Chapter 28

526 46 0
                                    


    Ya karanta yafi sau a 'kirga tamkar mey hadda,ji yake kamar yayi print out d'in sa'kon dan jiyake kamar ba zahiri ba yana ji kamar ya samu wanda zey fassara masa sa'kon yadda zey fi fahimta.

     "PLEASE FORGET ME" Yafi komai tsaya masa a rai.

      Tsam ya ajje wayar gefe ,kwakwalwarsa ta jagule lissafinsa ya rikice,tunanin ranar da Amrah suka zo da Barr Kamal ya shigayi tabbas ya tamabayeta amma ta gagara bashi amsa.

    "Ya Allah". Ya furta yana dafe kansa da hannu biyu yana brushing gashinsa da yatsunsa kamar zey  tsige  gashin.

    A ransa yayi tunanin ko dama lokacin da suka zo tare already anyi auren? Oh no.Meyasa ta za'bi wani akansa? Meyasa bata fad'a masa soyayyarsu ba d'orarriya bace? Amrah meyasa? Meyasa?

    Ya 'kare maganar a fili ,jiyai zaman gadon ya gagareshi besan lokacin da ya zame ya zauna 'kasa ba bugun zuciyarsa yana skipping. Hannu ya d'ora a 'kirji yana saisaita numfashinsa baze iya kwatanta tashin hankalin dayake ciki ba.Baya iya jin zeyi bacci kamar yadda yaso ya rama baccin da be samu a baya ba.

   _________________________

     Tana rawar jiki ta zuba number Ummi datake a kanta taji dad'i ganin da credit a layin, bugu na biyu ta amsa.

   " Ummi "Ta kira sunanta tana jin qwalla na cika idonta.

    " Ummi Amrah ce fa". Ta sake fad'a data tuna batasan layin nata na yanzu ba.

    "Amrah kece,dad'i gidan miji yau aka tuna dani"

    "Laaa wlhy a'a Ummi uhh..na chanja layi ne fa"

    "Shine se yanzu"

  "Wayar tawa ta fad'i 'kasa ne ta fashe shine ta lalace seyanzu na sake wata".

    " Toh Allah ya kyauta,shi Kamal d'in ai ya kira mu sau biyu ma muna waya".

    Wannan anyi munafikin mutum a rayuwarnan.Ta fad'a a ranta.

    "Uhm ya Abba?" Ta chanja maganar".

     "Yana lafiya".

     " Bayan mun gama wayar shima zan kirashi".

    "Toh yayi".

    " Ummi ya Mami ?"Ta tambaya murya a sanyaye.

    "Tana lafiya itama".

     " Ki turon da number ta na kirata Allah yasa ta bari mu gaisa nasan har yanzu tana fishi dani".

    "Zan turo miki ,nima idan muka gaisa bata bari miyi wata maganar mike sallama har yanzu bata bar fishin ba Mommy ma ta mata magana amma ta'ki saurara.

   Amrah jin an ambaci Mommy yasa tace " Yasu Mommyn?"

   "Duk lafiya suke,Shettiman ma fa ya dawo gida an sakeshi yau d'innan".

   D'an dumm tayi na lokaci kafin ta daure tace"Alhamdulillah an gode Allah ,Allah ya kiyaye gaba"

  "Ameen,gobe nakeso naje gidan ma nayi musu barka".

   " ok, toh ki gaishesu".

    "Zasuji,kar ki 'karar da katin kuma keda zaki kira Abbanki".

   " Huhmm Ummi ban gaji da jin muryarki bane".

   "Uhmm haka de aka ce ".

   Hakan da Ummi ta fad'a ya bata dariya.Bayan sunyi sallama da Ummi ta kirawo Abba shima suka gaisa kamar karta katse kiran ,bata jima da ajje wayar ba Ummi ta turo da number Mamin.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now