Chapter 58

585 44 8
                                    


*Not edited*

      _Washegari_

        Yau take lahadi ranar yini kunsan yau ranar mata ce,gida ya sake cika  ana ta hada-hada itade Amrah tun wayewar gari jikinta ya fara sanyi  komai nata da take a sanyaye ita haushi ma 'yan bikin sike bata kowa ta kalla fuskarsa da walwala ba damuwa a tattare dashi wasu ma har zumud'i sike yamma tayi a kai Amarya gidanta.

     Yanzu tana sanye da orange swiss lace met torches golden d'inkin riga da zani an d'auri met step taxa necklace golden ga makeup d'in fuskarta ba chan heavy ba amma tayi kyau sosai.

     Duk inda Ummi tayi tana kallonta tun yanzu ta fara jin kewarta.Tana wannan halin ne kira ya shigo wayarta ,koda ta duba taga angonta neh aiko ta galla was wayar harara a ranta tana fad'in "Kana chan kana murnarka kai".

    Har wayar ta gama rurinta bata d'aga ba daga baya we text ya yo mata.

     _My Baby Allah yasa ba laifi nai ba aka 'ki d'aga kirana? Hope kin tashi lafiya ? Take care ,I love you Amarya ta😘❤"_

      Turo baki tayi ta dungurar da wayar kwalla ta tarar mata a ido.

      
   *** Suma a gidan Mommy suna ta shan wunin su Amare sunsha kwalliya cikin atamfa purple mey rod'in ba'ki da fari sar'ko'kin wuyansu silver.Walida duk rawar kan ya gudu kowacce jiki yayi la'kwas yau de aure zey rabasu da Mommy bacin haka suma zasu rabun kowacce ta fara jin 'kewa.

    Shettima kuwa koh oho yana d'akinsa kamar ba a gidan yake ba hutawarsa yake abinsa yana tunanin sabon shafin rayuwarsu shida matarsa Amaryarsa Amrahansa.

     Ahmad ne ya kirashi ya shiga tsokanarsa jin yace yana gida.

    " Mallam ka tattare komatsanka ka bar musu gida".

     "Mtchw shiri kuma na yaushe ,aini tun yaushe na kwashe komai nawa Kaine de zancen a cigaba da gauranci"

     " Allah ko? Zan baka mamaki neh angon Amrah da duk ka tada mana da hankali yanzu kowa de hankalinsa zey kwanta zamu kai maka ita gidanka yaso ka cinyeta".Ya 'kare maganar yana dariya.

     'Kyit! Ya katse kiran

  
      Shettima yabi wayar da kallo yana murmushi.

       ★★★

    Aunty Hannatu yau kwananta uku a asibiti ciwo ya kwantar da ita ko magana da 'kyar take yi duk wanda ya ganta seya tausaya mata halin data ke ciki,Kawu yaje dubata sau biyu ,ganin Mommy na harkar biki yasa be fad'a mata ba ya basshi a se bayan an gama bikin.

     Ciwon cikinne ya takura mata har seda  wanda take d'aki dasu suka sanarwa da masu tsaronsu dan ita ta'ki fad'a ciwo se cinta yake.Tayi ba'ki ta rame sosai koyaushe idamunta na tsiyayar hawaye tana burin ganin Rahinatu ko sau d'aya ne ta nemi yafiyarta na kashe musu uba da tai sannan tana so tai mata nasiha akan abubuwa da take marasa kyau.

    
    **Kamal kuwa jiya kwana yayi a zaune Mamansa se ha'kura tayi ta tafi d'akinta dan ya'ki cewa komai tamkar bebe.Yau da safe tazo dubashi taga bata samesa ba a ciki, ta dubu bayi baya ciki nan hankalinta ya tashi tana tunanin ko gidansu Amrah yaje.

    Shiko da dukun -dukun safiya ya fita daga gidan be tsaya ko ina ba se gidansa gashi yau ko d'an sahun be hau ba da 'kafarsa yaje gidan.

    Gate d'in ma se 'balle padlock d'in yayi da dutse dan baida key a wajensa ,d'aya 'kofar ma da dabaru ya bud'e.

    Gidan yayi 'kura kuwa alamar ba'a zama ciki,d'akin Amrah ya fara shiga.Nan ba kaca-kaca yanda suka fita suka bar gidan haka yake, fasassun kwalabe a 'kasa.

     A bakin 'kofar toilet ya lura da 'karamar wayar daya siya Amrah wacce kota kanta bata bi ba sanda ta bar gidan.'Karasawa wajen yayi ya dur'kusa ya d'auko ,charge d'in wayar harya 'kare.

   Wardrobe ya bud'e nan ma yaga kayan Amrahnsa a jere ,d'aya daga cikin mayafanta ya ciro ya dawo bakin gado ya zauna.

   Purple d'in gyale ya shiga shinshinawa yana jin ragowar 'kamshin humrahnta da be gama disashewa ba.

    "Amrah". Ya furta sunanta a hankali har cikin zuciyarsa quanarta da rashinta yana masa 'kuna.Tsintar kansa yayi da kwanciya kan gadon ya ru'kun'kume mayafin a 'kirji ya had'esa cikin hannayensa biyu ,wasuzafafan hawaye ne suka fara tsiyayo masa suna bin bayan kunnensa.Nide daga nan na fita daga d'akin saboda tausayin Kamal.😖

       Haka aka 'kare wuni lokacin kai amare yayi,yaran Mommy a llu'besu fuska ana sheshhe'kar kuka musamman Walida rawar kai ta gudu.Mommy kanta dauriya take shiyasa dama tun kafin a fara biki tayi musu fad'an da zatai ,yanzu sallama kawai aka kawosu d'akinta sukai sannan aka fita dasu Sa'adatu ma ta raka'be a bayan 'kofa tana sharar kuka.

    
       Amrah abin ba'a cewa komai ,sanda zasi sallama da Ummi da Appa ta ru'kun'kume Ummi ta'ki sakinta  ,itanma tun kafin biki iyayenta sun mata fad'a.

    Da'kyar ta saketa tsoffin kai Amarya suka fita da ita 😭(Ta bayan fage niko😝😂).

   _*Ke kika ce kina so da ba'ki ce kina so ba da ba'a baki shi ba🎶🎵*_

    Alhamdulillah kowacce an kaita d'akinta se fatan zaman lafiya kuma.

     Mama de tana cikin rikici har wannan lokacin ba alamar Kamal,tana wannan halin ne Hafiz ya kirah,da 'kyar ta iya sanar masa halin da ake ciki ta bashi labarin abinda ya faru jiya.

   Shiya kwanta mata da hankali yace zey sa a duba masa ko yaje gidansa ,nan ne ta d'an samu nutsuwa tana fata Allah yasa hakanne.

      Ashede Shettima za'aji missing d'in Mommy, sanda yazo mata sallama seda yaji ba dad'i sosai dad'inta da akwai su Sa'adatu a gunta.A wani salu'be akai sallamar ta sake yi masa d'an fad'a na ya ri'ke 'yar mutane amana sannan tayi musu fatan zaman lafiya mey d'orewa.
  
      Aunty Mirah harda hawaye tausayin Mommy ya kamata 'ya'ya uku reras yau kowa ya tafi gidansa😖 (Komai yayi farko se yayi 'karshe,Allah yayi mana 'karshe mey kyau {Ameen}).

   ★★★

   Kowa ya tafi ita 'kwal ko Humaira tayi tafiyarta ,fuskarta lullu'be cikin farin gyalen material d'in jikinta doguwar riga fara da torches golden.Kukan ma ta ha'kura ta dena yanzu kuma gabanta ne yake fad'uwa.

     10:02pm taji shigowar mota ,kawai had'iyar yawu take tana jiran taga ya zata kaya kuma a wannan karon ,wancen de tasan daren na daban ne daren da tayi bacci a zaune daren da mari ne ya farai mata welcome a gidan Kamal kodayake wannan bata tsammin hakan amma batasan ya irin wannan d'in yake ba.

    Tunanin ta ne ya katse jin an bud'e 'kofar d'akin ,tunda ba opposite take da 'kofar ba kamar tana adjacent da ita ne bata ganshi ba ta deje motsinsa kafin sallama ta biyo baya.

        *Mu had'u a next page kuyi ha'kuri da wannan banida charge and again zan fita ,nima na matsu na gama.Lots of love😘*
        
      
Dijensy❤

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now