashi idan kunje gida"gyada kai emaan tayi suna hira jefi-jefi har magrib tayi,yau ce rana tafarko dataji batason barin gidan baban nata,ina ma zasu bari ta kwana koda daya ne
,rai bai so ba ya rakosu har parking space sannan yace"Allah ya muku albarka,Allah ya albarkaci aurenku"alameen ne ya amsa da amin saboda it doesn't make sense yayi shiru kamar yadda emaan tayi,gaban motar baban emaan ya bude mata tashiga yace"Toh daughter sai yaushe kuma?"samun kanta tayi da kallon alameen without saying a single word,alameen dake lure da hakan yace"very soon daddy,nan da 2months xamu dawo"murmushi baban emaan yayi yace"Allah ya tsare"sannan ya rufe mata kofar yana mata waving har suka fita daga compound din,Sosai emaan ke cikin farin ciki mara misaltuwa,she can't believe what just happened,ahaka suka karasa gida babu me cewa komai,saida alameen yayi parking sannan emaan ta ajiye mishi envelope din xata fita daga motar,juyowa tayi da mamaki jin ya rufe motar ta ciki,ahankali tace"ka bude "kallonta ya tsaya yana yi can yace"not until kin tafi da envelope din"da mamaki tace"ai ba nawa bane"yace"ehh,amma nina ce ki dauka"clearly tace mishi"baxan dauka abinda ba nawa ba"tsayawa yayi yana kallonta for few seconds sannan authoritatively yace"dauka ki tafi dashi".stubbornly tace"nifa na fada maka bazan dauki abinda ba nawa ba,if you truly don't want to accept da tun acan ka ajiye"dan xaro ido yayi yace"an fada miki kowa mara kunya ne irinki?"dan xaro ido tayi ta ce"see who's talking about kunyah"yace"dauki  kudin ki hada da kunyarki kibar min mota"akaikaice tace"dama bance xan dawwama acikin motar kaba"baisan ya akayi ba ya sa hannu akan lips dinta yana d'an ja da karfi,saurin runtse idanu tayi yace"saina cire miki baki the next time kika sake min magana in such way"yana kaiwa nan ya dauki envelope din ya saka cikin jakarta yace"kece me bukatar su,so use them"yana gama fadin haka ya bude mata motar,wani kallo ta mishi without saying a word,kusan atare suka sauka daga motar suna tafiya har suka shiga main parlor,part dinshi ya shiga tareda waiwayowa yana kallonta har ta shiga part din umma.da mamaki emaan ke kallon umma da anty habiba dake shirya mata kaya,ganin uban kayan dasuka hada mata yasa ta baki baki tana kallonsu,xama tayi agefen gado umma tace"sannunku da dawowa"murmushi emaan tayi ta rungume umma iya karfinta feeling like the happiest person in the whole world,she can't believe acikin lokacin kalilan ta samu soyayyar mahaifanta Data rasa shekara da shekaru,anty habiba tace"emaan ba kai,wato umma kawai kika gani ko?"murmushi emaan tayi tace"anty habiba ina yini?"harara anty habiba ta galla mata tace "ba ruwana dake emaan,tunda dakika shigo yi kikayi kamar baki ganni ba"sake rungume umma tayi tace"give me few seconds "tana kallon fuskar umma dake dauke da murmushi na musamman,kudin da babanta ya bayar ta ciro ta nuna ma umma tace"baba ne yaba alameen"murmushi umma tayi tace"Allah sarki",anty habiba tace"shine kika taho dasu?"rolling eyes emaan tayi tace"cewa yayi na rike"anty habiba ta jawo jakar tana xaro ido tace"me nake gani kamar pounds sterling?"emaan tace"sune fa"jijjiga kai anty habiba tayi tace"babanki na yinki yanxu,wancan kudin fa daya baki har yanxu suna nan,da cewa nayi asiya miki land umma tace a'a gold yafi,yanxu haka munyi order daga saudia da dubai"jinjina kai emaan tayi batace komai ba ta warware mayafin kanta,anty habiba tace"har yanxu bakya kitso,umma kina kallonta"murmushi umma tayi tace"Toh tace bata so,ko last week anyi min kuma tana kallo"anty habiba tace"haka take xama kamar namiji,ba kitso ba lalle"murmushi umma tayi tace"ke xaki fada mata amfanin su ai"daga haka bata sake cewa komai ba,anty habiba ta ce"wannan kudin ya xa'ayi dasu?"umma tace"bari xan bashi da kaina"itadai emaan kallon su takeyi bata ce komai ba,can dai tace"kayan me kuka hada haka?"anty habiba tace"idan kinje xaki gani"dan xaro ido emaan tayi takalli umma dake murmushi tanata kallon ta cikeda birgewa gefe daya tana jin kewarta mai tsanani na shigarta,anty habiba tace"sai yaushe kuma?"emaan tace"two months yace ma babana".daga haka bata sake cewa komai ba ta shiga bandaki,umma da anty habiba suka cigaba da tattaunawa....cikeda damuwa hajiya fanta tace"ban taba tunanin haka lamarin nan xai juye damu ba,amma kar ki damu tunda already yayi niyyar kara aure,kinga sai muyi amfani da wannan hanyar mu cuxguna musu"shiru mami tayi tana jin xuciyrta na suya,itadai burinta shine ta bude idanu ta ga babu aure tsakanin danta da emaan,hajiya fanta tace"kinyi shiru,nifa bana son Shirun nan naki"ajiyar xuciya mami ta sauke tace"har yanxu kin kasa fahimtata,nifa babban burina shine naga alameen ya saki emaan,duk wani abu wanda ba haka ba baxai gamsar dani ba"hajiya fanta tace"amma kinsan rabuwar su ba abu bane mai sauki,ki duba yadda Abba ya shiga maganar ya kanainaye "mami tace"wannan itace babbar damuwata fanta,i don't know what to do,wallahi da dukkan xuciyata nake kin emaan,saboda ta xame ma rayuwata bala'i da masifa,kuma babban tashin hankalina shine gobe xasu koma London,bana son alameen ya fada cikin tarkonta,na tabbatar idan yafada Allah ne kadai xai iya tsamo shi,ki duba fa yadda uwar tama Abba,kina ganin xasu xuba mishi ido ne?"girgixa kai hajiya fanta tayi tace"ina fa,nasan suna can suna iya bakin kokarinsu"wannan maganar ce tasa gaban mami faduwa tace"fanta fada min me zanyi,wallahi kaina duk ya kulle"shiru hajiya fanta tayi domin batada solution alokacin,sai kawai ta xuba ma mami ido tana kallonta cikeda tausayawa,gabadaya ta rame ta fita hayyacinta,fanta tace"abu nafarko shine ki kwantar da hankalinki mami,babu abinda xai yiwu idan hankalinki ba'a kwance yake ba"mami tace"taya hankalina xai kwanta fanta?ki duba fa kiga halin da fauxa ke ciki"Fanta tace"I know it's not easy, I know yaranki are your weakness amma daurewa xakiyi"shiru mami tayi domin bataga ta inda hankalinta xai kwanta ba awannan gabar.....misalin karfe tara na dare emaan ta xura hijab dinta ta wuce parlon Abba,tana shiga idanunta suka sauka akan fuskar alameen dake xaune agefen Abba suna business talks,xama tayi asaman carpet ta gaida Abba cikeda girmamawa tana kallon gefen da alameen yake gaban ta na faduwa,kunyar Abba yaji yasa for the first time tace mishi"barka da dare"kallonta yayi without blinking yana mamaki,saboda yau ne karo na farko data taba gaidashi,ahankali murya ciki-ciki yace"yawwa "agajarce,kallonta Abba yayi yace"xauna saman kujera emaan"ba musu ta xauna,Abba ya kalli alameen yace"baxan gaji da maka nasiha ba akan xama miji nagari,domin hakan shine cikar mutuntakar ka ta d'a namiji,ka rike emaan tsakani da Allah,kaji tsoronsa alameen,ka bata hakkokinta dasuke rataye awuyanka,sannan ka mu'amalance ta cikeda hakuri,tausasawa da kuma kyautatawa,ka xame mata miji kuma yaya ma'ana kariqa guiding dinta akan lamarin rayuwa da sauransu,idan kamin haka ka gama min komai arayuwa,domin burina shine emaan tasamu nagartacciyar rayuwa"jinjina kai alameen yayi yace"in shaa Allah Abba"murmushi Abba yayi ya kalli emaan yace"nasan bakida matsala daughter,dan haka ki rike mijinki ki bishi sau da kafa,ki mishi biyayya gwargwadon iyawarki kinji ko?"gyada mishi kai tayi,Abba yace"wani time ne flight dinku?"alameen yace"6 am"jinjina kai Abba yayi yace"go and get some rest daughter,goodnight "ahankali tace"saida safe Abba"sannan ta fita daga part din Abba tana jin kewar umma na ratsa ta...washegari tunda sukai sallar asubah basu koma ba,emaan na rungume ajikin umma tana matse kwalla tace"I'll miss you so much umma na "murmushi umma tayi tace"nide fatana shine ki rike auren nan da hannu biyu emaan,akwai abubuwan da antynki tasa miki acikin kayanki,make sure kiyi amfani dasu,and before that tace xakuyi magana da ita xata miki bayani Sosai,dan Allah emaan ki rike auren nan dakyau kinji ko?Allah ya muku albarka"bakin emaan na rawa tace"Amin umma"dakyar umma ta lallaba emaan tayi wanka ganin shida saura,koda tafito umma ta ajiye mata wata rantsassiyar sky blue atamfa da medium size veil,tana fitowa ta sa kayan wanda suka kasance straight gown mai kyan gaske,dinkin ya amshi emaan sosai,dankwalin atamfar da akayi mata hular turban tasa sannan tadan xame shi baya kadan ya xauna daram akanta,saida ta yafa mayafi sannan ta rataya Jakarta Christian Dior,wani amintaccen kyau tayi mara fasaltuwa kamar ka saceta ka gudu,asanyaye ta fito parlon umma lokacin an gama fitar da kayanta umma na xaune alameen ya shigo,kallon emaan yakeyi saboda bai taba ganinta da atampa ba sai yau,samun kanshi yayi da kura mata ido yadda take abubuwa ne ke tsaya mishi arai,ganin bashida niyyar daina kallonta yasa umma ta mika mishi kudin tace"ungo nan alameen,bana son jayayya"bai da yadda xaiyi ya karbi kudin yace"Nagode umma,mun tafi"daga haka ya juya emaan tabishi da kallo,sake rungume umma tayi for the last time sannan suka fita main parlor inda kowa na gidan ya fito domin musu sallama,fauxa da mami ne kawai basa wurin amma hatta mummy saida ta fito,afiya nata jefa ma emaan kallon hassada ganin emaan ta wuce ma saninta,driver ne yakaisu aminu kano international airport,alameen na gaba emaan na binshi abaya suna tafiya gwanin ban sha'awa,sai dai har suka isa Abuja babu wanda yayi magana acikin su....a first class lounge suka xauna a nnamdi azikiwe international airport,emaan sai waya takeyi da umma,tana ajiyewa ta kira babanta ta sake mishi sallama,anty habiba ta kira sannan kausar,duk wayar da takeyi idanunshi na kanta saide kasa-kasa yake kallonta yadda baxata fahimta ba,suna xaune wani first class guy yaxo ya xauna opposite dasu,gayen ya hadu sosai sai xabga kamshi yake fiyeda misali,bodyguards ne abayan shi alamar dan wani babban politician ne,sosai alameen ya gane dan waye emaan ce dai bata gane ba,wayar shi ya mika ma emaan yace"can I have your digits pls?"kallon shi tayi keenly sai kuma ta amshi wayar tasa digits din nata kanta tsaye,Shide alameen kallon su kawai yakeyi,Saurayin ya ce"thanks baby girl,ya sunan?"asanyaye tace mishi"emaan"yace"nice name,you can save mine with Saleem dikko "dan xaro ido emaan tayi sai alokacin ta tuna waye shi,he's the son of the current vice president of the country...bai dade ba ya wuce US sukuma sai after 30minutes sannan suka yi takeoff.har suka isa london baice mata komai ba haka itama ko gefen shi bata kalla ba,motar shi dake ajiye a airport ya dauko emaan ta sa kayanta sannan tashiga bayan motar,after few minutes shima ya shiga suka wuce gidansu dake Knightsbridge,suna gaf da karasawa ya tsaya awani fancy restaurant,takeaway yayi musu mai yawa sannan yacigaba da driving suka karasa gida,ga mamakinta taga ya ciro mata trolleys dinta dakanshi dan haka saita figi jakarta ta shige ciki abinta,har dakinta yakai mata kayanta sannan ya sauko yana kallonta tana xaune a parlor,yace"ga abinci"daga haka ya haye sama abinshi ta bishi da kallo,bayan like 5 minutes ta hau saman itama tayi wanka da sallah sannan ta kwanta tana baccin gajiya,sai yamma likis ta tashi kasancewar yunwar da takeji,dan haka shiryawa tayi cikin wata white balanciaga gown ta daura white veil,jakarta ta figa bayan ta cilla cash da atm card aciki,yana xaune a parlon kasa ta wuce shi ko kallon gefen dayake batayi ba,da kallo ya bita na tsantsar mamaki,aranta tana ayyana ba abinda xatayi da abincin shi,dan haka nearest cafe taje ta siyo abincinta mai rai da lafiya ta dawo,yana kallonta ta shigo parlon ta wuce sa,sallamar ma ciki-ciki tayi mishi ta wuce abinta,fridge ta bud'e ta saka abubuwan da xata saka sauran kuma ta sake warming dinsu,a dining ta zauna tana cin abincinta hankali kwance gefe daya kuma tana pressing wayarta,chatting takeyi da anty habiba me tambayar ta bude kayanta?emaan tace"saina huta tukunna"anty habiba tace"kisamu ki bude zuwa gobe dai"da toh emaan ta amsa ta cigaba da chatting da kausar wacce ke mata complain ta tafi ko sallama babu,murmushi emaan tayi ta bata hakuri ahaka ta kammala cin abincin,saida ta wanke plate dinta even though taga na alameen amma ko sake kallon gefen dayake batayi ba,tana fitowa ta haye sama abinta ta mike a parlo tana kallon chopped,dayake tana bala'in son girki shiyasa take son kallon cooking shows.After like 15minutes taji yana hawowa saman,dan haka ta sake tamke fuska tana maida hankalinta da nustuwarta xuwaga ga tv,kallonta yayi for few  seconds sannan authoritatively yace"kada ki sake fita daga gidan nan without my permission"tashi tayi xaune tana kallonshi cikeda mamaki,can tace"ban gane ba"akaikaice ya kalleta yace"kin dai ji abinda nace and I won't repeat myself"kallon datake mishi irin na me xakayi dinnan ne,dan haka yace mata"just try that again,xaki ga me xanyi,kina kallona da wasu kwala-kwalan idanunki"daga haka bai sake cewa komai ba ya shige dakinshi itakuma ta bishi da kallon mamaki.....




*CHEF 👩🏽‍🍳ZEEE ONLINE CLASS *
My fans kamar yadda kuka sani cooking is my passion, hasalima nafison girki fiyeda rubuta littafi, kunga kenan riba biyu xaku kwasa domin wanna class din will change your life for good, xan koyar daku enticing recipes tara Daga traditional cuisine's, continental cuisines, Arabian dishes, snacks da drinks a kudi kalilan, wanda suka shiga free class dina sunsan banxo da wasa ba, domin na shirya tsaff wurin kawo muku kalolin abinci masu dadi da tsayawa arai, ku garxaya ku shiga online class dina domin koyan kayatattun girkuna kala daban-daban.....amu fara class on the 8TH OF OCTOBER in shaa Allah.
Price-1k only
Pay into 6319878551 Zainab Yusuf
Fidelity bank and send your proof of payment via 09037909996.

Zaynabyusuf ✍🏼aka chef zeee 👩🏽‍🍳

EMAANWhere stories live. Discover now