Chapter 38

443 50 0
                                    


        Yana cikin motarsa dake fake gefen haya tun a daren jiyan daya fito be san ina ya nufa ba chan bayan gari ya tsaya.A idonsa gari ya waye Allah yasa ma yana da ruwa a motar harma da abin sallah nan ya fito waje ya gabatar da sallah ya koma mota yana mamakin kansa yau shine ya kwana a waje ba'a gida ba jikin kujera ya jingina kansa idonsa a rufe yana tunana makirci irin nasu yayi regretting ma daya shiga shirginsu da beje d'akin ba da hakan be faru ba ,ina ma komawa yayi ba ficewa daga gidan ba, ya rife su da duka duk abinda zey faru ya faru sam besan 'kiyayyyar tata takai haka ba meyasa Mommy bazata gane sharrinta ba?

   'Karar sa'ko daya shigo wayarsa ya katse masa tunaninsa ,kamar baze bud'e ido ya dubi wayar ba daga baya ya d'auko wayar ya shiga duba sa'kon ganin daga Mommy ne yasa ya gyara zama.

    _Bana son sake ganin ka tako 'kafarka zuwa inda nake,idan ka kuskura ka dawo ba abinda zey hana na tsine maka wlhy_

    Kamar wanda aka cirewa laka haka ya mayar da wayar ya ajje ,shi meyasa sa'ko mey kyau baya ta'ba zuwar masa?

     Nanata 'karshen sa'kon yayi tayi  bugun zuciyarsa na 'karuwa da sauri-sauri numfashinsa na fita sama-sama "Hasbunallahu wani'imala wakil" Ya shiga maimaitawa saboda halin daya tsinci kansa kwata-kwata numfashinsa dayake shigarsa baya wadatar dashi ,kansa ya jingina a kujerar yana fitar da numfashin ta baki.

     Anya ma bata riga da ta tsine masan ba? Shikuwa in zey  tsindima ransa a duniyar nan wayake da ita wacce ta fita ,fata yake idan mafarki ne ya farka.Ya shafe kusan sa'oi biyu ba tare da yasan mey zeyi ba kuma ,yasani inde ya sanarwa da kawu halin da ake ciki toh kuwa dole zey mayar dashi gidan wanda baze kuskura ya bari hakan ya faru ba daya koma gida Mommy ta tsine masa gwara ya 'kare rayuwarsa a waje.

       ***

   A kitchen Aunty Hannatu cikeda annashuwa take had'a breakfast zuciyarta wasai duniya tayi mata dad'i.Bayan ta gama girkin seda tayi breakfast d'inta ta had'a a tray ta nufi d'akin Mommy.Walida da suka sakko suka tarar da Rahinatu a dinning d'in ita kad'ai ke breakfast d'inta a wula'kance take binsu da kallo.

    Ita sam Walida batada niyyar sake tambayarta amma Wafah ta kada baki dan ta damu taji abinda ya faru jiya."Dan Allah ki fad'a mana meya faru jiya da daddare?"

    "Ko na fad'a muku zakuyi wani abu akai ne badan Allah ya taimake ni ba da tuni ya cuci rayuwata ". Ta fad'a fad'a-fad'a.

   " Shiwa kenan?"Cewar Walida.

     "Yayanku mana tsabar lalacewa ya rasa wa zey lalata se 'kanwarsa ,ni yaso yiwa fyad'e jiya". Tana 'kare maganar ta wancakalar da cokalin hannunta ta bar wajen.

    Baki a sake suka bita da kallo a take 'kwalla ta zubo daga idon Wafah.

    " Yaya Shettiman?"Walida ta fad'a zuciyarta bata gasgata ba.

    Shiyasa Mommy ta rufe 'kofarta tun jiya ,shine dalilin dayasa ya fita be dawo ba kenan har safiya.

    "Walida kinji mey tace kua?"

     "Naji 'karya take Yaya Shettima ba d'an iska bane wlhy".

    " Ke amma Mommy dashi jiya daga d'akin fa suka fito".

     "Koma meye sharri ne Allah bakusan makircin Rahinatu ba gafa irin 'kawayen datake kulawa".

    " Nide tashi muje wajen Mommy "Wafah ta  nufi sama itama Walidan binta tayi sede lokacin da suka je Aunty Hannatu ce a d'akin dian hakasuka koma 'kasa.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now