Chapter 7

947 83 4
                                    

    Tana jin sanda ya shigo parlour Ummie tana tambayarsa su Mommy,tama tsaya ta kasa ko zama ta rasa mey yake daminta bugun zuciyarta se 'karuwa yake musamman idan taji yayi magana fatanta Allah yasa  karya tambayeta.

     Bata idda wannan batu ba Ummie ta 'kwala mata kira "Amrah mey kike a d'akin ga Shettima yazo ?"

    Har cikin tsakiyar kanta taji kiran ,a hankali tace "Na'am,ganinan".

    Anfi minti 10 bata fito ba seda Ummie ta kuma kiranta,seda ta kalli jikinta a mirror haka kawai taji kunyar kayan jikinta riga da skirt na atamfa wanda yake dede jikinta skirt d'in yayi fitting d'inta ga rigar tayi chif da jikinta d'aurin kam step step ne aiko a take ta ware kar ace tayi kwalliya,mayafi mey kauri ta d'auko a wardrobe fari ta d'ora kan green d'in atamfar ta fito se sunkuyar da kai take ,ko kan kujerar ta'ki hawa a 'kasa ta zauna daga bayan kujerar kad'an ake hangota a yayinda Shettima yana adjacent da inda take shima kan dadduma ya zauna." Tunda ta fito be sauke kansa ba Ummie ma ita take kalla yadda tayi kamar wata sabuwar Amarya.

    "Sannu da zuwa ,ina yini" Ta fad'a a hankali.

    Shi gabad'aya mamakin yadda 'kibarta ta 'bace yake kamar ba itace timemiyarnan ba"Lafiya lau"Ya amsa cikin cool voice d'inshi da bata sani ba se yanzun.

   "Jibi yadda ta wani du'kun'kune wai ita saliha Allah ya shiryeki" Ummie ta fad'a.

   Jitai kamar ta nitse dan ba 'karamin kunya Ummie ta bata ba.Ummie ce ta tashi zuwa kitchen domin d'akko masa abun sha.

    Befi seconds da fitarta ba Shettima ya soma magana"Amrah nid'in kike rufewa fuska kamar wani ba'ko?"

    Yayi zaton ko zatai magana amma yaji shiru hakan yasa yace"Bade kunyata kike jiba idan ma haka ne ki bari danni yau anan zan kwana"

    Dukda bata gasgata zancen ba seda taji wani irin a ranta hannunta duk ya had'a gumi se murza yatsunta take kamar zata karya ashe ya gani."Karki 'balle d'an yatsa ki janyo mana asara"

    'Kam ta tsaya da abinda take jin Ummie ta shigo taji sa'ida a hankali ta mi'ke ta shige d'aki,Zo'bo mey sanyi ta kawo masa da ruwa mey sanyi se gurasa da miya.

    "Au d'akin ta koma?" Ummie ta fad'a bayan data ga bata wajen.

    "Ehyi ta koma d'aki".Ya fad'a.

    Duk tsahon lokacinda ya d'auka bata kuma fitowa ba da zo'bon kawai yasha Ummie tace seyaci gurasar shine yaci kad'an amma har lokacin bata fito ba kira da Mommy tayi a waya yasa kawai ya tashi zey tafi.

    A 'kofar gidansu ya tsaya yai dialing number Amrah ko zata d'aga amma ta'ki badan yaso ba ya tafi gida.Yana tafiya Amrah ta fito parlourn har lokacin 'kamshin turaren daya mamaye parlourn be gushe ba ,wannan 'kamshi ya mata dad'i ba irin turaren data sanshi bane da (Lokacin ana 'kwailaye😂)

     " Mey kika fita yi kuma tunda baki iya zama a gaisa ba ai shikenan ,daddawar d'aka".

    "Kai Ummie, kin bani kunya d'azu wai ina sunkui dakai .."

     "Ai gara na baki kunyar mutum yazo gidanku ai kya gaisa dashi ko yau kika ta'ba ganinsa balle kuma ba ba'ko bane sekace wata ba'kauyiya"

    Baki a cune ta fita daga d'akin ta koma tsakargida ta zauna kan kujera tana buga temple run d'inta.

    4missed call notification ya nuna ,ita kanta ba'a son ranta take 'kin d'agawa ba tana son jin muryarsa amma bazata iya hira dashi ba..

     ★★★

  Mommy tana d'akin ta sega knock d'insa "Shigo " Ta fad'a.

    "Ina kaje kaiko?" Mommy ta tambaya.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now