PAGE 11

142 5 0
                                    

Eman...🥀

Page 11

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Acikin duniyata data k'unshi al'amura marasa tabbas,a gajere da kuma guntun tunani na,acikin nazarina mara zurfi,nayi hasashen lokacin warwaruwar matsalolina ne yazo,duk da har yanzu tsahon sati uku umma bata sauko daga inda tahau na fushi daniba,haka zalika bata tab'a nemana ba tsahon wannan lokacin,sannan bata tab'a tambayar ya Fauza halin danake ciki ba,hakan datayi  ya tsinka mini zuciya sannan ya sanya ni cikin garari,amma bazan karaya ba,sannan bazanyi qasa a gwiwa ba,na tabbatar inde rana zata cigaba da fitowa tana faduwa,in har munada yawancin kwana,akwai ranar da fushin da umma ke yi dani zai zama tarihi.tamkar yadda umma ta banzatar da lamarina haka Aliyu yasanya k'afa ya shure ni daga cikin babin rayuwar shi,ya manta dani harma da existence dina,tun ina kukan rashin sa har idaniya suka daina zubar hawaye,zuciya tayi tauri, bakowani karamin abu bane ke firgitata,Addua na rike ta zamto mini bango abar jingina kuma tudu na dafawa da karatun Alqur'ani wanda dama shi makari ne kuma maganin damuwa da bak'in ciki,Yaya Sadeeq da ya Fauza bazan tab'a manta halaccinsu agareni ba,sun tsaya mini alokacin da kowa ya matsa daga gefena,sun share mini hawaye,sun mini komai arayuwa shiyasa na sanya su cikin addua ta ta khamsus salawat,a wannan  lokacin nake kokarin fuskantar rayuwa dakuma future dina,adaidai gab'ar da nake shirin fara sabuwar rayuwa,adaidai lokacin ne kundin kaddarata ya k'ara budo mini shafi mai tsanani,mai firgitarwa da rikid'a tunanin masu karatu,zanen k'addarata ya zana mini babban layi acikin rayuwar Yaya Sadeeq da ya Fauza mutanen da suka mini komai arayuwa,da nasan abinda zai faru kenan da ko amafarki bazanyi tunanin zuwa gidan ya Fauza ba!.
Kamar yadda nake tunanin umma akai akai haka tunanin babana ke damun zuciyata,duk da hukuncin daya yanke akaina me tsauri ne hakan bazai sa Na manta dashi ba,domin ko me zai faru bazaa canza ma tuwo suna ba,komai zaice akaina he's still my father har tashin duniya,babu wanda ya isa ya canza hakan,hawayen danake kokarin dakatarwa ne suka silmiyo suna zuba,cikin rashin zato da tsammani naga hawayena na diga akan tafin hannun yaya Sadeeq,saina juya da sauri ina kallon fuskar shi wacce ke d'auke da matsananciyar damuwa,idanunshi sunyi jajir sun k'ank'ance,murya asarke yace"kidaina kukan nan eman,bakisan halin da zuciyar wanda ya damu da damuwarki take shiga ba aduk lokacin da kike zubar da hawaye,rayuwa gabadayanta trial and test ce,kiyi hakuri ina nan ina kai k'ok'on ban hakurinki wurin umma".da mamaki nake kallon yaya Sadeeq,naga gaskiyar maganar da bakinsa ke furtawa acikin kwayar idanunshi,yaya Sadeeq mutum daya ne tamkar da dubu,nace"wurin babana nake son zuwa"saiya dan ja baya yana kallona cikeda mamaki,Yace"yaushe kikeson zuwa?"nace"ko yaushe ma,tunda gaishe shi zanyi".shiru yayi kamar me nazari sannan yace"dauko hijab dinki"jiki ba kwari na mike ina gyara zaman hular kaina,da kallo yaya Sadeeq yabini har na dauko hijab din nadawo,lokacin misalin k'arfe biyu da rabi ne na rana Ya Fauza Na wurin aiki,yaran kuma na school,agaban motar shi na zauna kamar yadda ya umarce ni,muka harba  kan titi yana driving calmly,baice mini komai ba haka nima bance komai ba duk da zuciyata nason tambayar shi abinda ke damunshi duba da  yadda suka damu da damuwata yasa nakasa yin shiru,nace"kamar akwai abinda ke damunka".murmushi yayi wanda yafi kama dana takaici sannan yace"ba kamar bane,akwai abinda ke damuna eman".ajiyar zuciyah na sauke sannan nace" meke damunka".yace"damuwata wata abace wacce a Hollywood za'a kiranta da blockbuster,wacce idan ta bayyana zata shayar da mutane mamaki,saide nikaina banida masaniyar lokacin da damuwar ta mamaye mini zuciya eman,addu'arki kawai nake bukata"asanyaye na gyada kai sannan nace"Allah ya yaye maka"yace amin,shiru ne ya biyo baya har muka karasa layin gidan mu,wanda yafi kowanne girma,kyau da kuma tsaruwa,Babana Alhaji Lameen Ibrahim hamshakin mai kudi ne wanda ya shahara akano kamar yadda Abba yayi kaurin suna,gabana ya fadi lokacin da yaya Sadeeq ya danna horn,masu gadi suka wangale gate muka shiga ciki,sai alokacin naji wata damuwa ta dirar mini,tayaya zan sanya kafa zuwa ciki?ya babana zaiji idan ya sanya idanunshi akaina?nayi ma kaina tambayoyin da banida amsar su,Yaya Sadeeq ne yace "sauka mana"yafada sannan shima ya sauko ,asanyaye nake binshi zamu shiga kofar babban falo muka jiyo muryar babana ta sama,"karki kuskura ki shigo mini gida".yafada da karfi Sosai wanda kowa na gidan zai iya ji,hakan yasa matar babana da siblings dina fitowa suna tambayar shi lafiya?bai saurare suba yace"get out of my house and never come back,never show your face ever again eman,na dade da cireki daga sahun 'ya'yana,dake da wanda kuke tare dashi should get your filthy body out of my house, ko ahanya banason ki nuna kin sanni,I don't want to see you ever again".yafada yana nuna mana hanyar waje,daskarewa nayi awurin kamar man kakide daya shekara,na kasa motsi nakasa cewa komai banda hawaye dasuke zubo mini,yaya Sadeeq ne yayi dauriyar cewa"muje eman"yanajin zuciyarshi na balbala da wuta,how can my father be so cruel,bai tab'a ganin inda uba kema yarshi haka ba,tun tasowar eman batasan miye dadin uba ba,dakyar nake iya daga kafata na shiga cikin mota ina jin numfashina nayin sama yana sauka da kyar,yaya Sadeeq yaja motar azuciye muka bar gidan,Ammi matar babana ta runtse idanu tana kallon sultana da Ali tace "ku koma ciki".cikeda damuwa Sultana tace"meyesa baba ke ma eman haka?i really love my sister amma kullum baba sai ya hana mu zuwa wurinta".hannunta Ammi ta riqe ta had'a dana Ali wanda shima yake cikin damuwar abinda ya faru,suna kaunar sister dinsu amma basusan meyasa babansu yayi cutting all ties with her.
  Ammi ce ta dawo zuciyarta  is so heavy,ita uwace she can imagine Emans pain,har yanzu babana ya hanata damar magantuwa da maganata,tana zuwa ya daga mata hannu alamar dakatarwa yace"not a single word akan eman,bana son jin komai daya shafeta "yana gama fadin haka ya koma falonshi yana kallon news hankali kwance.kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro nakeyi wanda ya cika motar yaya Sadeeq,wanda kallo d'aya ya mini yakasa kara kallona akaro na biyu saboda tsananin tausayina dayake ji,A gusto ya siya mana lunch sannan muka koma gida har lokacin bai ce mini komai ba,saida muka shiga ciki sannan ya zaunar dani yace"kiyi hakuri eman,watarana sai labari,kada kisa damuwa acikin ranki,khair in shaa Allah,nida Fauza are with you kinji?i'll always be there for you koda kuwa kowa ya matsa daga gefenki,nayi alqawarin shige miki gaba har karshen rayuwata eman,in shaa Allah saina mayar da kukan nan naki izuwa farin ciki mara gushewa."asanyaye na gyada kaina sama har lokacin ban daina kuka ba,abangaren yaya Sadeeq kuwa jin kukan yake tamkar zubar garwashi acikin zuciyar shi,bazai iya daurewa ba sai ya Mike ya shige daki ya kwanta rigingine yana jin wani zafi na taso mishi,damuwar eman ce ta samu wurin zama ta baje acikin zuciyar shi,sallar La'asar ce ta miqar dashi daga inda yake,koda yafito falo lokacin nakoma daki,sai ya zauna afalon yana hoping na fito ya kalli fuskata ko zaiji saukin abinda yake ji acikin zuciyar shi,nan ya cigaba da zama har lokacin da ya Fauza tashigo gidan agajiye,akan laps dinshi ta zauna dayake su Asad sun shige dakinsu,tayi cupping face dinshi tana fadin"sorry mun barka kai kadai,nasan eman ba fitowa zatayi ba kuyi fira"sai yayi murmushi dakyar yana b'oye mata damuwar dayake ciki yace"I miss you"yana kama bakinta kissing her passionately dan kawai tayi shiru,saboda yana cikin damuwa Sosai bayason magana,sun dade ahaka sannan suka shiga bedroom dinshi tanata jan shi da fira shikuma yana iya bakin kokarinsa wurin bata had'inkai saboda kada ta gane yana cikin damuwa.
Washegari ina zaune afalo naji an furta"Eman.."wanda yayi maganar ya furta lyrically cikin husky voice yana sakin murmushi with his well arranged teeths,na dade banji irin wannan voice din ba saina juya asanyaye tareda amsawa ahankali bakina ko motsin kirki baiyi ba,idanuna wanda sukayi luhu luhu Na sauke asaman fuskar shi ina  kallon shi da mamaki,na miqe da sauri still staring at him,dogo ne kamar tsahon yaya Sadeeq,yanada doguwar fuskar mai yalwatacciyar fara'a,hakan ya kara ma fuskar kyau gashi namiji ne Sosai atsaye mai cikar kamala a kallo Na zahiri,samun kaina nayi da kasa cewa komai saina saukar da idanuna k'asa trying to remember a ina na sanshi,"kin manta ni ko?"ya furta standing still yana kallona,"ehh"Nace tareda daukar tray nayi hanyar kitchen,ina jin wani iri acikin raina,"tsaya mana!."ya fada yana karasowa inda nake,ya karb'i tray din ya ajiye asaman dining yana kureni da wani irin kallo wanda yasa na Zama uncomfortable"Bilal ne,remember?"rolling eyes nayi staring at him surprisingly,last time dana ganshi was 3years back,gyada kai nayi ahankali nace"Sannu da zuwa","Kodai ba eman bace?"ya tambaya tareda rungume hannu a faffadan kirjinshi,na kalli idanunshi masu cikeda haiba da tsananin kwarjini sannan nace,"itace"saiya jinjina kai yana kallona tareda yin tunani mara zurfi,nasan tunanin canzawa ta yayi,ban bari yakara cewa komai ba Na dauki tray na shiga kitchen da sauri zuciyata na gudu,saina runtse idanuna ina tuno abubuwan dasuka faru abaya masu kokarin tarwatsa mini zuciya,yadda kundin kaddarata ya budo mini shafuka masu tsauri,I was always a burden acikin rayuwar mutane wacce ake  alla alla ayar,my past is all about suffering babu wani alamari mai dadi wanda zan tuna dashi da zai sanyani murmushi sai yayata Sabeeha,"Allah ya gafarta miki"na furta hawaye masu zafi Na zubo mini.turus yaya Sadeeq yayi sanda ya ga Bilal,yace"saukar yaushe?"."Last night na dawo,fatan na sameku lfy?"Cewar Bilal yana zama yake kara fadin"Ina Asad Anum da Ya Fauza ","suna ciki,kwana da yawa munyi missing dinka,how's US?".kayataccen murmushi Bilal yayi sannan yace"Fine alhamdulillah,eman ce haka ta kara girma"ya tambya yana kallona lokacin Na fito daga kitchen,bai daina kallona ba har na ajiye mishi tray full of drinks and small chops,"thank you"ya furta still yana kallona with so much admiration,sakin baki yaya Sadeeq yayi yana kallon Bilal,this is unlike him,yace"Ehh itace,amma hajiya bata fada mini kazo ba,jiya fa munyi waya"sam Bilal baiji maganar da yaya Sadeeq ke mashi ba,gabadaya ya tattara hankalinshi da nutsuwa akan Eman dake hawa staircase tana tafiya majestically,wani abu yaya Sadeeq ya hadiye yana kallon Bilal wanda gabadaya ya manta da wanzuwar shi awurin,saida ta kurema ganinshi sannan ya sauke ajiyar zuciyah tareda runtse idanu yanajin sonta mai karfi na tsarga mishi tun daga tsakiyar kanshi har tafin kafafunshi,it wasn't love at first sight saboda tun da jimawa yana kaunar Eman kauna mai tsanani,yanzu daya dawo daga US gabadaya is the right time dayakamata komai yayi falling into place,"tunanin me kakeyi?"Yaya Sadeeq ya tambaya yana tsura mishi idanu,karde abinda yake tunani ne,atake zuciyar shi ta tsinke gabanshi yayi mummunan faduwa,Bilal yace"I love her"ya furta yana lumshe idanu,zuciyar yaya Sadeeq tayi tsalle kamar zata faso daga kirjin shi,wasu gumi suka Tsastsafo mishi,idanunshi suka cika da maiko masu kama da ruwan hawaye,asanyaye ya furta"this is not the right time bilal,Yanzu haka tana cikin heartbreak,tana cikin gararin rayuwa shiyasa kaganta agidan nan,she's under my care and she's now my responsibility Dan haka abinda kake fada baze yiwu ba,kabata time Sosai tayi healing sai muga yadda zaayi".jinjina kai Bilal yayi yana kallon yaya Sadeeq keenly sannan yace"Shikenan " ya dauki juice ya kora yana tunanin eman,he's carried away by her beauty,mesmerised by her charisma and spell bound by her love,baze bari ta sake kufce masa ba akaro na biyu,zai tsaya ya jajirce har sai ya mallake ta,mikewa yaya Sadeeq yayi wanda hankalinshi yayi tsananin tashi,koda wasa bayason yaga wani Na kallon eman bare kuma azo kan maganar soyayyah,dole ya tashi tsaye akan wannan lamarin wanda shi kanshi besan matakin dazai dauka ba,farin cikin shi ya kau,sai ya hau sama yanajin shi kamar iska Zata d'ebe shi saboda tsananin damuwa,Ya Fauza ya sanarwa zuwan Bilal ta Mike da sauri cikin farin ciki ta sauka wurin shi,shikuma ya dafe kai cikeda tsananin damuwa,meyasa yake shiga cikin damuwa akan eman,meyasa yakejin zuciyar shi kamar ta tarwatse sanda Bilal yace he loves eman,wai he loves her ,ya maimaita cikeda tsantsar takaici,samun kanshi yayi da mikewa ya nufi dakin eman without knowing me zaice mata,kawai yabi umarnin zuciyar shi datake ce mashi yaje wurin ta kozai samu sassaucin radadin da zuciyar shi ke mishi,saida yakai hannu zaiyi knocking saiya fasa yana runtse idanu,he's feeling some how ya juya ahankali ya sauka kasa yana tunani,tun day before yesterday yake cikin damuwa mai tsanani daurewa kawai yakeyi,Asad ne yazo da Gudu ya na fadin"daddy"sai ya sakar ma yaron karamin murmushi sannan ya kama hannunshi suka koma falon da ya Fauza da Bilal ke fira,Bilal na son saka maganar eman acikin firar tasu amma wani abu na hanashi,sai ya share maganar saboda ya k'ara mata time kamar yadda yaya Sadeeq yayi suggesting,tunda Sadeeq ya zauna baice komai ba kallon su kawai yakeyi yafada duniyar tunani,Eman ta shiga ranshi shigar bazata cikin rashin zato da tsammani,what's happening to him?bai san meyasa yake tunanin Yarinyar ba more often,sai ya runtse idanu yana jin wani sabon alamari na ratsa shi,da mamaki ya Fauza da Bilal ke kallonshi,saitayi tapping shoulders dinshi fuskarta d'auke da damuwa tace"meya faru?"kasa koda murmushin karya yayi,sai ya lumshe ido sannan yace"nothing serious,kaina ke ciwo".ta bud'e baki cikeda mamaki sannan tace"migraine dinne ?"asanyaye ya gyada kai yana kallonta,shi kadai yasan zafin da zuciyarshi ke mishi,shi kadai yasan yadda yake kokarin yakice tunanin eman daga ranshi amma yakasa,jiya dakyar ya runtsa saboda tunanin halin datake ciki,ta tsaya mishi arai ta hanashi sukuni,ta shige can cikin zuciyar shi ta hanashi walwala har sai ya bud'e idanu yaganta,shikadai yasan meyake ji aduniyar shi.Cikeda damuwa ya Fauza ta dauko mishi magani,gabadaya tayi wani iri,duk wanda yasan Fauza yasan yadda take tsananin kaunar yaya Sadeeq wanda idan da hali ko k'uda bazata bari ya tab'a shiba,yadda tayi wani iri kai kace itace mai ciwon kan,nan kuwa damuwar eman ce tai mishi yawa take kokarin kwantar dashi,kallo daya yayi ma Fauza ya d'auke kai yanajin wani bala'in tausayinta na ratsa shi,yanajin kamar zuciyarshi zata tarwatse but he can't help it,besan meyasa yake tunanin eman ba akodayaushe yake jin baze iya daurewa ba,Bilal yace"love birds kenan,na dade banga couples irin ku ba,kalli yadda fuskar ya Fauza ta canza lokaci daya,karki damu ciwon kai ne kawai he'll be alright ".da "in shaa Allah ta amsa tana kallon fuskar yaya Sadeeq mai d'auke da damuwa,ta tabbatar bayan ciwon kan akwai damuwar dake damunshi,"Asad ya girma saura ayi mishi kani "cewar Bilal yana d'aga Asad sama,Anum na gefe tana game a iPad,murmushi kawai ya Fauza tayi tana cigaba da kallon yaya Sadeeq wanda ya tsayar da ganinsa harma da jinsa ga staircase,"kubari dai muyi atare dan nakusa fitar da mata"bilal yakuma fada akaro na biyu wanda sam hankalin ya Fauza baya wajen,itama ta tattara hankalinta zuwa kan yaya Sadeeq me kallon one direction,asanyaye nake saukowa daga staircase duk da banason ganin Bilal,bansan meyasa zuciyata take kaffa kaffa dakuma takatsantsan dashi ba,Sam bai kwanta mini arai ba sannan baya cikin jerin mazan danake so duk da bilal namiji ne son kowa kin wacce ta rasa,saina kasa gane meyasa irin wannan tunanin yake zuwar mini agame dashi,be kamata ma nayi irin wannan tunanin ba,nayi siririn tsaki ina cigaba da saukowa  ahankali,idanun yaya Sadeeq dasuka kasance ta direction din staircase suke hakan yasa ya zuba mini idanu yana kallo,ya Fauza kuma Na kallon shi cikeda damuwa,saina mayar da kallona kan yaya Sadeeq wanda yazama wani irin cikin kwana biyu,wani abu ne ya darsu acikin zuciyata,na karasa saukowa ina kallon gefen da bilal ke wasa da Asad,sai alokacin ya lura da zuwana,ya sakar mini wani shegen murmushi tareda lumshe idanu,zama nayi agefen ya Fauza,kafin nayi magana tace mini"yanzu nake shirin kiranki domin ki taya bilal fira,duk da nasan bawani magana zakuyi ba amma yafi yazauna shi kadai,kinga yaya Sadeeq bayajin dadi sama zan Kaishi na kwantar".
Dan waro idanu nayi nace"Allah ya bashi lafiya".suka amsa da amin banda yaya Sadeeq daya ce"kidaina damuwa Fauza,ciwon kan ya fara raguwa basai na kwanta ba".tace"kwanciyar ai tafi kaga nan ma ihun Asad kadai ya isheka".asanyaye yace"badamuwa tunda nace miki is okay,meya fito da budurwar kauye?"ya tambaya yana kallona,ya Fauza tace"good for her"tana murmushi,"ai gara dakika sauko,love birds dinnan sun manta dani anan".cewar Bilal,bance komai ba haka kuma ban daga ido na kalleshi ba,hakan yayima yaya Sadeeq dadi yace"ki koma sama,nasan you're feeling uncomfortable "da biyu yaya Sadeeq yafada hakan,saboda bayason irin kallon da Bilal ke mata,kamar yasan abinda nake shirin yi kenan,saina mike ina fadin"Allah ya kara sauki".Ina jin bilal na fadin"ya zakace ta tafi kuma,sai kace mai takaba tana zaune a d'aki ita kadai".
Yace"zama anan din takura ne,ni kuma banason ta takura"ya fada yana rik'e kai,ya Fauza tace"ya dai?"ta fada tana tattaba shi,haka yaya Sadeeq ya wuni sukuku damuwa tai mishi dirar mikiya,bansan lokacin da Bilal ya tafi ba amma ya dade Sosai,Adaddafe ya Fauza tayi jallop din shinkafa da pepper meat,gabadaya bata cikin nutsuwarta,idan kaga damuwarta akan yaya Sadeeq ne,haka ma farin cikinta.


*Hmmmmm new characters unavailed ,barkanku da shigowa cikin labarin eman,masu karatu ku gyara zama,yanzu ne zamu shiga labarin kai tsaye,ko ban fada ba kunsan akwai cakwakiya *



Zaynab Yusuf✍🏼

EMAANWhere stories live. Discover now