Chapter 11

921 58 0
                                    

    
    ~~~

      Nan da nan AC dake parlour ta fara yad'a gur'batacciyar iskar dake fitowa daga kitchen.Yaran dake parlour suka fara tari abu kamar wasa nan da nan tsofaffi wuyansu ya cika da yaji se tari gashi an rasa daga ina yake.

    Mommy da sakkowarta kenan taji 'kaurin yaji ya bigi hancinta take ta soma tari tana toshe hanci."Meye wannan? "

    Kowa seyace be sani ba cikin sauri tayi kitchen. Walida da Wafah suka shigo parlourn suma tuni suka soma kakari duk wanda yazo parlour seya d'and'ana.

     Mommy na shiga kitchen taga aika-aika,Rahinatu tama fita daga kitchen d'in.Cikin sauri ta kashe cooker gas ta sauke frying pan d'in ta fita dashi chan bayan gida ta bubbud'e windows da Rahinatu ta gar'kame ,banda haya'ki ba abinda kitchen d'in yake ita kanta Mommy daurewa kawai take ta fito se tari take kamar zata amayar da 'ya'yan hanjinta.

    Parlourn ma haka aka yaye labilen aka bubbud'e windows tukun aka fara samun sa'ida ,tsofaffi tamkar wad'anda aka shake sunyi firkai-firkai Mommy tana musu sannu.

    Ana haka sega Aunty ta sakko fuskarta cikeda nuna damuwa kamar batasan wanda yayi ba.

   "Mommyn Shetty mey aka sa haka ?"

    "Barkono na tarar a kitchen kan wuta a frying pan wlhy bansan ko wayayi hakan ba".

    " Subhanallah gasu goggo('Kanwar mahaifiyar Appa) a parlour".Ta 'kare da kallon tsofaffin ,jitai kamar tasa dariya dan yadda taga idanunsu.

    "Sannu goggo" Ta fad'a.

     Goggo gid'a kai kawai take ta kasa ko magana hannunta ri'ke da cup na ruwa se kwankwad'a take.

          -------

   Rahinatu tana komawa d'aki ta shige bayi ta dinga dariya kamar mahaukaciya seda ta gaji ta fito ,da kanta ta fad'awa Aunty abinda tayi.Itama Auntyn dariya tayi maimakon tayi mata fad'a.

     Mommy haka tayi ta tambayar yaran kowa yace bashi bane harta ha'kura ta koma sama.

      Shettima bayan ya shirya cikin dark blue shirt da jeans baki ya feshe jikinsa da turare ya fito zuwa d'akin Mommy.Tun daga 'kofa ya fara hango mutanen dake ciki amma hakan be hanashi 'karasawa ba.Binsu yayi d'aya-bayan d'aya ya gaishesu yana so ya 'karasa wajenta amma kuma ba dama.

   D'an sosa kai yayi tare da fad'in"Mommy.. "

    "Momi bazata zo ba d'in mey zatai maka ana ta jama'a wayake takai ,kaje anjima ka dawo idan ta zama less busy" Sistern Mommy ta fad'a.

    Sauran da suke d'akin ba wanda be dara ba,kunya ma duk ta lullu'beshi ba shiri yabar d'akin Mommy batace komai ba se murmushi da take.

     Tasan dama bawai ya tafi duka bane shiyasa bata damu daya fice ba ,tana fitowa daga d'akin ta tarar dashi ya juya baya yana danna wayarsa.

   "Yaron Mommy"

    Da sauri ya juya fuskarsa d'auke da 'kayataccen murmushi "Mommy kin yada ni,na tashi a gidannan baki tambayi lafiyar cikina ba"

   "Ai nasan iyayen naka dayawa ,nasan Mami bazata barka haka ba"

    "Toh Mami hakan ma yayi,Mommy jiya kuwa kinyi bacci?"

     "Mey kagani?"

     "Ga idonki ya nuna alama kin gaji sosai Mommy ya kamata ki huta"

     "Gajiyar ai ba yawa kuma ma ai mey wucewa ce"

      "Fita zakayi ne?"

       "Uhm zan biya gidansu Ahmad (Abokinsa) naga gidan ya cika"

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now