PAGE 70

177 6 0
                                    

EMAAN...PAGE 70

Written by Zaynabyusuf✍🏼

Emaan na kwance asaman kujera fauxa ta shigo parlon umma,sallamar datayi ce tasa emaan mikewa xaune tana kallon fauxa cikeda mamaki,agefen emaan fauxa ta xauna with a cute smile on her face,murmushi itama emaan tayi tace"good morning "fauxa tace"morning dear,fatan kin tashi lafiya?hows my baby doing?"alokaci daya ta jera mata tambayoyin,lumshe idanu emaan tayi tana jin kunyar tambayar da fauxa tayi ta karshe sannan tace"I'm good alhamdulillah,ya su Anum?"murmushi sosai fauxa tayi tace"su Anum sai next week zasu dawo"emaan tace"Allah ya kaimu"fauxa batace komai ba illa hannun emaan data riko tana kallon emaan din straight in the eyes,tace"I'm sorry for everything emaan..."fingers dinta biyu emaan ta dora asaman lips din fauxa tace"shhshh ya Fauxa,you haven't done anything wrong I promise you"murmushi fauxa tayi kana ta janye hannun emaan daga bakinta tace"ofcourse I did,i accused both you and alameen for what happened,dan Allah kiyi hakuri "emaan tace"nide baki min komai ba wallahi,in fact ni ce ma yakamata na baki hakuri,I'm sorry for everything ya fauxa..."murmushi fauxa tayi tace"ok let's do this,na hakura idan ma akwai abinda kika min na yafe miki,kema find a place in your heart and forgive me "emaan tace"nima na yafe miki and thank you for everything ya fauxa"rungume emaan tayi tightly tace"you're most welcome Sissyyy,I love you "hawayen farin ciki ne suka xubo ma emaan tace"thank you ya fauxa"fauxa tace"tell me how old is my baby?"murmushi emaan tayi batace komai ba,fauxa tace"ohh baxaki fada min ba?"emaan na sinne kai kasa tace"nima ban sani ba"dariya fauxa tayi tace"xan tambayi alameen nasan shi ya sani "emaan batace komai ba illa murmushin data yi,atare fauxa da emaan suka juya suna kallon alameen sanda yayi sallama,fauxa tace"d'an halak kak'i ambato,yanxu nake maganar ka"murmushi yayi ya xauna agefen fauxa yace"Allah ko?daga part din mami nake tace min kina nan"fauxa tace"ehh naxo duba babyna sannan kuma na ba emaan hakuri for what happened "alameen yace"ohh that's so sweet of you,Allah ya bar mana xumunci ya kori shedan daga cikin xamantakewar mu"fauxa tace"Amin ya rabbi"emaan kuma na kallon alameen kasa kasa,fauxa tace"yaushe xaku koma?"alameen yace"in two days time in shaa Allah "xaro idanu tayi waje tace"very soon kenan,kuma gashi next month xaku sake dawowa,dama kabar emaan anan muyi xaman mu"dariya alameen yayi yace"no way"fauxa ta galla mishi harara tace"xaka sani,ta bayan gida xan biyo maka"shima hararar ta yayi yace"kinga bana son haka"fauxa tace "sai kuma kayi"emaan dai murmushi takeyi batace komai ba,alameen yace"itama emaan din tafi son mu tafi,ko ba haka ba emaan?"ya jefa mata tambayar,saurin kallonshi tayi kana ta kalli fauxa ta girgixa mata kai alamar a'a,dariya fauxa tayi ganin gaskiyar maganar da alameen ya fada ta cikin idanun emaan amma tace"ni nasan ba ruwan emaan".alameen yace"i see "yana kashe ma emaan ido dake kallonshi,juyar da kanta tayi gefe tana murmushi batace komai ba,ahaka umma tashigo parlon hannunta rike da qaton tray,fauxa ce ta taimaka mata suka ajiye shi asaman centre table, tace"ga breakfast dinku nan"tana kaiwa nan tabar musu parlon,fauxa ce ta hada musu komai a plate daya suka sauko saman carpet suna ci fauxa na zolayar emaan alameen yana tayata,emaan dai saide tayi murmushi ko kuma ta girgixa kai without saying a single word,ahaka suka kammala breakfast din.fauxa ce ta kai tray din kitchen dan haka alameen yayi closing gap din dake tsakanin shi da emaan,pulling her closer yace"kece kika ce ma fauxa bakisan komawa?"shiru tayi mishi batace komai ba illa kallonshi datakeyi keenly,yace"I'm asking you,kece kika fada mata hakan?"girgixa kai emaan tayi alamar a'a sannan tace"nifa bance mata komai ba"murmushi alameen yayi yace"nima dai i tot as much,nasan babyna baxa tace haka ba"murmushi kawai emaan tayi alameen yace"basai kin hada kaya masu yawa ba tunda kinga in less than 26 days xamu sake dawowa"looking at him closely tace"meyasa xamu sake dawowa very soon haka?"ta jefa mishi tambayar da saida gumi suka taru asaman goshinsa,samun kanshi yayi da kasa fada mata dalilin dawowar daxa suyi,nan da nan zuciyar ta ta ayyana mata cewar bikinshi ne da yasmeen xa'ayi,tana ganin mami da yan uwanta nata shirye shirye,ajiyar xuciya kawai ta sauke feeling somehow,ita kanta batasan me take jiba acikin ranta,she just want to be alone alokacin,kokarin mikewa tayi alameen ya riketa sosai yace"ina xaki?"kai tsaye tace mishi"bedroom"yace"to do what?"tace mishi"bacci xanyi "looking at her closely yace"emaan are you sure?naga kamar akwai damuwa atattare dake"murmushi tayi tace"dama mutum yana rabo da damuwa ne?in one way or the other mutum dole akwai abinda ke damunshi"in confirmation alameen yace"yeah haka rayuwa take amma I don't want to see you sad baby,you can discuss your problem with me"idanunta ne suka ciko da ruwan hawaye tace"already munyi discussing akai kuma nace maka i don't want to talk about it ever again"ajiyar xuciya ya sauke yace"I understand your feelings and worries,amma inason kisani cewar hakan baxaisa relationship dinmu ya canxa ba,I love you so much and I'll always be there for you,kawai dai shi lamarin rayuwa dole sai anyi hakuri tunda dukkanin mu 'yan adam ne muna yin mistakes"emaan tace"haka ne,May Allah make it easy for us"da amin alameen ya amsa yana jin tausayin ta yana ratsa shi,gefe daya kuma kaunarta mai tsafta na sake shigar shi,soft hands dinshi ya dora asaman tummy dinta yace"I love you both,more than anything in this life"lumshe idanu emaan tayi feeling over the top,saboda ba iya tab'a tummy din yayi ba he did something daya kunna emaan take jin wani shauki yana fixgarta,alameen has his ways with her,ayanxu ya santa fiyeda yadda tasan kanta,yasan mexe mata tayi dariya,yasan mexe mata tayi kuka,yasan mexe mata yasata cikin farin ciki da akasain hakan,above all yasan hanyoyin dayake bin wurin nuna mata kauna fiyeda misaltuwa.mummy ce xaune asaman kujera ta xabga uban tagumi abin duniya ya taru ya mata yawa,ga breakfast nan agabanta amma ko kallonshi batayi ba saboda damuwa,idanunta sun rine saboda tsananin kuka xuciyarta kuwa kamar ana cinna mata wuta,damuwa tayi mata yawa ta rasa inda xata sa kanta taji dadi,afiya na gefe tana nata kukan,sai yanxu tasan ta cuci kanta arayuwa all thanks to mummy datake xugata akullum tana gurb'ata mata tunani,jiki ba kwari ta mike xuciyarta na suya,part din umma ta nufa domin ta ba emaan hakuri abisa laifukan data aika mata,mummy dake sharce kwalla tace"ina xaki?"afiya tace"xuwa xanyi na ba emaan hakuri,k'ila yin hakan xaisa Allah ya dubeni da idon rahma,na cuci kaina mummy,na cuci rayuwata"takarashe maganar tana fashewa da kuka mai tsanani,part din umma ta nufa gabanta na tsananin faduwa,cak ta tsaya abakin kofar ganin yadda alameen ke ma emaan kamar xai maida ita ciki,sabbin hawaye ne suka sake xubo mata,sai kawai ta juya takoma part dinsu tana fashewa da sabon kuka xuciyarta kamar tayi bindiga saboda damuwa.......dogon hijab mummy tasa ta nufi bangaren Abba gabanta na faduwa,lokacin yana xaune asaman kujera yana kallon channels news,sau daya ya kalleta ya maida hankalinshi ga Tv,mummy ta xube ak'asa tana fashewa da kuka mai ciwo tace"dan Allah Abba kayi hakuri,kai kadai gareni aduniyar nan,idan ka juya min baya ya xanyi da rayuwata,wallahi na tuba nagane kuskurena..."daga mata hannu yayi alamar dakatarwa yace"Aisha I've had enough,tashi ki bar min parlo"yayi maganar authoritatively,kuka Sosai mummy ta fashe da shi kana ta mike jikinta na b'ari tafita,part dinta takoma kanta na juyawa kamar xata fadi k'asa,gani take kamar Abba xai juya mata baya ne gabadaya,auren nan shine rayuwarta da farin cikinta,idan ya rabu da ita shikenan ta shiga uku ta lalace,Sosai take dirxar kuka kamar wata karamar yarinya tana data sanin abubuwan datayi arayuwa....da misalin k'arfe tara ne na dare umma na hada ma emaan few abubuwan da xata koma dasu,xama tayi agefen emaan bayan ta kammala shirya mata komai ta riko hannayenta gam gam tace"I want you to listen to me carefully emaan,lemme be prank and be honest with you,kinga arayuwar nan bakida kamar alameen yanxu,kafin kowa yasan halin da kike ciki alameen already yasani,yanxu shine sahun farko acikin rayuwar ki,dan haka ki rike shi hannu bibbiyu,ki mishi biyayya sannan ki kyautata mishi,alameen yana matukar kaunar ki nasan xai kula mana dake fiyeda yadda nake xato,inaso kema ki kula dashi emaan,ki ajiye abubuwan dasuka faru abaya kiyi facing future dinki,kiyi kokarin kafa gurbi arayuwar mijinki,irin gurbin da xaiyi wahala wata ta kafa shi saide idan kece kikayi rikon sakainar kashi dashi kamar yadda kikeyi aynxu,feel free and discuss your problems with me,idan ma baxaki iya ba kiyi magana da habiba,she'll put you through akan abubuwan dasuka shige miki duhu,nide inason ki gyara emaan,ki riqa reciprocating kaunar dayake nuna miki,koba komai he'll feel happy amma hakan dakikeyi yanxu you're just pushing him away kinga abinda ba'a so kenan,kuma bamu san inda rana xata fadi ba watarana,ta yiwu Allah ya kaddara xaki xauna da kishiya nan gaba,kinga kinyi foul tun akaron farko,dan haka inaso ki cire komai daga ranki and live your life to the fullest,Allah ya miki albarka"sosai maganar umma ta shigi emaan,kuma tasan abubuwan da umma ke fada are nothing but the truth,batace komai ba illa kallon umma datayi keenly,sallamar alameen ce tasa umma fita xuwa parlon,yana tsaye abakin kofa suka gaisa umma ta shiga bedroom dinta,dakin emaan ya shiga yana kallon emaan wacce jikinta yayi sanyi Sosai,ya mikar da ita tsaye baice komai ba,hijab dinta ya sa mata ya rike mata hannu suka fita,bangaren mami taga sun shiga dan haka taji gabanta ya fadi saide ba kamar kullum ba,shine yayi sallamar ita kuma tana binshi abaya kamar munafuka,akasa tayi saurin xama ta sunkuyar da kanta kasa,alameen ya tsaya yana kallonta da mamaki saide baice komai ba,hasalima bedroom din mami ya shiga wurin fauxa,ajiyar xuciya emaan ta sauke kenan nufinshi tayi ma mamin shi sallama da kyau bawai irin ta tsaye ba idan sun tashi tafiya gobe....bakin emaan na shaking tace"barka da dare mami "ga mamakinta taji mami tace"barka dai,how are you doing?"da sauri emaan ta dago tana kallon mami cikeda mamaki,can dai tace"I'm good alhamdulillah "mami kallon emaan kawai takeyi saboda batasan mexata ce ma yarinyar ba,emaan kuma ta kasa mikewa ta tafi kuma takasa cema mami komai ita ma,dama can basa wata magana daga gaisuwa shikenan,ga mamkinta taga mami ta miko mata room temperature fresh milk,hannun emaan na rawa ta karba tace mata"thank you "mami tace"you're most welcome daughter "Emaan couldn't believe her ears alokacin saboda tsananin shock,ta maimaita kalmar daughter yafi sau goma acikin ranta tana mamaki,fauxa da alameen suka kalli juna cikeda farin ciki saide basuyi magana ba suka xauna agefen mami,fauxa tace"me kikeyi haka akasa sai kace wata marok'iya"murmushi kawai emaan tayi batace komai ba,alameen yace"emaan sit properly mana"ba musu ta zauna asaman kujera saide har lokacin kanta na sinne akasa,su alameen da mami sai hira sukeyi cikeda nishadi emaan na gefe tana wasa da fingers dinta...wayar mami dake ring alameen yayi picking ganin mariya ce ke kira,kai tsaye yasa ta a speaker suka gaisa,fauxa tace"mareeyo how are you?"ta dayan bangaren mariya tace"I'm good alhamdulillah,nayi missing dinku duka,I can't wait next month yayi naxo bikin alameen"tafada excitedly,alameen da fauxa suka kalli emaan wacce har lokacin kanta ke sinne akasa saide babu murmushin dake shimfide asaman fuskarta,fauxa tace"ya yaran?"shide alameen keenly yake kallon emaan saboda abinda yafaru bai mishi dadi ba,haka ma ta bangaren fauxa har suka kammala wayar she wasn't comfortable saboda bata son mariya ta sake maganar bikin alameen agaban emaan,mikewa emaan tayi daga bisani tace "goodnight mami "tafadi hakan tana sakar ma mamin murmushi,mami tace"mun kwana lafiya daughter "daga haka emaan ta wuce bangaren umma xuciyarta na bugawa da sauri-sauri,bedroom dinta tashiga ta fada saman gado tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi gudun thousands of kilometres,saide tak'i barin damuwar hakan ya saukar mata da tunani sai kawai tayi playing surah-maryam tafara bi har bacci ya kwasheta...washegari da safe misalin k'arfe 8 umma ta tasheta a bacci dayake flight dinsu na karfe biyu ne kuma sai sunje abuja sannan su wuce london,agaggauce emaan tashirya cikin mustard color gown,tayi rolling red veil sede batayi applying komai ba asaman fuskarta,rungume umma tayi harda guntun hawayenta lokacin da xasu tafi,a main parlor suka tsaya suna sallama da kowa na gidan har dasu mummy da Afiya,mummy na matsar kwalla tace"Toh emaan Allah ya kaiku lafiya ya kiyaye hanya,dan Allah a yayyafe saboda bamusan halin rayuwa ba,kana naka Allah na nashi"asanyaye emaan tace"bakomai mummy,Allah ya yafe mana baki daya"da amin kowa amsa banda hajjo dake tabe baki.mami da fauxa ne suka rakasu har mota mami na rike da hannun alameen kamar yau ne yafara yin tafiya duk ta damu,saida suka shiga motar sannan ta riko hannun emaan wacce kanta ke sinne akasa saide mamakin mami yasa dole ta dago tana kallonta,mami tace"take care of yourself and your husband,Allah ya kiyaye hanya"sosai alameen ya washe baki cikeda farin ciki mara misaltuwa,emaan kuwa mamaki ne ya kusa kasheta,ta kasa cewa komai illa kallon mami datayi surprisingly,fahimtar hakan da alameen yayi ne yasa shi cewa "tunanin me kikeyi emaan"saurin girgixa kai emaan tayi tace"in shaa Allah mami"murmushi kawai mami tayi ta riko hannun fauxa suka koma ciki,suna matsawa daga wajen alameen yayi pulling emaan closer yana sakar mata murmushi yana kallonta da narkakkun idanunshi,baice mata komai ba haka itama ko motsin kirki batayiba har suka karasa airport,yana rike da hannunta suka shiga ciki......after completing all the  formalities suka xauna a first class lounge alameen na kallon emaan with so much love,yace"I'm the happiest man alive emaan..."yayi maganar with smile all over his face,emaan samun kanta tayi da yin murmushin itama even though har lokacin tana mamakin mami,alameen na caressing hannunta yace"tell me a story dear..."dan xaro idanu tayi waje dafarko kamar baxa tayi magana ba sai kuma can tace"wani irin labari kakeso"d'aga kanshi yayi alamar tunani yace"about your school life..."murmushi emaan tayi tace "ok,akwai wani incident daya taba faruwa when i was in ss1..."alameen eagerly yace"I'm all ears"emaan tace"you know ban fiye magana ba,back when i was in school abun yafi xama worst,i hardly talk in class,but there's this boy da muka saba dashi sosai,his name is yakubu he was my best friend back then,i never thought Christian ne even for once,sai daga baya nagane hakan...."tsuke fuska alameen yayi yace "niba irin wannan labarin nakeso ba"dariya emaan tayi tace "why?"yana kumbura baki yace"duk labaran dake duniya ki rasa wanda xaki bani sai na wani qaton banxa?"dariya Sosai maganar taba emaan,alameen kuma ya tsare gida irin ta b'ata mishi rai dinnan,yace"excuse me madam what you did wasn't funny"emaan ta xaro ido tace"tohm shikenan,kai ka bani naka labarin"harara ya galla mata sannan yace"i don't want to make you sad"emaan ta  harareshi kana ta turo baki gaba,alameen yace"xanyi owning lips dinnan yanxu nan"emaan tace"we're outside for crying out loud "yace"I don't care"tana murmushi tace"atleast do whatever you want indoors "murmushi yayi yace "are you sure "Ta gyada mishi kai alamar Ehh,Sosai mamakin emaan ya cika shi yace "awww so sweet of you my love"yafadi hakan kissing her hands.











Mssg or call me via 09037909996 for more information about my class.

https://whatsapp.com/channel/0029VaAxhFn3GJOpk4Zd7e09



Kuyi joining chef Zee novels channel domin cigaba da samun *EMAAN* update 5hours earlier akan yadda xaku riqa gani a groups.....

Akwai free recipes na kalolin abinci daban-daban.

Zanyi reposting old novels dina *JIDDERH* da kuma *SULTANA* and many other enticing goodies...

Share 🙏

EMAANWhere stories live. Discover now