Chapter 31

639 45 2
                                    

    
       Aunty Hannatu tuntuni  tana kallon wayarta dake ruri sunan Firera ya bayyana a screen amma ta'ki picking gudun kada ta bata labari tayi mata dariya.Seda ta kira sau biyar ana shidan ta d'auka.

   "Haba my  Hanne nayi laifi ne haka aka 'ki d'aga kiran nawa?"

    "A'a" Ta amsa a ta'kaice.

     "Toh ya akai ya kukai da Barr ya baki ?"

    Kamar an kunnota "Sh*ge d'an iska samfurin mayu wlhy Firera bansan inda kika samo min maye ba".

    " Maye fa kikace meyai zafi?"Firera ta tambaya dariya tana so ta ku'buce mata.

    "Allah ne ya ceceni da sede kiji mugun labari,Ba..." Shiru tayi bata iya fad'ar sunan ba dan gani take kamar yana jiyota a duk inda yake.

    "Harshena fa yace ze cire".Ta fad'a zuciyarta na mata 'kuna musamman idan.ta tuna yadda ya 'kone kud'in.

     " Hahaha harshe? Kiji min yaro shi ina shi ina cire harshen mutum,ya kud'in fah?"

    "Ya 'konesu ,Firera naga samu naga rashi".

     " Tir'kashi! Yanzu a gabanki ya 'kone kud'in? "

    "Ehhyi".

     " Ai na fad'a miki Barrister wani irin halittane na daban".

     "Nagani ai,kema d'in cayai bakisan halinsa ba balle ni".

      " D'an tasha ,baida mutunci fa".

     "Yanzun kin ha'kura de ai?"

      " Kema kinjika Firera da ya zanyi? Inde ta 100k ne na barshi amma wlhy bazan fasa abinda nakeson yi ba harse na cimma burina akansu".

    "Toh madallah".

      Haka sukai sallama bata fasa mita da tsinewa Barr Kamal ba ita kad'ai take ta maganganunta kamar zautacciya.

_________________________

   Amrah ko abinci ta kasa fitowa ta girka tunda ta shige d'aki ga tsoro daya addabeta.Wayarta ta d'auka ta gwada kiran Ummie sede bata samu d'agawa ba daga baya ta kira Mami.Dayake batasan number ba shiyasa ta d'aga ba jimawa.

     " Mami ina yini"Ta gaisheta bayan ta d'aga.

     "Lafiya lau". Ta amsa da alama bata tsunkayo muryar ba.

    " Mami Amrah ce".

     "Toh ya kike?" Taji ta tambaya dan bata zata ba.

     "Lafiya lau".

      " Mami "Ta kira murya 'kasa-'kasa.

      " Na'aam".

       "Dan Allah kiyi ha'kuri ki dena fushi damu".Tayi maganar qwalla na tarar mata a ido saboda wani tunani daya fad'o mata yadda Mami take goyon bayansu lokuta da dama idan sinyi laifi itada Shettima.

    "Idan ban ha'kura ba ya zanyi Amrah ? mutum baya gujewa qaddararsa Allah yasa haka shine alkairi".

     " Ameen Nagode Mami".

      "Ba godiyar ba yaushe za'a zo gaida tsohuwa?"
     
      Wani dudum taji zuciyarta ta buga ,bata jin zata iya d'aga ido ta kalli 'yan gidan balle kuma had'uwarta dashi.

   "Mami kefa ba tsohuwa bace".Ta fad'a tana son share zancen.

    Mami data gano haka ta rabu da ita bata sake cewa komai ba suka d'an ta'ba hira kad'an daga haka sukai sallama ta ajje wayar.Taji dad'i sosai jin muryar Mami da yadda ta sake sukai hira kamar ba abinda ya faru.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now