PAGE 04

174 5 0
                                    

Eman...🥀

Page 4

  Acan gefe Na zauna sannan na gaishe da kowa cikeda girmamawa, har lokacin idanun Aliyu suna kaina masu fitar da ruwan hawaye,alokacin komai ya dawo mini sabo acikin zuciyata,hawayen bakin ciki masu zafi suka fara mini ambaliya,maganar Abba ce tasa Na d'ago ina kallon shi ba shiri
"Babu wanda zaizo daga dangin baban Eman,sun tabbatar mini da hakan jiya da daddare cewar sun tsame hannunsu daga kanta,kowacce matsala ce awurina ni marik'in eman za'a warwareta bi'izinillah".
"Alhamdulillah,abinda dangin babanta suka fad'a ya tabbatar da babban kuskure kake kokarin aikatawa matukar ka amince acigaba da shirye shiryen Aurenku,har ynzu kai yaro ne,baka San masifar da kake son jefa kanka aciki ba,har yanzu ina kan bakata kamar yadda na fada tun akaron farko,bazan tab'a amincewa da auren Eman ba matukar I'm still breathing kuma ni ce na haifeka ".
Mommy Ta fada tana watso mini kallon tsana.
Alhaji Mukhtar Marshal yace"baki isa ki hana Aliyu auren eman ba kamar yadda na fada miki tun akaron farko,wannan bambamin naki baida wani amfani domin bazai hana abinda Allah zai qadarta faruwar shi ba,matukar Aliyu na son eman kuma ya amince zai aureta babu wanda ya isa ya hana,na bashi go ahead dakuma zabi,kuma zan tabbatar yayi abinda zuciyar shi takeso matukar I'm still breathing kuma nine mahaifinshi "yafada da babban murya.
Cikeda tashin hankali mommy tace"wannan yar yawon kake so Aliyu ya aura?wacce tagama watsewa da tambad'ewa a titi?wacce tagama rabar da mutuncinta ga kowani kare da doki?ita kake son Aliyu ya aura?har kana ikirarin zaka tsaya mishi ya auri yar iska yar shaye shaye?daidai nake dakai da Aminu dakuke daure mishi gindi ya auri karuwa ya ajiye acikin gidan shi,dama can yan uwanka ba kaunata suke ba,burinsu kullum mu zama topic of discussion awurinsu,dawani ido zan kalli mutane nace musu Eman ce matar da D'ana mafi soyuwa agareni zai aura? Wallahi bazai taba yiwuwa ba kaji na rantse".
Fuskar umma kawai nake kallo,wacce hawayen bakin ciki ke zubo mata,nasan tana cikin tsananin damuwa da tashin hankali,amma batada tacewa wai b'arawo ahannun mata,na rigada na lalata komai,gashi my mom and I are paying for the consequences,Sosai maganganun mommy suka tayar mini da hankali,na tabbatar she'll try her possible best ganin ta tarwatsa maganar auren.
"Haba hajiya Zainab,miye haka kikeyi kamar wata karamar Yarinya?ai ko mutuwa na kunyar idon mahaifi dazaki zauna kina tone abinda ke rufe,idan d'anku yafasa aurenta ki fada cikin mutunci da Kamala mana,zakizo kina aibatata agabanmu iyayenta saboda rashin kara da kawaici,babu wanda ya muku dole awurin nan,dan haka you're free to express yourself amma ki tabbatar cikin sigar mutuntawa zakiyi,bazai yiwu ki zauna kina fadar maganganu marasa dadi ba akan Eman,maganganu marasa tushe bare mafari,yaushe Eman ta rabarwa kare da doki darajar ta ta 'ya mace ?"cewar Hajiya kwaise.
"Ke hajiya kwaise bana ciki da salon munafurci,banda ke yar bani na iya ce ina ruwanki acikin wannan maganar?ke awa?dan haka ki kame bakinki kiyi shiru domin bakida wata alaqa data baki damar tsoma baki cikin wannan maganar,kuma bazaki burge niba sai kin aurawa Eman d'aya daga cikin 'ya'yanki,ai idan duniya da gaskiya ma hakan yakamata ayi,amma kin killace naki 'ya'yan kina son d'an wata ya aura saboda kema ta zame miki masifa kina tsoron kada afasa aure da Aliyu ayi da d'aya daga cikin 'ya'yanki". Cewar mommy cikin d'aga murya,jinjina kai Alhaji Marshal yayi ranshi ya b'aci Sosai,tabbas Mommy da gaske takeyi,kuma bazata sassauta ba,da fada yace"kada na kuma jin bakinki awurin matukar na isa dake kuma nine mijinki".
Abba yace"Aliyu kamar yadda mahaifinka yabaka damar yin shawara da zuciyar ka,muna son sanin matsayar ka akan wannan maganar".
Mommy ce tayi saurin katse shi "bayaso,yafasa aurenta koda kuwa ita kadai ce mace a duniya,bare ga mata nan masu tarbiyya da yawa agari".
Alhaji marshal yace"ban isa dake ba kenan ko?ni zaki zubarwa mutumci agaban surukai?".
Tayi saurin cewa"Allah ya kiyashe mu zama surukai dasu,kuma dama na fada maka,babu yadda zaayi na zuba ido acuci d'ana".
Girgiza kai yayi cikeda b'acin rai yace"tashi ki fita daga falon nan,tunda bazaki tsaya acimma matsaya ba".
Tace"babu inda zanje matukar maganar Aliyu za'a cigaba da tattaunawa ".Rike kai Abba yayi cikeda damuwa,yana juyashi ahankali,umma dake gefen shi  yake kallon yadda ruwan hawaye suke fita daga idanunta non stop,wani bala'in tausayinta ne ya shigeshi wanda yafi na baya,yace"Hjy kwaise,ku shiga ciki,inaga wannan maganar ayita iya mu iyaye maza zaifi".jiki ba kwari hjy kwaise ta mike ita da umma suka bar falon,Ya kalli bangaren da Mommy take yace"hjy zainab Munso ayi komai daku amma hakan bazai yiwu ba,mun baku dama amatsayin ku na iyaye mata but you misused it,yanzu zamuyi magana ne atsakanin mu dakuma yaran mu,ina me neman alfarmar ki bamu waje".kamar wacce aka tsikara tayi saurin mikewa tareda bin bayan su Umma,hakan yasa kowa ya sauke ajiyar zuciyah,shiru ne ya biyo baya Na d'an wani lokaci kafin abba yace"Aliyu muna sauraronka ".
Sosai Aliyu ke zubarda hawaye,musamman yadda yaga iyayenshi na sa'insa,abinda bai tab'a gani ba sai akan shi,ya tabbatar bazasu tab'a kasancewa cikin ra'ayi daya ba,saide dole ya farantawa daya acikinsu,shikuma duk duniya farin cikin iyayenshi ne abu mafi muhimmanci a gareshi,bakin shi na rawa yace"Eman ce zabin zuciyata,eman nake so kuma nake da muradin karasa rayuwata da ita,banida wani burin daya wuce zamtowa miji ga eman,ina sonta kuma zan iya zama da ita acikin kowani hali".

Ajiyar zuciyah mu ka sauke alokaci d'aya,wani sanyi naji yana ratsa zuciyata,nasan Aliyu baze tab'a matsawa daga gefena ba,Sosai Abba yaji sanyin maganar Aliyu,wani dadi ya lullube zuciyar shi.
Bayan su umma mommy tabi tana yatsine fuska,ta tabbatar hakarta bazata cimma ruwa ba ta ruwan sanyi,dole ta jajirce tayi rashin mutunci,zama tayi akujera mai facing umma tana cewa"gara ma kidena wannan kukan Na munafurci,domin ko kukan jini zakiyi bazan tausaya miki ba,kina kallon yar taki Na gantalin bin maza baki hana ba saida ta kwaso abin kunyah zakizo kina ma mutane kukan karya dan a tausaya miki,ki goge su tun wuri dan bazasuyi tasiri akaina ba,kuma ko duniya ce zata tsaya miki wallahi Aliyuna bazai auri tambad'add'iyar yarki ba ragowar maza".
Dariya mai sauti mummy keyi,ranar datake jira ce tazo,ranar da zataga umma Na kuka da idanunta,mama na gefe tana kunshe tata dariyar,ganin haka yasa mommy gyara zama,domin ko baa fada ba ta fahimci suna takun sak'a,Dan haka dole tayi amfani da wannan damar ta tozarta umma agaban kishiyoyi.
"Haka kawai dan wulakanci za'a mannawa d'ana gayyar tsiya,gayyar wa'iyazubillahi saboda bakida imani da tausayi,wannan ay rashin imani ne mara misaltuwa,ita hjy kwaise dake daure maki gindi ga 'ya'ya nan Allah ya bata wanda sukafi Aliyu amma saboda bak'in munafurci take so abaiwa Aliyu,toh ina me tabbatar muku d'ana yafi karfin ku".
Murya Na rawa umma tace"kidena saka hjy kwaise acikin rashin mutuncinki,kamar yadda kika fada batada alaqa da wannan maganar,dan haka kidaina alaqantata da 'ya'yanta acikin wannan maganar,yaranta da basuji ba basu gani ba,nima eman ce tabaki damar fadamin maganganun nan da ko amafarki baki isa ki mini kallon banza ba,tabbas dan kuka ke jawa uwa jifa".
"Ki barta muga karyar rashin dabi'a"cewar hjy kwaise cikin b'acin rai,"har wata rashin dabi'a kuke son gani wacce baku ganta ba?rashin dabi'a ai sede akoya awurinku,domin gata nan ta hayyafa tayi naso muna kallo".
Cewar mommy tana gyara zaman gyalenta,mama tace"bari naci gyaranki domin gaba,idan kina magana ki riqa warewa,kidaina saka 'ya'yanmu masu tarbiyya aciki".
Dariya mommy tayi tace"Hajiya fatima,narantse miki da Allah bazan raga miki ba,rashin mutunci yanzu nafara yin shi,bana fatan Aliyu ya auri eman,amma idan har hakan ta kasance toki tanadi likafanin birne'yarki domin bakin ciki zaiyi ajalinta,gara kuwa kada ki fara batun siyan shikafa,ki had'ota da maganin hawan jini da ciwon zuciya domin su zata buk'ata,ina me tabbatar maki tayi bankwana da farin ciki acikin lalatacciyar rayuwarta,muzuba shege ka fasa".
Hjy kwaise tace"aiko sainaga karshen haukarki mahaukaciya".
Dariya mommy tayi harda tafi sannan tace "ko kuma naga karshen taki haukar ba,lokacin da d'anki zai auri eman itace karshen".gaban hjy kwaise ne yayi mummunan fad'uwa,kallon bakin ciki hjy kwaise ke bin ta dashi tana jin kamar ta shak'e tsinanniya ta huta.
Sosai hakan yayiwa umma da mommy dad'i,yadda aka cima hjy kwaise mutunci,saboda yadda ta zame musu k'adangaren bakin tulu ta hanasu rawar gaban hantsi.
Mikewa mommy tayi tana wurga ma hjy kwaise da umma kalllon wulakanci tace"sainazo cin shinkafar bikin eman da d'aya daga cikin yaranki ko kuma yaran su"tafada tana kallon mama da mummy,"ku tashi tsaye kada ta cuce ku dan na lura kece azuciyar Abban kuma ba Allah bane aranta".Sosai hankalin mama yatashi,mummy dake kissima abubuwa da yawa cikin ranta tace"hjy zainab sa mini lambarki ".ba musu mommy ta saka mata tareda ficewa daga falon takoma falon da muke zaune,batareda b'ata lokaci ba tace"idan ka amince da auren eman saide ka nemi wata uwar bani ba".tana gama fadin haka tafice daga gidan gabadaya.

Ajiyar zuciyah Aliyu ya sauke sannan yace"Inada burin auren Eman amma  banda ayanzu da abubuwan nan marasa dadin ji suka faru,ayanzu da mahaifiyata bata kaunar auren,nayi nazari Sosai na fahimci iyayena,nasan yadda kowanne acikinsu ke daukar abu,na tabbatar mommy bazata hakura ba,koda ta hakura ynzu na tabbatar saita maida rayuwar Eman abar kwatance,bazata yadda mu zauna lafiya ba,nikuma inason nayi aure domin samun nutsuwa,bazanso na bata ran mommy ba tunda ga abinda tace,kuyi mata uzuri tunda akaron farko taso abinda nakeso,yanzu ne da abubuwan dasuka faru take ganin fasa auren shine mafi alheri,Har na mutu bazan daina sonki ba eman,amma zan jira har lokacin da mommy ta amince min na aureki,nayi miki alkawari zan dage Sosai wurin fahimtar da ita".tunda Aliyu yafara second phase din maganar shi kaina yafara juyawa,tashin hankali kenan wanda baa sa mishi rana,ban taba tunanin Aliyu zai furta mini wannan kalaman ba,yafasa aurena shikenan na shiga uku Na lalace,innalillahi wainna ilaihi raji'un,na kasa kuka nakasa furta koda kalma daya,i don't know what to do,brain dita tadaina functioning,I'm in so much pain,girgiza kaina kawai nakeyi wanda ya mini nauyi,ina kokarin mikewa tsaye ko ganin gabana banayi saboda duhun daya mamaye mini ido,sama sama naji Abba nacewa"Eman.."sai yayi shiru yarasa me zai ce mini banda hawayen dayake fitarwa.


*masu bibiyar eman kuyi hkr kun jini shiru,banida lfy amma alhamdulillah naji sauki,mu cigaba da gashi*
Zaynab Yusuf ke muku fatan alheri.

EMAANWhere stories live. Discover now