Chapter 50

789 57 0
                                    


  _Washegari_

         
        Da wurwuri ya kammala shirinsa seda ya fara zuwa d'akin mahaifiyar tasa ya gaisheta kamar yadda ya saba sannan ya duba d'akunan yaran duk cikinsu ba wanda ya tashi kasancewar yau d'in Saturday babu school dan haka ya wuce asibiti dama ba breakfast ya fiya yi ba a gida.

      Yau d'in a yadda ya saba ranar weekend baya fita da wuri amma sam ya kasa samun sukuni ,jiyake rayuwarsu Mommy ta shafesa ya kasa cire tunaninta a ransa ,yana mota ma yanzun tunanintan yake lokaci lokaci murnushi yana sumu'buce masa ba tare da ya sani ba ,driver dake yau shi zey kaishi asibitin yana saton kallonsa ta cikin glass "Toh fah yau meya faru da Alhaji da farar safiyarnan yana murmusawa?" Ya fad'a a ransa drivern.

     Yau Shettima jiki se hamdala tunda ya samu lafiyar har yayi wanka,Mommy ta taimaka masa ya shirya wani abun dariya wai da ita zata taimaka masa yayi wankan shiko ya'ki yarda.

    T-shirt shortsleeves ya sanya ash colour da blue jeans yayi fayau fuskarsa,kamar ya shekara  yana jinya.Breakfast yau d'in ma aka kawo kuma tana kyautata zaton ba daga asibitin bane sede doctor ne ya aiko.Tamkar wani d'an baby Mommy ta sashi a gaba tana basa.

    "Mommy ya isa fa haka na 'koshi". Yayi maganar yana kauda bakinsa daga spoon d'in.

    "Lomar 'karshe ko so kake sena maka d'ura?".

    Suna wannan dramar ne Dr Muhammad yayi knocking ,Mommy ce ta masa iso.

    Tare suka amsa sallamar da yai ,bayan sun gaisa da Mommy Shettima ma ya gaisheshi.

     Wani abu dayake sake burgehi da Mommy yanayin dressing d'inta koyaushe cikin abaya da wadataccen mayafinta.

    " Ya jikin naka?"Ya tambayi Shettima.

     "Alhamdulillah" Ya amsa.

     "Kana kuwa iya cin abinci?"

      Kafin ya amsa Mommy ta riga shi "Ya'ki ci gashinan".Tayi maganr tana komawa d'aya gadon.

     " Kana so kasa Mommynka wani kukan kenan?"Yana kallon Mommy yayi maganar.

    Sam bata zaci wannan maganar daga bakin dr ba a kunyace ta sunkui da kai Shettima yayi murmushi kawai yana kallon Mommyn a ransa yana fad'in Allah kad'ai yasan damuwa da tashin hankalin data shiga sanda suka kawo shi asibitin tunda har dr ma ya gano hakan.

    "Ka taimaka kaci kasha magani yaron Mommynsa". Ya 'kare maganar yana murmusawa.

    Da alama wannan dr akwai bar'kwanci.Shettima ya fad'a a ransa a fili ya amsa da toh.

    "Ka dena depressing kanka  duk abinda yafi 'karfin zuciyarmu barinsa ya kamata miyi mu danganawa Allah,miyi ro'kon samun sassauci .....don't be hopeless in your life .....always put this in your mind"

     _Komai yana faruwa ne bisa wani dalili ,amma wani lokaci idan muna so muga dalilin ,ana bu'katar ka bada lokaci na musamaan da kulawa ta musamman domin ganin sirrin dake 'kunshe cikin al'amarin...."

     Ba Shettima kad'ai ba hatta Mommy maganar dr ta shigeta,jitai kamar yasan ma halin da suka shiga ita da d'an nata bacin ita babu wata magana data had'asu akan hakan.

    Hannunsa ya d'ora kan kafad'ar Shettima a hankali yake maganar Mommy ma ba sosai take ji ba.

    "You never fail until you stop trying"

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now