PAGE 63

159 5 0
                                    

EMAAN...PAGE 63

Written by Zaynabyusuf✍🏼

  murd'awar da cikinta keyi ne yasa emaan bude idanu da sauri tareda taune lips dinta saboda tsananin azaba tana yarfe hannu already gumi sun gama wanke mata fuska duk da sanyin Acn dake cikin dakin,ahankali ta sauka kasa kana ta jinginar da kanta da jikin gadon tana fitar da numfashi sama-sama,bata tab'a jin xafin ciwo irin wannan ba her whole life,tun tana daurewa har hawaye suka fara xubo mata,Sosai ta rike gadon da karfi saboda ko motsin kirki batason tayi,gashi ta kasa magana balle ta tashi umma dake baccinta peacefully,Sosai cikinta ke ciwo irin ciwon da bata tab'a sanin akwai irinshi ba aduniya,ciwon da duk dauriyar emaan saida yasa ta fashe da wani marayan kuka mai tab'a xuciyar me sauraro,kukan ne yasa umma ta bud'e idanu ahankali tana shafa gefenta tace"emaan...."jin wayam yasa tayi saurin mikewa xaune tana xaro idanu ganin emaan durkushe akasa tana kuka mai ciwo da tsayawa arai,cikeda tashin hankali umma ta sauko daga gadon idanunta na cikowa da ruwan hawaye,"innalillahi wainna ilaihi raji'un "umma tace ganin yadda emaan ke juyi a k'asa,for a second xakayi tunanin nak'uda takeyi,nak'udar ma mai tsananin xafi,sosai umma ta rikice ta fita main parlour gumi na wanke mata fuska,bangaren Abba tashiga tana maimaita kalmar "innalillahi wainna ilaihi raji'un..."Abba dake kan sallaya ya yi saurin sallame sallar dayakeyi yana tambayar "lafiya?"bakin umma na rawa tace"emaan ce..."Abba yace"meya samu emaan din?..."bata tsaya bashi amsa ba ta fita da sauri jikinta na rawa,part dinta takoma taxauna agaban emaan wacce ta galabaita sosai sai jujjuya kai takeyi tana runtse idanu,Abba ne ya biyo bayanta gabanshi na tsananin faduwa,saida ya buga ma alameen kofa sannan ya shiga part din umma,cikeda damuwa yake kallon emaan wacce kallo daya zaka mata tabaka tausayi,yace"sa mata hijab akaita asibiti"jiki asanyaye umma ta ajiye hijab din har lokacin jikinta rawa yakeyi,sosai ta shiga cikin fargaba mai tsanani tana fatan ba cikin emaan bane yaxo da problem,tashin da Abba yayi ma alameen ne ya tayar da kowa nagidan,hasalima su mami,mummy,mama dasu fauxa sun riga alameen xuwa part din umma,lokacin emaan na saman kujera sai juyi take from right to left tana kuka mai tsanani da karya zuciyar me sauraro......xuciyar alameen skips a beat lokacin da idanunshi suka sauka akan emaan,ya shigo da sauri yana ture Afiya dake tsaye abakin kofa ta tafi luuu xata fadi mama tayi saurin rikota sauran kiris ta buge kai da kofa,da sauri ya karasa cikin parlon har yana tuntub'e da throw pillow,hajjo da fitowarta kenan tace "kayi ahankali kar ka fad'a kanta...."bai san lokacin da yayi kneeling agaban emaan ba duk ya rikice yace"Sannu babe...you'll be fine In shaa Allah"yafada sannan ya dauki abarshi kamar baby yayi waje da ita,hajjo ta kyabe baki tace"wannan fitsara da me tayi kama ni meram".....mami wacce xuciyarta tayi bakikkirin da bakin ciki ganin yadda alameen ya haukace saboda emaan ta dago tana kallon Abba sanda yace"ga card dina,duk yadda ake ciki kuma ki kirani ki fada min"cikeda takaici ta karbi atm card din tabi bayan alameen,lokacin data fita compound har driver ya tada motar,emaan na kwance ajikin alameen yana jera mata sannu duk ya wani xauce,kallo daya mami ta musu ta shiga gaban motar suka tafi asibiti,lokaci xuwa lokaci mami ke juyowa tana kallon alameen wanda gabadaya baya cikin hayycinshi da nutsuwar shi,lamarin daya sake karya mata xuciya kenan,cikin wani yanayi mara fasaltuwa tace"sun cuceni..."tafadi hakan tana girgixa kai cikeda damuwa mai tsanani,ita yanxu babban tashin hankalinta shine yadda alameen ya rikice akan yarinyar ya susuce dako shigowar ta cikin motar bai sani ba,tafiyar minti ashirin ce takaisu clinic din,alameen ya fita da sauri suka shiga ciki aka fara bata taimakon gaggawa,shirim mami taxauna tana kallon yadda alameen ya fita daga cikin hayyacinshi,yana tsaye abakin kofar emergency ya had'e kai da bango xuciyar shi cikeda xullumi da damuwa mai tsanani,he can't imagine Emaan tayi miscarrying cikinta,yana tsananin son cikin kamar yadda yake tsananin son matar shi,he wants both of them safe and sound,bai ankara ba yaji tamkar ruwa na sauka asaman cheeks dinshi,dan haka ya sanya soft hands dinshi ahankali yana tab'a cheeks din,ga mamakin shi yaga daga idanunshi ruwan ke fitowa,mami dake gefe ta furta kalmar kuka?cikeda mamaki tana jin kanta na jujjuyawa,rabon da taga alameen yana kuka tun yana yaro hasalima alameen mutum ne mai dauriya da juriya wanda abu baya saurin girgixa shi,ganin yadda hawaye ke mishi sintiri mami ta saddakar da lamarin shi,alokacin ta tabbatar da baya cikin hayyacinshi tabbas sun bashi a abinci yaci haka nan sun xuba mishi a lemo yasha,ya kwana akan asiri ya tashi akanshi idan ba haka ba alameen dinta ne wannan ya haukace akan yarinyar daya tsana?batada option dinda ya wuce ta mike tareda dafa shoulders dinshi,cikin wata iriyar raunatacciyar murya tace"calm down pls..."da sauri ya juya yana kallon mami domin sai alokacin yasan da xuwanta,bata ankara ba taga yayi hugging dinta yana sauke deep breath,with a trembling voice yace"mami..."sai kuma yayi shiru xuciyar shi na suya,runtse idanu mami tayi tana jin xafin yanayin da alameen yake ciki fiyeda kanshi ma,ita uwace mai sanya damuwar y'ay'anta asahun gaba acikin rayuwarta,xama sukayi daga bisani ta goge mishi hawayen tana girgixa mishi kai alamar ya daina,babu musu ya shanye sauran hawaye duk da xuciyar shi araunace take,yana jin inama xa'a iya cire mata ciwon asa mishi da hakan yafi mishi sauki,yana cikin wannan tunanin aka kirasu office,jiki ba kwari suka shiga likitan ya fuskance su sannan yace" i guess you're her husband right?"gyada kai alameen yayi doctorn yace"inada good news sannan inada bad news,but lemme start with the good one..."gaban alameen ne yayi mummunan faduwa,yayinda mami tayi tsuru-tsuru tana son jin meke damun emaan,likitan yace"cikinta is fine,babu abinda ya sameshi...."sassanyar ajiyar xuciya alameen ya sauke yayinda mami ta xaro idanu waje tana kallon alameen,Sosai maganar da doctorn yayi ta shayar da ita ruwan mamaki,ciki fa?ciki ne da emaan?cikin ma na d'anta?cikin alameen kenan?ajejjere take jefa ma kanta tambayoyin da batada amsar su,sai kawai ta lumshe idanu saboda abinda take gudu ne yafaru,likitan yacigaba da cewa"the bad news is cikinta yana cikin threat saboda ta tab'a buguwa acikinta,wannan dalilin ne ya jawo mata ciwon mara kuma idan ba'ayi ahankali ba cikin xai iya xubewa dubaga baiyi kwari ba",kasa apprehending maganar da likitan yayi ta karshe alameen yayi,domin babu shamaki shine dalilin abinda ya samu emaan,sai kawai ya dafe kai yana jin haushin kanshi me tsanani yana shigar shi,likitan yace"she's doing okay at the moment,xaku iya ganinta..."da sauri alameen ya shiga ward dinda emaan take tausayinta na ratsa shi,tun daga nesa idanunsu ya sarke dana juna suna starring each other kowa da tunanin dake ranshi,ganinta axaune ne yasa alameen sakin wani kayataccen murmushi wanda yake fitowa daga can kasan xuciyar shi,rungumeta yayi tightly yana shafa kanta yace"sannu emaan...."iya abinda ya iya cewa kenan alokacin yana sauke deep breath,ya dade Sosai rungume da ita yana regaining nutsuwar shi feeling complete and whole within few minutes ya dawo cikin hayyacinshi,breaking hugg din yayi ya xuba mata jajayen idanunshi yana kallonta cikeda tsantsar so da kauna,yace"my emaan i won't let anything happen to you,I'm sorry for everything kinji ko?"yafada tareda dora hannunshi asaman cikinta,batace mishi komai ba illa kallonshi datakeyi tana mamakin yadda ya birkice lokaci daya,for the first time datayi feeling somehow akanshi kenan,jin hannunshi ya kasa tsayawa wuri daya yasa ta yatsine fuska tace"kabari pls..."lips dinta yake kallo sanda tayi maganar,yadda take fitar da words din ne ke burgeshi,gashi cikeda shagwaba tayi maganar tana b'ata fuska ita adole bata so,hakan na daya daga cikin abubuwan dasuke burge shi da emaan,murya can kasa yace"meyasa zan bari?"ya tambayeta yana caressing hannayenta,shiru ta mishi tareda tura cute mouth dinta gaba,yayi murmushi yace"xan cinye bakin ki emaan..."xaro idanu tayi waje tana kallonshi,can kuma ta gyada kai tana jijjigawa ahankali irin no words for you dinnan,hakan ne yasa yayi owning lips din nata slowly even though yana so yayi resisting amma yakasa,bai San meyasa ba hannunshi da bakinshi basa tsayawa in one place idan suna tare da juna,kukan shagwaba ta sakar mishi wanda ya sake kunna mutumin kamar ma xugashi takeyi,gabadaya ya mance a asibiti suke kuma tare da mami,he's senselessly in love with emaan,dakyar ya bar abinda yakeyi yana sauke deep breath yace"emaan samuwarki a rayuwata ne ya koyar da ni har na san xahirin siffar so,ina fatan mu kasance a tare da juna na tsahon rayuwa har xuwa gidan aljanna,i love you so much fatima na..."yafada yana kissing cheeks dinta...lumshe idanu kawai emaan tayi batace komai ba hasalima hannayenta tasa tana ture fuskar shi,murmushi yayi yace"it feels good to be touched by you babyna....pls do that more often..."yafada in whisper yana sake kissing hannun nata,harara ta galla mishi tace"miye haka wai?nifa kana takura min.."lips dinta ya kalla knots din kanshi suna kuncewa,yace"idan kika ci gaba da min wannan shagwabar xanyi...."sai yai kasa da murya yafada mata abinda xaiyi din,Sosai ta sa karfi ta hankadeshi gefe wanda hakan yayi daidai da shigowar mami cikin ward din,ahargitse take kallonsu ranta ab'ace xuciyar ta na tafarfasa,hakan ne yasa alameen nutsuwa ya tsaya agefe yana kallon mami kasa-kasa,shi ta mik'a ma wayar ta tana jefa mishi wasu irin kallo,jiki ba kwari ya karba itakuma ko second daya bata sake yiba tafita kamar iska,karasawa yayi daf da emaan ya xauna agefenta ya rungumeta tightly sannan yasa wayar a speaker yana kallonta closely,ta dayan bangaren Abba yace"emaan how are you doing ?"saukar da idanunta tayi k'asa sannan tace"alhamdulillah abba"abba yace"ma shaa Allah get well soon"batace komai ba illa kallon alameen datayi wanda ya kashe mata ido daya yana dag'e mata gira,sai kawai ta xuba mishi idanu aranta tana ayyana alameen dinnan bayajin magana,tana mamakin yadda yake yin abubuwa kanshi tsaye batareda kunya ko kuma damuwar komai ba,time ya kalla yaga it's few minutes to fajr dan haka ya mike tsaye yace mata "will be right back"daga haka ya fita xuwa wurin mami yana jin faduwar gaba,axaune ya tarar da ita tana kallon direction d'aya,she was lost in thoughts,lost in the world of her own memories,har lokacin maganar cikin emaan ne ke xarya akanta yana mata yawo acikin xuciyar ta,xama yayi agefenta tareda riko hannunta,murya atausashe yace"I'm sorry for everything mami na,dan Allah kiyi hakuri"kallonshi tayi keenly sannan tayi murmushi tace"nikuwa alameen meka min dakake bani hakuri?"ta tambayeshi tana tsareshi da idanu,saukar da idanun shi kasa yayi tace"baka min komai ba dear,wa'inda suka min dai sun san kansu"shiru alameen yayi sai can yace"I'm sorry on  their behalf ..."xaro idanu tayi tana kallonshi cikeda mamaki,alameen yace"accept this marriage for my sake pls..."yafada voice dinshi na rawa,xame hannunta tayi daga cikin nashi ta girgixa kai sannan tace"baxan hanaka yin abinda kakeso ba alameen,saide baxaka tilasta ni yin abinda bana so ba,kowa ya rike ra'ayinsa gameda aurenka da emaan,I'm your mother I want the best for you,i want you to be happy alameen shiyasa kaga na kalmashe k'afa kuma na rungume hannu akan maganar aurenku da emaan"ajiyar xuciya ya sauke sannan yace"trust me,yadda kika dau emaan ba haka take ba"mami tace"dont try to convince me alameen,I've already made my mind kuma shine final,karkayi kokarin cusa min abinda banaso, karka manta nice na haifeka bakai bane ka haife ni"shiru alameen yayi amma jikinshi yayi sanyi sosai,mami tace"tashi ka maida ni gida"agogon hannunshi ya kalla yaga sauran 1hr emaan tagama karban treatment,har xaiyi magana sai kawai ya tashi kamar yadda tace din suka tafi,har ya kaita gida batace mishi komai ba haka shima baice komai ba,tana sauka ya koma asibitin lokacin Emaan ta kwanta saide har lokacin idonta biyu hasalima ta kasa yin bacci dukda she tried closing her eyes several times but to no avail,tun da ya shigo idanunsu ya sarke dana juna,emaan samun kanta tayi da kasa cire idanunta daga nashi,har kuma ya karaso daf da ita yana sakar mata murmushi masu sanyaya rai,sai alokacin emaan ta dauke kai,shikuma ya xauna agefenta yace"nayi tunanin kinyi bacci,,,"girgixa kai tayi without saying a single word,sai kawai ya mikar da ita xaune yace"tashi muyi hira toh"yafada tareda kwantar da kanta akan kirjinshi,yana skimming gashinta with one hand yayinda dayan ke murxa mata hannu yace"what would you like to know about me?"ya tambayeta kai tsaye,murya can ciki tace"nothing "dan xaro idanu yayi waje yana mamakinta,can kuma yace"baki damu dani ba ko emaan?me kikeso na miki wanda xai goge min bak'in fentin dana shafawa kaina awurinki?"batace komai ba illa kallonshi datayi,alameen yace"ko kaina kikeso na ciro na baki ?"girgixa mishi kai tayi alamar a'a,yace"ko xuciyata kikeso?"nan ma girgixa mishi kai tayi alamar a'a,Sosai jikin alameen yayi sanyi saboda yafara damuwa sosai da rashin reciprocating abubuwan dayake mata,dan haka yace"ina yin abinda bakyaso ne,iye baby na?"ahankali tace"bakomai fa"sosai yaji dadin maganar data mishi yace"Toh fada min menene?"ya tambaya cikeda xakuwa,tace mishi"nace ba komai".yace"then why are you always silent,you're always moody emaan,nikuma bana son hakan,i want to see you happy,tell me what it takes to make you happy".idanunta ta sa acikin nashi sannan tace "you know I've been through alot,wanda hakan yayi affecting dina sosai".alameen yace"emaan kidaina tunawa da past dinki pls,focus on your future..."murya can ciki tace"I'm trying my best..."yace"dan Allah try harder....yafada kamar xai fashe da kuka,baiyi tunanin xatayi magana ba sai kuma yaji tace"in shaa Allah"baisan lokacin daya sake rungumeta ba iya karfinshi yace"thank you wifey".....Lafiyayyan tuwo miyan vegetable daya sha different kinds of protein umma ta dafa ma emaan,kuma ba laifi taci abincin sosai beyond yadda umma tai expecting,umma ce ta tsaya akan emaan tun bayan dawowar su daga asibiti take mata hidima,kasancewar alameen ya sanar musu cewar emaan din na bukatar hutu,misalin k'arfe biyar alameen ya shirya cikin white color kaftan wacce tai mishi kyau fiyeda misali,part din umma ya shiga bakinshi dauke da sallama tareda xuba idanunshi akan emaan wacce ke kwance asaman kujera,tun kafin ya karaso kusa da ita kamshin turarenshi ya gama cikata,dan haka ta lumshe idanu tana shakar shi saboda yana mata masifar dadi,saida ya xauna sannan ya kamo hannunta yace"how are you feeling now?"tace"good alhamdulillah "yace"maa shaa Allah,me kikeso na taho miki dashi?"tace"ina xaka?"wani iri yaji aranshi dan haka yace "to meet a friend..."batace mishi komai ba ya sake cewa"fada min me kikeso?"without looking at his face tace"bakomai"yace"are you sure?"gyada mishi kai kawai tayi shikuma yayi pecking forehead dinta yace"lateer babyna,I love you "yafada sannan ya fita,da rakiyar idanu emaan ta bishi tareda sauke ajiyar xuciya.yana xaune a hadaddan garden dinsu yasmeen tafito jikinta sanye da wata milk color turkish gown,ta yane kanta da karamin veil tana tafiyar nan tata ahankali,tun daga nesa ya xuba mata idanu ganin ta sake kyau sannan tayi jiki ba kamar yadda ya santa ba,alameen bai sake mamaki ba saida ta xauna agefen shi tace mishi"welcome dear"murmushi yayi domin sai alokacin yasan yayi missing yasmeen,yace mata"thanks dear?ya kike?"smiling tayi tace"I'm good alhamdulillah yasu mami?l"yace"suna lafiya"yacigaba da tambayar "yasu mummmy?"yasmeen tace"ta fita siyo ma cousin dinnan tawa ta uk wacce nake fada maka abu..."girgiza kai yayi yace"ehya kinga kuwa har ynxu ban samu naje wurinta ba"yasmeen tace"ai sometimes bakada kirki"yace"nidin baby?"narke mishi idanunta tayi tace"ai gaskiya na fada"sai kawai ya jijjiga kai tace"i think jibi zan hadu da wacce xanba sakon,itama yarinyar aure takeyi acan"alameen yace"kinsamu friend kenan"murmushi yasmeen tayi tace"in shaa Allah,but let's meet first naga ya take".dariya yayi yace"yasmeen you're too much..."harara ta galla mishi tace"kaifa nko?three much ko?me boyen min problems dinshi kawai,ay ni ba ruwana dakai"tafada tareda b'ata fuska,Sosai hakan ya burgeshi yace"sorry my baby,i don't want to stress you with my problems "yafada tareda riko hannunta,nan da nan idanun baiwar Allah suka ciko da hawaye,tace"are you sure?"gyada mata kai yayi ya ce"sure babyna,you know how much I love you "yafada yana goge mata hawayen,murmushi tayi tace"i love more baby boy"b'ata fuska yayi yace "ni ne boy din?" gyada mishi kai tai tana dariya yace"xaki shigo hannu ne alokacin xaki banbance ni din man ne ko kuma boy"bata ce mishi komai ta karbi medium size tray din dake hannun rukayya wacce tunda ta karaso wajen kanta ke sinne akasa,tasan halin yasmeen sarai shiyasa tayi hakan,saboda ba karamin aikin yasmeen bane tace tana kallon alameen,murmushi alameen yayi saboda ya fahimci hakan yace"kidena stressing kanki akan issues dinnan..."ta kalleshi keenly tace"i want you all for myself alameen,i might sound selfish amma hakan ne acikin xuciyata,kuma bazan tankwashe kafa na kalmashe hannu ba wasu yan banxa su kwace min kai".dariya yayi yace"a kwace ni saika ce wani kaya?"ta jinjina kai sannan tace "ehh mana,"yace"Toh miye ma idan hakan tafaru,tunda kinsan gurbin dakika kafa acikin xuciyata "mood dinta ne gabadaya ya canxa,ta hade rai Sosai tareda hadiye wani qaton qullutu daga wuyanta,batace komai ba shima sai ya cigaba da kallonta,saboda yasan ya tab'o ta yau sai kuma Allah.tace"ai babu macen data isa ta rab'eka balle har ka fada abinda ka fada yanxu",gumi ne suka zubo mishi yayi saurin gogewa kana ya girgixa yace haka ne.Batace komai ba saboda ranta ya gama b'aci,itafa ko maganar kishiya ta tsana amata,sai kawai tafara mishi plating abincin,"thank you"alameen yafada sannan ya amshi plate din yana cin abincin slowly saboda yaci tuwon da umma tabashi kafin yazo,...

https://chat.whatsapp.com/IAyL0ePAUS42UGNBn7eHV6
EMAAN COMMENTS SECTION

*Wannan page din naku ne mutanen kirki na EMAAN COMMENTS SECTION,i heart 🫶🏻🫶🏻 you all,Allah ya bar xumunci*...💖💖🤩



Zaynabyusuf✍🏼

EMAANWhere stories live. Discover now