Chapter 12

782 56 0
                                    

      Alhamdulillah I'm plus one today is my birthday, Alhamdulillah.

   ~~~

    Cikin nuna damuwa guy d'in yayi saurin zaro handkerchief "Afuwan d'an uwa ban lura ba"

    Shettima ya rasa ma mey zeyi yabi kayan nasa da kallo da leman yayi musu jurwaye."Ba komai nima ban lura bane karka damu"Shettima ya 'kalo murmushi dan yasan seya koma gida sauya kaya.

     Guy d'in yana kallo Shettima ya fita daga wajen kawai yabishi da kallo sannan ya juya ya shiga hall d'in.

      Amrah da bata hango ma faruwar abin ba sede taji shiru be dawo ba tana zaune lacassera dake kan table ta d'auka tayi sipping d'aya biyu ta ajje.

      "Assalamu Alaykum" Tajiyo sallama a kanta kamar daga sama.

     A hanakali ta juya ta d'ora ido a kan wanna guy d'in da sukai gware da Shettima"Wa'alaikassalam"Ta amsa sannan ta sauke idonta daga kansa.
     
     "Ranki ya dad'e an bani izini na zauna?" Ya daga kujerar dake opposite da ita.

    Shiru tayi masa batace komai ba sema sake tamke fuska datayi dan haka kawai taji beyi mata ba ita murmushinsa ma sake 'bata mata rai yai.

    Gani tayi ya zauna "Ga dukkan alamu hajiyar nada kunya ,kamalarki kad'ai ta isa a gano hakan miss no name ina barar sunanki?"

    "Aiko bazaka ji ba" Ta fad'a a ranta.

     "Ni sunana Barrister Kamal Idris Al'kali"

      "Kinji sunan mey tsaho ko?"Yayi murmushin gefen fuska.

      Har lokacin Amrah bata takanshi ba ita shawara ma ta soma kota tashi amma kuma tana gudun karta mi'ke su 'yan gidansu su ganta ko Shettima dan batasan ya zatayi ba idan hakan ta faru.

     " Ranki ya dad'e ina jira kice wani abu, zanzo ace naji sunanki dan nasan yadda kike kyakkyawa haka sunanki yake"

    Jin ta'ki fad'ar sunan seya tambayi number ta "Zan iya samu number ki ? Ko kuma sena siya?"

     "Numberta bazaka iya siya ba kuwa" Ta fad'a tana kallon gefe.

     "Number?" Ya tambaya cikeda mamaki daga baya kuma seya yi murmushi "Au hakane fa toh ina barar number ki"

     "Kayi ha'kuri amma bazan iya baka number ta ba".

      " Ko baki yarda dani bane?"

      "Ba haka bane kawai bazan iya baka bane".

       Kai ya jinjina yanayin fuskarsa ta sauya ,d'an cije lips yayi kafin yace" Nagode da wannan ma domin ssamun damar yin magana da mace kyakkyawa kamar ki ba abi ne mey sau'ki ba,amma bazan 'boye miki ba a gaskiya ina sonki ina fata zaki fahimce ni".

     "Yaya Amrah" Husna ta taho a guce wajen Amrah.

     Amrah sam bata ji dad'i ba shikenan yanzu yasan sunanta "mtcw!"

     "Bari na barki Amrah" Ya mi'ke yana murmushi.

    "Nice name" Ya fad'a a ransa.

     Tana kallo ya fice daga wajen ta juya tana magana da Husna da take ta bata labari,gefe guda kuma tana tunanin Shettima.

     Shettima seda ya koma gida ya sauyo kaya sannan ya dawo.Sanda ya shigo wajen be sameta a table daya barta ba chan ya hango a cikinsu Wafah shiyasa be 'karasa ba amma every move nata akan idonsa.

      Tun sanda ya shigo hall d'in Amrah ta lura dashi amma tayi kamar batasan yana kallo ta ba a ranta tana tambayar"Meyasa ya sauya kaya".Ganinsa data  cikin 'kananan kaya red shirt da ba'kin jeans.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now