Chapter 30

658 53 0
                                    

      Tun daya shiga d'aki ya kasa samun kwanciyar hankali hankalinsa ya sake d'agawa fiye da na daga baya ya  fad'a bathroom ya tara kansa  a shower  ruwa mey sanyi yana ratsa ilahirin jikinsa ,the more yana tuna abinda Hannatu ta fad'a the more zuciyarsa na sake quntata duk yadda yaso ya kawar da tunanin ya gagara yin hakan seda ya shafe kusan 1hr yana ji'ka kansa da shower kan ya fito.

    Shirt fara ya saka da ba'kin jeans ya d'akko laptop d'insa cikin sauri-sauri ya samu ya cire password d'in haka wayarshi ma ya cire ,  password d'in ,jikin fuskar gadon ya jingina bayansa idanuwansa a rufe qwaqwalwarsa ta cika da tunaninnika kansa ba abinda yake se sarawa ,ganin zama haka cikin tunani baze amfana masa da komai ba ze zallar 'bacin rai ya soma kiran sunayen Allah ko ze sassaucin rad'ad'in da ke zuciyarsa.

      Wuni guda cir be sake sakkowa 'kasa ba balle cin abinci.

     ****
Washegari

      Aunty Hannatu da wuri tai shirinta tana yi tana kallon lokaci koda ta tashi fita setayi wa Mommy 'karya tace dubiya zata asibiti.

     Ko neman driver ya kaita batayi ba saboda takatsantsan ,bayan mey d'an sahu ya sauketa a wajen da zasu had'u ta sallameshi nan ta soma raba ido tana so taga Barr.

    Ganin ta shafe 15min yasa ta d'auko waya a jaka ta danna masa kira.

   "Barrister nifa harna isa wajen ina jira" Ta fad'a ganin ya amsa kiran.

    "Yanzu haka ina kallonki Hajiya Hannatu".

    " Daga ina kenan?" ta cigaba da kalle-kalle dan wajen ba wani mutane se motoci dake wucewa suma d'in jefi-jefi.

  "Nan". Taji muryarsa a bayanta.

   Da sauri ta waiwaya taganshi tsaye wayar a kunnensa.Wani murmushi ya sakar mata wanda shi d'aya yasan ma'anarsa.

    " Aff,aini ban kula ba".

     "Nagani ai". Ya fad'a a ta'kaice.

      D'an kallonsa tayi tana so taga ta ina kud'in nata zey bayyana,ya gano haka saboda haka yace." Minti d'aya"

   Be jira ta fad'i wani abun ba ya nufi inda yayi parking motarshi,nan ya bud'e 'kofa seconds kad'an taga ya dawo hannunsa ri'ke da bundle na kud'i.

    Ta 'kagu ya mi'ko mata ,yana 'karsowa inda take ya d'ago da kud'in bawai yana mi'ko mata bane a'a wani kallon wula'kanci yake musu yana jujjuyawa tamkar yana so ya gano wani abu gameda kud'in.

    "100k shine a matsayin ladan aikin Barr Kamal".Yayi maganar tare da yin gajeran murmushi kafin ya had'e fuska kamar be ta'ba murmushi ba a rayuwarsa.

    Kallonsa ya mayar kanta ya soma magana " Daga ranar da kika d'auki wannan abun da kika kira kud'i kika bani a matsayin aikin da zan miki na tabbata cewa bakisan waye ni ba,a tunaninki saboda su nayi miki aiki yadda ya kamata  akan wannan "Ya 'kare maganar yana karkad'a bundle d'in.

   Galolo take kallon kud'in take kallonsa, cigaba da maganar da yayi yasa ta kasa bud'e baki tayi magana.

   " Ko ita 'kawar taki bata gama sanin ni waye ba,gashi batasan bata sani ba kuma. Tsak ..tsak...tsak  a cikin 100% only 0.99% kad'ai nake jin ta sani gameda ni which is very poor".

    "Kud'inki ba abinda zey tsinanamin saboda haka duk wani abu da kika ga nayi ganin dama tane kuma badan kince kinaso nayin ba nayi ,ni kad'ai nasan dalili na".

    Ganin yanzu ya tsaya da maganar ta bud'e baki ta soma nata maganar." Ina so nasan meyasa ka sake tsaya masa har aka sakeshi"

    "Uwata idan kika sha'keni zaki samu amsar tambayar ki kinji". Yana 'kare maganar ya zira hannunsa a ajihun suit d'insa ya zaro lighter.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now