PAGE 51

132 5 0
                                    

EMAAN......PAGE 51

Written by Zaynabyusuf✍🏼

ahankali emaan ke blinking eyes dinta tana son budewa saide hakan ya gagara,saboda har lokacin baccin bai gama sakinta ba saide batada nutsuwar da xatayi,ko acikin baccin ma mafarkin rayuwarta takeyi mai cikeda kunci,hawaye masu zafi suna gangaro mata ta runtse idanun ta kuma har lokacin bata san a inda take ba,ta dade tana tunanin xuci kafin ta iya bude idanun nata tana kallon parlon datake kwance cikeda mamaki,bata gama gane a inda take ba mami ta shigo gabanta na tsananin faduwa tana kallon fuskar emaan,gani tai emaan ta sake fari sosai saide ta rame amma ba rama me muni ba, farin da emaan ta kara ne ya ba mami matukar mamaki,wanda hakan ya kasa boyuwa acikin ranta,saida ta karasa daf da emaan sannan emaan ta san da xuwan mami,jitayi gabanta yayi mummunan faduwa alokacin da idanunsu ya sarke acikin na juna, tana daga kwance amma jikinta rawa yakeyi saboda tsantsar firgicin kallon da mami ke watsa mata me cikeda xallar kiyayyah, mami tace "tun yanzu kin fara hawaye?dama kin dakata da xubar dasu domin lokacin xubarsu xaixo very soon, kina tunanin xan barki tareda ɗana na zuba muku ido ne?kina tunanin xan hakura da ɗana kamar yadda hajjo ta hakura da Abba ta damƙawa uwarki ragamar rayuwar sa?kina tunanin xanyi folding hands ne na xuba miki ido ki shanye ɗana kamar yadda uwarki ta shanye Abba?"jujjuya kai mami tayi tace"I won't let that happen, ki ajiye hakan acikin ranki,sannan ki sa kanki acikin jerin xawarawa saboda baxaki sake kwana da auren dana ba, ayau xai sakeki just wait and watch"hawaye ne masu zafi suka cigaba da zubo ma emaan tana having mixed emotions acikin xuciyarta, gefe daya kuma she's happy akan qudurin mami akanta, koba komai xata ceto rayuwarta daga wrap din alameen, wani sanyi-sanyi taji aranta domin tana da qudurin haka acikin ranta,dole ta rabu da alameen koda shine namiji guda ɗaya daya rage aduniya, mami ce ta katse mata tunani tahanyar cewa"sai ashirya dumama kujera keda uwar taki... "daga haka tafice daga part din emaan tabita da kallo,saidai ba kallon mamaki bane saboda dama can ta san mami bata son ta...bai sake kallon gefen da emaan take ba ya tafi Part din mami gabanshi na tsananta faduwa,cikeda tsantsar damuwa ya ke kallon fauxa dake kwance saman kujera tana yamutsa fuska alamar baccin baya mata dadi,keenly yake kallonta da idanunshi da suka cika da ruwan hawaye,tausayin fauxa ne ke ratsa xuciyar shi yana karya duk wata gaba ta jikinshi,yasan fauxa is going through alot shiyasa xuciyar shi is breaking into tiny pieces saboda tsantsar tausayinta,"alameen..."mami ta ambata xuciyarta na suya,juyawa yayi asanyaye yana kallon fuskar mami mai dauke da matsananciyar damuwa,ga wasu irin kallon datake mishi wanda suka sanya hantar cikinshi kadawa,gumi suka fara xubo mishi ba shiri saboda tsananin tashin hankali,he knows right mami isn't going to handle the situation lightly,dan haka ya sunkuyar da kanshi tareda russunawa ya gaishe ta cikeda girmamawa kamar yadda ya saba,amsawa tayi ciki-ciki wanda hakan ya daure mishi kai,dagowa yayi yana kallon fuskarta dake tamke kamar hadarin gabas,ga idanunta sunyi jajir alamar taci kuka,runtse idanu yayi xaiyi magana tayi saurin katse shi ta hanyar cewa"alameen the perfect time is right now...."kallon ta yayi keenly da idanun shi da suka cika da ruwan hawaye saboda ji yayi xuciyar shi ta karye da ganin halin da fauxa da mami ke ciki,can yace"mami let's focus on fauxa for now,komai mai sauki ne xamu iya yi daga baya saboda halin da fauxa ke ciki na karya min xuciya,I can't think straight at the moment ".shiru mami tayi tana kallonshi for a while,can tace"what do you mean by that alameen?"hannayenta ya riko yace"why don't you trust me mami?"afusace tace"just do as I say,divorce her right now..."kallonta alameen yakeyi cikeda mamaki,ta ce"do that son,nasan kana tunanin me xaije ya dawo ne,karka damu xanyi handling Abba".kallonta kawai alameen keyi kamar statue,duk da yasan halin mami farin sani bai kamata hakan yaxama abin mamaki agareshi ba,ajiyar xuciya ya sauke sannan yace"I'll divorce emaan for sure"yacigaba da cewa"amma ba yanxu ba,xanyi hakan idan lokacin dana ƙidaya mata sun cika".daga haka ya dauke kanshi daga kallon mami wacce tayi suman xaune saboda tsananin mamaki,firgici da kuma tashin hankali,she can't believe abinda alameen yafada mata yanxu talkless of her to apprehend,tace"repeat yourself"!.gabanshi ne ya fadi amma ya dake yace"xan saketa nace amma ba ynzu ba,abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalinki,put your mind at rest pls".shiru kawai ta mishi tana jin kamar xuciyarta xata tarwatse saboda tsananin damuwa,adaidai lokacin fauxa ta bude idanunta ahankali hawaye na xubo mata,tana ganin alameen tayi saurin mikewa tana fashewa da kuka mai tsanani da karfi,bai san lokacin da hawaye suka xubo mishi ba na tausayinta,gashi ya rasa kalaman daxai fada mata daxasu sanyaya mata rai alokacin,wannan lamarin ne yasa mami ta tsaya cak tana kallon su har lokacin kuma maganar alameen ce ke mata yawo acikin xuciya,fauxa tace"my Sadeeq is no more,all thanks to you alameen...."saurin kallonta yayi cikeda mamaki haka ma mami ta xaro ido tana kallon fauxa,fauxa tace"kaine silar faruwar komai alameen,you snatched away the most precious soul aduniyar Sadeeq,you see the result of your actions ko?gashi nan ya bar mana duniyar gabadaya"tunda tafara magana alameen yayi suman xaune,Abba dake tsaye abakin kofa ya saki baki yana kallon fauxa,tacigaba da cewa"kasan yadda yake bala'in son emaan,kasan cewar emaan ce rayuwar shi,kasan cewar he can't live without her shiyasa ka aureta saboda ka hanashi aurenta,I won't forgive you and emaan for this,kune silar rasa mijina kuma uban yayana,baxan yafe muku ba...."tafada tana fashewa da kuka mai tsanani,dafe kanshi alameen yayi wanda ya mishi nauyi kamar xai fashe,Abba na tsaye na kallon ikon Allah,sai kuma alokacin yake tuna ranar da Sadeeq yaxo wurin shi ranar da aka daura auren alameen kenan,sai alokacin yake tuna komai kuma yake fahimtar everything vividly ynxu,tabbas abinda fauxa ta fada is nothing but the truth,sosai yaji ranshi ya baci sai kawai ya juya yafita daga part din,Mami ji tayi kamar xata Shide saboda tsananin damuwa,emaan ta xame mata bala'i da masifa acikin rayuwarta Data ya'yanta,with a trembling voice alameen yace"all I did was for your own good fauxa..."saurin katse shi tayi tace"gashi nan kayi costing dina eternal sadness alameen,rayuwata will never be the same again all because of you two...."jin saukar kalaman fauxa yakeyi kamar zubar garwashi acikin xuciyr shi,even though yasan she's not in the rightful  state of mind amma duk da haka yaji xafin kalaman dasuke fitowa daga bakinta fiyeda misali kuma fiyeda tunanin me tunani,kuka Sosai mami ta fashe dashi ganin yadda fauxa ke accusing alameen cewar shine silar rasuwar Sadeeq,kuma duk inda xa'aje adawo emaan ce taja duk abinda ya faru,ji tayi kamar taje ta shake yarinyar saboda yadda xuciyarta ke mata xafi tana tafarfasa,alameen shiru yayi yana kallon fauxa dake fada mishi maganganu marasa dadi,sai kawai ya runtse idanu yana jin wani mahaukacin xafi na addabar xuciyar shi...Compound Abba ya fita damuwa na damun xuciyar shi domin the deed has been done saide a kiyaye faruwar nagaba,tarihine yakusa maimata kanshi sai kawai abba ya runtse idanu....jiki asanyaye emaan ta mike tana tafiya ahankali hannunta rike da drugs  tafito main parlor,hajjo na xaune tana jan carbi saliha ta ajiye mata fruits,tunda emaan ta fito hajjo ke kallonta akaikaice tana tabe baki,ajiyar xuciya emaan ta sauke sannan ta xauna tana kallon hajjo kamar yadda hajjo ke kallonta,shiru ne ya biyo baya hakan, emaan na jiran hajjo ta karasa laximi su gaisa,ganin haka yasa hajjo ta sake jan shi da tsaho lamarin daya sa emaan sakin karamin murmushi sai kawai ta mike xata wuce part din umma,da sauri hajjo ta sha gabanta tace"emaan anya kinada saiti kuwa?ina kike tunanin xaki je?"da mamaki emaan tace"kina sane kika min banza kenan?"harara hajjo ta galla mata tace"maxa juya ki koma inda kika fito"emaan ta dafe kujera kasancewar baxata iya tsayuwa mai tsaho ba,fuskarta d'auke da mamaki tace"ban gane ba"hajjo tace"dama ina xaki gane,bayan kin fitsare kafa ko kunya bakya ji"xaro ido emaan tayi without saying a single word saboda bata gane inda maganar hajjo ta dosa ba,hasalima tsayuwar ta isheta so take taje takwanta,dan haka bata saurari hajjo dake magana ba tayi shigewarta part din umma,da mamaki take kallon anty habiba da umma dake cin abinci a plate daya,anty habiba tayi murmushi tace"ynxu nake maganar ki"saida emaan ta kwanta asaman kujera sannan tagaisheta,anty habiba tace"weathern London ta karbeki,kinga farin dakika kara ?"murmushi kawai emaan tayi umma kuma ta bita da kallo tana gasgata hakan,itadai emaan lumshe idanu tayi gabanta na faduwa,so take taje wurin fauxa amma batasan kalaman daxata fada ma fauxa ba awannan yanayin,musamman da wani bangare na xuciyarta ke accusing dinta akan itace silar rasuwar Sadeeq,da ace ta fahimce shi da haka bata faru ba,closely umma ke kallonta tace"kinyi ma fauxa gaisuwa kuwa?"bude idanu emaan tayi ta xuba akan fuskar umma sannan ta girgixa kai ahankali tace"a'a"cikeda mamaki umma tace"what are you waiting for dear,tashi kuje da habiba itama yanxu xata je"mikewa xaune emaan tayi tana gyara veil anty habiba tace"kya bari na gama cin abinci ko?ko kuma kiyi gaba dama surukarki akama rasuwar".kallon anty habiba kawai emaan tayi domin baxata iya shiga part din mami kanta tsaye ba,dalilin daya hana bataje ba kenan bayan tafito daga bangaren alameen.kwanciya emaan tayi anty habiba ta kalli umma tace"meke damunta ne?naga duk tayi laushi".umma tace"ciwon ciki dazu suka dawo daga asibiti". juyawa anty habiba tayi tana sake kallon emaan wacce ta tattara hankalinta da nutsuwa ta baiwa Tv,bata ce komai har suka kammala cin abincin sannan tace"tashi muje"saida emaan ta mike sannan anty habiba ta lura da yanayin tafiyar ta,saurin rikota tayi tace"ke lafiyarki?"kallonta kawai emaan tayi batace komai ba,anty habiba tace"nifa banason iskanci,sai ariqa miki magana kina ma mutane banxa"umma tace"ni ma dai abinda nagani kenan"anty habiba tace"baxaki bud'e baki kiyi magana ba"take idanun emaan suka cika da ruwan hawaye,tana tuna damkar da alameen yayi mata,tace"I can't stand still for too long..."kallonta sukayi kowanne da tunanin dake ranshi,anty habiba ta rukota suka nufi part din mami xuciyr emaan na dukan tara-tara, sallama anty habiba tayi hakan yasa mami dake yima alameen magana yin shiru,yana zaune ya dafe kanshi mai tsananin sara mishi,ahankali ya dago yana xuba idanunshi masu maiko akan emaan wacce itama direction dinda yake take  kallo tana jin xafi acikin ranta,daga ita har shi kallon juna suke without knowing me sukeyi,duk da babu komai azuciyoyinsu sai kiyayyar juna kuma kowa da alwashin dayake dauka acikin ranshi,saida suka shiga ciki sannan emaan ta janye idanunta daga kallonshi haka yasa shima ya dauke kai,ayatsine mami ta amsa gaisuwar su shima ya gaida anty habiba fuskar nan tashi a tamke ko digon murmushi babu,anty habiba tace"Ina fauxa take?"babu wanda ya amsa tambayar tsakanin mami da alameen saboda tsananin damuwa,saboda yanxu ta gama kwance musu buhun hauka ta shige daki abinta,kamar kuma ankirata sai gata ta sake fitowa parlon idanunta suka sauka akan fuskar emaan,wani irin takaici da bakin ciki ne ya dirar mata lokaci guda,sabbin hawaye suna zubo mata,ahankali take closing gap din dake tsakaninsu ta karaso daf da emaan wacce ta runtse idanu takasa hada ido da fauxa,wani irin bakin cikin emaan ne da takaici ke taso ma fauxa,tana pointing emaan tace"na daukeki kamar kanwata ta jini...."gaban emaan ne ya tsananta faduwa,ta bude idanu ba shiri,fauxa tace"tamkar inteesar na daukeki but you betrayed me,you betrayed my trust,kin cuceni,kin cuci rayuwata,kin tarwatsa min farin cikina,kin cuceni emaaann...!"tafada da karfi tana sake fashewa da kuka,da sauri hajjo tashigo part din mami,haka umma dasu mummy,kasancewar kara mai karfi fauxa ta saki,tacigaba da cewa"you're the damn reason for everything that happened,ina xaune da mijina cikin farin ciki da kaunar juna kikaxo kika tarwatsa mana rayuwa,Sadeeq bai taba b'oye min komai ba sai akanki,bai taba aikata abu without my knowledge ba sai akanki emaan,akan ki nafara sanin matsala arayuwar aure,akanki nafara xubar da hawayen bakin ciki a xaman aurena,you snatched away my husband emaan, I will never forgive you for this "ta karashe maganar tana fashewa da kuka mai karfi da ciwo,xubewa tayi akasa tace"Sadeeq was a happy soul,akanki yasan menene bakin ciki da damuwa,akanki ya gwammace na xubar da hawaye,akanki ya gwammace abubuwa da dama and I'll forever blame you for everything,na rikeki da kyakkyawar xuciya,na mu'amalance ki da hakuri da fahimta,even in your worst times I was there for you emaan,amma dame kika saka min dashi arayuwa?answer me emaan why do you choose to betray me?"tafada tana jijjiga wuyan emaan dake xubarda hawaye masu zafi da ciwo,"kin raba ni da masoyina,mijina kuma uban yayana,you took away the precious soul in my life,me namiki to deserve this emaan?me namiki arayuwa da kike son ganin bayana?laifi ne dan na dauke ki kamar yar uwata?laifi ne dan ina sonki?laifi ne dan ina tausayinki,laifi ne dan ina kyautata miki?now tell me menene laifina"emaan couldn't say a single word domin batada kalmar daxata fada wacce xata kunce ta daga daurin xato,banda kuka ba abinda takeyi,durkushewa umma tayi anty habiba tayi saurin rikota ta riketa gam,saidai hakan bai hana hawaye masu zafi xubo mata ba,gefe daya kuma xuciyarta kamar xata tarwatse saboda damuwa,mutuwar tsaye hajjo tayi tana mamakin kalaman dasuke fitowa daga bakin fauxa,haka mummy da mama sun kasa gasgata abinda ke faruwa,Mami kuwa kuka take wi-wi saboda bakin ciki,dole ma alameen ya saki emaan ayau wallahi,that she promised herself,kamar yadda emaan ta tarwatsa rayuwar fauxa sai ta rama fiyeda haka,fauxa na jijjiga wuyan emaan tace"kin cuci su Anum,kin raba su da babansu alokacin da suka fi bukatar shi,yanzu haka xasu girma basu san waye babansu ba all thanks to you,yarana baxasu yafe miki ba emaan..."tana kaiwa nan ta mike jiri Na kwasar ta ta shiga bedroom din mami ta bugo kofar da karfin gaske,emaan dake rusa uban kuka tarasa me xatayi alokacin,wace irin kaddarar rayuwa ce wannan take xuwar mata a mataki-mataki na rayuwarta,ji tayi ta tsani kanta da komai na duniyar nan,domin babu komai acikin rayuwarta sai bakin ciki,anya tana daga cikin waɗanda xasu yi farin ciki arayuwa kuwa?....har lokacin babu wanda ya iya motsawa balle yayi magana,ko hajjo takasa cewa komai saboda mamaki,umma kam hawaye ne suke xubo mata daya bayan daya,sallamar Abba ce ta sa suka juya suna kallonshi banda emaan data fada duniyar tunanin,xama yayi ya kalli alameen yace"kira min fauxa"jiki asanyaye alameen yakirata even though bata amsa ba,hasalima wani banzan kallo ta mishi sannan ta fito parlon,gefen shi Abba ya nuna mata taxauna tana goge hawaye,yayi gyaran murya sannan yace"naji duk abubuwan da fauxa ta fada,kuma hakan bakomai bane illa tsantsar gaskiya wacce batada algus acikinta,alameen da emaan kun tafka babban kuskure,saide duk da haka abinda kukayi shi mutane da yawa xasuyi adaidai wannan gabar,kai kayi hakan ne saboda fauxa,haka xalika ita ma tayi hakan ne saboda fauxa,kenan duk ku biyun kun kasance masoyan fauxa ne,kuma bakwa son ganin bacin ranta,saidai kun manta da halin da Sadeeq zai iya shiga,baku damu da hakan ba kuka xartar da hukunci kanku tsaye,hukuncin dayayi affecting rayuwar fauxa....."shiru yayi yana kallon kowa na cikin parlon harda nurain da shigowar shi kenan,yace"abinda kukayi mistake ne ta wani bangaren,domin Allah bai haramta aure tsakanin emaan da Sadeeq ba,meyasa xaku haramta?meyasa xaku shiga cikin rayuwar shi haka?nasan kunyi hakan ne saboda fauxa amma ynxu wa fauxa ke blaming?ku take blaming,kuma still ku xatayi blaming da'ace kun bar sadeeq yaxo min da maganar emaan agabar data dace,kunga kenan kowacce hanya idan kukabi akwai kalubale acikin ta,domin either way fauxa will still blame you two,haka xuciyr dan adam take and you can't change that "."duk wannan surutan da mukeyi na banxa ne domin Allah ya qadarta faruwar hakan tun kafin xuwan mu duniya,Allah ya qadarta alameen xai auri emaan ta wannan dalilin,fatan mu shine Allah yasa hakan ya xamto mafi alheri acikin rayuwar mu baki daya,Allah ya jikan Sadeeq ya sanya hakuri da tawakkali axuciyar fauxa,haka xalika Allah ya ba emaan da alameen xaman lafiya,aure dai ya dauru no matter akan dalilin da aka yi shi,dole alameen ka rike emaan da mutunci sannan ka sauke duk wasu hakki nata,haka xalika emaan kibi mijinki sau da kafa,bana son naji wata magana mara dadi...and lastly yau xan fada muku wani abu daya faru,wanda xaku dau darasi Sosai acikin shi,domin dani karan kaina abin yafaru".mikewa Abba yayi yana xagaye parlon yace"nasan xakuyi mamaki idan nace muku dani da Alhaji lameen abdulfattah watau mahaifin emaan abokai ne na kut da kut,kusan tare muka taso kasancewar unguwar mu daya anan kano,duk da ni iyayena mutanen gombe ne shikuma tsatson shuwa ne na jihar borno,amininai ne mu sosai duk da cewar na girme shi,lameen mutum ne mai buri dan haka ya ajiye batun aure agefe yana jiran perfect time,what i meant by perfect time shine yafison komai yayi shi to his best of ability,idan ma auren ne yafiso sai ya shahara yayi kudi sannan yayi,ya dade baiyi aure ba har iyayenshi suka fara damuwa lokacin dana yi aure na biyu,ba nasihar da ban mishi ba akan yafitar da matar aure amma lameen sam baya saurara ta,bama niba lameen baya saurarar kowa akan batun aure,kullum ka mishi magana xaice yana jiran perfect time,Ana cikin haka ne iyayenshi suka aura mishi Fatima Watau umma kasancewar fatima family friends ne da lameen,ba irin tijarar da lameen baiyi ba akan auren amma akayi biris dashi,sai ya kasance yana gana ma fatima axaba saboda alokacin yarinya ce sosai,bata san me xatayi ba da kuma irin hukuncin da xata dauka ba,wannan dalilin ne ya ba lameen damar azabtar da ita fiyeda misaltuwa,ya maida ita tamkar baiwa wacce batada gata da galihu,ahaka suka haifi babbar yarsu Sabeeha yayar emaan kenan,Yarinyar tafara tasawa tarasu,xa'a iya cewa lameen shine silar rasuwar yarinya tunda shi ya hana kudin maganin da xa'a mata treatment har ciwo yaci karfinta ta rasu,awannan lokacin ne fatima taci alwashin rabuwa da lameen,saidai duk hanyar databi sai an toshe mata,akullum hudubar da ake mata itace tayi hakuri watarana xai daina,Ana cikin haka tasamu cikin emaan wanda ya kasance worst nightmare arayuwar fatima,dalilin daya sa lameen ya sake bullowa da hanyoyin rashin mutunci,tasha wahala sosai even though I was there for her,nine ke taimaka mata alokuta mabanbanta duk da lameen na warning dina akan nadaina interfering acikin harkar gidanshi,amma still ban daina ba saboda ina tausayin fatima awancan lokacin,Kanwar lameen hajiya mairo itace ummul-aba'insin faruwar komai,itace ke daure ma lameen qaniya akan yaci mutuncin Fatima yadda ranshi keso,na mishi nasiha har nagaji,kuma har lokacin da emaan takai shekara shidda aduniya bai daina ba,hasalima anan ne ya sake daura daramar wulakanta su,awannan lokacin nayi aure na uku kuma har lokacin nakan ziyarci fatima da emaan lokaci xuwa lokaci domin ganin halin dasuke ciki,ahaka emaan ta shekara goma ahannun lameen cikin bakar ixaya da wahala,ban taba ganin uban da bai damu da ƴar shi ba sai lameen,haka xalika fatima ma batada damu da yarinyar ba Sosai kasancewar abubuwan da lameen keyi yana affecting dinta mentally,kamar yadda lameen ke fada shine zai saki fatima alokacin daya so kuma yayi ra'ayi,dan haka emaan na shekara goma sha daya ya saki fatima,abin takaici shine no body was there for fatima.....Fatima kwaise,Aisha da kuma maimuna sun girma fatima Sosai amma hakan bai hana su xama kawaye ba,time to time umma na lekowa mu gaisa saboda yadda take girmamani,kasancewar nina tsaya mata alokacin da kowa ya matsa daga gefenta,ni nacigaba da daukar dawainiyar emaan da fatima har lokacin dana aminta cewar na shirya xan iya auren fatima nacigaba da kula da emaan kamar diyar dana haifa,lokacin danaje da maganar kowa yayi mamaki amma kasancewar sun yarda da nagarta ta suka amince na auri fatima duk da bata sona amatsayin miji,ban wani damu ba saboda da niyyar na kyautata mata na aure ta sannan kuma na inganta rayuwarta,tun da lameen yasamu labarin nan muka samu sabani mai girma,anan na tabbatar da bakin ciki yake mata,shi bai riketa da arxiki ba kuma baya son wani ya mutunta ta bayan alokacin ya sake aure abinshi,sanda na aureta su kwaise sun dauki abin personal amma daga baya komai ya wuce,muka cigaba da shimfida sabuwa kuma nagartacciyar rayuwa,saidai har yanxu gaisuwa ce kawai ke hadani da lameen,cikin hukuncin ubangiji Allah ya axurta mu da yaya da kuma farin ciki mara gushewa..."ya kamo hannun fauxa yace"you might not understand this now,amma xaki fahimci abinda nake nufi xuwa gaba,abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalinki,ki nutsu pls,Allah yana tare dake kuma shine xai share miki hawayenki".tunda Abba yafara magana sai yanxu yayi shiru yana kallon kowa na cikin parlon,authoritatively yace"wannan ya xamto karo na karshe da xanji wannan maganar,enough of the blame game"yana kaiwa nan ya fice daga part din,anty habiba da umma suka mara bishi baya,emaan ce ta mike tana ganin dishi-dishi saboda jirin dake neman xubar da ita,maganganun da fauxa ta fada mata ne ke damun xuciyrta,saurin dafe bango tayi tareda rike kanta mai barazanar tarwatsewa,da bin bango sai kace kadangaruwa ta karasa part dinsu,tana shiga parlon ta durkushe tareda sakin wani marayan kuka,umma ta juyo tana kallon ta itama har lokacin kuka takeyi,sosai gaban emaan ya fadi ganin irin kallon da umma ke mata,unexpectedly taga umma ta rungumeta sosai tana sakin kuka mai taba xuciyr me sauraro,Abba ya fama mata ciwon data dade da birnewa acikin xuciyrta,gefe daya tausayin yarta ke ratsa ta tana tunda irin wahalar dasuka sha da emaan mara fasaltuwa,kuma har yanzu emaan bata samu farin ciki ba tun daga kuruciya har ixuwa yanxu,wannan tunanin ne ke breaking heart din umma into tiny pieces....



















*CHEF 👩🏽‍🍳ZEEE ONLINE CLASS *

My fans kamar yadda kuka sani cooking is my passion, hasalima nafison girki fiyeda rubuta littafi, kunga kenan riba biyu xaku kwasa domin wanna class din will change your life for good, xan koyar daku enticing recipes fara Daga traditional cuisine's, continental cuisines, Arabian dishes, snacks da drinks a kudi kalilan,wanda suka shiga free class dina sunsan banxo da wasa ba, domin na shirya tsaff wurin kawo muku kalolin abinci masu dadi da tsayawa arai, ku garxaya ku shiga online class dina domin koyan kayatattun girkuna kala daban-daban....xamu fara class on the 8TH OF OCTOBER in shaa Allah.

Price-1k only

Pay into 6319878551 Zainab Yusuf

Fidelity bank and send your proof of payment via 09037909996.



Zaynabyusuf ✍🏼aka chef zeee 👩🏽‍🍳

EMAANWhere stories live. Discover now