PAGE 39

107 4 0
                                    

EMAAN......PAGE 39

*Assalam Alaykum EMAAN lovers,before delving into today's update,I'd like to clarify few things,Abu na farko shine EMAAN FREE BOOK ne,secondly  mutane da yawa suna mistaken EMAAN ɗina da wani IMAAN wanda an kwana biyu da rubuta shi,wasu ma har suna ganin kamanceceniya atsakanin both books,pls and pls don't judge a book by its cover,title din ne yaxo ɗaya which is very okay but different contents ne aciki,naso yin shiru amma I've been receiving alot of messages akan hakan so I decided to clear the air kafin ku mayar dashi big deal...abu naƙarshe shine masu min complain suna tambayar Why is EMAAN always sad???I seriously couldn't digest this question da farko saboda kwata-kwata a 39 pages muke,we still have a long way to go,so you guys should calm down pls.*
asanyaye Eman ta miƙe xaune tana kallon umma me cewa"eman sit properly"gyara xaman tayi ta dafe fuskarta tana kalllon umma da manyan idanunta wanda suka cika da ruwan hawaye,umma tace"Eman tell me what your problem is?" sauke idanunta tayi hawaye masu xafi suna xubo mata,bata ce komai ba ta goge hawayen still looking down,Umma tace"I know everything is my fault Eman,but I want you to support me in my changing process of becoming a better mum for you,idan kina min shirun nan banajin daɗi "cikin sanyi Eman tace"I'm sorry umma...."ta haɗe kai da gwiwa tana fashewa da kuka mai tsanani da karya xuciyar me sauraro,tana tunanin irin rayuwar da xatayi da alameen wanda ya tsaneta fiyeda misali,by now ta tabbatar da she's very unfortunate kuma she's not meant to be happy,not in this life,hannunta Umma ta riƙo tace"just give it a try daughter "ji tayi kamar an ɗaure mata baki da igiya ga wani nauyi da bakin yayi mata,tana son faɗama Umma damuwarta amma ta kasa,tana son fada mata everything akan Sadeeq sai de batada courage ɗin yin hakan,batasan meyasa kwana biyu tunanin Sadeeq ke damun xuciyar ta ba,she's feeling guilty for than two weeks now,she needs clarity akan abubuwa dayawa dasuke faruwa da ita,saide batasan ta hanyar da xata fada ma umma ba,musamman akan aurenta da alameen,umma tace"I wont force you,share hawayen ki kinji"gyaɗa kai Eman tayi sannan ta goge hawayen har lokacin Idanunta suna kallon ƙasa ,ta kasa haɗa ido da Umma,ita dai umma kallon ta takeyi tana jin she failed woefully as a mother,tana ganin damuwa mai yawa atattare da ƴarta yet she can't discuss her problems with her,ruwan hawaye ne suka cika idanun umma,ta juya asanyaye tashiga dakinta ta jingina da kofa tareda lumshe idanu tana jin haushin kanta,she vividly remembered yadda Anty Habiba ke fahimtar da ita akan abubuwan datakeyi are not right amma taƙi tsayawa ta fahimceta,sai yanxu when it's too late sannan tagane inda anty Habiba ta dosa,shigowar Hajjo cikin parlon ne yasa Eman kwanciya tana tura kanta cikin kujera,hajjo ta taɓe baki tace"kyaji dashi "daga haka bata sake cewa komai ba ta wuce part din Abba.daki Eman ta koma with so many thoughts going through her restless mind,bata san meyasa takejin tsoro da fargaba suna shigarta ba,tasan Mami won't take the situation lightly,saboda yadda take nuna mata ƙiyayyah tun farko,balle yanxu idan tasan da xancen auren babban tashin hankali xa'ayi,ajiyar xuciya ta sauke tana dafe kirjinta,ina ma ace Fauxa na nan,ta tabbatar maganar baxatayi escalating ba saboda ita kadai ce xata iya shawo kan Mami,damuwarta guda daya ce yadda Umma xatayi overcoming situation din,tasan dole xasu samu matsala da Mami, su mummy kuma will use that opportunity to instigate Mami against Umma.........Cikeda damuwa mummy ta kalli Afiya wacce batada aiki sai kuka,tace"kuka ba mafita bane agare mu,tashi xakiyi mu san abinyi kafin mu tsaya kallon ruwa kwaɗo yayi mana ƙafa"shiru Afiya tayi batace komai ba saboda bakin ciki da takaicin yadda Aliyu ya tarwatsa mata rayuwa,ya barta da abin kunyar da tabonshi xai daɗe bai gogu ba acikin duniyarta,tsanar shi ce ke saukar mata tana jin ina ma xata ganshi babu abinda xai hana ta shaƙe shi har lahira,mummy tace"Ina miki magana kinyi min shiru"ahasale Afiya tace"dan Allah mummy ki ƙyale ni naji da abinda ke damuna"mummy tace"dama shi ba'ayi aiki akanshi bane?"banxa Afiya tayi ma mummy tana cigaba da dirxar kuka,mummy tace"answer xaki bani kinyi shiru"afusace Afiya tace"dan Allah mummy ki ƙyale ni ,xuciyata xafi take min,ina cikin damuwa da tashin hankali, kinxo kina adding salt to my injury"da mamaki mummy tace"ba haka bane Afiya,aganina it's high time dayakamata musan abinyi,yanxu fa satin ki uku agidan nan,idon kowa na kanki,gashi bakida aiki sai kuka dole su xargi akwai damuwar dake damunki"shiru Afiya tayi tana sake fashewa da kuka mai ciwo,wani irin wulaƙanci ne wannan?ace wai an sake ka a day after your wedding,labaran datakeji agari ne yafaru da ita alokacin da she least expected,mummy tace" baki nuna min takardar sakin ba,tana ina??? idan sun san wata ai basusan wata ba"atakaice Afiya tace"tana wurin maman shi"without twice thought mummy takira hajiya Zainab wacce nadama da bakin ciki suka cika mata xuciya,bata san meya shigeta ba ta aikata hakan gashi nan tayi loosing beloved son dinta in the process,kiran mummy ne ya ɓata mata rai,ta daga cikeda masifa tace"hajiya Aisha lafiya kike kirana?"mummy tace"inafa lafiya,yarinya gabadaya ta birkice batada aiki sai kuka,hawan jini na neman kwantar da ita,fisabilillahi abinda Aliyu yayi ya dace kenan,sannan kin ƙi cewa komai akai"Hajiya zainab tace"hawan jinin bai burge ni ba sai ya kwantar da ita agadon asibiti,yadda na rasa ɗana sai kin rasa taki,matsiyatan mutane wanda saninku ba alheri bane"mummy tace"ke hawan jini xai kwantar  badai Afiya ba,gayyar tsiya gayyar wa'iyazubillahi,mujiya wacce ganinki ba alheri bane,yadda Aliyu ya wulakanta Afiya sai ya yaga fiyeda hakan acikin rayuwar sa,shiga duniyar da yayi baiga komai ba tukunna,sai ya jawo muku bala'i da masifar da sai kin rasa xanin ɗaurawa agarin nan ,yadda ya wulaƙantani da ƴata sai an mishi fiyeda haka arayuwa"hajiya Zainab tace"kanki akeji wai mahaukaci ya fada rijiya,kwana daya na baki kixo ki kwashe kayan tsiyar ku daga gidana,idan ba haka ba wallahi a titi xaku tsince su "tana kaiwa nan ta kashe wayarta mummy tace"da kuwa kinga rashin mutuncin da baki tana gani ba arayuwarki,shegiya tsinanniyar mata wacce babu Allah aranta,kijira kiga yadda rayuwarki zata wulakanta a idon duniya,yadda kuka xalinceni sai anyi muku fiyeda haka,macuta kawai axxalumai marasa imani,"Rafee'ah ce tayi saurin xare wayar daga kunnen mummy tana ƙoƙarin maida hawayen daya cika mata ido,irin wannan ranar take guje musu,saboda tasan hajiya Zainab ba'a ƙulla abin arxiki da matar,mummy na huci tace"kibar ni na fada mata asalinta,shegiyar mata wacce babu Allah aranta"sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tana cewa"Allah ya isa tsakanina dasu"hawayen dake maƙale a idanun Rafee'ah ne suka gangaro,ta ajiye wayar agefe tana kallon yadda mummy ke kuka abinda bata taɓa gani ba kenan,rungumeta tayi saide ta rasa abin cewa saboda maganar tafi ƙarfinta.cikeda takaici Afiya tace"shikenan mummy kin lalata komai yanxu,maimakon ki lallɓata ta shine kika biye mata"mummy na shessheƙar kuka tace"uban me na lalata? duk abinda nake yi akanki bakya gani,har kinada bakin cewa na lalata komai,shiru kikeso na mata tana xagina saboda bakida mutunci kanki kawai kika sani,matar da ɗanta yamiki saki uku kike supporting akaina ni mahaifiyar ki afiya?"tafada cikeda bakin ciki,xuciyarta na mata xafi,Rafee'ah tace"Dan Allah kiyi hakuri mummy kar BPn ki ya tashi"mummy tace"duk abinda nakeyi akan yarinyar nan bata gani?me na lalata in the first place?auren da akayi saki uku na lalata?"rafeeah tace"dan Allah kiyi hakuri,she's frustrated ne"hararar Rafee'ah tayi saboda maganar tayi mata ciwo fiyeda misali,tace "ni yanzu babbar damuwata itace ina xan kai kayan dakinta?hajiya zainab tace 24hrs ta bayar mu kwashe kayan idan ba haka ba sede mu tsince su a titi,kinsan ta ƴar iska ce ta gaske tsaff xata aikata"cikeda mamaki Rafee'ah ke kallon mummy wacce tasake birkicewa tafita hayyacinta saboda tsananin damuwa,can tace"kira mun numbar rasheeda "tafada hakan sabbin hawaye na zubo mata,Afiya na jin batun kayan daki ta kara sautin kukan datakeyi tana jin kamar ta hadiyi xuciya saboda bakin ciki........ya dade Sosai yana tunanin mafita saide har lokacin bai samu solution ba,al'amarin ya wuce tunanin shi da lissafin shi,duk hanyar daya dauko mai cikeda potholes ce wacce baxata kaishi ga madakata mai kyau ba,lumshe idanu yayi yana mirxar fingers dinshi wayar shi tafara ring,gaban shine yayi mummunan faduwa lokacin da kiran ya shigo,ya duba kiran xuciyar shi na tsinkewa ya sauke ajiyar xuciya at once sannan ya daga,Fauxa dake xaune a saman hotel bed ta goge guntun hawayen daya zubo mata tace"alameen how are you doing?"yace"im good,how about you?hope Sadeeq is feeling better?"gyada kai tayi kamar yana ganinta tace"alhamdulillah "jin tayi shiru yace"kuka ko fauxa?"samun kanta tayi da kasa resisting kukan,saboda her heart is very weak at the moment,yace"I tot you promised me kindaina yin kuka,adduar mu kawai yake bukata "saurin goge hawayen tayi tace"In shaa Allah"atakaice,yace"I'm all ears,meya faru?"shiru fauxa tayi tana rera kuka ahankali mara sauti sannan tace"yanxu haka Sadeeq xai cigaba da rayuwa with life supporting machine?jikin shi babu wani improvement illa ramewa daya sakeyi, i asked dr harry yace min bakomai amma xuciyata ta kasa samun sukuni,I'm blaming myself for what happened,da ace mun saurareshi da duk hakan bata faru ba"lumshe idanu alameen yayi yace"calm down fauxa,Sadeeq will be fine in shaa Allah put that at the back of your mind "shiru fauxa tayi for few seconds sannan tace "sadeeq is in love with someone related to me,so nake na san wacece Yarinyar tun yanxu"yace "me xakiyi idan kin santa?"without twice thought tace"xanyi supporting dinshi ne"alameen yace"at the cost of your happiness?"ta gyada kai tace "yes I can make that sacrifice for him"juya kai alameen yayi yace"I won't let that happen,just focus on his recovery,Allah ya bashi lafiya"yana kaiwa nan ya katse wayar yana jin tausayin ta saboda most times so baya mana adalci.Juice mai sanyi hajjo ta kora bayan ta gama cin grilled chicken din da Abba ya siyo mata,ta jefa toothpick abaki tana ciro naman daya makale mata tace"kirasu ayi maganar"da toh Abba ya amsa sannan ya jawo wayar shi ya kira Hajiya kwaise,jiki ba kwari tayi answering yace"you and your Co-wives should come to my parlour immediately "daga haka ya katse wayar,da mamaki hajiya kwaise ke kallon wayarta kamar Abba take kallo ,yadda taga Abba yaxama very serious ne ya bata tsoro,ta mike jiki asanyaye ta kira kowacce acikinsu sannan suka shiga part dinshi,hajjo tayi karamin tsaki tana jin haushin turancin da Abba yayi,Itafa ta tsani ariqa turanci agabanta yanxun nan sai tace xaginta kakeyi,da sallama kowacce ta shiga parlorn,mummy wacce idanunta sukayi luhu-luhu ta xauna acan karshe tana yin kasa da fuskarta,agefen hajjo Umma ta xauna,Mami da Mama suka xauna akujera daya,kallo daya kowacce tayi ma Abba ta shiga taitayinta ganin yadda ya tsare gida with no nonsense face,sai da yayi few minutes sannan yace"kamar yadda na fada muku daxu akwai maganar da xan yi daku,wacce babu musu ko kuma jayayya acikin ta,no one should question my decision ko kuma nace decision dina dana yara na"gaban hajiya kwaise ne yafadi ta dago da sauri tana kallon fuskar Abba me cikeda tsananin kwarjini da haiba,looking very calm saide a kausashe yake maganar,yacigaba da cewa"magana ce akan alameen my first male child watau dan wajen hajiya kwaise,da kuma Fatima Eman yar wajen Fatima"jikin Mami ne yafara rawa jin ya ambaci sunan alameen dana Eman ahade,da mamaki umma ke kallon Abba haka mummy da mama,kowa lamarin ya daure mishi kai saide babu wacce ta yi questioning Abba kamar yadda ya fada tun akaron farko,dole kowacce tayi shiru masu faduwar gaba nayi masu xullumi nayi kowa dai da abinda ke ranshi,Abba ya cigaba da cewa"ahalin da muke ciki yanxu alameen miji ne ga Eman,haka xalika Eman matace ga alameen,an daura auren su ranar 1 ga watan july din 2023, wata daya kenan daya wuce...."shiru Abba yayi yana kallon Mami wacce ta mike agigice tana kallon shi straight in the eyes,idanunta sun cika da ruwan hawaye,jikinta na shaking,hakoranta na sama suna dukan na kasa giving a loud sound,kallo daya zaka mata kaga tsantsar tashin hankali atattare da ita,with a trembling voice tace"kasan me kake fada kuwa?"ta tambaya Abba looking dumbfounded and confuse,kwakwalwarta takasa apprehending maganar,haka xalika kunnuwanta sun kasa digesting kalaman Abba wanda ta gwammace a kikkifa mata xafafan maruka akan afurta mata hakan,Abba yace",karki damu I'll repeat myself but have your seat first"hawayene masu xafi suka xubo mata,ta xauna shirim jikinta gabadaya yayi sanyi,Abba yace"eman and alameen are married couples,kuma in few days time xata bishi can inda yake aiki"hajjo ta dora da cewa"abu ne yaxo babu shiri,dan haka kwaise da fatima hakuri xakuyi karkuce anyi abu ba'a sanar daku ba tun farko,kara ce mukayi ma Sadeeq ganin halin dayake ciki,yanxu kam dole mace ta riqe hakan da hannu bibbiyu tunda aikin gama ya gama,ke kwaise banda masifa miye abin damuwa?tunda yaron nan da kanshi yazo yace yana son eman kuma aurenta xaiyi ,wannan ai abun farin ciki ne banga abin kuka ba,da alama dai xubar hawaye baya miki wahala ne ,da nice ke share hawayena xanyi nasa musu albarka domin Eman tayi namijin kokarin amincewa da aurenshi,can fa wata uwa duniya ta yadda zata bishi su xauna garin arna makiya addinin musulunci,Wanda ya maka haka ay ya gama maka komai aduniya"bakin Mami na shaking hawaye masu zafi suna xubo mata tace"Eman fa,eman ka aura ma ɗana abdulhameed?"ta tambaya tareda ambatar sunan shi kai tsaye,abinda bata saba yibane shiyasa Abba yakalleta cikeda mamaki,hajjo tace "kwarai dagaske Eman aka aura mishi "kamar iska haka Mami ta fita daga parlorn tana jin kamar xuciyarta is about to explode,mummy tasaki baki suna kallon kallo da mama,hajjo tace"kwaise anyi asarar hali"ta kalli umma dake gefenta gabadaya bata cikin hayyacinta ta fada duniyar tunani,takasa yadda da abinda Abba ya fada sai maimaita wa take acikin ranta,mummy da mama ne suka fita without saying a single word aka bar Ummu xaune kamar statue,hajjo tace"tashi ki koma part dinki zanyi magana dashi"mikewa umma tayi jiki ba kwari ta fita,ga mamakinta taga hajiya kwaise xaune a main parlor ta xabga uban tagumi,har kuma lokacin hawaye zubo mata sukeyi,mummy na gefenta tana tapping shoulders dinta cikeda makirci,tana tunanin this is her perfect opportunity,yadda take cikin tashin hankali sai kowa ya shiga cikin tashi kalar damuwar ,jiki asanyaye Umma ta wuce su xata shiga part dinta domin har lokacin bata gama dawowa daidai ba,hajiya kwaise tace"dakata fatima"cak umma ta tsaya tana runtse idanu domin tasan xa'a rina,Mami ta kalleta ido cikin ido tace"kada kiyi farin cikin samun yar gajeriyar nasara,ina me tabbatar miki ɗana baxaiyi xaman aure da Eman ba,that I promise you,ki shirya xama da yar karamar baxawara"tana kaiwa nan ta wuce part dinta tana jin jiri yana dibarta,mummy tabi bayanta tana cewa"kiyi ahankali "ganin yadda mami tayi ball dawani throw pillow dake parlon,Umma tafi 15 seconds ahaka sannan ta shiga part dinta,ta xauna tareda xabga uban tagumi tarasa me xatayi adaidai wannan lokacin.Cikin rashin xato da tsammani taji saukar wasu xafafan hawaye asaman cheeks dinta,asanyaye tasa hannu tana shafo hawayen wasu na sake xubowa,samun kanta tayi ta mikewa ta shiga dakin Eman wacce ke kwance ta lumshe idanu sede ba bacci takeyi ba,xama tayi agefen gadon tace"eman sit up"ba musu Eman ta tashi xaune tana kallon fuskar Umma,cikeda damuwa tace"umma why are you crying?"shiru umma tayi tana jin xuciyarta na mata xafi,itama har ga Allah kuma har cikin xuciyarta bataso hadin nan ba,ba dan kowa ba sai dan Mami,har xatayi magana sai kuma tayi shiru daga baya ma ta wuce bedroom dinta,da kalllo Eman ta bita har ta kurema ganinta.Tana shiga dakinta ta kira anty habiba tace"habiba kixo it's urgent "daga haka ta kashe wayar tana lumshe idanu,acikin 25 minutes anty habiba taxo,tashiga dakin Umma tana sauke ajiyar xuciya ganin Umma na lafiya,xama tayi agefenta tace"yaya lafiya?"hawaye suka fara xubo ma umma intstead of answering Habiba's question,anty habiba tace"Subhanallahi,meya faru ne?"ta tambaya tana goge mata hawayen,shiru Umma tayi domin ji tayi maganar tayi mata nauyi alokacin,anty habiba wacce gabadaya hankalin ta ya tashi tace"dan Allah kidaina kukan nan and tell me what's going on?"kallonta umma tayi tace"yanxu abba ke fada mana wai ya daura ma Eman da alameen aure one month ago "wani farin ciki ne ya mamaye xuciyar anty habiba,ta saki murmushi sannan tace"dan Allah fa yaya,kodai lefenta yabani contract last few weeks?"Umma tace"ban gane ba"anty habiba tace"ok lemme explain,last 3 weeks Abba yakira ni akan yanaso ahada mishi lefe nagani na fada,har nake tsokanar shi nace hala acikin friends dinshi ne wani zai kara aure,yace min a'a Idan lokaci yayi xanji labarin,sai ya nuna min kada na fada miki komai gameda lefen,nikuma ban kawo wani abu ba shiyasa ban fada miki ba"umma ta jinjina kai tace"ehh lallai biri yayi kama da mutum"anty habiba tace"shine kuma kike kuka wannan ai abin farin cikine yasame mu?"cikin wani irin yanayi umma tace"ke kullum baxaki tsaya ki fahimci abu ba habiba,har yanzu kin kasa fahimtar da irin mutanen danake xaune,ke atunaninki hajiya kwaise xatayi farin ciki da wannan auren ne?"gajeran tunani anty habiba tayi tace"I doubt much gaskiya,kinsan tun ba yauba take cewa yar er uwarta take son ya aura"umma tace"bayan wannan ma baxata amince ba saboda abinda yafaru da Eman,kinsan yadda take da gudun magana,tana tsoron koda wasa ayi pointing finger akanta ko kuma yayanta da abu mara kyau"anty habiba tace"ita ma Eman din ay ba halin ta bane aikata mugun abu,kaddarace wacce ta riga fata,kuma ko ita batafi karfin Allah ya jarabceta da hakan ba akanta ko kuma akan yayanta harma jikokinta "ajiyar xuciya umma ta sauke tace"Kinsan dai ba xama xatayi ta xuba ido ba ko?ce min tayi nafara shirin xama da karamar baxawara...."anty habiba tace"ita din banxa ita din wofi,ta isa ta kunce abinda Allah ya hada ne?,ki barta ta cigaba da haukanta aure dai ya dauru,kuma duk abinda xata miki koda wasa kada ki nuna hakan ya dameki,aure kuma idan kinga ya mutu Allah ne ya kaddara hakan amma babu matar data isa ta kashe ma eman aure saidai nata ya mutu"daga haka ta janyo wayarta tana nuna ma Umma hadaddan lefen Eman datake hadawa,umma ta kawar da kanta gefe,anty habiba tace"Matsalata dake kenan yaya,daurawa kai damuwa,yanxu miye abin damuwa acikin wannan maganar?"shiru umma tayi tana kallon anty habiba without saying a single word.Mummy ta kalli Mami cikeda damuwa tace"gaskiya an shaki an warke,an gama cutar ki wallahi,alameen din aka aurawa wannan gantalalliyar Yarinyar data gama yawon ta xubar agarin nan?ko dai kin manta da pictures dincan ne na sake tura miki kigani?"kallonta kawai Mami tayi bata ce komai ba,mummy tasake cewa"yanxu miye abinyi?"ta sake tambyar Mami wacce hankalinta yabar jikinta tuntuni,tunanin yadda xata bullowa lamarin kawai takeyi,mummy tace"Duk makirci fatima ne,wallahi babu kaffara nasan itace ta ƙulla wannan auren"sai alokacin hajiya kwaise ta kalleta tace"Aisha kije kiji da damuwarki nima inji da tawa"mummy tace "daga abin arxiki?shawara naxo baki fa"Mami tace "ce miki akayi na rasa abokan shawara ne?banason shisshigi kinji ko?sanda Afiya ta dawo gidan nan waye ya tsareki da tambayoyi?"cikeda takaici mummy ta wuce part dinta xuciyarta kamar xata fashe saboda bakin ciki,Mami ta sauke ajiyar xuciya tana tuna wacece Eman,a tunanin farko taji baxata tab'a yadda da auren nan ba no matter what,ta jawo wayarta ta kira alameen cikin yanayin da bai taba ganinta aciki ba tafara cewa"thank you for betraying me alameen,dakai aka hada baki aka cuceni ko?da kai aka taru aka b'oye min wannan mummunan labarin ko?"xaiyi magana tayi saurin katseshi tace"not a single word alameen,from now henceforth i will talk and you just listen,kana jina?"gyada kai yayi cikeda damuwa kamar yana ganinta,kalamanta na farko are breaking his heart into tiny pieces,tace"you must divorce her immediately,ka turamin sakin ta WhatsApp I'll forward it to them"tashi xaune yayi afirgice yace"what?"cikeda masifa tace"you heard me right,idan baxa kayi bane ka fada min"...cikeda damuwa yace"mami I never liked eman,infact I hate her with every fibre of my being..."atsawace tace"shut up!"tacigaba da cewa"ni xaka rainawa hankali alameen?"saurin girgiza kai yayi tace"who am I to you?"shiru yayi yana runtse idanu,ta sake maimata tambayar cikeda masifa,asanyaye yace"you're my mother"tace"idan ka tabbatar ni ce na haifa then divorce her immediately else..."saurin katseta yayi yace"divorcing her is the easiest thing ever,amma consequences din shine matsala"tace"ok tunda ka xabi aurenta akaina shikenan "cikeda tashin hankali yace"wait mami,but divorcing her will lead to Fauxas permanent destruction!!!!!arikice tace "whattt?!"




Zaynabyusuf✍🏼💕
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now