Chapter 56

668 50 2
                                    

     Amrah a yanzu ne tasan zatai auren gaske tasan zatai aure babu 'kuncin zuciya ba kamar wancen lokacin ba da ko walwalar kirki bata yi.

      Lokaci kamar zu'koshi ake yi,dama wuyarta ba'a sa lokaci bane inda rai da lafiya za'a gani.Kowa ya kacame da shirye-shirye abinda ba'ai tsammani ba wai Mommy zata aurar da duka 'ya'yanta kowa wannan ranar yake jira tazo dangi da abokanan arzi'ki.

    Shettima duk yadda ya kai ga nacin ya sata a ido ta'ki bari su had'u,haka zey biyo gidansu ta wajen aiki seya kirata tace ta fita nan kuwa tana gida ,duk wani kud'i da zata bu'kata iya kaci ya tura mata ta acct dan bazata yarda ta fito ba.

     Mommy kanta ba itace Amaryar ba amma dr haka zeta tambayarta mey take bu'kata wani sa'in sede taga yayo mata aike dan ta'ki bashi acct number ta.Kasancewar aiki ya masa yawa acan yasa baze samu damar halartar bikin ba sede fa yaransa ba'a barsu a baya ba wajen shirin bikin.Mommy da kanta ta kwashe su zukaje siyayyar duk abinda zasu bu'kata a fitar biki,amare su Walida ma an shiga busy ga gyaran jiki ga sauran hidindimu.

        ★°★°★°★°★°★°

     Ana e gobe d'aurin aure ,dayake d'aurin aure za'a fara kafin events.

    Daga yau hutun sa ya fara amma ko jiya seda ya shiga office duk yabi ya gaji,gashi yau gidansu ba'ki daga maid uguri sun duro hayaniya ba'a magana Mommy kam tayi wuyar gani, kowa Mommy kowa Mommy.

     Su Walida an tafi 'kunshi ,su Sa'adatu kuma ana musu nasu a gida da sauran 'yan biki Mommy ma an mata nata tun jiya da dare.

    Amrah ma yanzun ake rangad'a mata wannan karon harda ba'ki ba kamar waccen lokacin ba da janma da 'kyar ta yarda, wannan ko hankali kwance har wani kula take da kyau karya jangwale.Su ma gidan nasu a cike yake 'yan Gombe sunzo ana ta gujuba-gujubar biki Allah yaso tun jiya an mata gyaran gashi 'kunshinne se yau.Tun kafin ya gama bushewa yayi rad'au a fatarta data sha gyara se glowing take banda 'kamshi daya gama ma'kale jikinta          (Amarya Amrah fa ta fitoh my ppl).

    Wayarta ce tayi 'kara tana daga gefenta amma ba damar d'agawa saboda hannayenta duk sunsha 'kunshi,d'an le'kawa tayi taga angonta ne ,tun jiya da yamma rabonta dasi waya  har yanzu yammar ta sake zagayowa ,text kad'ai sukaiwa juna dan daren jiya bata samu yin charge ba se d'azu da rana.

    Mey 'kunshin ce ta samu ta d'aga tasa mata a kunne ,ita Amrah bata ma bu'kaci hakan ba kawai ita ce ta kula da yanda Amrah ke satar kallon wayar.

    Ma'kale wayar tayi a kunne mey 'kunshin ta cigaba dayi mata daman 'kafa d'aya ya rage.Cikin siririyar murya tayi sallama ,bayan ya amsa yace.

    "Wai anya kua Amaryarnan ta damu da angonta?"Yayi maganar cikin kwantar da murya da kalar tausayi wanda yasa Amrah ta wani lumshe ido batasan tayi ba se mey 'kunshi ce ta kula (Uhmnm su Amrah 🔥😂).

    " uh uhm bafa haka bane,wayata ce ba charge tun jiya se d'azu yanzu kuma  ana min 'kunshi "Tayi maganar a shagwa'be kamar zatai kuka😱

    Shettima daga 'bangarensa seda wuta ta d'auke masa ta seconds,be sake wani complain ba ya chanja topic.

   "My Amrah ya za'ai naga 'kunshinnan?"

    Kallon yatsunta tayi tana d'an motsatsu cikeda burgewa kafin tace"Na siya ne ai".

      "Ohh sekin goranta min ban biya sadaki ba koh? Hmm kwana nawa ne ? Gobe ne fah".

     Murmushin fuskarta ne ya sake fad'ad'a har ha'koranta na bayyana.

    "Toh ko goben ma ai ba ganina zakai ba".

     " Allah koh? Hmmm lalle kuwa da ba'a kwana lpy ba".

TAGAYYARA(Complete)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora