PAGE 14

121 4 0
                                    

Page 14

  Ahankali take tafiya majestically,jikinta sanye da black color plain abaya,tayi rolling black veil din rigar,tana rungume da pharmacology textbook,kafadarta d'auke da fancy school bag wacce tayi matching da kayan jikinta,Anum da Asad ne suka fara gaisheta sannan tajuya with a little smile tace"good morning A2 parents "tafada tana xama a dining,ido yaya Sadeeq ya xuba  mata yana kallo,tayi wani fari da kyau even though ta tad'an rame kadan,Fauxa tace"morning dear,I was about to call you najiki shiru,yanxu muke maganar xuwan ki school da yaya Sadeeq,tinda kusan hanyar ku d'aya shi xai rik'a kaiki sannan idan ya tashi ku dawo tare nasan zuwa 5 kuke gama lectures,nikuma saina ji dasu Anum".kallonta eman keyi for some seconds sannan tace "that isn't necessary,xan riqa zuwa dakaina".hararar wasa Fauxa ta mata sannan tace "my house my rules"yaya Sadeeq yace"sure ma'am "sukayi dariya atare ita kuma tayi dipping fork acikin chips tafara ci,k'aramar waya ya fauxa ta miqa mata tana fadin"umma ta hana abaki babba,you should manage this for now,akwai sim card aciki,xakiga saved number Na dana umma dana yaya Sadeeq "asanyaye ta karbi wayan hawaye na cika idonta,tace"thank you ya Fauxa "girgiza kai fauxa tayi batareda tace komai ba ta haura sama domin dauko veil da handbag dinta,Anum da Asad already sun fita sauran eman da yaya Sadeeq akan dining,he was staring at her passionately without blinking,ajikinta taji ana kallonta,hakan yasa ta dago da fuskarta suka hada ido,saita yi saurin saukar da fuskarta shikuma ya cigaba da kallo har lokacin da ya fauxa ta sauko,boyayyar ajiyr xuciya ya sauke sannan ya mike yana sanya hula,Fauxa tayi saurin Daidaita mishi ita tana kallon fuskarshi,saida ta gyara mishi sannan tace"you look so muaah,Allah ya tsiyayar da ruwan idanun duk macen data kalleka"dariya yayi yana fadin"sweetheart take it easy"tareda riko hannunta suka jera suna tafiya eman Na binsu abaya har suka fita tsakar gidan,bayan mota eman ta bud'e xata shiga,fauxa dake reverse tayi sliding mirror tace"mijin nawa zaki mayar driver,c'mon enter front ",gaban motar eman ta shiga ta ajiye katon textbook akan laps dinta,yaya Sadeeq yace"bai miki nauyi ba?ki ajiye a baya mana"murmushi tadanyi tace"ok"sannan ta ajiye littafin abaya,ta k'asan ido yake kallonta can yace"madam put on your seatbelt "juye juye tafara yi saboda ya sakale shi ta baya,saida ya cire sannan tasaka tana gyara xamanta wanda yafito da hips curve dinta kasancewar yadin abayar me kwanciya ne,shi be ma San tanayi ba gabadaya hankalin shi nakan titi yana driving carefully,asanyaye yace"promise me you won't cry today..."sai ya gyara xama sannan yacigaba da fadin "nasan kina cikin tsananin damuwa,kin rasa masoyinki,kin samu problem da both of your parents,tabbas rayuwa sometimes is unfair,bawai ina fama miki ciwon dake cikin xuciyar ki bane,inaso ki fahimci nida Fauxa are trying our best to make you happy,damuwar ki tamu ce sannan kukan ki yana affecting dinmu yadda bakya tunani,mu akullum fatan mu shine ki kasance cikin farin ciki,dan Allah try your possible best kidaina saurin kukan nan"yakarasa maganar in a pleading tone,sai alokacin ta kalleshi tana motsa eye lashes dinta suna sama da kasa adorably,saurin Daidaita kanshi yayi saboda shi kadai yasan me yaji sanda ta mishi wannan kallon,tace"in shaa Allah yaya Sadeeq,I'll try my best "daga haka bata sake cewa komai ba ta mayar da kanta titi, wayar shi dake ring ya kalla yana mamakin ganin kiran Bilal da safe,yasan baxai  wuce maganar eman xai mishi ba hakan yasa yaki picking cox he'll never hook them up no matter what,ya kalli eman yaga ta langabar dakai still tana kallon titi,she's so cute ya furta acikin ranshi sannan  yayi parking asanyaye sanda suka karasa school din saboda be gaji da kallonta ba,shifa idan kallon eman aiki ne he'll apply for the job and work 24/7,ta lumshe idanu sanda ta daga kai tana kallon gate din an rubuta Baba ahmed university kano,sai taji kamar ta shekara bata xoba nan kuwa just 4 weeks ne,ta balle kofar bayan ta dauko textbook dinta da jaka tace"bye yaya Sadeeq "yace"wait"sannan yaciro 3k daga wallet ya mika mata,hannu tasa tayi mishi godiya sannan ta shiga department dinsu tana jin dadi.saida ta kurema ganin shi sannan yayi reverse ya tafi office zuciyarshi maqale da tunanin eman,wanda haka ya xamar mishi jiki.
Ta baya Kausar tayi hugging dinta wanda hakan yasa gaban eman tsananin faduwa,ta xaro ido tana mamakin wanda xai mata wannan wasan,ganin Kausar ce yasa ta sauke ajiyar xuciya sannan tace"stupid girl kin tsorata ni".murmushi Kausar tayi tace"wannan kadan kenan daga cikin halin da kika sa ni,gabadaya ba'a jinki,your phone isn't going through,kisan jiya muka dawo daga umrah I was planning to give you a visit later today sai gaki kinxo,amarya sai glowing kike".kalmar amarya data furta ce tasa wani takaici ya tsaya mini arai,saina share nace"welcome back dear"tace "thank you amaryar mu,meya samu wayarki kullum switch off?nasan by now an fitar da anko ko?what are the plans?tell me dame dame xanyi?"kallonta kawai eman keyi tarasa bakin magana,ta ina xata fara ce mata anfasa bikinta?can tace"its a long story,sai mun xauna tukunna"Kausar tace"alright dear, but i hope everything is fine naga kin kara xama so cool".eman tace"kin fiye surutu muje anfara lectures "daga haka suka wuce lecture hall eman Na tunanin ta yadda xatayi breaking bad news din to Kausar.
Salima da inteesar ne ke kirga invitation cards hjy kwaise ta shigo tana fadin"har yanxu baku gama ba?"inteesar tace"we're almost done,duk da yau bawani rabo zamuyi mai yawa ba saboda xamuje gidan ya Fauxa "hjy kwaise tace"kuyi ma 'yan uwanku magana saiku tafi tare,kar suga kamar kuna ware su ".Salima ce ta amsa da "Toh Mami "sannan ta mike ta tafi part din mummy,lokacin mummyn na xaune tasa su Rafee'ah agaba tana masifar ita wannan bak'ar rayuwar ta isheta,tashiga uku ta lalace an sa ma 'ya'yanta hannu sun rasa miji,sallamar Salima ce tasa tayi shiru tana kakalo murmushi,bayan sun gaisa tace"anjima xamuje rabon invitation daga can xamu wuce gidan ya Fauxa to plan for the sisters night,you can join us if you're free".Afiya ta kyabe baki sannan tace"inada lectures anjima".Sadeeya da Rafee'ah sukace "sure dear,karfe nawa".Salima tace"in the next two hours "tana gama fadin hakan takoma part din tabar bakin mummy asake,bakin ciki kamar ta had'iyi xuciya,wato saboda wulakanci yayanta ne yan rabon i.v cards,ta wurga ma Rafee'ah da sadeeya wata uwar harara tace"abinda kuka iya kenan,celebrating people's success ku kuna nan xaune babu saurayin arxiki amma kunfi kowa iya rabon i.v din jama'a".
Rafee'ah tace"mummy she's our sister,this is the only support daxamu iya mata".dogon tsaki mummy taja sannan tace"sanin hali yafi sanin kama,idan kowa baiyi magana ba ke sai kinyi fitsararra mara kunyah,inde rabon i.v ne ban hana kiba amma karki xauna kima rayuwar ki karatun ta natsu ki tashi tsaye ki nemi miji kema atayaki rabon i.v,ki cigaba da xama kina mayar mini da magana kina kokarin goga kafada dani".
"Kiyi hakuri"cewar Rafee'ah asanyaye hawaye na xubo mata,tasu irin jarabawar kenan.
1pm daidai su eman suka fito lunch break,a wani fancy restaurant suka xauna suna lunch,kausar tace"I'm all ear dear".ajiyr xuciya eman ta sauke sannan tace "the wedding is cancelled "cikeda damuwa da mamaki kausar ta xaro idanu waje tace"ke kawata stop joking mana,ban gane an fasa ba".hawaye ne suka xubo ma eman non stop,wasu na sauka sababbi Na kara xubowa,hakan ne ya tayar da hankalin kausar,wani tausayin eman Na ratsa ta tace"I'm so sorry dear,pls stop crying "tafada in a pleading tone,eman batace Komai ba ta dauki strawberry daiquiri tana sha duk da bata jin dadin shi sam,kausar tayi shiru tana kallonta cikeda tausayawa,tasan akwai maganganu da yawa abakin eman amma she won't ask her for now,she can imagine emans pain,tace"kiyi hakuri eman,khair in shaa Allah,I won't ask you again"still eman couldn't say a word,sai kallon kausar take tana sauke ajiyar xuciya,ahaka suka gama lunch sukai sallah sannan suka wuce practical classes,few people dasuka san da xancen auren sunata tambaya saide eman tayi murmushi wanda hausawa ke cema kafi kuka ciwo,5 daidai suka tashi,already driver dinsu kausar yaxo most times ma a school din yke yini har sai sun tashi sannan su koma gida tare,karamar wayarta data fara ring ta ciro daga cikin jaka,sai alokaci ta riqe wayar tun safe da ya Fauxa ta bata,ganin numbar yaya Sadeeq yasa tayi picking tace"hello".ahankali yace"naxo "ok tace sannan ta tafita tashiga motar Da sallama sannan tace"good evening "kallo daya ya mata yace "kinyi kuka ko?"tamkar xata fashe da wani kukan tace"kausar asked about my wedding shiyasa"jinjina kai yayi ahankali sannan yafara reverse suka hau kan titi,can yace"me zamu miki kidaina damuwa?"dan xaro ido tayi tace"bafa damuwa nayi ba,ina xamana ta tambayeni shine kukan yaxo"jinjina kai yayi yace"next time don't cry kinji ko"asanyaye ta gyada mishi kai batareda tace komai ba har suka karasa gida,lokacin ya Fauxa tadawo saboda xuwan su inteesar,ganin motar gidan yasa gaban eman faduwa tana tunanin waye yaxo?yaya Sadeeq dake lura da actions dinta yace"su inteesar ne"sassanyar ajiyr xuciya ta sauke sannan tashiga,a main parlorn ya fauxa ta tarar dasu,Salima da Rafee'ah a kujera daya,sadeeya da inteesar da ya fauxa suna k'asa,Anum da Asad nata tsalle tsallen su,ganinta yasa suka rungumeta suna Oyoyo,Salima tayi saurin tashi ta rungume ta,inteesar tace"Sannu da xuwa "with a wide smile haka su Rafee'ah suka jawota ta xauna atsakiyar su kowanne na bayyana yanda yayi missing dinta,hakan yasa hawaye suka xubo mata irin kaunar dasuke mata kamar wacce suka fito ta jini d'aya,Salima tace"I miss you so much sis,pls yaushe xaki dawo gida?kinga fa sauran kwana kadan nima nafita "tafada gwanin ban tausayi,sai kukan eman ya k'aru Sosai saboda yadda Salima ke kaunarta da son ganin farin cikinta is on another level,tun farkon xuwanta gidan take mata mutunci babu abinda ya canxa har yanxu.sauran sisters dinma suka cigaba da fadin yadda gidan yaxama ba dadi without her,ita dai saide ta kallesu tana xubar da hawaye.
Sai alokacin yaya Sadeeq ya shigo ciki,suka gaisheshi cikeda girmamawa yana tsokanar su dayake shi duk abinda ya shafi fauxa baya wasa dashi tun farko,dan haka ya dauki sisters dinta tamkar nashi suma suke girmamashi over.
A katon tray ya Fauxa ta xuba musu xaxxafar chicken biryani wacce tun daga waje kake jin kamshin abincin,suna ci suna fira anan suka tattauna yadda sister's night din xai kasance,even though they were very considerate with their convo gudun eman taji wani iri,sai past 9 suka tafi eman ta rakasu har waje tana musu waving bayan sun tabbatar mata jibi xasu dawo,Salima ma tace anan gidan ya fauxa xatayi gyaran jiki to spend more time with her,da wannan kalaman tabarsu suka tafi batareda tayi kuka ba,saide hawayen dasuka xubo mata,tasa hannu ta sharce sannan ta juya ciki,a entrance taga yaya Sadeeq ya tsaya da alama tun daxu yana wurin,ya kalmashe hannu akirjin shi fuskarshi ahade babu alamar rahama akanta,kallonta kawai yake yana had'a abubuwa akanta acikin ranshi,samun kanta tayi da rikicewa ta tsaya still tana kallonshi kamar yadda shima yake kallonta.

Zaynab Yusuf ✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now