Chapter 21

546 41 0
                                    


         Kira na farko beyi picking ba se ana biyu ya d'aga ba tare da yayi magana ba se itace tayi sallama.

    "So kin amince ko yaya?" Taji ya tambaya ba alamar wani walwala a yadda yayi tambayar.

    "Amrah think twice "Taji zuciyarta ta fad'a.

      " Are you there?"Ya tambaya daga d'aya 'bangaren jinta shiru.

    "Eh na amince muddin zaka cika al'kawarin daka d'auka".

     " Glad,kinsan mey kike,karki damu Barrister baya magana biyu"

    Shiru ba wanda ya sake magana na tsahon lokaci daga baya ma kashe kiran tayi hawaye ya fara kwaranyowa a fuskarta.

    Murmushin gefen fuska yayi jin ta katse wayar shi kanshi be zaci zata amsa da wuri haka ba yanzu ya sake tabbatarwa ba 'karamin so takewa Shettima ba.

      _____________________

    Yana tsaye jikin mota jira yake ta fito.Ya shagala da kallon wayarsa yaji sallamarta ,d'agowa yayi ya d'ora idanuwansa a kanta tun daga 'kasa har sama ya 'kare mata kallo kafin ya maida wayarsa aljihu.

    Sam fuskarta ba walwala a tattare da ita duk wanda ya kalleta baze sake so ya kalleta ba amma shi be damu da hakan ba."My  fiancé what wrong?"

     Yasan ba amsawa zatai ba dan haka ya cigaba da magana."Mey aka tanada min akeson ganina dukda de gani nazo d'in amma an'ki fad'a min ko duk cikin jan ajin ne?"

    Tabbas ita ta kirashi tace yazo akwai maganar da zasi,tayi wa Ummi bayanin zuwansa amma bata fad'a mata komai ba.

     "Alfarma nake nema a gurinka" Ta fad'a ba tare da ta kallesa ba.

      "Ina jinki"

      "Ina ro'konka daka fara fitar dashi kafin ka aureni"

     "Meyasa kikace haka?"
 
      "Saboda lokaci yana 'kurewa"

       "Sede kiyi ha'kuri amma ba haka na tsara ba,se min fara yin aure tukun"

     "Baka yarda dani bane?"

   
     "Komai zey iya faruwa"

     "A ganina wata biyu yayi wuri ,gida dole zasi zargi wani abu"

     "Sede kinso hakan ya faru Amrah" Yanzu sosai ya tsireta da ido yana kallonta.

     "Don't let your self down miss Amrah ,complete your mission do what ever it takes to and save him,then I will handle the rest".

       Yau ma babu sallamar arzi'ki kowa ya kama hanyarsa ,tana shiga gida ta shige d'aki ta dasa sabon kuka.

             ***

      2 days later

        6 :13pm ,tana kwance cikin bacci tajiyo fad'an Abba kamar a mafarki ,tana bud'e ido taji ba mafarki bane bata fahimci kan zancen nashi ba amma taji alamar kamar a kanta neh.

     " Amrah! "Ummi ta 'kwala  mata kira.

     Da sauri ta m'ike ta gyara d'an'kwalin kanta ta fita zuwa d'akin Abba.Cikin rissinawa ta tsuguna tayi masa sannu da dawowa dan shigowarsa kenan,Ummi tana zaune kan wani kujera daga gefe shikuwa yana tsaye.

     "Tunda mike dake kin ta'ba yi mana maganar  Kamal ?"

     Cikeda mamaki ta d'ago kai ta kalli Abba sannan ta sauke idanta 'kasa a ranta tana fad'in "Mey kuma ya 'kullo?"

TAGAYYARA(Complete)Kde žijí příběhy. Začni objevovat