PAGE 08

140 4 0
                                    

Eman...🥀

Page 8

Written by Zaynab Yusuf✍🏼

   "wasu files zan d'auka,sorry for the disturbance".yamutse fuska nayi batareda cewa komai ba na bashi hanya,sai ya tsare fuskata da kallo kamar me yin nazari sannan yashigo,samun kaina nayi da tsayawa abakin kofar ina wasa da medium size fingers dina,side drawer ya bud'e ya ciro wasu papers yana sakin karamin murmushi,wani government project ne daya cire rai da samu aka mishi approving yau,ya kalli fuskata wacce Na manta da wani abu wai ita dariya yace"Eman..."asanyaye na kalleshi idanuna suka Sarka akan fuskar shi,Ya Sadeeq chocolate color ne wanda kudi da hutu suka ratsa shi,gashi da dogon hanci da karamin baki kewaye da dark gemunshi wanda ya karawa fuskar shi kyau ,"Naam"nace tareda sunkuyar da kaina,tsananin kunyar shi na kasheni,nasan dole ya riqa mini wani irin kallo,sai na zama very uncomfortable,na hau Sosai k'ewa ina juya gangar jikina daga facing dinsa,shiru yayi ya tsaya yana kallona,ya rasa me cece damuwata,aganinshi yakamata ace na saki jiki anan tunda babu yawaitar idanun mutane,ahankali ya yafice daga dakin saboda ya lura bana son yin magana,shikuma bayason takura mini kawai yanason na saki jikina ne,Ya Sadeeq mutumin kirki ne,kuma jinin mu ya hadu from day one shiyasa ya damu da damuwata,sai bayan tafiyar shi naji babu dadi,daki nakoma ina sak'a da warwara,tunanin Aliyu ne yayi nasarar yi mini dirar mikiya,Allah ne kadai yasan son danake ma Aliyu wanda ko shi Aliyun ba lallai yasan dashi ba,kasancewata mara sa'a yasa na rasa shi alokacin da saura kad'an na mallakeshi ya zamo mini miji kuma uban'ya'yana,ya shiga rayuwata shigar bazata,Numfashi Na sauke mai nauyi ina tuno maganganun da yayi mini"zan yi kokarin fahimtar da mommy har lokacin da zata fahimceni "maganar ce ta dawo mini wacce ta sanya naji sanyi acikin raina,wannan maganar da Aliyu ya mini ita ce ta zamto Hope dina na aure guda Daya a duniya.Agajiye ya Fauza ta shigo tana k'are mini kallo sannan tace"Haba eman,waya saki yin girki keda kike fama da kanki,naki kawai nace kiyi shima dan bana nan ne".
Da mamaki nace"miye amfanin zaman nawa?".
Tace"kinga ba ruwana,amanar ki Abba ya bani bece Na riqa saki aikin wahala ba".tafada cikeda k'ara dakuma kawaici,Saida ta gabatar da sallar Magrib sannan tayi serving Ya Sadeeq dasu Anum,sunaci suna fira gwanin ban sha'awa,yace"guess what?"langab'ar da kai ya Fauza tayi tareda yin sama da fararen idanunta alamar tunani,sai kuma ta saukesu akan fuskar Ya Sadeeq tana bata rai,tace"I can't,fadamin".yana sakin karamin murmushi yace"anyi approving contract dinnan dana dade ina nema,kinga ikon Allah ko?saida na cire rai da samu sannan Allah ya kawo mini haske acikin lamarin".
Washe baki ya Fauza tayi cikeda farin ciki domin wannan project din will change their lives Sosai,zai karawa Ya Sadeeq girma,kudi dakuma daraja,kasa cewa komai tayi saboda farin ciki domin nasarar tasu ce baki daya,so take tabashi kyakkyawar tight hugg babu dama kasancewar su Anum dake zaune suna homework,takasa rufe baki ,kana ganinta kasan tana cikin farin ciki fara misaltuwa,"congratulations baby"tafada tanayin kasa da murya,yace"thank you sweetheart ".
Tace"this calls for a celebration "ya girgiza mata kai yana cewa"sure".mikewa tayi ta shiga bedroom dinshi shima yabi bayanta domin su tattauna sannan su Taya juna murna,yana shiga tayi hugging dinshi tightly sonshi na kara sauka abirnin zuciyarta.They've been through it all together,tabashi duk wani support arayuwa,ta kyautata mishi,ta kyautatawa 'yanuwanshi,tana mu'amalantar shi cikeda girmamawa,mutuntawa dakuma darajawa,tana yi mishi tsantsar biyayya  wacce babu algus cikin rashin gajiyawa,kosawa ko fushi,kullum fuskarta d'auke da murmushi koda kuwa sun samu sab'ani bata bari wani ya fahimci hakan,ta d'auki iyayenshi tamkar nata,tana kula mishi da yaranshi Sosai,bai tab'a complain akan wani abu nata ba,duk da tanada tsananin kishi wanda dakyar take iya controlling kanta,shiyasa komai wuyar aikin gidanta take yinshi babu gajiya ko nuna gazawa,Ya Sadeeq is very supportive shima yana tayata ayyukan gida,alokacin baya yayi kokarin convincing dinta akan daukar masu aiki amma ta hade fuska ita bataso,masifar kishinta ne kadai aibun dake tattare da Ya Fauza.Yasan kishi halitta ne,shiyasa yake takatsantsan da duk wani abu da zai tayar mata dashi,yake iya bakin kokarin shi ganin ya Daidaita relationships dinshi da 'yan uwanshi mata dakuma abokan aikin sa,duk da beyi mata alkawarin daga ita babu k'ari ba.Yana banzatar da maganar aduk lokacin datake kokarin bugar ruwan cikinshi akan hakan,"tunanin me kakeyi?"tafada tana cupping fuskar shi tareda circling small cute lips dinshi,yana daidaita tsayuwar shi yace"tunanin rayuwarmu nakeyi Fauza,thank you for everything ".sakin baki tayi tana kallonshi,miye na mata godiyar?maganar shi ta sanyata cikin confusion,amma ta daure tace" you worth more".kudade masu dadi yayi niyyar bata itama ta watayawa son ranta.
K'ishin ruwa ne ya fitar dani,saina tsaya ina kallon su Anum dasuka bingire suna bacci,jikinsu sanye da pyjamas alamar sunyi wanka,dakinsu Na kaisu Na kwantar tareda tofa musu addua,kitchen naje na dauko ruwa na zauna afalon ina sha,idona suka sauka akan karamar wayar Aunty Fauza,kamar tsohuwar munafuka Na Mike jiki ba kwari Na dauki wayar Na shige daki,numbar Aliyu wacce Na dade da haddacewa nayi dialling hawaye masu zafi suna zubo mini,yana zaune yatasa Tv agaba amma gabadaya damuwa ta mishi dirar mikiya,kallo daya zaka mishi kaga tsantsar damuwa afuskar shi,ya rame Sosai sannan fatar shi mai haske ta disashe,tunanin Eman dinsa yakeyi wanda hakan ya zamo mishi full time job,wayar shi dake ring yakalla,kamar baze daga ba saikuma yayi answering batareda cewa komai ba,muryata dake rawa nace"Aliyu".yana jin voice dina ya tashi zaune babu shiri yana jin dadi Na ratsa zuciyar shi,yace"Eman"muryar shi cikeda damuwa,lamarin daya kara tayar mini da hankali,fitowar mommy tana waya yasa yazame tashi wayar ya kife yana kallon ta tana fadin,"ai saida na tashi tsaye Na rabasu ta karfin tsiya,yo gani mara hankali zan bar d'ana ya auri wannan?ai ina rushe  maganar auren nafara nema mishi mata,Yarinya mai tarbiyya son kowa k'in wanda ya rasa".a razane Na mike tsaye duniyar na juya mini up side down,na kasa kuka nakasa kashe wayar narasa me zanyi naji dadi anan gidan duniya,rayuwar gabadaya ta isheni damuwa ta mini dirar mikiya,bansan lokacin da wayar ta fadi daga hannuna ba,na durkushe tareda fashewa da wani irin kuka mai ciwo da iya karfina,jijiyar kaina sun fito radau ga gumi suna keto mini,jikina na rawa so nake Na sume domin nasamu saukin rad'ad'i,zafi da k'unar da zuciyata ke mini,Arikice Ya Fauza da Ya Sadeeq suka shigo dakin,ya Fauza ta rungumo ni hankali tashe tana tambayar"Meya faru?".gabadaya bana cikin hayyacina,na kasa digesting maganar Mommy nacewar tana nemawa Aliyuna Mata,innalillahi wainna ilaihi raji'un,Aliyu is my one and only hope aduniya.
Wayar Anty Fauza dake yashe a kasa ya Sadeeq ya dauka sannan yace"waya tayi "yafada yana dubawa,already an kashe kiran saiya tsurama numbar idanu sannan yayi forwarding to his inbox.
Yace"kwantar da ita ne".Ya Fauza tayi narai narai da ido tace"kasan bazan iya d'agata ba saika taimaka mini".da mamaki yake kallon Ya Fauza,ta shayar dashi ruwan mamaki da bata nuna kishi akan Eman,tabbas ta d'auki Eman yar uwa ta jini.!Alokacin baya yayi tunanin saboda nesa suke yasa bata damu da shirinsu ba but she proved him wrong.
"kamata mana"cikeda d'ari d'ari ya taimaka mata suka kwantar dani,nidai ina jinsu amma nakasa cewa komai,banason motsa koda eyelashes dina,ni kadai nasan zafin da zuciyata ke mini,rayuwata is just a mess,nataso agidan babana cikeda rashin kulawa da kauna,ya cireni daga cikin sahun 'ya'yan shi alokacin da k'addarar rayuwa ta afka mini,Umma ta takasa fahimtata,Na rasa Aliyuna,narasa karatuna dakomai na rayuwata!.lumshe idanu nayi dan kawai su matsa daga kaina,cikin sa'a kuwa suka fita daga dakin atunaninsu nayi bacci.
"I think eman na bukatar Therapy ".cewar Ya Sadeeq,ajiyar Zuciyah Ya Fauza ta sauke sannan tace "no she'll be fine,in shaa Allah".koda suka kwanta kasa bacci Ya Sadeeq yayi,ya nutsa cikin kogin tunanin damuwata,yana so yasan tushe kuma mafarin matsalar rayuwata domin ya taimaka mini,yana jin zuciyar shi bazata tab'a samun hutu ba har sai lokacin daya share mini hawaye ya mayar da kukana izuwa farin ciki mara gushewa!.
Washegari da misalin k'arfe takwas Na safe na tashi,kasancewar bacci b'arawo bansan lokacin da daya sace niba,maganar mommy ce tafara dawo mini mai barazanar tarwatsa zuciyata,Shigowar Ya Fauza yasa Na katse tunanin,bance mata komai ba itama sai kallona takeyi,taso zama dani agida amma hakan ya gagara kasancewar yau friday dole takarasa aikin karshen sati,Ya Sadeeq ma yaso ta zauna da ita domin taji meya faru amma duk kokarin su nayin haka ya tashi ga banza,gashi bata son barinta agida ita kadai,tasan tunani kawai zanyi,tace"I'm sorry eman"da mamaki nake kallonta bance komai ba,hakurin miye take bani?,"ina baki hakuri ne akan abinda yafaru jiya,naso yau na zauna dake amma hakan ya gagara,dan Allah kicire damuwa acikin ranki,anjima idan na dawo zamu fita".
Da "adawo lafiya"na amsata ina jin kaunar ya Fauza a raina da zuciyata.

Yau aka sanya date din Auren Salima,nan da wata d'aya da sati biyu,farin ciki wurin hjy kwaise baa magana,umma ma tayi kokarin sakin jikinta akayi komai da ita,saide can kasan zuciyarta na fama da matsananciyar damuwa,Sosai Hankalin mummy yakara tashi,bakin ciki kamar ta shak'e kanta ta mutu takeji,yanzu sauran inteesar da Afnan suka rage ma hjy kwaise,ita kuma gabadaya 'ya'yanta hudu na gida azube sun jeru reras dasu basuda niyyar motsawa,abinda yafi kona mata rai shine Afiya da Rafee'ah sun girma Salima,yanzu inteesar ce tarage sa'ar Eman sai auta Afnan wacce keda sauran lokaci,tana zaune agefen gado tana karkada kafa tana huci,gabadaya abin duniya sun taru sunyi mata yawa,kuka ne ke kokarin kufce mata hjy kwaise tashigo dakin,hannunta dauke da laces biyu atamfa daya,tace"kayan iyaye daga wurin Ango na kawo miki".dakyar ta iya kakalo murmushi tace"nagode Allah sanya alheri da albarka ".da amin Hjy ta amsa sannan tafita,mummy ta bita da rakiyar wata muguwar harara,ta kalli laces din masu shegen kyau da tsada,ita dama ace talaka ne sai tadan ji dadi aranta.
Kamar an jefosu Afiya,Rafee'ah da sadeeya Suka shigo dakin Ajere kuma lokaci daya,zuciyar mummy kamar ta tarwatse,haka taso haihuwar d'a namiji amma burinta yabi ta shanun sarki,wacce irin rashin sa'a ce ke bibiyarta a mataki mataki na rayuwa?ta tsani wannan jerowar dasukeyi,kamar ma da gayya suke mata saboda ranta ya b'aci,cikeda b'acin rai tahau zazzaga musu masifa,tana daga lace take cewa"kunga inda akayi sa'ar haihuwa ko?kunga inda ake abin arziki har ya hayyafa yayi naso,ku kalla dakyau kugani,wannan lace din 100k ne,wannan kuma 120k,nifa aka ba wannan?inaga wacce tahaifi Salima?".
Tafada ranta Na k'una,kuka Rafee'ah da sadeeya suka fara,suna jin zuciyar su Na suya,suma ba haka suka soba,kawai basu da yadda zasuyi ne tunda Allah be kawo ba,mutum ya isa yama kanshi miji ne?
"Daga nayi magana ku hau kuka kuna mini wa'azin kasuwa,ku bud'e kunnuwan ku dakyau ku saurari abinda zan fada maku,ba tsayawa zakuyi kamar wasu wawaye ba da bikin Salima,gayu zakuyi Na kece raini ku shiga adama daku,ku shisshigewa abokan Ango ku samu karbuwa ".wani hawayen bakin cikine ya kara zubo musu banda Afiya wacce hakan kema dadi,Rafee'ah da sadeeya sun cika kamar suyi bindiga su fashe,shin wannan dabi'ar uwar kwarai ce?da "Toh"suka amsa saboda a zauna lafiya,sun San fadan mummy yanzu saita dora daga inda ta tsaya tana jifansu da kalamai marasa dadi...

***Kina son turaren wuta masu classy and unique scent?masu kamshin gidan 'yan gayu,turare mai kama gida ya mayar dake abar so yar kwalisa?kinason turaren da tun daga tsakar gida za'a San yes Ke Cikakkiyar mace ce?hajiyata kina son durot mai tsananin kamshi da akayi shi cikeda tsafta?kina son exclusive room freshners?kina son amsa sunan cikakkiyar mace ?wacce ta amsa sunanta Na Sarauniya?BAKHOOR INCENSE PLACE gidan kamshi got you covered,maza ku garzaya Bakhoor incense place domin siyan d'aya ko sari,ni na gwada kuma naji dadi domin nagari ne kuma na mayar da kudina gida Chasssss💃🏼💃🏼ku tuntubesu ta wannan lambar domin siyan Turaren wuta yan gaske.
09037909996

Zaynab Yusuf ✍🏼

EMAANWhere stories live. Discover now