Chapter 26

489 44 0
                                    

 
     Yayi kusan awa d'aya yana abu d'aya daga bisani ya zaro wayarsa aljihu ,contact ya shiga scrolling nan ya tsaya kan number Kawu take yayi dialing....

    Jin alamar kamar ya bar wajen ta mi'ke da'kyar zuwa yanzu ta dena kukan se ajiyar zuciya.A hankali ta bud'e 'kofar taga wayam baya wajen ,a gajiye ta lumshe ido tana had'iyar yawu ta rufo 'kofar ta dawo ciki.Toilet ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta dawo kan gadon ta zauna ,zaman ma be mata dad'i ba dan haka ta zame ta kwanta a 'kudundune ta 'kan'kame jikinta wani sanyi sanyin zazza'bi na ratsa jikinta.

     _____________________

   
    Kawu yana zaune opposite dashi suna facing juna,bayan sun gaisa ya dubeshi kafin ya soma magana.

    "Shettima" Ya kira sunansa.

    "Uhmm" Ya amsa.

     "InshaAllah ka kusa fita daga wajennan".

   Murmushin gefen fuska yayi  a kasalence, dan gani yake ma kawai 'bata baki ne yin maganar.

    " D'azu Barrister Kamal ya kirani yake fad'a mini yana so ya sake samun had'inkai domin kareka a karo na biyu".

    Shiru yayi na 'yan seconds kafin yace."Kawu nifa a bar wannan maganar duk abinda zey faru ya rigada ya faru ,qaddarace bazamu iya chanjawa ba kuma maganar sake shiga court ni bazani ba"

    "Mey kake fad'a haka ai mun sani dama qaddararce tasa ka shiga wannan halin kasan mey Allah ya tanada maka anan gaba meyasa zaka ce bazaka ba bacin kasan irin halinda 'yan uwanka suke ciki"

    "Kawu..."

    "Kodan mahaifiyarka Shettima". Kawu ya fad'a.

     Yasan fad'in haka dole zeyi masa tasiri shiyasa ya 'bullo masa ta haka.Daga haka yayi shiru be sake musu ba hakan yasa Kawu ya gano ya amince.

     _______________________

      2 days later

        Court ta saka ranar da za'a sake gabatar da shari'a,ana e saura kwana d'aya 3 month su cika ,deadline kenan.

     Amrah ba abinda ya sauya koyaushe tana d'aki ,yanzu de ba sosai yake tayar mata da hankali ba dan kullum ma seya fita yana dad'ewa be dawo gidan ba.Tana yin girki da kanta sede baya ta'ba ci koda kuwa ta ajje masa a dinning,gashi yanzu baya shigowa d'akinta tun abinda ya faru rannan dan haka ta d'an sake jiki tana yin bacci ba fargaba sede maganar al'kawari wanda batada tabbacin ma zey cika dan haka ta barwa Ubangiji koyaushe cikin addu'a take da tashin dare.

     
     ***

     Barr Kamal da shirinsa  ya isa zuwa court ,yau zey cika al'kawari duk wasu hujjoji da zasi amfani tuni ya gama tanada,Amrah duk wannan abin da ake batada labari.

      Kaida ka ganshi kasan da seriousness a tattare dashi ba kamar waccen lokaci ba,yau a cikakken lawyernsa yazo wanda ya 'kware a sanin makamar aiki.

    Cikeda 'kwarewa da tsari ya dinga zayyanowa court evidence,hujjoji 'kwarara.

    Marigayi Alh mansur bisa ga bincike da akayi an gano ya rasu ne ta hanyar shan fura dake d'auke da poison a ciki.Marigayi Alh mansur ya kasance a dukkan 'karshen ma'kwanni yana zuwa gidan gona wanda yake mallakinsa ,Fura da nono yana daga cikin abin shansa wanda ya zame masa sabo duk lokacinda ya 'kebance a gidan gonarsa 'yan Fulani(Masu tallan kindirmo kenan) suna zuwa talla gidan gonar.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now