Chapter 40

622 51 0
                                    

Oh I'm sorry a baya nayi updating page har biyu ba tare da na lura ba Ashe na tsallake   37 and ba Wanda ya tuna min,ga can 37  en.

     Ganin ta shige d'akinta kamar yabi bayanta se kuma ya fasa ya wuce nashi d'akin.Tun daga bakin 'kofa ya tsaya yana 'karema d'akin kallo qwaqwalwarsa na tariyo abinda ya faru da d'akin se lokacin ya tuna da yadda akai ya samu ciwo a hannunsa cikin takatsantsan ya 'karasa har bakin gado ya zauna hannunsa ya shiga brushing cikin gashinsa kamar zey cire gashinsa.

    "Why? Kamal". Yai tambayar a fili.

     Idonsa ne ya sauka akan wayarsa dake kan drawer take ya mi'ka hannu ya d'auka yana kunnawa.Mamaki ne ya kamashi lokacin da yaga date,yana ina har kwana uku suka shud'e be sani ba? "Wannan shegiyar allurar".Ya fad'a a ransa.

      Yana jiyewa kansa tsoro Allah yasa ba ciwonsa ne zey dawo masa ba ,inde ko haka ne dole ya ziyarci doctor dan yanaji wannan alluran da magungunan baze iya dasu ba.Zimbir ya tashi daga zaunen ya fad'a bayi ,bayan yayi wanka ya fito ya shirya cikin  red T-shirt long sleeves da ba'kin jeans da kansa ya gyara d'akinsa ya tattare pieces d'in glass d'in yana fatan Allah yasa Amrah bata shigo taga ni ba.

    Phone d'insa ya zira a aljihu ya d'auki key bayan ya feshe jikinsa da turare.

    Tana d'aki ta jiyo alamar ya fita sanyi har cikin ranta, wata zuciyar tana ta raya mata kota tafi gida.Yana isa asibitin direct ya wuce consultant room inda yasan zey sami doctor d'in be damu da ko da akwai patient ba ko babu ya bud'e 'kofa ya shiga,bama kowa doctor d'in ne kawai a ciki.

    Aiki yake a laptop amma shigowar Kamal tasa ya rufe ya dawo da kallonsa kansa.Yasan ba lafiya ba  rabon daya ganshi harya mance yau se gashi ya duro ba zato ba tsammani.  " Barrister Kamal you're welcome"Cewar doctor d'in yana 'kalo murmushi.

    Wani kallo yake masa kamar hararar 'kasan ido haka ya zauna kan kujerar opposite dan doctor d'in sede ya karkatata left side baya kallon doctor d'in.

     Seda ya gama 'bata lokaci ya gama harare hararensa."Kayi min al'kawari zan d'auki shekara 3 ba tare da ciwona ya dawo ba right?"Ya 'kare maganar yana kallon doctor d'in.

    "Yes inde kana kar'bar treatment using drugs dana baka Barr Kamal".

      " Cha nai maka bana kula da kaina ,kuma banson wannan Barrister d'in daga yanzu ka kirani da Kamal Idris ko Al'kalin banaso"

    Doctor had'iyar yawu yayi a ransa yana tunanin meya faru kuma yau Kamal yake gudun a kirasa da sunansa na Barr Kamal Idris Al'kali.Yasan yadda yake respecting aikinsa as a lawyer amma kuma yau da kansa yake gudun sunan.....

    "Na zame maka ma abin kallo doctor saboda nazo neman lafiya?" Ya wurga masa wani mugun kallo.

     "Ahh No.. no ba haka bane ,ina so naji when last kasha maganin....."

     Be 'karasa ba ya katse sa."Ba iya magani ba ma doctor just 3 days da suka wuce nayi allura amma ba abinda ta tsinananmin se bacci".

    Shiru ya d'anyi doctor d'in yana nazari kafin yace."Yalla'bai ina tunanin akwai condition daka shiga wanda yayi leading drugs da allurar baze yi ...ma..aiki ba sede a chanja m.."

    "Ni doki neh ko jaki koh?"Yayi saurin 'katsetsa.

     " No sir ba haka bane akwai matsayin da ake kawai patient ya zama  drug dayake yawaita amfani dashi ya....."

    "Kai ka isa ka yimin bayani akan harkar lafiya ? Ko ka manta ni waye?"

     "Please sir relax nasani ka sani na wai tuna ma ne".

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now