Chapter 25

542 46 2
                                    

 
    Kamar a cikin mafarki ta soma jinta a jikin mutum ,a hankali ta soma bud'e nannayau idanunta,d'an yun'kurawa tayi zata juya a zabure ta mi'ke bata tsaya a ko ina ba se chan 'karshen gadon ta takure 'kiris ya rage ta wuntsula 'kasa.Ta cure gu d'aya hannayenta zagaye a gwiwoyinta se haki take kamar tayi gudu.

    Shima zaune ya mi'ke yana kallonta "Amrah mene?"

      "Tsorona kikeji kuma sekace dodo"

      "Naga kamar you're not comfortable shiyasa na rufa miki blanket".

     Duk wannan surutan shikad'ai yake abinsa ta'ki ko tankashi".

    Sauka yai daga kan gadon ya kewayo inda take ji take kamar ta zura da gudu,har inda take ya tako ya tsuguna yana kafeta da ido.

    Hannunsa yayi 'ko'karin d'orawa a bayan hannunta tayi saurin zamewa ,hakan yasa ya maida hannunsa baya.

    " Amrah kinsan...."Sekuma yayi shiru yayi guntun murmushi ya mi'ke tsaye.

    "Ha'k'kina neh na kula dake,nasan jiya  baki bacci ba dan haka inaso ki kwanta yanzu".

      Yana fad'in haka ya wuce d'ayan side d'in yayi kwanciyarsa yama juya baya.

    Kallo kawai ta bishi dashi tabbas baida niyyar barin d'akin,shawara ta shiga yi kota koma d'aya d'akin amma kuma tasan nan d'inma da wuya be bita ba.Ita yau ta shiga uku tana so tayi bacci tsoro ya hanata.

    " Kinsan de rashin baccinki ba abinda ze hana koh? you better sleep or else..."Yayi maganar 'kasa-'kasa.

     "Else what?" Ta fad'a cikin ranta.

     Dukda taji tsoron abinda ya fad'a bata motsa daga inda take ba,a haka har gyangyad'i ya soma d'ibanta.

        ________________________ 

      Rahinatu

        Cikin sand'a ta mird'a key ta bud'e 'kofar gate d'in gidansu,tana bud'ewa ta mayar ta rife ta jefa key d'in a jakarta.Cikin sand'a tana ta waige-waige kamar 'barauniya ta shiga cikin gidan 'kofar parlourn ma tana da key a jakarta takalmin 'kafarta ta cire ta ri'ke a hannu ta haye sama tana addu'a kar a ganta.Sede ta tabbata ta shiga d'akinta tukun ta ji sanyi,12:12am ma dare agogon d'akin ya nuna.

    Se lokacin ta fara 'ko'karin cire uban matsatstsiyar gown dake jikinta ko gyale babu.

       Mommy idanta biyu a wannan daren sede tana d'aki yasa bata ganta ba ,hasali ma ita nafilfili take yi tana kai kukanta wajen ubangiji kan al'amarin d'anta.

     ______________________

    Washegari

      6:03am ta farka daga bacci ,tayi mamakin yadda tayi bacci haka mey tsaho ,gefe ta kalla bata ga Kamal ba batasan ma sanda ta zame ta kwanta kan gadon ba a jiyan se yanzu taga hakan.

    Toilet ta fad'a tayo alwala ta yafa babban mayafi tayi sallah dan bataga hijab ko d'aya cikin kayan ta ba.

    Bayan ta kammala azkar ta komo kan gadon ta zauna daga gefe ,side drawer ta duba tana so taga ko zata samu Qur'an a ciki bata gani ba ta d'ayan side d'in tabi nan ma babu gashi ya fashe 'yar wayar tata da ta karanta a nan.

   
    Tashi tayi ta ciro kayan sawa a wardrobe ta shige bathroom.A shirye ta fito cikin atamfa red mey ratsin ba'ki riga da skirt d'inkin ya zauna a jikinta dukda ramar datai ,yanzun ma mayafi ta ciro ta yafa sannan ta tako zuwa mirror,yau kam ba iya mai ta shafa ba har gashinta ta taje ganin comb sabo set iri-iri a cikin drawer.Spray mey taushin 'kamshi ta fesa a jikinta ,kallon kanta ta shiga yi cikin mirror ,ita kanta tana ganin irin ramewar datai fuskar ta d'ashe idanunta sun kod'e fari fat se yanzu ta lura da d'an kunnenta tun na shekaranjiya sar'kar kawai ta cire jiya,ciresu tayi ta sami mara nauyi ta saka daga haka ta komo gefen gadon windown d'akin ta tsirama ido dukda labilen ya rufe kusan rabi a hankali ta taka ta tsaya jikin windown tana hango premises  d'in gidan ,ga flowers a tukane tano kallowa ,jitai tana son fita wajen maimakon hakan seta bud'e windown kawai tana sha'kar iskar wajen,sosai hakan yayi mata dad'i dukda zuciyarta na cike da damuwa ,kujerar gaban mirror d'in ta dasa a wajen tayi zamanta.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now