Chapter 33

548 45 2
                                    


     Sak tayi tsaye a wajen tana kallonsa a ranta tana fad'in shikenan ya d'arfo ni.

    Murmushi ya sakar mata yana dubanta daga sama har 'kasa yadda ruwan yake ji'kata ga rigarta da ta manne a jikinta ta bayyana shape d'inta na ko'ina.

  Bata ankara ba taji ta fad'o jikinsa kanta a 'kirjinsa ya zakaye hannayensa biyu a ku'binta ,dede saitin kunnenta ya rad'a mata "Mun samu lafiya kenan"

   Gabad'aya tsigar jikinta seda ta tashi dad'i da sanyin ruwan saman wanda da bataji se yanzu.

    "Wasan ruwan ya isa haka koh?"

    Itade tayi tsuru-tsuru ta kasa fad'ar komai ,hannunta cikin nasa suka shiga gidan gwiwoyinta sunyi mugun yin sanyi kawai binsa take.Gefen gadon d'akinta ya zaunar da ita tana zaunen ya d'akko towel se gani tayi ya zame yalolon mayafin kanta  ya d'ora towel d'in yana goge mata gashinta ribbon d'in dama sakwa-sakwa ne tuni ya zame gashinta ya sakko kafad'arta.

     Hannunta ta d'ora kan towel d'in tana so ta janye."Zanyi da kaina"Ta fad'a cikin siririyar murya.

    "Ai nasan kin iya d'in ni nace zanyi Mrs Kamal"

    "Ko ba ita bace?"

   Shiru tayi ta'ki amsawa a ranta tace"Ba ita bace wlhy".

   Zimbir ta mi'ke  "Zan sauya kaya"Ta nufi jikin wardrobe ta ciro doguwar rigar bacci mey kauri har 'kasa mey dogon hannu.

   " Aiki nane ai "Taji ya fad'a.

    A wani rikice ta juyo tana zaro ido ga tsoro sabo daya shigeta.

    "Ka bari kawai".

     " Toh sekin bani amsar tambayata".

    "I'm waiting.."

     "Itace". Tana fad'a ta shige bathroom.

    Ruwa mey zafi tayi wanka dashi sannan ta zira kayanta ta tsaya jikin 'kofa tana tsoron fitowa ,seda taji alamar rufo 'kofa tukun ta fito,turare kawai ta fesa a jikinta bayan ta shafa lotion dama ta d'aura alwala ta gabatar da sallahr isha'i.
     
    Tana kan dadduma ya shigo d'akin hannunsa ri'ke da tray,shima ya sauya cikin pjamas ash colour,wannan turaren de datake jin 'kaurinsa yanzunma shi ya mamaye hancinta.

    Gefen drawer side ya ajje ya tako inda take " My Amrah dinner".

    Bata ce komai ba ta mi'ke tsaye babban mayafin datai sallah dashi bata cire ba ta 'karasa.

     "Wannan fa". Yayi  pointing mayafin.

   Ba shiri ta cire kar ai irin ta rannan,da kanta taci abinci  lokacin ya fita tayi tunanin ma baze dawo ba taga ya sake shigowa.Kafin ta mi'ke ya zauna daga gefenta hannunta ya ri'ko yasa a nashi yana murza yatsunta." Amrah"Ya kira sunanta da wata irin tattausar murya da be ta'ba yin irinta ba.

    A hankali ta d'ago ta dubeshi "I Love you " Taji ya fad'a.

    Mayar da kanta tayi 'kasa zuciyarta na bugawa.

   "Amrah ke kad'ai ce macen dana fara so zuciyata ta aminta da ita ,da farko nayi tunanin 'karya zuciyata take min amma naga ba hakan ba.A kullum a kodayaushe kina sake shiga raina ,nasan ba lalle ne ki yarda da hakan ba and kinada reasons akan hakan.I hurt you before Amrah because I was stupid, jealous Amrah I truly love you ,ina so ki yafen abinda nayi miki a baya.I promised to change ,bazan sake hurting d'inki ba bazan bari wasu siyi hurting d'inki ba,bazan sake yin abinda bakya so ba.Amrah believe me or not ke kad'ai nake so a duniyarnan and I promised to love you forever Amrah ,kiyi ha'kuri ki yafemin abinda nayi miki bazan sake ta'baki ba da niyyar cutar dake.I am begging you to love me back please Amrah don't say no munada lokaci munada dama,inaso mi gina rayuwarma da farantawa juna da qauna Amrah please love me".

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now