Chapter 23

498 36 0
                                    

      Seda tayi mey isarta tukun ta lafa da kukan,duhun d'akin ma kad'ai ya isheta ga zama banda yunwa dake nu'kur'kusarta ko motsi tsoron yi take,tana zaune inda take.Yadda taga rana haka taga dare ko gyangyad'i.

    Ta nisa cikin tunane tunaninta wanda basa 'karewa ta had'a kai da gwiwa.Hasken dataga ya mamaye d'akin yasa ta saurin d'agowa.

    Suna had'a ido ta sunkui dakai ,a wani wula'kance yake kallonta kafin ya tako zuwa inda take.

    "Tunaninsa kike ko?"

     "Zakiyi bayani dalla-dalla"

    Wucewa yayi tana binsa da kallo ya bud'e 'kofa ba ta jiya da ya shigo ba.Minutes later taga ya fito da alama alwala yayi,tana so taga ya fita amma se gani tayi ya shimfid'a dadduma a d'akin ya tada sallah.

    Bangon d'akin ta soma kalla ko zata ga agogo,5:08am ya nuna agogon d'akin.Tayi tunanin ko zeje masallaci amma taga ba hakan ba.

   A hakan tana zaune ya idar."Ko sena miki alwalar?"

     A hankali ta mi'ke 'kafarta da tayi tsami da'kyar take takawa,tana tafiya yana binta da kallo har ta shige toilet d'in.

    Kallo d'aya tayiwa kanta a mirrorn dake toilet d'in ta d'auke kai,ita toilet d'in ma a manage tayi amfani dashi  dan tana sauri tayi alwala  ne.

    Koda ta fito bata sameshi a d'akin ba gashi ya d'auke daddumar dan haka ta shinfid'a d'ankwalinta.

       Harya shigo tana kan d'ankwalinta tana addu'oi ,ta'be baki yayi ya wuce ya zauna daga gefen gadon yana kallonta komeh ya tuna yayi murmushin gefen fuska.

        "Waliyyiya ya isa haka ,kai 'karan ya isa kuma"

     Yitai kamar batajishi ba ta'ki sauke hannunta ,tana jinsa hadda guntun tsaki dukda haka bata ko motsa ba kuma bata fasa addu'ar ba.

     Seda ta 'kara kusan 15min tukun ta sauke hannunta.

   "Ke haka aka koya miki kula da miji?"

      "Ina kwana " Ta fad'a can ciki-ciki.

     "Haka ake gaida mutum kin juya baya d'in? Kin ko san mey aure yake nufi?"

     Tana jin alamar ya mi'ke zuciyarta ta soma bugawa ganin ya wuceta zuwa toilet tayi ajiyar zuciya.

    Kamar wacce aka sassa'ka a wajen ta kasa mi'kewa har ya fito ,ganin daga shi se towel daga waist to down tayi saurin sauke kanta 'kasa.

  Murmushin gefen fuska yayi ya wuce wajen wardrobe harya bud'e sekuma ya waigo ya kalleta har yanzu kanta a 'kasa.Komawa yayi gefen gadon saitin mirror ya zauna .

    "Amrah wife" Taji ya kira.

    "Ke ba magana nake miki ba"Ya fad'a ganin ta'ki responding.

    A sanyaye ta mi'ke tsaye ta'ki juyowa ta kallesa.Da kanshi ya mi'ke ya 'karasa inda take ya ri'ke hannunta har gefen gadon ya 'karaso da ita ya zaunar ,lotion dake kan mirror ya d'akko ya ajje kan cinyarta kafin ya zauna daga gefenta very close.

    "Shafa min" Ya fad'a ba alamar wasa.

    Da'kyar take had'iyar yawu tana kallon lotion d'in ko sa hannu ta d'auka ta'ki yi.

    "Taurin kai koh?"

     Jin furucinsa yasa ta d'auka da hannu biyu ,jujjuya man ta soma yi ta rasa ta ina zata soma.

    "Kina 'batan lokaci"

      Cikin sanyin jiki ta bud'e ta matso a tafin hannunta  idanunsa a kan tafin hannunta dake d'auke da jan 'kunshi.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now