Chapter 1

5K 196 7
                                    

Assalamu Alaykum to you guys,"Tagayyara" wannan shine sunan, banbara'kwai koh??😁 let's find out mey wannanan labari ya 'kunsa ,follow vote and drop your comment.lots of love😘


To listen click👇

Yarane guda biyu wanda sin dage se dambatuwa sike macen irin mey garun jikinnannce 'yar lukuta ta zaune namijin wanda yake siriri dukda kuwa ya d'arata tsaho.Wannan yarinyar bazata wuce shekara 8 ba shikam 12,ganin ya kasa 'kwatar kansa daga hannunta yasa ya 'kwala kiran"Mommy! Mommy!

Cikin lokaci 'kalilan sega wata matashiya dan baza a kirata dattijuwa ba ,daganinta bazata wuce 30 ba mace mey matsakaicin tsaho baza a kirata ce 'kiba ba haka ba siririya bace,fara tass mey kyawu irin na Fulani da ganin fatarta zaka gano hutu a tattare da ita,daga bakin 'kofa ta tsaya tana kallonsu su biyun dariya ta shiga yi sosai harda ri'ke ciki.

"Shettyna ka bani kunya"

Jin haka yasa yarinyar ta saki wuyan rigarsa ta sauka daga kansa da sauri ta matsa gefe tana sunkui dakai se haki take,shikuwa se nishi yake da'kyar ya mi'ke yana goge fuska .

"Banza 'yar sukuta Nonsense mumu stupid!" Yayi maganar a wahalce.

"A'a ya isa shetty sisternka ce fa Amrah bestyn ka"

Itade bata ce ko 'kala ba fuskarta kuwa bata nuna alamar karaya ba ko yanzu a shirye take."Kuzo nan"Ta mi'ka hannayenta.

Wanda take kira da shetty shiya fara zuwa gunta sannan Amrah ta 'karasa.

"Meya had'aku yanzu?"

"Littafina ta yaga" Yayi saurin amsawa.

"Wlhy 'karya yake " "Timemiya" yace mini"

"'Karya koh shetty? Papa zan fad'awa"

"Mommy please don't, idan kika fad'a masa baze siyo min spider man ba"

"Toh ka dena tsokana kaji,yanzu bata ha'kuri"

"Shoyi" Ya fad'a.

"A'a ban yarda ba sorry zaka ce"Mommy ta fad'a.

Haka baya so ya bata ha'kuri ,tana ri'ke da hannunsu suka sauka 'kasa se gwalo yake mata ita kuwa se harararsa take.A parlour kowannensu ya samu gu ya zauna fruits dake bowl akan center table Mommy ta d'auka kowannensu ta bashi apple ,duk cikinsu ba wanda ya soma ci nan Mommy ta barsu ta shige kitchen.

" Kalli"Shetty yayi maganar yana nuna mata apple dake hannunsa.

Amrah fuska a cukule ta d'ago ta kalleshi "Timeme kamarki!" Yana gama fad'ar haka ya cillar da Apple d'in ya fita da gudu.Kuka ta fara yi sha'be-sha'be koda ta d'auki Apple d'in dake yashe a 'kasa taga yayi masa ido da baki ta hanyar rarake flesh d'in.

Tana kuka ta tafi kitchen "Mommy kinganshi koh wai ina kama da Apple" Ta mi'ka mata.

"Rabu dashi sena fad'awa Papa ya siyo miki babie doll shikuwa baza a siyo masa ba my beautiful princess" Ta fad'a tana kar'bar Apple d'in.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now