Chapter 55

647 52 1
                                    

  
      
           Shettima a office abincin ma ya kasa ci tunanin Amrah ya mamayeshi gashi numbern ta dayake da ita ta dena aiki ,koh be ganta ba yanaso yaji muryarta kuma yasan idan yaje gidansu ba lalle ta fito ba.

    Jinsa yake kamar wani maraya yana jinsa he's not completed. Wajajen 12pm ya shiga meeting wanda har aka 'kare rabin hankalinsa baya wajen.Yau ko asr be kai ba ya bar wajen aiki direct gida ya wuce.

     A parlour ya tarar dasu Mommy daga ita se su Wafah  yaran doctor sun tafi gida su Sa'adatu kuma sunje islamiyya shiyasa aka samu sa'ida.

     "Yau ka dawo da wuri haka ,sannu da dawowa"

     "Yawwa Mommy barka da rana ,bataliya sun tafi?"

    "Ehhyi sun koma gida"

    " Ba abinda naci yau Mommy ko ruwa".

  Da mamaki ta dubeshi "Kana mey har 3 baka ci komai ba seka tada ma kanka ulcer"

    "Toh ai ba'a bani ba ko tea d'in ma ba'ai min tayi ba"Yayi maganar cikin sigar kalar tausayi.

    Dariya Mommy tayi dan ta fahimci zancen yanzu."Toh  ga abinci chan yana jiranka yanzu ai babu masu tare maka gu "

     "Kafin si dawo kenan". Ya fad'a.

       Su Walida da suka shagala kan waya da alama  chat sike se murmushi suke saki lokaci-lokaci ko sannu da zuwan basi masa ba.

    " Bara Mommy na d'anyi shower sena ci abincin".Ya fad'a.

    Wayar Walida ya wafce ya wuce ta sakankace sam bataga lokacin daya 'karaso inda take ba,hankalinta ne ya d'aga karya kalle mata chat d'in datake da saurayinta ta shiga bashi ha'kuri.

     "Mutum ya dawo bakusan kuce masa sannu ba". Be tsaya ba yayi wucewarsa d'aki.

     Kamar zatai kuka ta kalli Mommy " Kice ya bani"

    "Nina saku shagala a wayar? gwara ma daya 'kwace ko girkin ranar baku taya ni ba saboda danna waya haka zaku dinga 'kona abinci a gidajenku koh?"

    
   "Kinji fah Mommy ya za'ai mu 'kona abincin da.... " Walida bata 'kare maganar ba tayi shiru kunya ta hanata.

    "Abincin da mazajenku zasu ci koh" Mommy ta 'karasa mata.

    Rife fuska tayi "Ni ba haka nake nufi ba".

Ta'be baki Mommy tayi rana fad'in  " Matsa min mara kunya" Ta wuce kitchen.

     Shiko Shettima daman da biyu ya kar'bi wayar,yana so ya d'auki number Amrah  dan be manta ba rannan yaji Walida tana fad'awa Mommy tayi chat da Amrah take cewa a gaidata ,su Walida yanzu an dena jin haushin Amrah bayan da suka samu labarin duk abinda ya faru a wancen lokaci.

      Oho shi be ko duba chat d'in datake ba wannan ba huruminsa bane abinda yake so ya shiga laluba,tunkan ya kwashe digits d'in yaji sanyi a ransa.

      Bayan daya gama zubeta a tashi wayar yayi saving da  'Baby❤" kamar yayi dialing a lokacin sekuma ya fasa ya bari akan anjima ya kira sanda ya gama nutsuwa kenan.

     Wayar Walida aka wani yi cilli da ita kan gado amfaninta ya 'kare(lol).

         ★★★

      Bata jima da idar da sallahr asr ba dan tana kan daddumar ma kira ya shigo wayarta.

      Hannu ta mi'ka kan drawer ta d'akko wayar tana 'karewa number kallo ,ta rasa number wace/waye ba shakka ba yau ta ta'ba ganin number ba sede ta manta mey ita.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now