Chapter 32

540 50 1
                                    

       Juma'at Kareem

    Sanda ya sake dawowa d'akin ya tarar tayi bacci ,takawa yayi har bakin gadon yana 'karewa fuskarta kallo ,haurawa yayi kan gadon shima ya kwanta tare da jawota jikinsa ya d'ora kanta a 'kirjinsa ,kan goshinta ya manna mata kiss ya lumshe ido kafin shima baccin ya d'aukeshi.

    ***

      Wajajen 8:30am ya sakko 'kasa gidan shiru su Walida duk suna makaranta dasu Sa'adatu.Kitchen ya nufa domin sakawa cikinsa wani abun Aunty Hannatu ya tarar a ciki yayi kamar be ganta ba ya bud'e fridge yaji tayi magana."Gafa potato ball Mommy tayi sabida kai d'an gatan Mommy"

    Waiwayowa yai kallo d'aya yayi mata yace "Ta fad'a min".

    Lokaci guda earring d'inta ya tsaya masa u kallo d'aya yayi mata hakan be hana ya lura da earing d'in ba kasancewarsa mey d'an girma.Abinda ya tsinta jiya a 'kasan gado ne ya sake fad'o masa rai tabbas yayi kama da earing d'in ,take ya sake juyowa ya dubeta itada tun maganar daya fad'a ta tsiresa da ido tana kyassasa irin tarkon da zata d'ana masa.

    Direct dubansa yakai kan earing d'in seya lura na kunnen hagun tsahonsa yafi na dama ,na daman kamar yayi lacking wani sashen a jikinsa,tabbas blue stones ne yake d'auke dashi.Ba tare da yace komai ba ya fita abinda yazo d'aukan ma be d'auka ba ya wuce sama.Kan drawer ya nufa ya d'auko sosai yake dubawa kamanceceniya ta fito ba shakka daga jikin d'an kunnen ya fito.Amma meya kawota d'akinsa? Yaushe ta shigo be sani ba?

   Tunani barkatai ya shiga yi tun yana tsaye ya zauna zuciyarsa tana so ta nusar dashi ,amma kuma baya son zargi akan abinda ba tabbas ba.Tabbas yasan baida wata ala'ka da poison da aka gani d'akinsa amma waya kawo masa d'aki? Inde ba shigowa d'akinsa tayi ba ba abinda zey kawo abin d'ankunnenta d'akinsa.

   Kansa ya dafe dayaji ya sara masa ko tuna wannan ranar baya son yi ,bayason tuna halin daya tsinci mahaifinsa amma ya kamata ya zama abin duba yana bu'katar yasan wani abu gameda mutuwar Appa."Kamal"

   Videon da aka haska a court ya shiga tunanowa kansa ya sake d'aurewa tuna amsar da Mommy ta bashi lokacin da ya tambayeta wanda ya samo lawyer daya kareshi.

    "Aunty Hannatu" Amsar data bashi kenan.

     Dole wannan lamarin akwai abin dubawa a ciki yana so yasan yadda akai har Aunty Hannatu ta iya samo lawyer har ta biya shi kud'in ba tare da ta tambayi su Kawu ba matar da baya ganin alamar wani damuwa da rayuwarsa a tartare da ita wanda har yanzu Mommy ta'ki gano hakan duk yadda yayi 'ko'karin fahimtar da ita amma bata ta'ba sauraransa balle ta yarda.

          _________________

   
    A hankali ta soma bud'e idanunta kafin ta fuskanci a jikinsa take,da hanzari ta janye jikinta cikeda takaici take kallonsa wata uwar harara ta watsa masa kamar yana kallonta."Mutum ba abinda yake se 'kauri sunan an fesa turare". Tayi tsaki har fili.

   Sauka tayi daga kan gadon ba tare da ta sake waiwayarsa ba ta gyara guntun mayafin data d'aura a kanta ta fita daga d'akin a slow take takawa ,a parlour ta zauna kan sofa banda ciwon jiki ba abinda take ji.Tun tana had'iye kukan dayake tokare a ma'kogoronta har ta sake sa cikin siririn sauti.Ba abinda ya rage se 'karin ciwo da ciwon kai ,tashi tayi ta koma d'akin toilet ta fad'a ta sake had'a wani ruwan mey zafi ta shiga ,ta d'au tsahon mintina sosai kafin ta fito kayan data shigo dasu toilet d'in ta saka.Doguwar rigace simple milk colour mey dogon hannu ta d'aura brown mayafi ta fito ba laifi taji dama-dama ,be jima da farkawa ba yaga fitowarta ko kallon inda yake batai ba dukda tana jin idanunsa  a kanta.

    Tana gama abinda zatai  ta fita daga d'akin ta koma parlour ta zauna kan sofa ta lafe jiki tana lumshe idanunta.

     "Amrah" Taji ya kira sunanta a tausashe ,yana zaune hannun sofa  yana murza hannunta data d'ora a cinya.Shiru tayi ta'ki amsawa kamar bataji ba.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now