PAGE 48

116 4 0
                                    

EMAAN......PAGE 48

Written by Zaynabyusuf✍🏼

Tragic things happen so suddenly and unexpectedly that no human can predict what tomorrow will bring...kamar yadda kaddarar rayuwar Sadeeq ta juya daga farin ciki ixuwa makamancin haka,kwana biyun da suka wuce are the worst days of his life,ya rasa nutsuwar shi gabadaya ga tunanin emaan dayake neman hallaka shi tun lokacin shi baiyi ba,shi kanshi atimes yana mamakin tsananin son emaan dayake mata wanda baxai iya fasalta shi da fatar bakin shi ba,haka xalika ba xai iya bayyana wa da idanunshi ba,gefe daya kuma xuciyarshi cike take da soyayyar ta,xuwa yanxu tsoron kanshi ne ya fara shigar shi,domin abin yafara yin yawa,lamarin ya fara wuce tunanin shi dakuma hankalinshi,ya kasa tsayawa ya naxarci halin dayake ciki balle yasan yadda xai cigaba da tafiyar da rayuwar shi akan turbar hakan,Idan ya kalli fauxa yana jin mashahurin tausayinta na ratsa xuciyar shi,saboda yadda ta dage kwarai dagaske tana bashi kulawa fiyeda tunanin shi,acikin kwanan biyun ta sake kafa babban gurbi acikin xuciyar shi,saidai unfortunately his life will never be the same without emaan acikinta,rayuwar shi baxata taba cika batareda emaan acikin taba,saidai dole yayi hakuri sannan ya rungumi kaddara,dole yayi moving on da rayuwar shi for the betterment of his life and future,baxai so yacigaba da rayuwa cikin damuwa da bakin ciki ba,amma xaiyi iya bakin kokarin shi wurin ganin ya rage tunanin emaan,wanda ayanxu ya xama wani jigo kuma bangare nacikin rayuwar shi,kamar kullum yau ma pictures dinta yake kallo yana imagining emaan yake kallo axahiri,ahankali kuma asanyaye ya furta"I love you so much emaan,more than anything in this life,i love you beyond every single word,sonki da numfashi na yake tafiya and I'll continue to love you for the rest of my days,hatta a aljanna I'll love to be with you emaan,acikin rayuwata kin xamto tauraruwar dake haska rayuwata da mafi hasken haske,you're my strength,my weakness, and my knight in shining armour ....."hawaye masu xafi ne suka zubo mishi,ya saki karamin murmushi yace"loving you is an honour I'll continue to cherish for the rest of my days,I love you senselessly emaan".adaidai lokacin Fauxa ta shigo dakin jikinta sanye da wata baby pink skimpy dress,fuskar ta d'auke da murmushi na musamman,Sosai Sadeeq ke mamakin yadda take shige mishi kwana biyun,ko kwakkwaran motsi bata barin shi yayi kullum suna manne da juna,yanxu ma saida tashige jikinshi tareda xagaye hannunta ta wuyan shi sannan tace "mami tace your favourite food is ready,mu take jira"murmushi yayi tareda pecking goshinta yace"ok baby"sannan ahankali yasauko down to her nose yana kissing then to her chilled lips,lumshe idanu tayi tana jin wasu irin feelings suna tsarga mata tun daga cikin kwanyar kanta har ixuwa tafin kafafunta......Cikin black plain abaya ta shirya yayinda Sadeeq yayi complementing look din da dark blue kaftan wacce ta amshi jikinshi Sosai,fauxa ce ke driving tana bashi labarai masu dadi da ratsa xuciya,haka ne yasa basuga dadewar tafiyar ba suka karasa gidan,direct part din mami suka nufa dayake Abba baya gida alokacin,tun daga nesa mami ke kallon Fauxa tana jin wani dadi na fuxgarta ganin Sadeeq on his feet kamar wanda bai taba ciwo ba,Sosai hakan ya mata dadi taita xuba musu albarka acikin ranta,tana musu adduar dacewa aduniya da lahira,da kuma adduar kasancewa tare cikin aminci so dakuma kaunar juna har abada,fauxa ce ta rungume mami cikeda farin cikin ganinta,saide bataji dadin yadda taga mami ta rame ba wanda hakan baya rasa nasa da damuwar da mami ke ciki,"fauxa matsa ki bani waje nayi ma ɗana sannu"cewar mami tana ture fauxa daga jikinta,dariya fauxa tayi Sadeeq ya gaida mami ta amsa tana tambyar ya jikin shi,cikeda girmamawa yake amsawa saide har lokacin kanshi yana kallon kasa,har lokacin ya kasa sabawa sosai agaban mami,Saliha ce ta kawo musu abinci kamar yadda mami ta umarce ta da yi,yayinda fauxa ta sauko kasa ta cika masa plate da abincin,satar kallonta yayi yace"ya isa haka"hararar wasa ta mishi tace"bude ciki xakayi kaci abinci kona hada ka da mami "cute smile yayi yace"muje mu gaida umma..."fauxa tace"idan ka gama cin abincin sai muje "....yana cin abinci tana mishi hira har ya gama sannan suka wuce part din umma dake parlour tareda hajjo suka shiga,hajjo ta xaro ido tana mamakin ganinsu can kuma ta ce"lale marhabun gawa taki rami"murmushi Sadeeq yayi yace"fatan mu sameku lafiya?"cikeda mutuntawa suka gaisa umma sai kallon Sadeeq takeyi tana tsorata da lamarin ubangiji,farin shi da kyanshi yana nan saide ya rame sosai,basu dade a part din ba suka koma bangaren mami wacce tacika kamar xata fashe,fauxa ta zauna tana fadin"mami banga emaan ba,koda yake nasan ta kulle acikin daki tana aikin tunani"gaban mami ne yayi mummunan faduwa,ta wani runtse ido cikeda bakin ciki da takaici sannan tace"hmmm kefa bakisan meya faru ba ko?"xaro ido fauxa tayi gabanta yana faduwa,sadeeq ya runtse ido yana jin kamar xuciyar shi xata tarwatse saboda damuwa,fauxa dake dafe da kirjinta tace"meya faru?"mami wacce yanayinta ya canxa lokaci daya tace"ai tana London,burin su ya cika.."cikeda mamaki Fauxa tace"London kuma?me takeyi acan??"ta jefa ma mami tambayar saboda ta xama confused,mami tace"bakisan an daura aurenta da alameen ba?"wata irin xabura fauxa tayi cikeda tsananin mamaki,takasa yadda da maganar mami,tace"aure da alameen?but how comes?kuma banida labari?"gyada mata kai mami tayi cikeda tabbatar wa,fauxa ta saki wani cute smile tace"wow,Allah mai iko,and both of them didn't bother to tell me"ta fada tana kallon fuskar mami wacce ta tamke lokaci guda,fauxa tace"I'm so happy for them,Allah ya basu xaman lafiya"banxa mami tayi mata tana jin wani bakin ciki yana mamaye mata xuciya,baxata huta ba harsai taga bayan auren emaan,Sadeeq ne yace"Amin"yana girgixa kai cikeda damuwa da bakin ciki,itadai fauxa baxata iya bayyana farin cikin datake ciki ba,tace"yaushe ne bikin auren?dan gaskiya dole mu rakashe "Sai alokacin ta lura da kallon da mami ke wurga mata,sadeeq dake xaune awurin ne yasa takasa cewa komai daga uhmm sai uhmm uhmmm...basu dade ba Sadeeq yace su koma gida idan yaso sai su dawo gobe In shaa Allah,hakan ne ya hana mami da fauxa kebancewa balle su samu damar tattaunawa,da matsananciyar damuwa Sadeeq ya shiga gida direct kuma dakinshi ya shiga ya fada saman gado yana sauke deep breath masu nauyi,daga bisani kuma ya jawo wayar shi yana kallon emaan tareda lumshe idanunshi ahankali.....

EMAANWhere stories live. Discover now