Chapter 53

615 46 0
                                    


     *Barkanmu da dawowa ,da fatan kowa yayi sallah lafiya Allah ubangiji ya maimaita mana (Ameen).*

       *_Ina fata ba'ai over load ba de ahan😂_*

     *_Deeja one love na jinjina miki👍 kuma ina miki murna na kammala littafinki "ASHE KECE" muna jiran a sake sibirbid'o mana wani sabon. Lot's of Love❤😘_*

       _______________________

  
     *Four months later*....

     
     Tana zaune kan kujera hannunta ri'ke da wayarta tana playing  temple run a hakan tana hira da Ummi kad'an-kad'an.

      Kwananta uku kenan da dawowa daga Gombe seda tayi kwana goma a can ta dawo badan taso ba seda Ummi tayi waya tasata ta dawo tukun ,chan d'in tafi jin dad'insa saboda akwai 'yan uwa sa'anninta nan kuwa 'kwale ita kad'ai.

    "Ummi dan Allah ki barni naje kazaure(gidan cousin sistern Ummi) koh kwana uku ne nayi"

    "Ba inda zaki sake zuwa kuma shikenan kinga ba igiyar aure a kanki seki ta gallafiri kije chan kije chan wlhy bazan yarda da haka ba".

    Cuno baki tayi ta cigaba da game d'inta ba tare da ta sake wata maganar ba ,ita yanzu ko zancen ta ta'ba aure bason yi take ba wata ran idan ta tuna rayuwar gidan Kamal har kuka take.

      Yanzu idan kaga Amrah zaka san tana cikin kwanciyar hankali farinta da kyawunta ya dawo babu wannan uwar ramar sosai hankalinta ya kwanta yanzu batada wata damuwa a ranta Abbanta ne ya sake saya mata wata sabuwar wayar  shiyasa tayi ta game d'inta duk asabar da lahadi kuma tana zuwa islamiyya da safe.

       
     ***

      Yana zaune a office d'insa  laptop ce a gabansa amma ya kasa gudanar da aikin daya kamata yayi sam hankalinsa baya gun maganganun abokinsa Ahmad suna dawo masa a ka.

      _Dama ce ta biyu daka samu idan kayi wasa da ita zaka rasa ta ne har abada"_Ahmad ya fad'a.

     "Mey zatai da wanda baida cikakkiyar lafiya? Duk ranar da ciwona ya tashi ...zuciyata tana iya bugawa at once na mutu,gwara ta auri wanda zasu dad'e tare". Cewar Shettima.

     " Saboda ranka a hannunka yake ? Inde haka ka za'ba shikenan Shettima but ka sani ka bari damarnan ta wuce ka you failed ka zama looser.Amma ka sake tunani it's your second and may be last chance..."_

      Nannauyar ajiyar zuciya ya saki ya d'auki wayarsa 4:13pm agogon ya nuna,ba wani abu dayawa yayi a laptop d'in ba ya rife.Nan da nan ya tattara ya fice daga office d'in ,parking lot ya nufa inda motarshi take ya shiga ya tafi.

     A watanni hud'unnan  gidan Mommy an samu sauyi sosai ,Shettima bayan an sallemesa daga asibiti ba'a jima ba akai rabon gado kamar yadda shari'a ta tanadar su Sa'adatu da farko wani yayan Aunty Hannatu ne ya kar'ba zey dinga juya musu sede ya kasa ri'ke amana dan haka aka dawo da dukiyarsu hannun Kawu,an samu d'aya daga cikin 'yan uwan Hannatun tace zata d'auki Husna ko wata d'aya batai ba ta dawo da ita wajen Mommy koyaushe yarinyar cikin kuka ta rame bata iya cin abinci sam ta'ki sakewa dole aka ha'kura aka maidowa da Mommy dan yaran sunfi jin dad'in zama a gunta kuma itama tafi son hakan.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now