Chapter 51

631 54 0
                                    

     
        *Juma'at Mubarak*

    ~~~

     Ko kaiwa bakin 'kofar basi ba suka fara jiyo sautin muryar Kamal yana kiran "Amrah".

    A gaggauce Hafiz ya kira doctor, kwata-kwata basi tsammanin zey farka haka da wuri ba amma se gashi allurar ta sakeshi.Lokacin da doctor d'in ya shiga Kamal ba abinda yake se yun'kurin  kwancewa daga d'aurin belt d'in seda doctor d'in ya 'karaso ya lura dashi.Wani kallon tsana ya wurga masa da ace ba'a d'aure yake ba Allah kad'ai yasan abunda zey masa a wannan halin,wani irin wutar tsanar mutane yake ji a ransa idan aka cire Amrahnsa babu wanda yayi trusting gani yake kowa mugu ne.

    " Ka kwancemin wannan shirgin"

     Nurses biyu ne suka shigo tare da kayan aikinsu ,a tsorace doctor d'in ya shiga had'a allurar yana gamawa ya nufo wajen Kamal d'in a damtsensa ya d'ure ruwan allurar.

   "Sena kashe ka ....you will pay .....I will kill y..ou" Yake ta fad'a har bacci ya ci 'karfinsa abin tausayi Mamansa tana daga waje duk anbinda yake fad'a tana ji kuka ta shiga yi Hafiz yana rarràshinta.

    Har ruwa suka d'aura masa saboda rashin cin abinci ,ruwan zey taimaka masa.Bayan doctor d'in ya fito Mama tace ya barta ta shiga d'akin tana son ganin d'anta be'ki ba ya amince  suka shiga.

    Gwiwa ba 'kwari ta 'karasa bakin gadon tana kallon fuskarsa a 'kalla an d'auki 3years rabonsu dashi.D'an du'kawa tayi kad'an  tunda tana tsaye,hannunsa ta ri'ke cikin nata.

    "Kace yayi aure koh?" Tayiwa Hafiz tambayar.

    "Eh" Ya amsa mata.

     "Yana so yayi rayuwa kamar kowa ,mahifinku ya'ki bani goyon baya mu kula da Al-ameen(Kamal)"

   "Yace bayaso ya ganni na koma dashi,Hafiz bazan iya tafiya ba wlhy ina ganin halin da yarona yake ciki bazan iya ba bazan ta'ba komawa ba Al-ameen ba".

    "Ita matar tashi tana gidansu?"

      "Eh ta koma gidansu". Ya amsa.

      " Toh yayi ,ina so anjima ka kaini chan d'in".

      Bayan sun fito daga d'akin suka gana da doctor ya tambatar musu zasi iya 'ko'karinsu na ganin ya samu sau'ki .Dande ba yadda zatai ne da bazata barshi a duba lafiyarsa ba a Kano sede ko Abujan amma yanzu ga uban warning da mijinta ya gindaya mata dole ta zauna anan d'in.

     Seda ya fara kaita gidansa na nan d'in inda zata yada zango bayan ta d'anyi uzurirrika ,Hafiz ya siyo mata abinci ta d'an ci tukun suka d'auki hanyar gidansu Amrah.

       ★★★

       Walida sun shiga tsaka mey wuya ita da 'yar uwatta Wafah ,tun jiya sun kasa fad'awa Aunty Mirah maganar dake cinzu harta fara d'arfosu suna d'akinsu ta iskesu.

     "Yarannan akwai abinda kuke 'boyewa baku da gaskiya tun d'azu kun'ki fitowa daga d'aki"

    "Aunty mey kuma zamu 'boye?"Cewar Wafah.

     "Walida fad'a min mey kuke 'boyewa?"

      Shiru Walida tayi ta kalli Wafah ta kalli Aunty Mirah,ido Wafah tayi mata alamar karta fad'a itako ta ma'ke kafad'a.

    "Mommy ce ai zatai mana fad'a idan muka fad'a nasan kuma sekin fad'a mata".

    Zama tayi kan gadon " Ku fad'amin bazan sanar mata ba na iya ri'ke sirri"

   "Kinga dama... nida Walida ne saurayinta da nawa sukace wai zasije asibiti duba Yaya Shettima kuma Mommy bata san da maganarsu ba".

  " Iyye ..yara an girma".

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now