Chapter 9

869 73 0
                                    


    Yau take laraba Aunty Mirah ta dawo gida Amarya ansha gyara duk yaran gidan basanan suna makaranta se Rahinatu kada'ai itama tana 'kuryar d'aki.Gabad'aya yanzu ta sake sauya taku parlorn ma da take d'an zama ta dena ,Shettima kuwa totally ma ta dena masa magana Mommyn ma setaga dama, dan gaisheta ma yanzu bayi take ba.

     Aunty Hannatu ma har yanzu fushi take da Appa shima hakan ta bashi ha'kuri ma ta'ki,duk wannan abun da ake Mommy bata sani ba.

     ***

      Shettima daya shigo d'akin Mommy ya tarar da ita da Aunty Mirah.

     Baki ta rufe tana fad'in "Wa nake gani Mommy yaushe kika samu wannan a gidanki?"

     "Amarya Auntyn mu irin wannan glowing da kike idan a hanya na ganki ai bazan gane ki ba,duk hubbu hayatin akewa wannan adon?"

     "Idan bakai hakan ba banace Shettyn Mommy bane"Ta fad'a tana dariya suma dariyar sukai.

    Hira sosai sukai, harsu Wafah suka dawo daga school,suma sosai sinyi murnar dawowarta nan suka cikawa kowa kunne da maganar bikin har Shettima ya gaji da hirasu ya koma d'akinsa.

     Tunda ya koma d'aki yaji ba abinda yake son ji kamar muryar Amrah da da hali ma gidansu zeje yasan ba lallai ta fito ba.

   Wayarsa ya d'auka  ba tareda 'bata lokaci ba yai dialing number d'inta a ransa yana addu'a Allah yasa ta d'aga.

    
      Tana kitchen ta gama had'a miya tana jira ta 'karasa ta sauke tajiyo 'karar wayarta.Cikin sauri ta tafi d'aki kafin ta kaiga duban sunan wayar ta tsinke.Sunan data gani yasa taji dudum,a lokaci guda tana son jin muryarsa haka ta wani 'bangaren tana jin kunya.

     Tana wannan batu wani kiran ya sake shigowa nanda nan hannunta ya had'a gumi se shawara take 'eh' ko 'a'a',rufe ido kawai tayi ta d'aga.

    Seda akai 'yan sakanni tukun tace" Assalamu Alaykum".

      Tun kafin aje ko ina ma muryarta ta gama tafi da zuciyarsa balle kuma su dad'e suna hira.'Sekace ba Amrahn daya sani ba.'Yayi tunani a ransa.

     "Waalaikisallam" Ya amsata.

     Wayar na ri'ke a kunnenta da hannu d'aya haka d'ayan ta d'ora kan lips d'inta se mirzawa take tana jin d'ari-d'ari ko zama ta kasayi.

    Jin ya tambayeta ko ta gane mey magana ta sake rikicewa ,na farko de tana jin kunyar idan ta amsa da eh zey tambayeta tana da number sa tasan 'eh' itace amsar amma 'how'

   "Amrah??"

    "Uhh...A'a" Ta amsa.

     "Allah sarki ni, number tawanma ashe bata samu guri ba a wayar taki" Taji ya fad'a a ranta tace"Niko nake da number ka" murmushi tayi data tuna yadda ta samu number.

     Wani lokaci dataje gidansu tana zaune Mami tayi waya da shettima harta gama ,ganin Mami ta shiga bayi tayi sauri ta d'auki numbersa duka biyun da wacce yake amfani a Dubai da Nigeria. A tunaninsa bata da numbers d'insa.

     Katse mata tunani yayi da fad'in "Shettima ne wannan abokin naki ko kin manta?"

   "Na gane" Ta amsa.

   "Yanzu za'ai saving number d'in tawa?"

    "Uhm"

     "Da wane sunan  za'ai saving?"

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now