PAGE 33

111 4 0
                                    

EMAN.....PAGE 33

With a trembling heart ya miƙe xaune yana goge gumin dake xubo mishi duk da sanyin ACn dake daƙin,ya runtse idanu asanyaye thinking about abinda yayi niyyar aikatawa a safiyar gobe,bai taɓa samun kanshi cikin rauni da karyewar xuciya irin na ranar ba,at some point yana jin kamar baxai iya aikata hakan ba,tuna cewar Fauxa xaiyi ma hakan shine yake samun ƙwarin gwiwa,but he must say this is the worst night of his life,daren daya banbanta da sauran dararen cikin rayuwarshi,daren daxai kafa mummunan gurbi acikin duniyar shi,duk taurin xuciyar shi saida idanunshi suka ciko da ruwan hawaye,musamman idan ya tuna da Yasmeen ɗinshi,yanajin xuciyar shi na ƙuna,wani hali xata kasance idan tasamu wannan mummunan labarin saboda baxe iya faɗa mata hakan da kanshi ba,miƙewa yayi yafara safa da marwa acikin dakin,so many things are going through his restless mind,why is life so unfair?awannan lokacin ne yaso yayi settling down with the love of his life amma he can't believe this unforeseen circumstances dasuke faruwa that left him with no choice but to sacrifice his happiness for his sister,hawayen dake maƙale a idanun shi ne sukayi nasarar xubowa,bai hanasu cigaba da gangarowa ba hasalima barinsu yayi suna xuba son ransu daga idanunshi wanda sukayi jajir kamar garwashin wuta, xuciyar shi na ƙuna,tsanar Eman na sake ninkaya acikin ranshi,she's the cause of every single pain he's going through at the moment,al'amari ne wanda bai taɓa tsintar kanshi aciki ba in his whole life,babu mahalukin daya taɓa sashi xubar da hawaye sai ita,babu damuwar  data taɓa hanashi bacci amma yau gashi bacci ya gagari idanunshi,babu wanda ya taɓa mishi kutse acikin rayuwa sai ita,shiyasa yakejin tsanar ta acikin ranshi fiyeda misali,yadda ta  ruguxa mishi long time plan ɗinshi wanda ya daɗe yana planning,she ruined his life kawai xa'ace at the very end daya ke tunanin every single thing is set right .bai taɓa tunanin xai iya hurting din mutum to feel relieved ba sai akan Eman,he never thought xai iya kallon wani da irin kallon dayake ma Eman,he never thought he's this kind of person sai yanxu,she successfully unveiled that other side of him,wanda baiyi tunanin akwai halayyar ajikinshi ba sai yanxu da Eman tayi unavailing....ajiyar xuciya mai nauyi ya sauke sanda yaji an buɗe gate,yanada tabbacin Abba ne ya dawo,agogon dake dakin ya kalla yaga 2am na dare,sai ya koma ya xauna tareda dafe kanshi mai tsananin ciwo wanda yakeji kamar xai tarwatse saboda damuwa,xaxxafar soyayyar Yasmeen ce ke ɗawainiya da xuciyar shi,wannan ne babban dalilin daya hargitsa mishi tunani,he can't believe xaiyi betraying dinta,Yasmeen dinshi da yake tsananin so da ƙauna,babban burinshi aduniya is to make her his wife,amma Eman ta wargaxa komai,jinjina kai yayi asanyaye domin he's not going to forgive her,sai ya maida rayuwarta a living hell,he'll make sure she cry a river,he'll surely teach her a befitting lesson,wanda har ta mutu baxata manta ba.sai ya rama duk bakin cikin data sa shi aciki harma da ɗoriya.da wannan tunanin wani wahalallan bacci ya ɗaukeshi,wanda kallo daya xaka mishi kaga ba baccin dadi yakeyi ba kawai dai yanayi ne kasancewar bacci barawo baka sanin lokacin dayake saceka.Adaren ranar Eman couldn't sleep properly,sai juyi takeyi gabanta nata faɗuwa,she could tell akwai abinda ke shirin faruwa da ita,tashi tayi xaune tareda dafe kirjinta dake pounding kamar ana daka acikin kirjin nata,taji baxata iya cigaba da baccin ba,sai kawai ta xuro kafafuwanta kasa tareda mikewa tashiga toilet,alwala tayi jikinta asanyaye tafito daga bandakin,yau ne rana tafarko datayi sallar dare domin samun sassaucin abinda ke damun xuciyrta,tun faruwar al'amarin can yau ne ranar data fara kai kukanta xuwaga Allah acikin tsakiyar dare,ta daɗe tana sallah tareda yin addu'o'i masu yawa,saidai har lokacin gabanta bai daina faduwa ba,runtse ido tayi ahankali hawaye suke xubo mata wanda ta rasa dalilin xubarsu,ji tayi tausayin kanta na shiga kowani lungu da sako na cikin xuciyrta,haka tacigaba da tunane-tunane har akayi kiran sallar farko,Umma dake dafe da kirjinta ta sauke ajiyr xuciya mai nauyi,tun goman dare take fama da nauyin kirji tana jin numfashinta yana yin sama da kasa,she's not breathing well,addua kawai takeyi tana kalmar shahada domin a tunanin ta lokacin tane yayi,runtse idanu tayi wasu xafafan hawaye suna xubo mata na tausayin yaranta,yaya xasu cigaba da rayuwa idan babu ita?musamman Eman,gabanta ne ya sake faduwa a karo na biyu,ta damƙe bed sheet da iya karfinta tana kuka kasa-kasa,tausayin Eman ne ke ratsa xuciyrta,domin idan tayi tafiyar da babu dawowa babu wanda xai wahala acikin ƴaƴanta fiyeda Eman,sai awannan lokacin taji ƙaunar ƴar tata na ratsa ta,tana tuna irin wahalar dasuka sha agidan Lameen,and what she went through akan auranta da Aliyu,she hated herself for leaving eman all by herself,da sauri Umma ta mike sakamakon numfashinta dayaƙi sauka,ta bude bakinta da hanxari tana breathing in,idanunta suka fiffito waje sabbin hawaye na kwararo mata,curtains din dakin ta bude tana shakar fresh air,adaidai lokacin da Eman tashigo cikin dakin,saboda yadda takasa daurewa,tana jin jikinta na mata wani iri,da sauri ta shiga dakin ganin Umma ajikin Window,tayi saurin cupping face dinta tana tambayar"Umma are you okay?"asanyaye Umma ta girgixa mata kai kamar ba wacce ke cikin ciwo ba tace"I'm fine "tareda rungume Eman iya ƙarfinta,jikin eman ne yayi sanyi,taji har lokacin gabanta bai daina faduwa ba,can dai tace"Umma I'm feeling restless,nakasa yin bacci tun karfe biyu gabana ke faduwa"Ummma dake boye pain dinta tace"babu komai Eman,khair in shaa Allah"xama sukayi agefen gadon Umma,Eman ta tsura mata ido na lokaci mai tsaho sannan tace "Umma meke damunki?"tambayar Eman ce ta karya xuciyar Umma,abinda takasa yima Eman kenan alokacin data fi bukatar ta arayuwarta,idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye tace "Babu abinda ke damuna,Karki damu kinji ko?"asanyaye Eman ta gyada mata kai,Umma ta riqo hannayen Eman tace"kiyi hakuri da rayuwa aduk yadda taxo miki,sannan put this at the back of your mind,ina sonki,ina kaunarki and I wish for your happiness in every falling star,just keep being yourself,Allah yacigaba da karemin ke"kuka Eman ta fashe dashi,Umma tace"shhhhhh!! Miye na kuka kuma?"eman tace"normally I should be happy about this but I'm feeling the opposite "saurin rungumeta Umma tayi tana jin kamar ana sa wuka ana caccakawa acikin xuciyar ta,the pain is becoming unbearable for her,sai kawai ta runtse ido bata son ta fashe da kuka agaban Eman amma sauran ƙiris hakan takasance saboda tana cikin ciwo mai tsanani,asanyaye kuma dakyar tace"go back to your room,xanyi bacci "Sosai Eman taji hankalinta bai kwanta da hakan ba amma bata san me xatayi ba alokacin,sai kawai takoma bedroom dinta.Asanyaye alameen ya bude idanshi dasukayi nauyi saboda rashin samun wadataccen bacci,kallon dakin nashi yayi for few seconds sannan ya shiga toilet,wanka yayi ya shirya yana kallon time,karfe 9am daidai yagani,saida ya sauke wata deep ajiyar xuciya sannan ya nufi part din Abba,gaban shine ya fadi ganin Mami da Abba suna breakfast, gaishesu yayi sannan ya koma can gefe ya xauna,Abba could tell akwai magana abakin alameen din,hajiya kwaise ma sai kallonshi take kafin tace"kayi breakfast?"girgixa mata kai yayi yace"I'm okay for now"shiru tayi nawani lokaci,Abba dake karantar reactions dinta yace"idan ban manta ba,na taba baki ajiyar wata safe box ko?"saurin gyada kai tayi tace"sure "yace"kawo min"da hanzari ta mike ta wuce part dinta domin daukowa,shikuma Abba ya kalli alameen attentively sannan yace"tell me what your problem is "dawowa kusa da Abba yayi yana jin jikinshi very weak,can dai yayi jarumtar cewa"alfarma nake nema awurinka"Abba yace"go on,ina jinka"wata warm breath ya furxar sannan ahankali yace"ina son kabani auren Eman"cak Abba ya tsaya yana kallonshi cikeda mamaki,yafi minti biyu yana kallon fuskar alameen din,can ya mike tsaye yace"maimaita abinda kace"da mamaki alameen yake kallon Abba,saboda da hausa yayi maganar kuma ya tabbatar Abba yaji meya fada,then why is he asking him to repeat himself?Abba yace"I said repeat yourself kasan me kake fada kuwa?"with a pounding heart alameen yace"cewa nayi ina neman alfarma kabani auren Eman"Abba still yayi yana kallon alameen,har lokacin bai daina mamaki ba,sannan fuskar shi babu digon murmurshi akai,xama yafi for few seconds sannan ya saki wani kayataccen murmushi,farin ciki ya lullube shi,baisan lokacin daya rungume alameen ba yana dariya yace"nabaka ita halak malak "ajiyar xuciya alameen ya sauke sannan yace"amma ina son hakan yaxama between the two of us,sannan inason a daura auren in few days time"Abba yace"ahada dana afiya kenan?"girgixa kai alameen yayi yace"kafin na Afiya "shiru Abba yayi can yace"tell me the truth,what's going on in your mind "saurin xaro ido alameen yayi yace"babu komai acikin raina Abba,I just want to make her my wife,kuma nan da kwana kaɗan zan koma London, inaso mu tafi tare ne,sannan ni bame son taro bane,parlour wedding is enough,idan an daura auren kowa sai yaji alokacin"cikeda gamsuwa Abba yace"it's alright then,but I need to ask her naji nata opinion din "alameen yace"sure,nagode Sosai Abba,Allah ya kara girma"yana gama fadin haka ya fita daga parlon,a entrance yaga hajiya kwaise tsaye tana kallonshi,ji yayi gabanshi ya fadi sai kawai ya karbi box din daga hannunta ya ajiye agaban Abba sannan yafita,part dinshi yakoma bayan yace ma Saliha ta kira mishi Eman.Da sallama Saliha ta shiga part din Umma,lokacin Eman na Xaune a parlor tana jiran Fitowar Umma wacce har lokacin bata fito daga daki ba,kuma hakan ba dabi'ar ta bace,hasalima Umma ce ke fara fitowa ta gabatar da breakfast ,Eman ce tayi wasu abubuwan atunaninta bacci Umma keyi,asanyaye ta amsa sallamar,Saliha tace"Ina kwana anty Eman"lafiya kalau Eman ta amsa,Saliha tace"yaya na kiranki"da sauri ta kalli Saliha atakaice tace"ok".gabanta na tsananta faduwa,hijab dinta dake gefe tasa tana jin wani tsoro da fargaba suna saukar mata,takasa apprehending dalilin kiran nasa,asanyaye tashiga part din nashi bakinta dauke da sallama,Mummy da Mama suka saki baki suna kallon juna cikeda mamaki,suna tunanin me Eman tashiga yi a part din alameen wanda ko ƙannenshi bai fiye so suna shiga ba sai yaxama dole,jikinsu na tsuma suka wuce part din hajiya kwaise domin abinda suke tsammani long time ago ne ya faru yau din.Xaune taganshi ya riƙe kai tareda lumshe idanu,bai amsa sallamar ta ba haka nan baice mata komai ba,da bango ta jingina murya na rawa tace"gani"yana jinta amma ya mata banxa,ta dade tsaye awurin har ƙafafuwanta suka fara xafi,data gaji da tsayuwar sai kawai ta juya xata fita,wata tsawa ya daka mata yana cewa"how dare you walk out of me?"yafada tareda mikewa yana kallonta da jajayen idanunshi wanda suka firgita Eman tayi saurin runtse ido,yace"come here"yafada atsawace yana nuna mata can karshen falon kusa da bedroom dinshi,kafarta na rawa take tafiya har ta je wajen,ahankali Kuma majestically yake closing gap dinsu,ji tayi kamar ƙasa ta buɗe ta shige saboda tsoro,tana tambayar kanta meya kawota part dinshi,ahankali ya furta"Fatima Lameen Abdulfattah ko?"taji ya ambaci asalin sunanta dakuma full name dinta at once,Yace"tambayarki nake"saurin gyada mishi kai tayi hawaye masu xafi na gangaro mata,yace"why do you feel the need to betray Fauxa?me ta miki?"gaban Eman ne yayi tsananin faduwa,bakinta na rawa tace"I didn't betrayed her...."yayi saurin cewa"shut your dirty mouth up!."yafada da karfi iskar bakinshi tana sauka asaman fuskarta,"duk abubuwan da Abba ya miki na alheri sakayyar da xaki mishi kenan?"yacigaba da fadin"you tried really hard wurin tarwatsa rayuwar fauxa,adalilinki take xubar da hawaye akowacce rana,she's going through a whole lot because of your selfish interest,and you left me with no option than welcoming you into my life,now answer me,idan na mayarda rayuwarki a living hell kinyi deserving ko baki yi ba?".shiru Eman tayi tana digesting maganar tashi,domin wannan shine karo na farko da wani ke nuna mata xallar qiyayya agaban idanta ,dukan bango yayi da karfi yace"answer me!"jikin ta na shaking ta girgixa kai sannan tace"I didn't deserve....."yayi saurin katseta ta hanyar cewa"liar,you're indeed a terrible liar,bayan kasancewar ki macuciya ashe harda ƙarya acikin lamarinki,two faced that is who you are,Musa a fuska fir'auna a xuciya ,dama na fada muku keda bloody ingrate Sadeeq I won't let you succeed,anjima Abba xai kiraki to hear your opinion akan aurenki da xanyi,idan ya tambayeki me xakice mishi?"tambayar tashi ce taxo mata a baxata,ta riqa kallonshi ko kiftawa babu,her opinion akan auren su?wani irin aure in the first place?kuma auren ma ita dashi?tsawar daya daka mata ce tasa ta lumshe ido,"nace mexaki ce mishi??"ahankali ta bude ido sannan tace "I'll say no" ta fada da iyakar gaskiyarta,Yace"idan baki nuna wannan halin ba ay baki cika Eman ba,the ungrateful person I've ever seen,inaso kisa abinda zan fada miki at the back of your mind,I won't force you,baxan miki dole ba,amma abubuwan daxan miki dakanki xaki dawo running back to me kina roƙona akan hakan,so you've two options,duk wanda kika bi daidai ne".jikinta na rawa take kallonshi for few seconds tarasa me xatayi alokacin,ratsawa tayi xata wuce ta gefen shi yace"I'm not done yet!"yacigaba da fadin"how dare you think that xan kiraki na  ajiye ki Cikin parlour na for so long without a big reason???,lemme tell you something Na tsani kallon fuskar ki balle magana dake,and I'm assuring you daga rana me kama ta yau kin ƙulla xumunci da bakin ciki kamar yadda kika jefa rayuwata into a dilemma,and mind you wannan maganar is between me,you and Abba,nobody should hear about this,now get your filthy body out of my room"yana gama fadin haka ya shige bedroom dinshi tareda bugo kofar da karfin gaske.ta runtse ido ahankali sannan ta juya xata fita daga dakin taga hajiya kwaise tsaye ta rungume hannu akirji tana kallon ta keenly,she can't believe her eyes,Eman ce a part din alameen,what brought her here?gabanta ne ya fadi tunda suka hada ido da hajiya kwaise,asanyaye Tace "what are you doing here?"hjy kwaise ta tambaya,shiru Eman tayi ta rasa me zatace mata wanda xai wanke ta daga ɗaurin xato,tace"tambayarki nake,me kikeyi anan?"nan ma shiru Eman tayi gabanta na tsananin faduwa,alameen ne yafito daga bedroom dinshi yana kallon Eman da hjy kwaise,murya can kasa yace"saƙo xan bata ta kaiwa Abba"daga nan ya mika mata wata ƴar short note batareda yace komai ba,hannu na rawa ta karba tayi saurin fita daga part din,da kallo hajiya kwaise tabi ta,alameen ya sauke ajiyar xuciya,ta kalle shi tace"what's the meaning of this nonesense?"kallonta yayi carefully yace"Mami I ...."daga mishi hannu tayi alamar dakatarwa sannan tace"not a single word "tafaɗa tana kallon shi rai ɓace ta sake cewa"wannan yaxama karo na ƙarshe daxanga irin haka"gyaɗa mata kai yayi baice komai ba,ta mike tafita wearing a very serious face.Kamar ɓarauniyar datayo sata haka Eman ke xabga sauri xuwa part din umma,tana shiga falon ta sauke ajiyar xuciya,saide ganin bakowa afalon yasa gabanta faduwa,jiki asanyaye tayi knocking bedroom din Umma,ta dade tsaye awurin bataji motsin kowa ba,sai tayi saurin shiga xuciyarta na bugawa da sauri-sauri,short note din hannunta ce ta fadi kasa lokacin dataga Umma kwance a kasa almost lifelessly,kamar bata numfashi,da gudu Eman ta shiga dakin tana jin wani migraine yana saukar mata,tayi saurin dora hannu ajikin Umma alokaci daya tayi saurin daukewa saboda xafin da jikin Umma yayi,ta xaro ido tana tapping shoulders dinta "umma wake up"ga mamakinta taga kamar Umma bata jin abinda take fada,da sauri ta mike hawaye suna gangaro mata ta shiga toilet jikinta na rawa ta yayyafawa Umma ruwa,wata doguwar ajiyar xuciya Umma ta sauke sannan ahankali eyelashes dinta suka fara motsi,cikin dauriyar da bata san tana da ita ba ta taimaka ma Umma ta mike xuwa kan gado,sai nishi Umma ke saukewa kamar wacce tayi race,toilet Eman ta koma ta hada mata ruwan wanka sannan ta taimaka mata tayi wanka,ba laifi umma taji dadin jikinta, xubar da hawaye kawai takeyi all through,ta kasa cewa komai banda shima Eman albarka datakeyi acikin ranta,aranar ta sake tabbatar da cewar naka sai naka,saboda yadda taga tsantsar damuwa a fuskar Eman din is unexplainable,hakan ne ya sake karya mata xuciya ga kuma ciwon da jikinta ke mata mara misaltuwa,kitchen Eman tashiga ta hado ma Umma spiced tea da chicken pepper soup,saida Tayi shredding kaxar sannan takai mata,da farko ƙin ci Umma tayi saida Eman tayi mata dagaske tukunna,tana kammalawa ta nufi part din Abba,she looks calm amma ita kaɗai tasan me takeji acikin xuciyarta.
Sakin baki mummy tayi cikeda damuwa tana sauraron hajiya Zainab me cewa"Nima ban San da hakan ba Sai ynxu Aliyu ke fada min,ashe bayan an fasa auren nashi da Eman bai kammala ginin ba,nikuma dayake inada commitments ban sake bi takan maganar ba,to kana ta kanka wake ta kaya?gida dai nan da one month xa'a gama"shiru mummy tayi can tace"Toh ya xa'ayi kenan?"hajiya Zainab tace"idan ita Afiya tafi son shiga gidan nashi sai a ɗaga biki xuwa nan da one month din,idan kuma xa'ayi nan da 10 days xa'a iya mata jeren ta anan gida,tunda akwai apartment saidai karami ne,yanada parlour daya,2 bedrooms sai toilets,kinga xai ishe su for the mean time kafin a kammala ginin"shiru Mummy tayi tana jin abin banbarakwai wai namiji da suna hajara,jiki asanyaye tace"baxa'a iya gamawa a kwana goman ba?"ta dayan bangaren hajiya zainab tace"kinga hajiya Aisha karki ɗaga min hankali,nace miki nan da wata daya xa'a gama,kuje kuyi shawara xuwa anjima ki fada min abinda kuka yanke"kafin mummy tayi magana Hajiya zainab ta kashe wayarta,kallon Afiya mummy tayi cikeda takaici tace"kinji yar iskar mata daga magana xata min tijarar data saba "Afiya tace"haka nan xa'a hakura da karamin flat din"ajiyar xuciya mummy ta sauke ba don ta so ba,tana jin wani bakin ciki na turnuke mata wuya.Rafee'ah dai tana gefe tana kallonsu,suka hada ido da Afiya wacce jikinta yayi sanyi,afusace tace"munafuka ina ruwanki sai wani kallon mu kikeyi,abinda kikeso ne ya faru saiki xuba ruwa akasa ki sha"murmushi Rafee'ah tayi batareda tace komai ba,Mummy ta kalleta tace"Tashi kibar wurin nan"mikewa tayi tafice daga falon Afiya na bin ta da rakiyar tsaki.Ko second goma Eman batayi da fita ba Hajiya kwaise ta shigo part din Umma,yadda hankalinta yaki kwanciya da xuwan Eman part din alameen ke damun xuciyarta,dakin Eman tashiga tarar bata nan sai kawai ta shiga dakin Umma dalilin kofa data gani abude,da dan mamaki ta kalli Umma dake bacci tana sauke numfashi da kyar,sai ta juya falo jiki asanyaye tanata tunane-tunane,kamar ance ta juya taga yar kamar short note din da alameen ya ba Eman wacce yace sakon Abba ne,da mamaki take kallon short note din da iska ta koro cikin falon,gabanta ne yafadi,hannunta na rawa ta tsugunna ta dauka tana ta jujjuya ta ahannunta with different thoughts,kenan alameen raina mata hankali yakeyi akwai wani abu tsakaninshi da Eman?wasu munafukan gumi ne suka tsastsafo mata hannunta na rawa ta bude takardar,ji tayi kafafuwanta baxasu iya cigaba da daukan taba,asanyaye ta xauna akan kujera tana damke takardar da iya karfinta.

Dedicated to my lovely Mum Ummu faisak💕

Zaynab Yusuf ✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now