Chapter 70

1.1K 66 5
                                    

*Last page*

"Sadaukarwa ga dukkan makaranta wannan littafin*

~~~

Tunda akai hutun makaranta ba zaman lafiya kullum kokaye_kokaye Amrah idan bakinta ya gaji tayi musu shiru wani sa'in harda autarta ake had'awa a daka seta tsawata ko ta had'asu ta hukuntasu.Yanzun ma tana d'aki tana jiyosu a parlour se hayaniya suke ana chachar baki Fauzan da Farhan sun had'a kansu shiko Aasim shi kad'ai ba d'an uwa ,fad'an ma akan game ake musu ya kaure.

"Banzaye kawai da'ki'kai mazu zuwa na 15 a cikin su 20".

" Kai kuma dolo ba banzan Fauzy ('Yar gidan Walida) ma zaneka take tana 'kanwarka d'in".

"Sena fad'awa Papa wlhy kuna yi masa rashin kunya".Zarah tasa baki.

" Dawa kike?"Cewar Farhan.

"Da ku nake".Tana amsawa ta gudu sama suka bita a million Humaira kuwa wasan 'yan tsanarta take ita bata fiya hayaniya ba.

D'akinsu ta shige ta gar'kamo 'kofa Amrah tana jiyosu da bugun 'kofar ya isheta ta fito." Yayi kyau ku 'balla 'kofar se kuji dad'i"

"Mamah Allah zaginmu tayi". Cewar Farhan.

" Zagi?".

"Eh". Suka amsa a tare.

Tana daga d'aki tace "Wlhy 'karya suke".

" Kin bud'e ko sena shigo!"Ta tsawata mata.

Shettima da yanzu ya shigo gidan ya tarar da Humaira ita d'aya tana wasanta."Papa sannu da dawowa".Ta fad'a tana takawa zuwa inda yake.

"Yawwa Humay ina sauran?".

" Fad'a sike yi suna d'aki".

Kai kawai ya girgiza ya shawo gajiyar aiki ya dawo gida zey huta kuma ya had'u da wata hayaniyar.

"Dawa dawa ye suke fad'a?" Suka jiyo muryarsa.

"Zaginmu tayi". Suka had'a baki.

" Ita wa?"

A tare suka amsa ,jikin 'kofar ya 'karasa."Mommyna fito".

"Papa Allah 'karya suke min".

" Eh naji ki fito ai za'a banbance mey gaskiyar da mey 'karya".

"Allah ya kyauta". Amrah ta fad'a ta wuce hanyar d'akinsu.

Da'kyar ta bud'e 'kofar suka sauka 'kasa akaje jin sheda a wajen Humaira ta fad'i yanda akai kuwa duk wasan datake d'azun tana sane da fad'an nasu,shi wanda aka fara fad'an dashi ma yana d'akinsu.

Seda aka gama al'kalancin kuma suka tuna yau yace musu zey kaisu gidan Mommy tunda sunzo itada yara banda Doctor da Imran daga su Husna se Abdallah chewing gum d'in Mommy baya ta'ba yarda ta fita wani wajen bashi.

Dukansu suka shirya suka rankaya gidan Mommy a motar ma basu bar bakinsa ya huta ba komai aka gani a kan hanya se anyi jawabi.

Sanda suka isa gidan a parlour suka tarar da Mommy aiko Abdallahnta yana zaune kusa da ita ya d'ora kansa a cinyarta se kukan shagwa'ba yake hancinsa ya toshe sakamakon mura da yake yawanci inde suka zo 9ja se mura ta tashi.

Sallamar 'yan jikokinta taji sun shigo Shettima na biye dasu a baya idonsa ya sauka kan Abdallah.

" Kai gwarjeje dakai d'in kake wani kwanta mata a cinya? Tashi". Shettima ya d'ala masa duka a cinya.

"Mommy". Ya kira ta yana kwa'bewa.

" Mura yake".Cewar Mommy.

"Dan yana mura wani ciwo ne? Ku bashi tuwo yaci ya mi'ke".

" Karde kace komai aha"Mommy ta fad'a tana murmushi.

Shettima yasan mey take nufi kuma ya tuna dan haka ya murmusa "Ga sunan Mommy kwana biyu jal zasi miki".

" Mommy muna ta gaisheki baki amsa ba".Zarah ta fad'a.

"Daga nesa ake gaisuwar ?ai 'karasowa zakui nan".

"Atoh sunga wannan 'katon ya kankane wurin da zasu zauna".

Abdallah kamar besansu ba suda suke kusan sa'anninsa yayi banza dasu nan shi takansa yake,suma kuwa 'kyalesan sukai suka zo wajen kakarsu suka gaisa daga baya su Husna suka sakko suma suka gaisheda Shettima su Humaira suka bisu sama.

Shikad'ai ya komo gida sa'kayau ya dawo ya iske matarsa data sauya wanka ta kashe kala.

" We're free se sinyi week zan d'akko su daga nan ma ba nan zasu dawo ba gidan Ummi zan kaisu.(Ummi da suma Shettima ya gyara musu gidansu an sauya fasalin ginin gidan ya sake fitowa ,daga gombe an bata yarinya tana ri'kewa Dan zaman shirun yana isarta)".

Tana tsaye a jikin mirror ya 'karaso inda take d'in tana kalloshi ta mirror.

"Baby yaushe rabon da kice min I love you? Ina ga fa tun satin daya wuce shi d'in ma dan na siya miki gift ne".

" Ko d'azu seda na fad'a maka sanda mukai waya kana office".

"Da gaske? Na manta". Yayi maganar yana hugging d'inta ta baya ta mirror suna kallon juna.

" Kode ka fara rikicin tsufa?"Ta juyo tana facing d'insa tana kasheshi da kallon qauna.

"No, I'm still Shettyn Mommy da kika sani nada ".

"Uhnmm".

Matso da ita yayi numfashinsu yana had'ewa yakai bakinsa saitin bakinta tasa tafin hannunta ta rufe kiss d'in ya sauka kan hannu".

Gira ya had'e cikeda tuhuma tana murmushi tace." Daka shigo kace nayi kyau?"

"Toh ai tukuicin zan baki kika kare".

" Really? "

"Yes ,ban fad'a maki kodayaushe ked'in kyakykyawa bace? kina a haske ko duhu a ko'ina you're always beautiful my starlight".Yana maganar ya sauke hannun nata a karo na biyu ya sunkuya zeyi sumbaceta bata kare ba sema 'karawa miya gishiri🙈

*ALHAMDULILLAH*

*Ina wa Allah godiya daya bani ikon Kammala rubuta littafin TAGAYYARA,abinda na rubuta ba dede ba Allah ka yafemini.(Ameen) ina fatan an anfana da abinda me ciki*

_*Godiya ta musamman gareku my ppl baza ta'ba dena qaunarku ba ,nagode da comments da addu'oinku Allah ya had'a fuskokinmu a gidan Aljanna tare da ku da readers da sauran fans ma da bansan ku ba.Lots of love.😘*_

Special thanks to;

*TAGAYYARA FANS GROUP*

*DEEJA ONE LOVE NOVEL GROUP*

*BBC HAUSA NOVEL GROUP*

Ban mance daku ba Wattpadians saboda ku na sake editing wannan page en bansan ya zan misalta muku yadda nake jinku ba amma ku sani ina tare daku a ko'ina a kodayaushe💕💗😘

aysherudahmad ina mi'ka godiya ta musamman gareki💕💕

Dijensy❤




TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now